Jump to content

Kisa Makamancin Ganganci

Daga wikishia

Kisa mai kama da ganganci, (Larabci: القتل شبه العمد) wani nau'in kisa ne wanda mai kisa ba shi da niyar yin kisa, hakazalika aikin da aka yi ya kai ga kisa a al'adance ba a lissafa shi a matsayin aikin da yake kashe mutum a kankin kanshi, sai dai kuma mai kisa ya yi wannan aiki ne bisa ganganci, kamar aikin likitanci wanda ya kai ga kashe mara lafiya, amma ba tare da niyar kisa ba. Kisan da ya yi kama da ganganci kisa ne wanda yake saɓanin kisan ganganci, da kisan da ba na ganganci ba, na farko shi mai kisa yana yin niyyar kisa, amma na biyu, watau kisa mai kama da ganganci wanda ya yi kisan bai yi niyyar kisa ba, kuma aikin na shi ma ba ya kisa amma sai aka yi rashin sa'a, sai ya yi kisa.

Kan abin da malaman fiƙihu suka ambata cewa shi kisa da ya yi kama da na ganganci ba a kashe mutum saboda shi, amma sai dai shi wanda ya yi kisan zai ba da diyya cikakkiya ga ƴan uwan wanda ya kashe kuma ya ba da kaffara, ta ƴanta bawa, idan ba zai iya ba, to sai ya yi azumi na wata biyu a jere, idan bai iya ba sai ya ciyar da talakawa 60.

Muhimmanci

Kisa mai kama da ganganci ɗaya ne daga cikin nau'ukan kisa da aka ambata a fiƙihun Musulunci,[1] kuma tabbas malaman fiƙihu sun ambaci wannan kisa a babuka na ƙisasi da diyya kuma sun ambaci hukuncinshi dalla-dalla,[2] nuni da bayani kan wannan kisa ya zo a wasu litattafai na hadisi a ƙarƙashin take na masamman,[3] aya ta 92 suratul nisa'i tana nuni kan kisan daba na ganganci ba, da bayani kan wajabcin ba da diyya kan shi, kazalika malaman tafsiri sun ɗabbaƙa wannan aya kan yanayi na kisa makamancin ganganci.[4]

Ma'anar Kisa Mai Kama Da Ganganci

Kisa mai kama da ganganci shi ne kashe mutum ba tare da niyya ba, saboda shi aikin da ya kai ga kashe wannan mutum a bisa al'ada a kan-kanshi ba ya kisa, sai dai cewa kuma ya yi wannan aiki ne da gangan,[5] Alal misali aikin likita wanda ba tare da niyya ba yana iya kai wa ga kashe mara lafiya,[6] ladabtar da yaro da ubansa yake yi, duk da ba da niyya ba yana iya zama sababin mutuwar yaro.[7]

A litattafai na fiƙihu da na dokoki an amabci nau'i biyu na kisa waɗanda suke kishiyantar kisan da ya yi kama dana ganganci, gasu kamar haka; kisan ganganci da kisan da ba na ganganci ba.[8]

Kisan ganganci yana tabbata da hanyar aikata wani aiki wanda bisa al'ada yana kai wa ga kisa sannan ya zamo mutum ya aikata haka ne domin ya yi kisa, amma shi kisan da ba na ganganci yana tabbata ne ta hanyar aikata wani aiki da bisa al'ada yana kaiwa ga kisa, amma shi wanda ya aikata aikin ba shi da niyar kisa, kamar mutum ya harbi wani naman daji, amma bisa kuskure sai harbin ya sami wani mutum sai ya mutu,[9]. a daidai lokacin da shi kisan da ya yi kama da ganganci shi bisa al'ada abin da ya yi ba ya kaiwa ga kisa kuma ba shi da niyyar kisa.[10]

Kisan ganganci yana da wata matsala guda ɗaya cewa malamai sun sami saɓani wajan bayyana haƙiƙanin mene ne kisan da ya yi kama ganganci, saboda da shi kisan ganganci an fitar da shi ne daga cikin abu biyu daga kisan ganganci da wanda ba kisan ganganci ba,[11] saboda shi kisan da ya yi kama da na ganganci ta fuskacin yin aikin da gangan yana kama da kisan ganganci, amma ta fuskacin rashin niyyar kisa yana kama da kisan da ba na ganganci ba,[12] misali idan mutum ya zama sanadiyar jin ciwu ko rashin lafiya ga wani, ta yadda ba zai mutu ba nan take, sai dai daga baya, to anan malaman fiƙihu sun sami saɓani kan cewa wannan kisa na ganganci ne ko kuma kisa ne da ya yi kama da na ganganci.[13]

Hukuncin Kisan Da Ya Yi Kama Da Ganganci

Bisa fatawar malaman fiƙihu, ba a kashe wanda ya kashe mutum ta hanyar kisan da ya yi kama da na ganganci, sai dai cewa ya wajaba kan wanda ya yi kisan ya ba da diyya,[14] za a ba da diyya ne cikin shekara biyu kuma daga cikin dukiyar wanda ya yi kisan,[15] ya zo a cikin litattafai na fiƙihu cewa wajabcin biyan diyya yana saraya ta hanyar yafiya daga mai haƙƙin kazalika biyan diyya yana saraya ta hanyar wanke wanda ake tuhuma, misali idan likita ya sa sharaɗi kafin ya fara aiki cewa idan marar lafiyar ya mutum ba zai biya diyya ba, sai marar lafiyar ko makusantashi suka yarda da hakan, to anan bisa fatawar mashahurin malamai ba wajibi bane likita ya biya diyya.[16]

Bisa abin da malaman fiƙihu suka faɗa shi ne a kisan da ya yi kama da na ganganci bayan biya diyya wajibi ne ya ƙara da yin kaffara,[17] Bisa ra'ayi Mashahur[18] kaffarar ita ce ƴanta bawa idan ba zai iya ba sai ya yi azumi na wata biyu a jere idan ya kasa sai ya ciyar da talakawa 60.[19]

Kisan Da Ya Yi Kama Da Ganganci A Dokokin Wasu Ƙasashe

An ambaci kisan mai kama da ganganci cikin dokokin hukunta mutum a wasu daga cikin ƙasashe. Daga cikinsu akwai Iran da Aljeriya da Iraƙ, a Iran an iyakance nau'in hukunci guda biyu a doka a shekara ta 1925 miladiyya, amma bayan juyin juya halin Muslunci da aka yi a shekara ta 1979 miladiyya, an rubuta dokar da an amince da dokokin hukunci kan lefin aikaa kisa kashi uku wanda na ukun shi ne kisan da ya yi kama da na ganganci.[20]

A Iraƙi dokar hukunta masu lefi ta tabbatar da cewa duk wanda ya kashe wani mutum bisa kuskure ko kuma ya yi sanadiyar kashe wani mutum ba da gangan ba, ta hanyar sakaci ko rashin kulawa, to za a hukunta shi ta hanyar tsare shi a gidan gyaran hali ko a yi mi shi tara.[21]

Amma dokokin Aljeriya sun kira kisan da ya yi kama da na ganganci da cewa wani nau'i ne na duka da ciwo mai kaiwa ga mutuwa wanda aka yi da gangan ba tare da niyyar kashe mutum ba, to wanada ya aikata hakan za a yi mi shi hukuncin zaman gidan gyaran hali na wani lokaci, daga shekara goma zuwa ashirin.[22]

Bayanin kula

  1. Qutb al-Din al-Rawandi, Fiqh al-Qur'an, 1405 AH, Juzu'i. 2, shafi. 414.
  2. Al-Muhaqq al-Hilli, Shara'i"ul Islam, 1408H, juzu'i. 4, shafi. 228; Al-Najafi, Jawaher Kalam, 1362 AH, juzu'i na 42, shafi na 7; Al-Sabzwari, Mahazzab al-Ahkam, 1413 AH, juzu'i. 29, shafi na. 62.
  3. Elkini, Kafi, 1407 AH, vol. 7, ku. 278; Al-Hurrul al-Amili, Wasa'il al-Shia, 1409 AH, juzu'i. 29, shafi. 35.
  4. Al-Tabari, Jami al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, 1412 AH, juzu'i. 5, shafi. 136; Fakhr al-Din al-Razi, Al-Mafatihul al-Gheeb, 1420 AH, vol. 10, shafi na 176-177; Makarem Al-Shirazi, Tafsir al-amsal, 1374, juzu'i. 4, shafi. 71.
  5. Karaji, Ayat al-Ahkam al-Huquqiyya Wal Jaza'iyya Juza'i, 2015, shafi. 45.
  6. Al-Najafi, Jawaher Kalam, 1362 AH, Juzu'i. 43, shafi na 46-47; Montazeri, Ahakam al-Atibba, 1427 AH, shafi. 51; Fazil al-Ankarani, Ahakam al-Tibbi Wal Marda, 1427 AH, shafi. 187.
  7. Karaji, Ayat al-Ahkam al-Huquqiyya Wal Jaza'iyya Juza'i, 2015, shafi. 45.
  8. Qutb al-Din al-Rawandi, Fiqh al-Qur'an, 1405 AH, Juzu'i. 2, shafi. 414.
  9. Al-Muhaqq al-Hilli, Shara'i'ul Islam, 1408H, juzu'i. 4, shafi. 228
  10. Al-Muhaqq al-Hilli, Shara'i'ul Islam, 1408H, juzu'i. 4, shafi. 228
  11. Hatami Wa Akharin., "Tashkis Qatle Shabhi Amdi Fi Fiqhil Imamiyya Wa Nizami Iran Wa Faransa," shafi. 115.
  12. Malmir Wa Akharin., "Mi'iyar Qatle Shabhe Amdi Fi Fqhil Imamiyya Wa Qawanin Iran Alwaz'iyya", shafi na. 56.
  13. Muassase Da'irat Ma'arifl Fiqhil Islami, Farhanq Fiqh, 2017, juzu'i. 6, shafi. 492.
  14. Al-Halli, Tahrir al-Ahkam al-Sharia, 1420 AH, juzu'i. 5, shafi. 527; Qutb al-Din al-Rawandi, Fiqh al-Qur'an, 1405 AH, Juzu'i. 2, shafi. 415.
  15. Al-Muhaqq al-Hilli, Shara'i'ul al-Islam, 1408H, juzu'i. 4, shafi. 229; Al-Shaheed al-Thani, al-Rawda al-Bahiyyah, Jamal al-Fakr al-Islami, Juzu'i. 4, shafi. 488; Al-Imam Al-Khomaini, Tahrir al-Wsilah, Dar al-Alam, juzu'i. 2, shafi na 556-557.
  16. Al-Najafi, Jawaher Kalam, 1362 AH, Juzu'i. 43, shafi na 46-47; Montazeri, Ahakam al-Tibbi, 1427 AH, shafi. 51; Fazil al-Ankarani, Ahakam al-Atibba Wal Marda, 1427 AH, shafi. 187.
  17. Qutb al-Din al-Rawandi, Fiqh al-Qur'an, 1405 AH, Juzu'i. 2, shafi. 415; Al-Najafi, Jawaher Kalam, 1362 AH, vol. 43, ku. 407; Montazeri, Al-Ahkam al-Shar'iyya, 1413 AH, shafi. 564.
  18. Muassaseh Da'irati Ma'arifil Islami, Farhanq Fiqh, 2017, juzu'i na 4, shafi na 495.
  19. Qutb al-Din al-Rawandi, Fiqh al-Qur'an, 1405 AH, Juzu'i. 2, shafi. 415; Al-Najafi, Jawaher Kalam, 1362 AH, vol. 43, ku. 407; Montazeri, Al-Ahkam al-Shar'iyya, 1413 AH, shafi. 564.
  20. Hatami Wa Akharun, "Tashkisil Qatli Shibhil Al-Amdi FI Fiqhil Imamiyya", shafi. 124.
  21. Madda (411) Min Qanunil Al-uqubat Al-iraqi
  22. Didan Mavloud, Penal Code, Disamba 2012, Dar Balqis, Bayda, shafi 89-91.

Nassoshi

  • Ahmadi Nejad, Nima, Al-qatlul Amdi Fi Qanun Iran Wa Fiqhul Imamiyya, Mujallar AL-,ilal, No. 58, Nuwamba 2019.
  • Al-Imam Al-Khomaini, Sayyid Ruhollah, Tahrir Al-Wasila, Qum, Dar Al-Alam Press, bugun farko, D.T.
  • Al-Jaziri, Abd al-Rahman, Al-Gharawi, Sayyed Muhammad, Mazeh, Yasir, Fiqhu Ala Al-mazahibil Al-arba'a Wa Mazhab Ahlul Baiti (A.S), Beirut, Darul Saqlain, bugu na farko, 1419 Hijira.
  • Hatami, Mahmoud Wa Akharin., "Tashkis Al-qatlil Amdi Fi Fiqhil Imamiyya Wa Nizam Iran Wa Faransa Al-huquqiyyin", Jaridar Huquqil Islam Wal Garbi, fitowa ta 2, Summer 1401.
  • Al-Husseini Al-Shirazi, Sayyid Muhammad, Fiqhu Al-Awlama, Beirut, Mu'assasa Al-fikril Islami, bugu na farko, 1423H.
  • Al-Halli, Al-Hasan bin Yusuf, Tahrir al-Ahkam al-Shar'iyya Ala Mazhabil Imamiyya, Qum, Cibiyar Imam Sadik (a.s), bugu na farko, 1420H.
  • Al-Sabzwari, Sayyid Abd al-Ala, Mahazzab al-Ahkam fi Bayan halal wal-haram, Qum, Cibiyar Al-Manar, bugu na 4, 1413H.
  • Al-Shaheed al-Thani, Zainul-Din bin Ali, al-Rauda al-Bahiyya fi Sharh al-Lamaa al-Damishqiyya, Qom, Majma al-Fakr al-Islami, D.T.
  • Al-Shaykhul Hurrul Al-Amily, Wasa'ilul Shi'a, Qum, Mu'assasa Al-Baiti (A.S.), bugun farko, 1409H.
  • Al-Tabari, Muhammad bin Jarir, Jame al-Bayan fi Tafsiril Al-Qur'an, Beirut, Darul Marafa, bugun farko, 1412H.
  • Fazel al-Lankarani, Muhammad, Ahkamul Al-Atibba Wal Marda, Qum, Cibiyar Imaman Athar (a.s), bugu na farko, 1427H.
  • Fakhr al-Din al-Razi, Abu Abd Allah Muhammad bin Omar, Al-Mafatihul al-Gheeb, Beirut, Dar Ahaya al-Tarat al-Arabi, bugu na uku, 1420H.
  • Qutb al-Din al-Rawandi, Saeed bin Abd Allah, Fiqh al-Qur'an, Research: Sayyed Ahmad al-Husseini, Qum, Ayatullah Al-Marashi Al-Najafi Library Publications, bugu na biyu, 1405H.
  • Al-Kulaini, Muhammad bin Yaqoob, Al-Kafi, gyara: Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Darul Kutub al-Islami, 1407H.
  • Karaji, Abu al-Qasim, Ayat al-Ahkam al-Haquqiyya Wal Jaza'iyya, Tehran, Mizan Publishing House, bugu na uku, 1385.
  • Muassaseh Da'irati Ma'arif Fiqhil Islami, Farhange Fiqh, Qum, Cibiyar Shari'a ta Musulunci, 1387.
  • Malmir, Mahmoud Wa Akharun. Miiyar Al-qatli Shibhil Amdi Fi Fiqhil Imamiyya Wa Qwanin Iran Al-waz'iyya, Journal of Al-Fiqh al-Elamiyya, Issue 10, Fall 2017.
  • Al-muaHaqqiq al-Hilli, Najm al-Din Jafar bin al-Hassan, Shara'i'ul Islam di Masa'il Halal Wa Haram, bincike da gyarawa: Abd al-Hussein Muhammad Ali al-Baqal, Qum, Mu’assasa Ismailiya, bugu na biyu, 1408H.
  • Musbah Al-Yazdi, Mohammad Taqi, Nazriyyatu Al-Huquq FIl Islam, Research: Mohammad Mahdi Naderi Al-Qami and Mohammad Mahdi Karimi Niya, Qum, Imam Al-Khamini Foundation Publications, 2013.
  • Makaram Al-Shirazi, Nasser, Tafsirul Al-amsal, Tehran, Darul Kutub al-Islamiyya, bugun farko, 1374.
  • Muntzari, Hossein Ali, Ahkam al-Tibbi, Qum, bugun Sayaya, bugu na uku, 1427H.
  • Muntzari, Hossein Ali, Al-Ahkam al-Shar'iyya Ala Mazhab Ahlul Baiti (a.s.), Qum, bugun Tashkar, bugu na farko, 1413H.
  • Al-Mohdi Al-Sawji, Muhammad Hassan, Bahas Tadbiqi HaulaHaqqil Hayat Min Manzur Qur'ane Kareem, Mujallar Al-Din da Al-Dunya al-Mudhamadah, fitowa ta 10, 2018.
  • Najafi Javaheri, Mohammad Hassan, Jawaharil al-Kalam Fi Sharh Sharail Islam, Beirut, Dar Ihiya al-Trath al-Arabi, 1362H.