Jump to content

Jihadin Mace

Daga wikishia

Jihadin mace, (Larabci: جهاد المرأة) magana ce kai tsaye kan rikici da ɗauki ba daɗi na soji wanda ba wajibi bane kan mace a bisa koyarwar fiƙihun Muslunci[1] Ba'arin malaman fiƙihu suna da ra'ayin cewa bai ma halasta ba mace ta je jihadi[2] Wannan hukunce ya karkata kan jihadi Ibtida'i[3] Amma jihadi difa'i, a halin buƙata, zuwa jihadi yana wajabta kan mata.[4] Bisa ra'ayin Sayyid Muhammad Husaini Tehrani malamin Shi'a, rashin wajabcin jihadi a kan mata, ba ya nufin an hana su zuwa filin yaƙi; bari dai abin nufi daga rashin wajabcin shi ne rashin tarayyarsu ta kai tsaye cikin yaƙi, amma suna iya ba da gudummawa cikin ayyuka kamar kula da wanda suka jikkata da ba da tallafin kayayyakin buƙata.[5] Cikin litattafan tarihi, an ba da rahotanni na misalsalai daga halartar mata yaƙe-yaƙen Annabi (S.A.W); alal misali a cikin yaƙin uhudu mata goma sha huɗu daga jumla Sayyida Faɗima (S) da A'isha sun kasance suna ba da taimako kawo ruwa da abinci da kula da waɗanda suka jikkata.[6]

Imam Musa Kazim (A.S):

جِهَادُ الْمَرْأَةِ حُسْنُ التَّبَعُّل

Jihadin mace kyawunta zama da miji

Kulaini, Al-Kafi, 1407H, J 5 shafi 507.

Cikin matanonin hadisai, ba'arin ayyuka da ake lissafa matsayin jihadi ga mata sune:

Bayanin kula

  1. Najafi, Jawahir al-Kalam, 1404ƙ., juzu’i na 21, shafi na 7; Shaikh Ṭusi, al-Nihayah, 1400 H., shafi na 289; Ibn Idris, al-Sara’ir, 1410ƙ., juzu’i na 2, shafi na 3; Allamah Ḥilli, Tadhkirat al-Fuƙaha’, 1414 H., juzu’i na 9, shafi na 12; Ibn ƙudamah, al-Mughni, 1388ƙ., juzu’i na 9, shafi na 197.
  2. Muntazari, Risalat al-Istifta’at, Ƙum, juzu’i na 1, shafi na 102; Ḥusayni Ṭihrani, Risalah Badi‘ah, 1418ƙ., shafi na 121.
  3. Shahid Thani, Masalik al-Afham, 1413ƙ., juzu’i na 3, shafi na 8.
  4. Don misali duba: Shahid Thani, Masalik al-Afham, 1413ƙ., juzu’i na 3, shafi na 8; Kashif al-Ghita, Kashf al-Ghita’, Mawallafar Ma’hadawi, shafuka 395–396.
  5. Ṭehrani, Risalah Badi‘ah, 1418ƙ, shafi na 121
  6. Waƙidi, Kitab al-Maghazi, 1409ƙ., juzu’i na 1, shafi na 249.
  7. Kulayni, al-Kafi, 1407ƙ., juzu’i na 5, shafi na 9; Shaykh Ṣaduƙ, Man la Yaḥḍuruhu al-Faƙih, 1413ƙ., juzu’i na 3, shafi na 439.
  8. Fattal Nishaburi, Rawḍat al-Wa‘iẓin, 1375SH., juzu’i na 2, shafi na 376.
  9. Shaikh Ṭusi, al-Amali, 1414ƙ., shafi na 618.
  10. Shaik Tusi, Al-Amali, 1414ƙ, shafi 618

Nassoshi

  • Allama al-Hilli, Hassan bin Yusuf, Tadhkirat al-Fuƙaha', Cibiyar Al al-Bait, Qom, bugu na farko, 1414ƙ.
  • Fattal al-Naisaburi, Muhammad bin Ahmad, Rawdat al-Wa'izin wa Basirat al-Mutta'izin, Qom, Mawallafar Radi, bugu na farko, 1375SH.
  • Husaini Tehrani, Sayyid Muhammad Husain, Risalah Badi'ah, Mashhad, Mawallafar Allamah Tabatabai, 1418ƙ.
  • Ibn Idris al-Hilli, Muhammad bin Ahmad, As-Sara'ir al-Hawi li Tahrir il-Fatawa, Qom, ofishin-Mawallafar musulunci, bugu na biyu, 1410ƙ.
  • Ibn Ƙudamah, Abdullah bin Ahmad, Al-Mughni, Al-ƙahirah, Maktabat ul-ƙahirah, 1388ƙ.
  • Kashif al-Ghita', Ja'far bin Khidr, Kashf al-Ghita' an Mubhamat ash-Shari'at al-Gharra', Isfahan, mawallafar Mahdawi, bugu na farko, ba tare da kwanan wata ba.
  • Kulaini, Muhammad bin Ya'ƙub, Al-Kafi, Masu bincike da gyara: Ghaffari, Ali Akbar, Akhundi, Muhammad, Tehran, mabugar: Gidan litattafan Musulunci, bugu na hudu, 1407ƙ.
  • Muntaziri, Husain Ali, Risalah Istifta'at, Qom, bugu na farko, ba tare da kwanan wata ba.
  • Najafi, Muhammad Hasan, Jawahir al-Kalam fi Sharh Shara'i' al-Islam, Gyara: Abbas Ƙuchani da Ali Akhundi, Beirut, Gidan farfaɗo da gadon adabin Larabci, bugu na bakwai, 1404ƙ.
  • Shahid Thani, Zain al-Din bin Ali, Masalik al-Afham ila Tanƙih Shara'i' al-Islam, Qom, Cibiyar ul-Ma'arif al-Islamiyyah, bugu na farko, 1413ƙ.
  • Sheikh Saduƙ, Muhammad bin Ali, Man la Yahduruhu al-Faƙih, Mai bincike: Ali Akbar Ghaffari, Qom, ofishin Mawallafar musulunci, bugu na biyu, 1413ƙ.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin al-Hasan, Al-Amali, Qom, Gidan saƙafar Muslunci, bugu na farko, 1414ƙ.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin al-Hasan, An-Nihayah fi Mujarrad al-Fiƙh wa al-Fatawa, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, bugu na biyu, 1400ƙ.
  • Waƙidi, Muhammad bin Umar, Kitab al-Maghazi, Bincike: Marsden Jones, Beirut, Cibiyar al-A'lami, bugu na uku, 1409ƙ.