Murtaddi Milli
Wannan wani rubutu ne na siffantawa game da wata ma'ana ta fiƙihu, kuma ba za ta iya zama ma'auni ga ayyukan addini ba, domin ayyukan addini sai a koma zuwa ga wasu madogaran na daban. |
| Sashe dagaHukunce-hukuncen Aiki da na Fiƙihu |
|---|
Murtaddi milli, (Larabci: المرتد الملي) kishiya ne na murtaddi fiɗri, wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa ba su kasance Musulmi, shi da kansa ne bayan ya balaga ya zaɓi Muslunta da kansa, sai dai kuma daga baya ya fice daga Muslunci.
Murtaddi milli ana katange shi daga amfani da dukiyarsa, haka kuma ana fasakin aurensa (Warware shi), idan namiji murtaddi milli bai tuba ba, za a zartar masa da hukuncin kisa, amma idan mace ce za a tsare ta a kurkuku ko dai ta tuba ko kuma da ci gaba da zama har mutuwa.
Nazarin Ma'ana
Murtaddi milli, shi ne wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa lokacin haihuwarsa da bayan haihuwarsa ba su kasance daga Musulmi ba, shi ne da kansa ne bayan balaga ya zaɓi zama Musulmi, amma kuma daga baya ya kafirta.[1] Kishiyar murtaddi milli shi ne murtaddi fiɗri, wanda mahaifansa Musulmi ne, amma bayan ya balaga sai ya kafirta.[2]
Hukuncin Wanda Ya Fice Daga Muslunci
An tanadi hukunci ga murtaddi milli: Idan namiji ne za a bashi damar tuba, idan ya ƙi tuba za a kashe shi.[3] Amma idan mace ce za a tsare ta a kurkuku za a dinga ladabtar da ita a lokutan sallah har ta tuba ko kuma ta mutu a cikin kurkuku.[4]
Idan mace ta ƙara yin ridda bayan tuba, bisa fatawar wasu adadin malaman fiƙihu, idan ta maimaita ridda sau uku ko huɗu za a zartar mata da hukuncin kisa.[5] Sai dai cewa bisa fatawar Sayyid Abul Ƙasim Khuyi, mace murtadda milli tare da maimaita ridda ba za a zartar da hukuncin kisa a kanta ba.[6]
Hukunce-hukunce
Hukunce-hukunce da saƙonnin ridda milli sun kasance kamar haka:
- Hana amfani dukiya: Bisa fatawar wasu daga malaman fiƙihu murtaddi milli har zuwa lokacin da bai tuba ba za a barshi ya yi amfani da dukiyarsa ba.[7] Amma tare da haka Sayyid Abul Ƙasim Khuyi ba ya ganin halaccin katange murtaddi milli daga amfani da dukiyarsa.[8]
- Warware igiyar aure: ridda yana janyo fasakin aure (Warware aure), na'am idan ya zamana gabani sun yi jima'i da juna, za a warware igiyar auren bayan ƙarewar iddar mace (Iddar saki: tsarkaka daga al'ada uku daga jinin haila)[9]
- Rashin ingancin aure: Gini kan shahararren ra'ayin malaman fiƙihu na Shi'a, aure ba ya inganta tsakanin kafiri da Musulmi.[10] Amma tare da haka Sayyid Abul Ƙasim Khuyi yana ganin ingancin auren murtaddi tare da mace kafura.[11]
- Haramtuwa daga gado: Murtaddi ba ya cin gadon Musulmi, amma Musulmi yana cin gado daga Murtaddi.[12]
- Najasa: Murtaddi milli najasa ne[13]
A ra'ayin malaman fiƙihu na Shi'a, tuba yana kuɓutar da murtaddi daga hukuncin uƙuba da shari'a ta tanada a kansa.[14]
Maƙaloli Masu Alaƙa
Bayanin kula
- ↑ Shahid Thani, Al-Rawdah al-Bahiyyah, 1410ƙ, Juzu’i na 8, shafi na 30.
- ↑ Muhakkik Hilli, Shara’i al-Islam, 1408ƙ, Juzu’i na 4, shafi na 170.
- ↑ Muhakkik Hilli, Shara’i al-Islam, 1408ƙ, Juzu’i na 4, shafi na 170; Khui, Mabani Takmilat al-Minhaj, 1422ƙ, Juzu’i na 1, shafi na 396.
- ↑ Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362ƙ, Juzu’i na 41, shafi na 610–613; Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila, 1379SH, Juzu’i na 2, shafi na 365–368; Khui, Mabani Takmilat al-Minhaj, 1422ƙ, Juzu’i na 1, shafi na 399–401.
- ↑ Duba: Muhakkik Hilli, Shara’i al-Islam, 1408ƙ, Juzu’i na 4, shafi na 172; Shahid Thani, Masalik al-Afham, 1413ƙ, Juzu’i na 15, shafi na 31
- ↑ Khuyi, Mabani Takmilat al-Minhaj, 1422ƙ, Juzu’i na 1, shafi na 401.
- ↑ Koma ga: Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362ƙ, Juzu’i na 41, shafi na 620..
- ↑ Khuyi, Mabani Takmilat al-Minhaj, 1422ƙ, Juzu’i na 1, shafi na 396
- ↑ Misali: Shaikh Tusi, Al-Mabsut, 1351 SH, Juzu’i na 7, shafi na 289; Muhaƙƙiƙ Karaki, Jami’ al-Maƙasid, 1429ƙ, Juzu’i na 12, shafi na 423; Muhakkik Hilli, Shara’i al-Islam, 1408ƙ, Juzu’i na 4, shafi na 172; Allama Hilli, Tahrir al-Ahkam, Mu’assasat Aal al-Bait, Juzu’i na 2, shafi na 21; Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362ƙ, Juzu’i na 41, shafi na 602.
- ↑ Najafi, Jawahir al-Kalam, Juzu’i na 41, shafi na 615; Khui, Mabani Takmilat al-Minhaj, 1422ƙ, Juzu’i na 1, shafi na 396.
- ↑ Khuyi, Mabani Takmilat al-Minhaj, 1422ƙ, Juzu’i na 1, shafi na 405.
- ↑ Misali: Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362SH, Juzu’i na 39, shafi na 17.
- ↑ Misali: Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362SH, Juzu’i na 6, shafi na 293.
- ↑ Duba: Shahid Thani, Al-Raudah al-Bahiyyah, 1410ƙ, Juzu’i na 8, shafi na 30.
Nassoshi
- Allama Hilli, Hasan bin Yusuf, Tahrir al-Ahkam, Qom, Cibiyar Aal al-Bayt Li Ihya al-Turath, ba tare da shekara ba.
- Imam Khumaini, Sayyid Ruhullah, Tahrir al-Wasila, Qom, Mawallafar Gidan Ilimi, 1379ƙ.
- Khuyi, Sayyid Abulƙasim, Mabani Takmilat al-Minhaj, Qom, Cibiyar Raya Ayyukan al-Imam al-Khuyi, 1422ƙ.
- Muhakkik Hilli, Ja‘far bin Hasan, Shara’i al-Islam fi Masail al-Halal wa al-Haram, ba tare da shekara ba: Abdulhusayn Muhammad Ali Baƙal, Qom, Wallafar Isma‘iliyyan, 1408ƙ.
- Muhaƙƙiƙ Karaki, Ali bin Husayn, Jami‘ al-Maƙasid fi Sharh Al-ƙawa‘id, Qom, Cibiyar Aal al-Bayt don raya gado, 1429ƙ.
- Musawi Ardabili, Sayyid Abdulkarim, Fiƙh al-Hudud wa al-Ta‘zirat, Qom, Cibiyrr Buga Littattafan Jami’ar Mufid, bugu na biyu, 1427ƙ.
- Najafi, Muhammad Hasan, Jawahir al-Kalam, bita: Ibrahim Sultani, Beirut, Madabba'ar Gidan Rayar da Gadon Al’adun Larabawa., 1362ƙ.
- Shahid Thani, Zayn al-Din bin Ali, Al-Rawdah al-Bahiyyah fi Sharh al-Lum‘ah al-Dimashƙiyyah, sharhin Sayyid Muhammad Kalantar, Qom, Kantin Littafi Dawari, 1410ƙ.
- Shahid Thani, Zayn al-Din bin Ali, Masalik al-Afham ila Tanƙih Shara’i al-Islam, Qom, CibiyarIlimin Musulunci, 1413ƙ.
- Shaikh Tusi, Muhammad bin Hasan, Al-Mabsut fi al-Fiƙh al-Imamiyyah, Muhammad Baƙir Bahbudi, Tehran, Dakunan Karatu na Ridawiyyah, 1351SH.