Bagyu
Bagyu, (Larabci: البغي) tawaye ko bore kan kan halastaccen shugaba na Muslunci. Duk mutumin da aka samu da lefin aikata bagyu (Tawaye) ana kiransa da sunan Albagi (ɗantawaye). Bagyu yana da hukunce-hukunce da aka tattauna game da su a cikin litattafan fiƙihu. Bisa fatawar malaman fiƙihu, shugaba na Muslunci da farko ya kamata ya fara da yi musu nasiha da ƙoƙari cikin shiryar da su da dawo da su cikin ɗa'a, idan haka bai ba da fa'ida ba, sai ya yaƙe su.
Ba'arin malaman fiƙihun Muslunci sun fitar da hukunci kafirta ƴan tawaye, wasu kuma sun tafi kan kasancewarsu fasiƙai. Malaman fiƙihu na Shi'a sun yi la'akari da mutanen da suka yaƙi gwamnatin Imam Ali (A.S) matsayin misalai na Albagi (Ƴan tawaye); kamar misalin Khawarijawa da mutanen da suka yaƙe shi a lokacin yaƙoƙin Jamal da Siffin.
Cikin dokar hukunci ta Muslunci an tanadi hukuncin kisa da ɗaurin kurkuku da ladabtarwa kan mutanen da ake ɗaukarsu a matsayin Albagi (ɗantawaye).
Nazarin Ma'ana
Albagyu a isɗilahin fiƙihu yana da ma'ana tawaye da bore kan Imami adali da yake kan gaskiya kuma duk wanda ya yi bore da tawaye kansa ana kiransa da Albagi (Ɗan tawaye).[1] Cikin madogaran fiƙihu, mutanen da suka assasa yaƙar hukumar Imam Ali (A.S) kamar mutanen Jamal, Siffin, musammam ma Khawarijawa ana ɗaukarsu misali na bagyu da tawaye.[2]
Yaƙi Da Ƴantawaye Da Sharuɗɗansa
Bisa fatawar malaman fiƙihu na Shi'a, shugaban Muslunci wajibi da farko ya fara ƙoƙarin nasiha da dawo da ƴan tawaye cikin ɗa'a da raba su da tawaye.[3] Idan suka ƙi saurarensa to sai ya yaƙe su.[4] A cewar Kashiful Giɗa (Rayuwa: 1156-1228H), haƙiƙa kaɗai yana halasta a yaƙi ƴan tawaye a lokacin da babu wata hanya da ta rage da za a hana su tawaye banda a yaƙe su.[5]
Kan asasin abin da ya zo a litattafan fiƙihu, ba'ari daga sharuɗɗan yaƙar ƴan tawaye sune kamar haka:
- .Ahlul bagyi, sune mutanen da suka ware kansu daga shugaba adali da al'ummar Musulmi kuma suka yi masa bore da tawaye,[6] da yanayin da za a iya la'akari da su cikin ƴan fashi da makami da masu yaƙi da al'umma (Muharaba).[7]
- A ra'ayin Allama Hilli da Shahidus Sani, bagyu (Tawaye) kaɗai yana tabbatuwa ne idan ya kasance kan Imami Ma'asumi;[8] amma a ra'ayin Kashiful Giɗa tawaye da bore kan na'iban Imam Mahadi na musamman ko gama-garin na'ibansa shima ana lissafa shi matsayin bagyu.[9]
- Ahlul bagyu sune mutanen da suka fice daga ikon Imami ko shugaba suka koma rayuwa a wasu wurare kamar jeji da hamada.[10]
- Ƙarfinsu ya kai ga babu wata hanya da za a iya bi cikin hana su tawaye sai dai a yaƙe su kawai.[11]
- Adadinsu ya kasance mai yawa.[12] Na'am Shahidul Awwal bagyu yana iya tabbatuwa hatta cikin mutum guda.[13]
Wasu Hukunce-hukunce
Wani ba'ari daga hukunce-hukuncen fiƙihu kan bagyu sune:
- Ahlul bagyi dole su biya diyyar rayuka da suka halakar kuma su biya dukiyar da suka lalata.[14] Musulmi ba za su biya diyya rayukan ƴan tawaye ba haka ba za su biya dukiyarsu da ta lalace ba.[15]
- Shaik Ɗusi, ya halasta cin ganimar dukiyar ƴan tawaye a lokacin yaƙi da su;[16] Amma shi kuma Sayyid Murtada da Ibn Idris Hilli ba sa ganin halascin cin ganimar dukiyar ƴan tawaye.[17]
- Mata da ƴaƴan ahlul bagyi ba kama su matsayin fursunonin yaƙi.[18]
- Mu'amala da fursunonin Ahlul bagyi tana bambanta bisa la'akari da kasancewarsu ma'abota tsari na bai ɗaya da shugaba guda ɗaya (Zul Fi'ati) ko kuma akasi (Wanda ba Zul Fi'ati ba), cikin ƙaddarawa ta farko (Kamar mutanen Siffin), za a kashe fursunoninsu da aka kama, za ku a bi sawun waɗanda suka tsere a kamo su;[19] amma a bisa ƙaddarawa ta biyu (Kamar mutanen Jamal) ba za a kashe fursunoninsu ba ba kuma za a bi sawun waɗanda suka tsere ba a kamo su;[20]
- Wasu daga malaman fiƙihu, kamar Sahibul Jawahir sun ce Ahlul bagyi bisa zallan bore ba za a lissafa su cikin kafirai ba;[21] Amma a cewa Ɗusi, ba'arin malaman fiƙihu na Shi'a suna da ra'ayin cewa Ahlul bagyi kafirai ne.[22]
Ra'ayin Ahlus-Sunna
Ba'ari daga ra'ayoyin Ahlus-Sunna game da abin da suka fahimta daga bagyu da hukunce-hukuncensa sune kamar haka:
- A cewar Ibn Ƙudama (Rayuwa:541-620H),،[23] daga malaman fiƙihu na Ahlus-Sunna, mafi yawa daga malaman fiƙihu na Ahlus-Sunna suna ɗaukar Ahlul bagyi daga Khawarijawa wanda aka halasta jini da dukiyarsu.[24] Malamin ya yi imani cewa yaƙarsu ya halasta ne sakamakon kasancewarsu daga Mufsidu Fil Ardi (Masu ɓarna a doran ƙasa), bawai ana lissafa su ne cikin kafirai ba.[25]
- Ba'arin Hanafiya, sun bayyana bagyu matsayin fita daga ɗa'ar shugaba;[26] A fiƙihun Malikiyya da Shafi'iyya, ƙari kan tawaye kan shugaba, rashin ba da haƙƙi ga shugaba ma ana lissafa shi cikin bagyu;[27] Kamar dai yadda Ibn Arabi ya yi la'akari da yaƙar masu hana zakka a zamanin halifa na farko a matsayin yaƙi da Ahlul bagyi.[28]
- A mahangar malaman fiƙihu na Ahlus-Sunna, in banda hanafiya, sun tafi kan cewa abin nufi daga yaƙi tare da Ahlul bagyi shi ne tunkuɗe sharrinsu. Saboda haka fursunoni da gudaddunsu ba za a kashe su ba ko a bi bayansu a kamo su ba, dukiyarsu har zuwa lokacin da suke tawaye za a jiye t a hannun shugaba.[29]
Dokokin Hukunci Na Musulunci
Cikin dokokin hukunci na Muslunci (Dokar da aka rattabawa hannnu a shekarar 2012M), an tanadi hukunci game da bagyu da Ahlul bagyi kamar haka:
- Hukunci kisa: ƙungiyar da suka ɗauki makami domin yaƙar tsarin jamhuriyar Muslunci Na Iran, za a yi la'akari da su matsayin ƴan tawaye, idan kuma har ta kai ga sun yi amfani da makamai, za a yanke musu hukuncin kisa.[30]
- Ɗaurin ta'aziri: Ƴan tawaye idan ya zamanto an kama su kafin su fara amfani da makami za a yanke musu hukunci ɗauri na ta'aziri.[31][Tsokaci 1]
Maƙaloli Masu Alaƙa
Bayanin kula
- ↑ Shaykh Tusi, al-Nihaya, 1400 ƙ, shafi 296. Allama Hilli, ƙawa'id al-Ahkam, 1413 ƙ, jild 1, shafi 522
- ↑ Mufid, al-Irshad, 1413 ƙ, jild 1, shafuka 258–260. Shahid Thani, al-Rawdat al-Bahiyya, 1403 ƙ, jild 2, shafi 407. Zuhaili, al-Fiƙh al-Islami wa Adillatuhu, 1405 ƙ, jild 6, shafi 142
- ↑ Allama Hilli, Tadhkirat al-Fuƙaha, 1414 ƙ, jild 9, shafi 410.
- ↑ Zuhaili, al-Fiƙh al-Islami wa Adillatuhu, 1405 ƙ, jild 6, shafuka 142–143. Shahid Thani, al-Rawdat al-Bahiyya, 1410 ƙ, jild 2, shafuka 407–408
- ↑ Kashf al-Ghita', Kashf al Ghita' an Mubhamat al-Shari'a al-Ghara, 1422 ƙ, jild 4, shafi 368
- ↑ Tusi, al-Wasila ila Nail al-Fadila, 1408 ƙ, shafi 205
- ↑ Tarabi, “Baghi”, 1378 Sh, jild 3, shafi 596
- ↑ Allama Hilli, Tadhkirat al-Fuƙaha, 1414 ƙ, jild 9, shafuka 393–398. Shahid Thani, al-Rawdat al-Bahiyya, 1410 ƙ, jild 2, shafuka 407–408.
- ↑ Kashiful al-Ghita', Kashful al-Ghita' ‘an Mubhamat al-Shari'a al-Ghara, 1422 ƙ, jild 4, shafi 367
- ↑ Shaykh Tusi, 1387 ƙ, al-Mabsut, jild 7, shafi 265
- ↑ Najafi, Jawahir al-Kalam, 1404 ƙ, jild 21, shafuka 323–327
- ↑ Muhaddith Karaki, Jami‘ al-Maƙasid fi Sharh al-ƙawa'id, 1414 ƙ, jild 3, shafi 483
- ↑ Shahid Awwal, al-Lum‘a al-Dimashƙiyya, 1410 ƙ, shafi 83
- ↑ Muhaddith Hilli, Shara'i‘ al-Islam, 1408 ƙ, jild 1, shafi 309. Shahid Thani, Masalik al-Afham, 1413 ƙ, jild 3, shafi 94. Salehi Najafabadi, Jihad dar Islam, 1382 ƙ, shafi 142
- ↑ Najafi, Jawahir al-Kalam, 1404 ƙ, jild 21, shafuka 345–347. Zuhaili, al-Fiƙh al-Islami wa Adillatuhu, 1405 ƙ, jild 6, shafuka 144–145
- ↑ Shaykh Tusi, al-Iƙtisad, 1400 ƙ, shafi 315
- ↑ Omani, Majmu‘at Fatawa Ibn Abi ‘Aƙil, bita, shafi 111. Ibn Idris Hilli, al-Sara'ir, jild 2, shafuka 15–19
- ↑ Mushkini, Mustalahat al-Fiƙh, bita, shafi 102
- ↑ Khoei, Minhaj al-Salihin, 1410 ƙ, jild 1, shafuka 389–391.
- ↑ Allama Hilli, Tahrir al-Ahkam, 1420 ƙ, jild 2, shafi 233
- ↑ Najafi, Jawahir al-Kalam, 1404 ƙ, jild 21, shafuka 337–338
- ↑ Tusi, al-Khilaf, 1407 ƙ, jild 5, shafuka 335–336
- ↑ كتاب المغني لابن قدامة - ط مكتبة القاهرة، Gidan yanar gizon Al-Maktaba al-Shamila.
- ↑ Ibn Ƙudama, al-Mughni, 1388 H, juzu'i 8, shafi 524.
- ↑ Ibn Ƙudama, al-Mughni, 1388 H, juzu'i 8, shafi 524.
- ↑ Ibn Ƙudama, al-Mughni, 1388 H, juzu'i 8, shafi 524'.
- ↑ Uwdah, al-Tashri' al-Jina'i al-Islami, juzu'i 2, ba tare da kwanan bugu ba, shafi 673..
- ↑ Ibn 'Arabi, Aḥkam al-ƙur'an, 1408 H, juzu'i 4, shafi 1721
- ↑ Ibn 'Arabi, Aḥkam al-ƙur'an, 1408 H, juzu'i 4, shafi 1720–1723; Zuhayli, al-Fiƙh al-Islami wa Adillatuhu, 1405 H, juzu'i 6, shafi 143–146.
- ↑ Mu'awanate Huƙuƙi Riyasate Jamhuri, Ƙanune Majazate Islami, 1392 SH, shafi 68, Mataki 287.
- ↑ Mu'awanate Huƙuƙi Riyasate Jamhuri, Ƙanune Majazate Islami, 1392 SH, shafi 68, Mataki 288.
Tsokaci
- ↑ Hukuncin ɗaurin kurkukun ta'zir ana tanada shi ne saboda wasu laifukan da suka saba wa shari'a da aikata haram, kuma yana shafi irin waɗannan laifukan da ba a fayyace musu takamaiman hukunci a shari'a ba. A cikin fikihu, ana amfani da kalmar ta'azir wajen nufin irin hukuncin da, sabanin hudud da Shari'a ta ƙayyade, ba a ƙayyade masa iyaka ko adadi na musamman ba." Daga "Farhang-e Feƙh-e Farsi" bincike da rubutawa na Ma'aikatar Da'irat al-Ma'arif na Fiƙhun Musulunci bisa mazhabar Ahlul Baiti (a.s.), ƙarƙashin jagorancin Mahmad Hashimi Shahradi, Juzu'i na 2, shafi na 532.
Nassoshi
- Allamah al-Hilli, Hasan ibn Yusuf, Tadhkirat al-Fuƙaha', Qom, Mu'assasat Al al-Bayt, 1414ƙ.
- Ibn 'Arabi, Ahkam al-ƙur'an, bincike: 'Ali Muhammad Bajawi, Beirut, Dar al-Jil, 1408ƙ.
- Ibn Idris al-Hilli, Muhammad ibn Mansur, Kitab al-Sara'ir, Qom, Ofishin Wallafar Musulunci, 1410ƙ.
- Ibn Ƙudama, Abu Muhammad, al-Mughni, Masar, Maktabat al-ƙahira, 1388 ƙ.
- Kashif al-Ghita', Kashf al-Ghita' 'an Mubhamat Shari'at al-Gharra', Qom, Wallafar Ofishin Tablighat-e Islami na Hawza ta Qom, 1422ƙ.
- Ma'aikatar Shari'a ta Ofishin Shugaban Ƙasa (Iran) , ƙanun-e Mujazat-e Islami (Kundin Hukunce-hukuncen Laifuka na Musulunci), Ma'aikatar Tsarawa, Tsabtawa da Yada Dokoki, 1392 SH
- Mu'assasar Da'irat al-Ma'arif Fiƙh al-Islami bisa Mazhabin Ahlul Baiti (a.s.) , karkashin kulawar Mahmud Hashimi Shahroudi, Farhang-e Fiƙh-e Farsi, Qom, 1382 SH
- Muhaƙƙiƙ Karki, Ali ibn Husayn, Jami' al-Maƙasid fi Sharh al-ƙawa'id, Qom, Mu'assasat Al al-Bayt (a.s.), 1414 H
- Muhaƙƙiƙ al-Hilli, Ja'far ibn Hasan, Shara'i' al-Islam, bincike: 'Abd al-Husayn Muhammad 'Ali Baƙƙal, Qom, Isma'iliyan, 1408ƙ.
- Najafi, Muhammad Hasan, Jawahir al-Kalam fi Sharh Shara'i' al-Islam, bincike: 'Abbas ƙuchani, Beirut, Dar Ihya' al-Turath al-'Arabi, 1404ƙ.
- Shahid al-Awwal, Muhammad ibn Makki, al-Lum'a al-Dimashƙiyya fi Fiƙh al-Imamiyya, Beirut, Dar al-Turath – al-Dar al-Islamiyya, bugu na farko, 1410ƙ.
- Shahid al-Thani, Zayn al-Din ibn 'Ali, Masalik al-Afham ila Tanƙih Shara'i' al-Islam, Qom, Mu'assasat al-Ma'arif al-Islamiyya, 1413ƙ.
- Shahid al-Thani, Zayn al-Din ibn 'Ali, al-Rawda al-Bahiyya fi Sharh al-Lum'a al-Dimashƙiyya, bincike: Muhammad Kalantar, Beirut, 1410ƙ.
- Shaykh al-Mufid, Muhammad ibn Muhammad, al-Irshad fi Ma'rifat Hujaj Allah 'ala al-'Ibad, Qom, Taron Shaykh al-Mufid, 1413ƙ.
- Shaykh al-Tusi, Muhammad ibn Hasan, al-Iƙtisad, Qom–Tehran, Matba'at al-Khiyam, wallafar Maktabat Jami' Chaharbagh, 1400ƙ.
- Shaykh al-Tusi, Muhammad ibn Hasan, al-Khilaf, Qom, Ofishin Wallafar Musulunci, 1407ƙ.
- Shaykh al-Tusi, Muhammad ibn Hasan, al-Mabsut fi Fiƙh al-Imamiyya, Tehran, mawallafar al-Murtadawiyya li-Ihya' al-athar al-Ja'fariyya, 1387ƙ.
- Shaykh al-Tusi, Muhammad ibn Hasan, al-Nihaya fi Mujarrad al-Fiƙh wa al-Fatawa, Beirut, Mawallafar Dar al-Kitab al-'Arabi, bugu na biyu, 1400ƙ.
- Turabi, kbar, "Baghi", mawallafar Da'irat al-Ma'arif-e Jahan-e Islam, Tehran, Gidauniyar Da'irat al-Ma'arif al-Islami, 1378 SH.
- Uwdah, Abd al-ƙadir, al-Tashri' al-Jina'i al-Islami, Beirut, mawallafar Dar al-Kutub al-'Arabi, ba tare da kwanan wata ba.
- Zuhayli, Wahbah Mustafa, al-Fiƙh al-Islami wa Adillatuhu, Dimashƙ, Dar al-Fikr, 1405ƙ.
- «کتاب «بغی و تمرد در حکومت اسلامی» به چاپ دوم رسید)»، (Ibn Ƙudamah, littafin Al-Mughni bugun Maktabat Al-Ƙahira) , shafin Maktaba al-Shamila, ranar dubawa:10 Janairu 2023M.
- Ṣaliḥi Najafabadi, Ni'matullah, Jihad dar Islam, Tehran, Nashr-e Ney,1381Sh.