Ayar Izinin Jihadi
| bayanan aya | |
|---|---|
| sunan aya | Izinin Jihadi |
| akwai shi cikin sura | Suratul Hajji |
| lambar aya | 39 |
| sha’anin sauka | Mahajirun, Ahlil-Baiti |
| bayanan abin da yake ciki | |
| wurin sauka | Madina |
| maudu’i | Fiƙihu |
| game da | Izinin yaƙi da Mushrikai |
| ayoyi masu alaqa | Ayar Saifi |
Ayar izinin jihadi, (Larabci: آية إذن الجهاد) suratul hajji aya ta 39, ita ce aya ta farko da ta baiwa musulmi izinin jihadi kan mushrikai. Wannan aya ana lissafa ta cikin ayoyi muhkamat a cikin kur'ani, kuma aya ce da ta goge bin mushrikai ta lallami. Wannan aya bayan ta sauka ne bayan hijira zuwa Madina sakamakon cutarwa da mushrikan Makka suke yi kan musulmi; gabanin saukar wannan aya Annabi (S.A.W) ya kasance yana rarrashin musulmi da su yi haƙuri da cutarwar da suke fuskanta daga mushrikai.
Malaman tafsiri na Shi'a da Ahlus-Sunna tare da jingina da wannan aya, sun yi bayanin sharuɗɗa wajabcin jihadi, daga jumlarsu akwai batun cewa wannan aya ta sauka ne game da jihadi difa'i (Jihadin kare kai) nau'in wannan jihadi ba ya buƙatar izinin Imami. Ba'arin malamai sun tafi kan cewa wannan aya ta na nuni zuwa ga iyakokin jihadi da kuma watsi da tuhumar Muslunci da cewa addini ne mai son kausasawa, saboda shi yaƙi kaɗai yana kasancewa halastacce bayan zalunci da kuma korar musulmi.
Cikin riwayoyin Shi'a, an yi aiki da wannan aya kan Ahlul-baiti (A.S) da Imam Mahadi (A.F), Har ila yau, sahabbai da tabi'ai su ma sun yi amfani da wannan aya domin samun halasci kan matakai da suka ɗauka, haka kuma sun kafa hujja da ita, kamar dai misalin Usman a lokacin da aka kewaye gidansa, Imam Ali (A.S) a lokacin yaƙin siffin ko Jamal da Ibrahim Imam a lokacin miƙewar Abu Muslim Khurasani.
Bayar Da Izinin Yaƙar Mushrikai
Ana kiran aya ta 39 suratul hajji da sunan ayar jihadi.[1] Haka nan wannan aya ta samu shahara da sunan ayar yaƙi[2] ko ayar izinin yaƙi[3] A cikin wannan aya an baiwa musulmi da mushrikai suka zalunta izinin jihadi da su. Kuma ana lissafa wannan aya cikin jerin ayoyin kur'ani muhkamat.[4] Aya ce ta farko da aka halastawa musulmi jihadi tare da mushrikai domin kare kawukansu da kuma kare da'awar Annabi (S.A.W).[5]
Ayar izinin jihadi aya ce da ta goge ayoyi misalin aya ta 48 suratul ahzab wace ta kasance tana ƙarfafa lalami da bi a sannu-sannu tare da mushrikai.[6] An ce a cikin kur'ani akwai ayoyi fiye 70 da suka sauka wurin Annabi (S.A.W) game da bi sannu-sannu da lalami tare da Mushrikai.[7] Har ila yau, wannan aya ta goge aya 14 suratul jasiya.[8]
أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَاتَلُونَ بِأَنَّهُمْ ظُلِمُوا وَإِنَّ اللَّهَ عَلَى نَصْرِهِمْ لَقَدِيرٌ
An ba da izini ga waɗanda ake yaƙi da su, saboda an zalunce su. Kuma lallai Allah Mai iko ne a kan taimakon su
(Quran: Hajji: Aya ta 39)
Malaman tafsiri suna ganin gaɓar «أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَاتَلُونَ» a cikin ayar jihadi, a matsayin dalili da yake nuna cewa Annabi (S.A.W)[9] da musulmi sun kasance gabanin saukar wannan aya an hana su jihadi da mushrikai.[10] Amma tare da saukar wannan aya sai suka samu izinin yin jihadi kan mushrikai.[11] Har ila yau, an ce jihadi tare da hijira sun kasance sababin nasarar Muslunci.[12]
Sha'anin Sauka
Dangane da sababin saukar ayar izinin jihadi, malamai sun ce mushrikan Makka sun kasance suna takurawa sahabban Annabi (S.A.W) da wannan dalili suka kai kukansu wurin Annabi (S.A.W) cikin rarrashi da kuma umartar sahabbansa da bi a sannu, ya kasance yana gaya musu ni har zuwa yanzu ba umarce ni da jihadi ba, bayan yin hijira zuwa Madina sai wannan aya ta sauka.[13] Bisa dogara da wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) wannan aya ta na magana ne da waɗanda suka yi hijira da ƙuraishawa suka kore su daga garin Makka.[14]
Ayar izinin jihadi ta sauka wata bakwai bayan hijira zuwa Madina.[15] Wannan aya da take a suratul hajji, ta na jerin surori madaniyya. Ba'arin malaman tafsiri suna da ra'ayin cewa kaɗai wasu ba'arin ayoyi ne daga wannan sura aka saukar da su a Makka.[16] Kishiyar wannan magana, wasu adadin malamai sun tafi kan cewa suratul hajji sura ce da aka saukar da ita a Makka, kaɗai ayoyi biyar ne aka saukar da su a Madina.[17]
Ayyana Sharuɗɗan Jihadi A Cikin Wannan Aya
Wasu adadi daga malaman fiƙihu na Shi'a da Ahlus-Sunna tare da dogara da ayar izinin jihadi sun yi bayanin sharuɗɗan wajabcin jihadi; daga jumlar wannan malamai akwai Husaini Ali Muntazari ɗaya daga cikin maraji'an taƙlidi na Shi'a, bisa wannan aya, yana ganin cewa jihadi difa'i baya buƙatar izinin Imam.[18] Saraksi daga malaman fiƙihu na Ahlus-Sunna shi ma bisa wannan aya, yana da ra'ayin cewa kaɗai musulmai suna da izinin yaƙi da mushrikai idan mushrikan suka fara kai hari a kansu,[19] Na'am Shafi'i malamin fiƙihu na Ahlus-Sunna ya tafi kan cewa cikin wannan aya Allah ya baiwa musulmi izinin jihadi ibtida'i kan mushrikai.[20]
Hassan Jawahiri ɗaya daga cikin malaman fiƙihu a hauza ilmiyya Najaf, yana ganin ayar izinin jihadi ba ta taƙaita da muƙamin bayanin halascin jihadi ba kaɗai, aya ce da take bayanin iyakoki da sharuɗɗan jihadi.[21] Ba'arin malaman Shi'a suna ganin sharaɗin izinin yaƙi a wannan aya ya dogara da sharuɗɗa guda biyu: na farko: ya zamana an zalunci mutane, na biyu bisa lura da «الَّذِينَ أُخْرِجُوا مِنْ دِيَارِهِمْ بِغَيْرِ حَقٍّ...» (Waɗanda aka kore su bisa zalunci daga garuruwansu) da take cikin ayar.[22]
A cewar Jawahiri, ba'ari tare da jingina da wannan aya, sun bayyana Muslunci matsayin addinin kaifin Takobi; a daidai lokacin da ya kamata a ba da amsa ga wannan da'awa da cewa shi Muslunci kafin ya fitar da umarnin yaƙi, ya fara da amfani da hanyar hujja da kyakkyawan jidali cikin magana da mutanen da yake magana da su, kuma ya yi baƙin ƙoƙarinsa na kaucewa yaƙi, amma lokacin da aka zalunci mabiyansa sai ya ba da izinin yaƙi domin kare kai.[23]
Aiki Da Wannan Aya Kan Ahlul-baiti
Kan asasin wata riwaya daga Imam Kazim (A.S), an bayyana cewa ayar izinin jihadi ta sauka ne game da iyalan Muhammad (S.A.W).[24] Zaidu Bin Ali shi ma yana ganin wannan aya ta sauka game da Ahlul-baiti (A.S).[25] Har ila yau, bisa riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) gaɓar «أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَاتَلُونَ» cikin wannanta kasance game da Imam Ali (A.S), Jafar Bin Abi Ɗalib da Hamza Bin Abdul-Muɗɗalib.[26] A wata riwayar daban ya zo cewa wanda ayar take magana da su, su ne Sayyidina Ali (A.S), Imam Hassan (A.S) da Imam Husaini (A.S).[27]
Ba'arin malaman Shi'a tare da jingina da wata riwaya, sun bayyana cewa mutanen da aka ambata su ne waɗanda aka baiwa izinin jihadi.[28] Haka nan abin nufi da waɗanda aka zalunta a cikin ayar, su ne Imam Zaman (A.F) da sahabbansa.[29] Haka nan an naƙalto daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa musulmin da ba ƴanshi'a ba suna raya cewa wannan aya ta sauka ne a daidai lokacin da Annabi (S.A.W) yake hijira daga Makka zuwa Madina, sai dai kuma a tawilin ayar tana magana ne da Imam Zaman (A.F) a lokacin da zai fito neman fansar jinin Imam Husaini (A.S).[30]
Har ila yau, an jingina da wannan aya kan tabbatar da raja'ar Ahlul-baiti (A.S), kan wannan asasi ne aka ce, ita raja'a tana cikin mafi girman alamomi bayyanannu a cikin shi'anci,[31] kuma bisa dogara da wata riwaya ita raja'a alƙawari ne na Allah ga Ahlul-baiti (A.S), saboda haka wajibi ne Ahlul-baiti (A.S) su yi raja'a domin Allah ya taimaka musu.[32]
Kafa Hujja Da Wannan Aya Cikin Abubuwan Da Suka Faru A Tarihi
Daidai da abin da ya zo a wasu rahotanni na tarihi, wasu adadi daga sahabbai da tabi'ai a ƙoƙarinsu na tabbatar da gaskiyarsu da manufofinsu sun jingina da ayar izinin jihadi; daga jumla an ce a lokacin da aka kewaye gidan Usman a kwanakin ƙarshen halifancinSa, an zaɓi Sa'asa'a Bin Suhan domin ya je ya tattauna da Usman, lokacin da Sa'asa'a ya samu ganawa da Usman ya karanta ayar izinin jihadi, cikin raddin da Usman ya yi wa Sa'asa'a, ya gaya masa cewa wannan aya ba ta sauka ba kanka da sahabbanka, ta sauka ne kaina da sahabbaina;[33] a lokacin da aka kore mu daga garin Makka.[34]
A wani rahoto daban ya zo cewa a lokacin yaƙin siffin[35] ko Jamal, Sayyidina Ali (A.S), domin kutsawa gumurzun gaba da gaba domin kada a gane shi ya sanya kayan Abbas Bin Rabi'a ya kutsa fagen yaƙi, tare da karanta ayar «أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَاتَلُونَ...» ya gwabza yaƙi da mutanen da suke neman gwabza yaƙi da shi.[36]
Har ila yau, an ce Ibrahim Imam (Daga cikin jikokin Abdullahi Bin Abbas kuma ɗan uwa ga Saffahu Da Mansur daga halifofin Abbasiyawa) lokacin da suka zaɓi Abu Muslim Khurasani domin miƙewa, sun ɗaura masa wata tuta wace cikin aka rubutu ayar «أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَاتَلُونَ...» (An yi izini ga waɗanda ake yaƙa…).[37] Na'am a wasu madogaran an ba da rahoto cewa Ibrahim bayan ɗaura tuta ya kasance yana karanta ayar izinin jihadi.[38]
Bayanin kula
- ↑ Ayat Namedar na Khurasani, a shafi na 368
- ↑ Najafi – Jauharul Kalam, Jild 21, Shafi 57 (1362 Hijira Qamariyya). Sabzuwari – Muhadh-dhabul Ahkam, Jild 15, Shafi 119 (1416 Hijira Qamariyya)
- ↑ Tafsirul al-Mizaan na Allama Tabataba’i – Jild 14, Shafi 384 (1412 Hijira Qamariyya
- ↑ Ibn Jauzi – "Nawasikhul Qur’an", Shafi na 225
- ↑ San'ani – al-Musannaf, Jild 5, Shafi 397. Shaykh Tusi – al-Tibyan, Jild 7, Shafi 321. Hakim Nishaburi – al-Mustadrak, Jild 2, Shafi 246. Sayyid Sabiq – Fiqh al-Sunnah, Jild 2, Shafi 620. Hasani – Tariikh al-Fiqh al-Ja’fari, Shafi 56.
- ↑ Najafi – Jauharul Kalam, Jild 21, Shafi 57 (1362 H.S). Sabzuwari – Muhadh-dhabul Ahkam, Jild 15, Shafi 119 (1416 H.Q). Qurtubi – al-Jami’ li Ahkam al-Qur’an, Jild 12, Shafi 68 (1405 H.Q).
- ↑ Shafi’i Baydawi – Anwar al-Tanzil (Tafsirin Baydawi), Jild 4, Shafi 73 (1418 Hijira Qamariyya)
- ↑ Sheikh Tusi – al-Tibyan (Jild 9, Shafi 252). Ibn Jauzi – Nawasikhul Qur'an (Shafi 225)
- ↑ Sheikh Tusi – Tafsir al-Tibyan, Jild 1, Shafi 407 (1409 H.Q)
- ↑ Abdulrahman bin Nasir al-Sa’di – Taysir al-Karim al-Rahman (1418 Hijira Qamariyya), Shafi 539
- ↑ Ibn Jauzi – Nawasikhul Qur’an, Shafi 225
- ↑ Fassarar Hausa ta al-'Ayni – Umdatul Qari
- ↑ Wahidi Nishaburi – Asbab al-Nuzul, Shafi 208 (1388 H.Q). Ahmad ibn Hanbal – Musnad Ahmad, Jild 1, Shafi 216. Imam Tirmidhi – Sunan at-Tirmidhi, Jild 5, Shafi 7 (1403 H.Q)
- ↑ Allama al-Majlisi – Bihar al-Anwar, Jild 19, Shafi 183 (1403 Hijira Qamariyya)
- ↑ Ibn Shahrasub – Manaqib Aal Abi Talib, Jild 1, Shafi 161 (1376 H.Q)
- ↑ al-Sam’ani – Tafsīr al-Sam‘ānī, Jild 3, Shafi 416 (1418 Hijira Qamariyya)
- ↑ al-Firuzabadi – Tanwīr al-Miqbās min Tafsīr Ibn ʿAbbās, Shafi 276
- ↑ Ayatollah Hussain Ali Montazeri – Dirasāt fī Wilāyat al-Faqīh, Jild 1, Shafi 121 (1408 H.Q)
- ↑ Sarkasi – Al-Mabsūṭ, Juz’i na 10, Shafi na 2 (1406 H.Q)
- ↑ Imam Shāfi’ī – Al-Umm, Shafi na 169 (1403 H.Q)
- ↑ Jawahiri – Buḥūth fī al-Fiqh al-Muʿāṣir, Jild 6, Shafi na 232 (1429 H.Q)
- ↑ Fyaz Kashani – Al-Wafi, Jild 15, Shafi 70 (1411 H.Q). Majlisi – Rawdat al-Muttaqīn, Jild 3, Shafi 164
- ↑ Jawāhirī – Buḥūth fī al-Fiqh al-Muʿāṣir, Jild 6, Shafi na 239 (1429 H.Q)
- ↑ Qummi – Tafsīr Kanz al-Daqā’iq, Jild 9, Shafi 102 (1411 H.Q)
- ↑ Shawāhid al-Tanzīl, Jild 1, Shafi na 520 (1411 H.Q)
- ↑ Ali ibn Ibrahim al-Qummi – Tafsīr al-Qummi, Jild 2, Shafi na 84 (1387 H.Q)
- ↑ Ibn Qulawayh – Kāmil al-Ziyārāt, Shafi na 135 (1417 H.Q)
- ↑ Naʿmānī – Al-Ghayba, Shafi na 248 (1422 H.Q). Nūrī – Khātimat al-Mustadrak, Jild 1, Shafi na 125 (1415 H.Q)
- ↑ Alī al-Kūrānī – Muʿjam Aḥādīth al-Imām al-Mahdī, Jild 5, Shafi na 264 (1411 H.Q)
- ↑ Ali ibn Ibrahim al-Qummi – Tafsīr al-Qummi, Jild 2, Shafi na 84 (1387 H.Q)
- ↑ Ayatollah Muhammad Reza Golpāyegānī – Irshād al-Sāʾil, Shafi na 203 (1403 H.Q)
- ↑ Aḥmad al-Qaṭīfī – Rasā'il Āle Ṭawq, Jild 1, Shafi na 126 (1422 H.Q)
- ↑ Ibn Abī Shaybah – Al-Muṣannaf, Jild 8, Shafuka 585 & 681 (1409 H.Q)
- ↑ Kanzul-Ummāl na Alā’uddīn al-Muttaqī al-Hindī, 1409 Hijira – Juz’i na 2, shafuffuka 470 da 471. Tārīkh Madīnat Dimashq na Ibn ʿAsākir, 1415 Hijira – Juz’i na 24, shafi na 88
- ↑ Tafsīr al-ʿAyāshī, Juz’i na 2, Shafuka 79–82
- ↑ Ibn Shahrāshūb, Manāqib Āl Abī Ṭālib, Juz’i na 2, Shafi na 359
- ↑ Ibn Shahrāshūb (Juz’i na 3, Shafi na 86) da Nūrī (Juz’i na 3, Shafi na 328). Mustadrak al-Wasā’il – Juz’i na 3, Shafi na 328:
- ↑ A Tārīkh al-Ṭabarī – Jild 6, Shafi 25. A al-Kāmil fī al-Tārīkh – Jild 5, Shafi 358:
Nassoshi
- Ibn Abi Shaybah – Al-Muṣannaf Fil Ahadis Wal Asar, bincike Sa'id Lahham, Beirut, wallafar Darul Fikri, 1409ƙ.
- Ibn al-Athir – Al-Kamil fi al-Tarikh, Beirut, Wallafar Daru Sadra, 1386ƙ.
- Ibn al-Jawzi – Nawasikh al-ƙur’an, Beirut, Wallafar Darul Kutubil Ilmiyya, Babu kwanan wata.
- Ahmad ibn Ḥanbal – Musnad Ahmad, Beirut, Daru Sadra. babu kwanan wata.
- Ibn Shahrashub – Manaƙib al Abi Ṭalib, bincike kwamitin malaman Najaf Ashraf, Annajaful Ashraf, Haidariyya, 1376SH.
- Ibn 'Arabi – Aḥkam al-ƙur’an, Beirut, Wallafar Darul Fikri, babu kwanan wata.
- Ibn 'Asakir – Tarikh Madinat Dimashƙ, Bincike (ko Gyara) na Ali Shiri, Beirut, Dar al-Fikr.1415ƙ.
- Ibn ƙuluyah – Kamil al-Ziyarat,Bincike (ko Gyara) na Nashr al-Fiƙaha, Ƙum, al-Nashr al-Islami, 1417ƙ.
- Al-'Ayni – 'Umdat al-ƙari: Sharhi kan Ṣaḥiḥ al-Bukhari,Beirut, Wallafar Dar Ihya al-Turath al-Arabi, ba tare da kwanan wata ba
- Al-Bayhaƙi – Ma'rifat al-Sunan wa al-athar: "Bincike na Hassan Kasrawi, Beirut, Dar al-Kutub al-Ilmiyyah, ba tare da kwanan wata ba.
- Al-Tirmidhi – Sunan al-Tirmidhi: Beirut, Dar al-Fikr, bugu na biyu.1403ƙ.
- Ḥasan al-Jawahari – Buḥuth fi al-Fiƙh al-Mu'aṣir: Beirut, Wallafar Dar al-Zakha'ir. 1429ƙ.
- Al-Ḥakim al-Naysaburi – Al-Mustadrak 'ala al-Ṣaḥiḥayn: Bincike na Yusuf Abdurrahman, Beirut, Dar al-Ma'rifah, ba tare da kwanan wata ba.
- Al-Ḥaskani – Shawahid al-Tanzil: "Bincike na Mohammad Baƙir Mahmoudi, Tehran, Gidauniyar al-Tab' wa al-Nashr al-da take ƙarƙshin Ma'aikatar Shiryarwa.
- Hasani, Hashim Ma'ruf. Tarikhul-Fiƙh al-Ja'fari, Bincike na Muhammad Jawad Mughniyyah, ba tare da wurin bugawa ba, Dar al-Nashr lil-Jami'iyyin, ba tare da kwanan wata ba.
- Khorasani, Ali, ayat-e Namdar,Da'irat al-Ma'arif Al-ƙur'an al-Karim: Sunan littafin (Ensaiklopediya ta Alkur'ani mai girma) 1382SH.
- Muhadhdhab al-Aḥkam fi Bayan al-Ḥalal wa al-Ḥaram – Sabzawari, Abdul-Ali An wallafa shi ba tare da ambaton wuri ba, ta Maktab Ayatollah al-'Uzma al-Sayyid al-Sabzawari a shekarar 1416ƙ.
- Sarakhsi, Shams al-Di, Al-Mabsuṭ An wallafa shi a Beirut ta Dar al-Ma'rifah a shekarar 1406ƙ
- Yasir al-Karim al-Raḥman fi Kalam al-Mannan – Sa'adi, Abdulrahman bin Nasir An bincika littafin nan da Ibn 'Uthaymin, an wallafa shi a Beirut ta Gidauniyar al-Risalah a shekarar 1421ƙ.
- Tafsir al-Sam'ani – Sam'ani, Mansur An bincika littafin nan da Yasir bin Ibrahim da Ghunaym bin Abbas, an wallafa shi a Riyadh ta Dar al-Waṭan a shekarar 1418ƙ.
- Fiƙh al-Sunnah – Sayyid Sabiƙ An wallafa shi a Beirut ta Dar al-Kitab al-‘Arabi, bugun na uku, shekara ta 1397ƙ.
- Anwar al-Tanzil wa Asrar al-Ta'wil (Tafsir al-Bayḍawi) – 'Abdullah ibn Muḥammad al-Shafi'i al-Bayḍawi An wallafa shi a Beirut ta Dar al-Fikr a shekara ta 1418ƙ.
- Al-Umm – Muḥammad ibn Idris al-Shafi'i An wallafa shi a Beirut ta Dar al-Fikr a shekara ta 1403ƙ.
- Shaykh al-Ṭusi, Al-Tibyan fi Tafsir Al-ƙur'an Muḥammad An gyara shi ta Aḥmad Ḥabib ƙaṣir 'amili, an wallafa shi ba tare da ambaton wuri ba, ta Maktab al-I'lam al-Islami, shekara ta 1409ƙ.
- Shaykh al-Ṭusi, Tahdhib al-Aḥkam fi Sharḥ al-Muƙni'a , Muḥammad An gyara shi ta Ḥasan Musawi, an wallafa shi a Tehran ta Dar al-Kutub al-Islamiyya, bugun na huɗu, shekara ta 1365SH.
- Abd al-Razzaƙ al-Ṣan'ani, Al-Muṣannaf An gyara shi ta hannun Ḥabib al-Raḥman al-A'aẓami, an wallafa shi ba tare da ambaton wuri da shekara ba, ta hannun Al-Majlis al-'Ilmi.
- Muḥammad Ḥusayn al-Ṭabaṭaba'i, Al-Mizan fi Tafsir Al-ƙur'an An wallafa shi a Ƙum ta Gidauniyar al-Nashr al-Islami a shekara ta 1412ƙ.
- Muḥammad ibn Jarir al-Ṭabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk (Tarikh al-Ṭabari) An wallafa shi a Beirut a Gidauniyar al-A'lami lil-Maṭbu'at, babu kwanan wata.
- Muḥammad ibn Ya'ƙub al-Firuzabadi, Tanwir al-Miƙbas min Tafsir Ibn Abbas, An wallafa shi a Beirut ta Dar al-Kutub al-'Ilmiyyah, ba tare da ambaton shekara ba.
- Muḥammad Muḥsin Fayḍ Kashani, Al-Wafi An gyara shi ta hannun Ḍiya'uddin Ḥusayni, an wallafa shi a Isfahan ta Maktabat al-Imam Amir al-Mu'minin, shekara ta 1411ƙ.
- Muḥammad al-ƙurṭubi, Al-Jami' li-Aḥkam Al-ƙur'an, An gyara shi ta Aḥmad 'Abd al-'Alim, an wallafa shi a Beirut ta Dar Iḥya' al-Turath al-'Arabi, shekara ta 1405ƙ.
- Aḥmad ibn Shaykh al-ƙaṭifi, Rasa'il al Ṭawƙ An gyara shi ta Shirkah Dar al-Muṣṭafa, an wallafa shi a Dimashƙ ta Shirkah Dar al-Muṣṭafa li-Iḥya' al-Turath, bugu na huɗu, shekara ta 1422ƙ.
- Muḥammad ibn Muḥammad Riḍa al-ƙummi, Tafsir Kanz al-Daƙa'iƙ wa Baḥr al-Ghara'ib An gyara shi ta hannun Ḥusayn Dargahi, an wallafa shi a Tehran a gidauniyar al-Ṭab' wa al-Nashr na Ma'aikatar Al'adu, shekara ta 1411ƙ.
- Muḥammad ibn Ya'ƙub al-Kulayni, Uṣul al-Kafi , An yi taƙaitaccen sharhi ta 'Ali Akbar Ghafari, an wallafa shi ba tare da ambaton wuri ba, a Dar al-Kutub al-Islamiyyah, shekara ta 1367SH.
- Muḥammad Ḥasan al-Najafi, Jawahir al-Kalam fi Sharḥ Shara'i' al-Islam, An gyara shi ta Maḥmud ƙuchani, an wallafa shi a Tehran ta Dar al-Kutub al-Islamiyyah, bugun na biyu, shekarar 1366SH.
- Muḥammad ibn Abi Zaynab al-Nu'mani , Al-Ghaybah An gyara shi t Faris Ḥassun, an wallafa shi a Ƙum a Anwar al-Huda, shekara ta 1422ƙ.
- Ḥusayn al-Nuri, Khatimat al-Mustadrak An gyara shi a Cibiyar alul-Bait, an wallafa shi a Ƙum a gidauniyar alul-Bait, shekara ta 1415ƙ.
- Ḥusayn al-Nuri, Mustadrak al-Wasa'il wa Mustanbaṭ al-Masa'il An gyara shi a Cibiyar alul-Bait, an wallafa shi a Beirut a Cibiyar alul-Bait, bugun na biyu, shekara ta 1408ƙ.
- Ali ibn Aḥmad al-Waḥidi al-Nayshaburi, Asbab Nuzul al-ayat An wallafa shi a Cairo a Gidauniyaral-Ḥalabi wa Shuraka', shekara ta 1388ƙ.