Hassan Da Husaini Su ne Shugabannin Gidan Aljanna

Daga wikishia


Hassan Da Husaini Su ne Shugabannin Gidan Aljanna (Larabci:اَلْحَسَنُ و اَلْحُسَینُ سَیِّدَا شَبَابِ أَهْلِ الْجَنَّة) Ruwaya ce daga Annabi (S.A.W) game da fifikon Imam Hassan (A.S) da Imam Husaini (A.S) a kan sauran ƴan Aljanna.A fahimtar Wasu malaman Shi'a suna ganin abin da wannan hadisin ya ƙunsa shi ne waɗannan Imamai guda biyu a nan duniya ma sunfi kowa in aka ɗauke iyayensu da kakannsu Annabi daraja a doran ƙasa, don haka dole ne a yi musu biyayya. Idan muka duba ruwayoyin wasu daga malaman Sunna sun ce, ruwayoyi sun siffanta ‘yan Aljanna a matsayin matasa, ma'anar ruwayar ita ce, Hassan da Husaini (a.s) su ne shuwagabannin ƴan Aljannah, Sai dai Tabbas an cire wasu kamar Annabi (S.A.W) da Imam Ali (A.S)

Wannan hadisin yana cikin madogarai irin su Amali Sheikh Ɗusi, Man la yahduruhul-Faƙih da Sunan Tirmizi. Haka kuma an ruwaito daga sahabbai 25 na Manzon Allah (S.A.W), kamar Imam Ali (A.S), da Abubakar da Umar Ibn Khaɗɗab, malaman Sunna da Shi'a suna ganin wannan hadisi mutawatiri ne , A cikin wasu madogaran Ahlus-Sunna, akwai wata ruwaya mai kama da wannan hadisi, wacce ta gabatar da Abubakar da Umar a matsayin shugabannin 'yan Aljanna, Amma wasu malaman addini na Sunna suna ganin wannan hadisin mai rauni ne kuma karya ne.

Bayaninsu da Sanin Matsayinsu

Hadisin Sayyida Shabab Ahl al-Janna , shahararriyar ruwayar Manzon Allah (SAW) ce,[1]wacce aka yi amfani da ita wajen tabbatar da fifikon Imam Hassan da Imam Husaini (A.S) akan sauran ‘yan Aljanna[2] ya zo a cikin littafin Bihar al-Anwar cewa Imam Hussain (a.s.) ya kawo wannan hadisi a gaban makiya a waƙi'ar Karbala domin tabbatar da gaskiyarsa[3]

Nassin hadisin kamar haka: “Al-Hassan da Al-Hussain su ne Shuwagabannin samarin ‘yan Aljannah ".[4] An rawaito wannan ruwayar a wasu ma'anonin hadisin Shi'a da Sunna; Daga ciki: "Al-Hassan da Al-Hussain su ne majiɓintan samarin 'yan Aljanna kuma mahaifinsu ya fi su biyun"[5] da kuma “Al-Hassan da Husaini su ne shugaban matasan ‘yan Aljanna da cewa. Fatimah ita ce uwargidan matan ‘yan Aljanna”.[6]

fifikon Hasanaini Kan Dukkanin Mutanen Cikin Aljanna

A cikin wasu hadisai an siffanta dukkan ‘yan Aljanna a matsayin samari,[7] Wasu malaman Sunna dogaro da irin waɗannan hadisan ne yasa suka fassara kalmar Shabab (matasa) ga ‘yan Aljanna , [8] wato Hassan da Husaini su ne shuwagabannin ƴan Aljanna baki ɗaya[9] Haƙiƙa Annabi (SAWW) da Ali (a.s) sun keɓanta daga cikin wannan hadisin[10] A wani hadisin kuma. An ambaci cewa Manzon Allah (S.A.W.) ya keɓe Isa da Yahaya daga wannan ruwaya[11] Amma Muhammad Hassan Muzaffar ɗaya daga cikin malaman Shi'a yace an saka hannu a ruwayar (an canzata) kuma bai yarda da abin da aka ambata ba; Domin akwai annabawa irin su Ibrahim da Musa (a.s) waɗanda suka fi Yahya, amma ba a keɓe su a hadisin ba.[12]

Dalilin Da Yake Tabbatar Da Imamancin Hasanaini

Ali Bahrani (ya rasu: 1340H), ɗaya daga cikin malaman Shi'a, ya yi nuni da hadisin da ke bayani kan cewa shugabannin Ranar Mahshar wato ranar alƙiyama , sune sarakuna anan duniya,[13] ya yi imani da cewa, kamar yadda hadisin Sayyida Shabab Ahlul Janna ya zo akan Imam Hassan da Imam Husaini (A.S) haka yake a ɗayan hadisin ma sune shugabannin a nan duniya[14] Don haka ne aka ce wannan hadisi yana daga cikin dalilan tabbatar da imamancin waɗannan Imaman biyu.[15] Ana amfani da kalmar “Saiyid” ga wanda yake da shugabanci da girma da daraja,[16] haka nan wanda ya fi wasu a dukkan kyawawan halaye ana kiransa Sayyid.[17]

Yawaitar Ambaton Hadisai (Tawatiri)

Alama Majlisi malamin hadisi na Shi'a yana ganin hadisin Sayyida Shabab Ahlul-Janna ya kasance mutawatiri a gun malaman Shi'a da Ahlus-Sunna[18] Wasu malaman Sunna da suka haɗa da Suyuɗi da Nasiruddin Albani, suma sun bayyana tawatirin wannan hadisi.[19] Abu Na'im Isfahani malamin hadisin Ahlus-Sunna a cikin wani tawili mai ban tsoro game da ƙarfin isnadin wannan hadisin, Ahmad dan Hanbal ya ruwaito cewa, idan aka karanta isnadin wannan ruwaya ga mahaukaci to haukansa zai iya tafiya Saboda ƙarfinsa.[20]

Inda yafi shahara da aka rawaito wannan hadisi shi ne littafin Amal na sheikh ɗusi[21] da shaik Saduk.[22] Ahlus-Sunna su ma sun ruwaito wannan ruwaya[23] Wasu masu bincike sun ruwaito shi da ibara da madmuni daban-daban - daga sahabban Manzon Allah (SAWW) 25, waɗanda suka haɗa da Imam Ali (a.s), da Abubakar da Umar.[24]

Kirkirar Kwatankwacin Wannan Hadisi Domin Abubakar Da Umar

A cikin majiyoyin Ahlus-Sunna, akwai wani rahoto mai kama da hadisin Sayyida Shabab Ahlul-Jinna, na girmama Abubakar da Umar cewa su ne shuwagabannin Aljanna.[25] Haisami da Ibn Jauzi, daga cikin malaman Ahlus-Sunna sun ɗauki wannan labari a matsayin mai rauni kuma ƙarya.[26]

Ɗabarsi ya ruwaito a cikin littafin sa na Al'ihtijaj a cikin muhawarar da Yahya Ibn Aksam yayi da Imam Javad (A.S), Yahya ya tambayi Imam cewa: Menene ra'ayinka game da ruwayar da ke cewa "Abubakar da Umar Sune shuwagabannin ƴan Aljanna"? Imam ya bayyana ƙin fitar irin wannan magana daga bakin Annabi sannan ya ce: Bani Umayya ne suka ƙirƙira. don suyi takara da hadisin "Hassan da Hussaini su ne shuwagabannin ƴan Aljanna".[27]

Bayanin kula

  1. Fathi, “Hadisu Sayyida Shabab Ahlul-Jannah wa Mas'alati Afdaliyat Imam” shafi na 62
  2. Fathi, “Hadisu Sayyida Shabab Ahlul-Jannah wa Mas'alati Afdaliyat Imam” shafi na 82
  3. Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 45, shafi na 6.
  4. Sheikh Tusi, Amali, 1414 AH, shafi 312; Sheikh Sadouq, Man La Yahzara al-Faqih, 1413 AH, Juzu'i na 4, shafi na 179; Tirmizi, Sunan al-Tirmidhi, 1395 AH, juzu'i na 5, shafi na 656; Ibn Abi Shiba, al-Musannaf, 1409, juzu'i na 6, shafi na 378, H. 32176.
  5. Himyari, Qarb al-Isnad, 1413 AH, shafi 111; Ibn Majah, Sunan Ibn Majah, Dar Ihya Al-Katb al-Arabiya, Juzu'i na 1, shafi na 44.
  6. Sheikh Mufid, Amali, 1413 AH, shafi na 23; Ahmad bin Hanbal, Musnad Ahmad, 1421 Hijira, Juzu'i na 38, shafi na 353, Hijira 2329.
  7. Sheikh Mofid, Al-Khissas, 1413 AH, shafi na 358; Tirmizi, Sunan al-Tirmizi, 1395 AH, juzu'i na 4, shafi na 679; Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 43, shafi na 292.
  8. Manavi, Faiz al-Qadeer, 1356 AH, juzu'i na 6, shafi na 151.
  9. Manawi, Al-Taysir bi sharh Al-Jamae al-Saghir, 1408 AH, Mujalladi na 1, shafi na 507; Albani, Silsilatu -Ahadith Sahih, 1415 Hijira, juzu'i na 2, shafi:431.
  10. Muzaffar, Dalai Al-Sidq, 1422 AH, juzu'i na 6, shafi.463; Fathi, "Hadisin Sayyi Shabab na Ahlul-Jannah wa Mas'alati Afdaliyat Imam", shafi na 59.
  11. Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 43, shafi na 316.
  12. Muzaffar, Dalai al-Sidq, 1422 AH, juzu'i na 6, shafi na 461-462.
  13. Ibn Abi al-Hadid, Sharhu Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 7, shafi na 64
  14. Bahrani, Manar Al-Huda, 1405H, shafi 582.
  15. بازوند، «بازخوانی سندی و دلالی حدیث سیدا شباب اهل الجنة»، مرکز حقایق اسلامی.
  16. Bahrani, Manar Al-Huda, 1405H, shafi 582.
  17. Samani, Tafsir Alkur'ani, 1418, juzu'i na 1, shafi na 316; Khazan, Labab al-Tawil, 1415 AH, juzu'i na 2, shafi na 242.
  18. Majlesi, Haq al-yaqin, Islamic Publications, shafi na 287.
  19. Manawi, Al-Taysir bi hsarhe Al-Jamae al-Saghir, 1408 AH, Mujalladi na 1, shafi na 507; Albani, Silsilatu Ahadith Sahiha, 1415 Hijira, juzu'i na 2, shafi:431.
  20. Isfahani, Tarikh Isfahan, 1410H, shafi na 73.
  21. Sheikh Tusi, Amali, 1414 AH, shafi na 312.
  22. Sheikh Sadouq, Man La Yahzara al-Faqih, 1413 AH, Juzu'i na 4, shafi na 179.
  23. Tirmizi, Sunan al-Tirmidhi, 1395 AH, juzu'i na 5, shafi na 656; Ibn Abi Shiba, al-Musannaf, 1409, juzu'i na 6, shafi na 378, H. 32176.
  24. Fathi, "Hadisin Sayyida Shabab Ahlul-Jannah wa Mas'alati Afdaliyat Imam", shafi na 62.
  25. Tirmizi, Sunan al-Tirmidhi, 1395 AH, juzu'i na 5, shafi na 611; Ahmad bin Hanbal, Musnad Ahmad, 1421, juzu'i na 2, shafi na 40, H. 602.
  26. Haytami, Majma al-Zawaed, 1414 AH, juzu'i na 9, shafi na 53; Ibn Jozi, al-Ubaat, 1386 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 398.
  27. Tabarsi, al-Ihtijaj, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi na 447.

Nassoshi

  • Ibn Abi al-Hadid, Abdul Hamid, Sharh Nahj al-Balaghah, Qum, Mazhabar Ayatullahi al-Marashi al-Najafi, bugu na farko, 1404H.
  • Ibn Abi shaibah, Abdullah bin Muhammad, Al-Musannaf fi al-Ahadith and Antiquities, bincike: Kamal Yusuf al-Hout, Riyadh, Al-Rashad School, bugu na farko, 1409 AH.
  • Ibn Jozi, Jamal al-Din, Al-Ubaat, Bincike: Abdur Rahman Muhammad Othman, Madina, Al-Maktab al-Salfiyyah, bugun farko, 1386H.
  • Ibn Majah, Muhammad Ibn Yazid, Sunan Ibn Majah, Bincike: Muhammad Fouad Abdul Baqi, Bija, Dar Ihya Al-Kitab al-Arabiyyah, Bita.
  • Isfahani, Abu Naim, Tarikh Isfahan, wanda Hassan Kasravi ya yi bincike a Beirut, Darul Katb al-Alamiya, 1410H.
  • Tabarsi, Ahmad bin Ali, Al-Ihtijaj Ali Ahl al-Jajj, Mashhad, Morteza Publishing House, bugun farko, 1403H.
  • Ahmed bn Hanbal, Abu Abdullah, Musnad na Ahmad bn Hanbal, bincike: Shuaib Al-Arnaut da Adel Murshid, Bija, Al-Risalah Foundation, bugun farko, 1421H.
  • Albani, Muhammad Nasarul-Din, Silsilatu Hadith al-Sahiha wa shai'ain min fiqihu wa fawa'idiha.
  • Fathi, Ali, "Hadisu Sayyida Shabab Ahl al-Jannah wa Mas'alati Afdaliyat Imam" a cikin Mujallar Kalam ta Musulunci Juzu'i na 21, lamba 82, Qum, Satumba 2011.
  • Haitami, Noor al-Din, Majma al-Zawaed w manba'il Fawa'i, Bincike: Hossam al-Din Al-Qudsi, Alkahira, Mazhabar Qudsi, 1414H.
  • Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar Al-Anwar, Beirut, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
  • Majlesi, Mohammad Baqer, Haq Alyaqin, Tehran, Islamia Publications, Beta.
  • Manawi, Abdul Raouf bin Taj, Al-Taysir bi sharhe Al-Jamae al-Saghir, Al-Riyadh, Mazhabar Imam Shafi'i, 1408H.
  • Manawi, Abdul Raouf, Faiz al-Qadeer, Sharh al-Jamae al-Saghir, Misr, al-Maktab Tejariyyah al-Kabari, bugu na farko, 1356H.
  • Mozaffar, Mohammad Hasan, Dalai al-Sidq, Qum, Al-Bait (A.S.) Foundation, bugun farko, 1422H.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Amali, wanda Hossein Ustadwali, Ali Akbar Ghafari, Qom, Sheikh Mofid Congress ya buga, bugun farko, 1413 AH.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-IKhtisas, Ali Akbar Ghafari, Qom, Al-Tomar al-Ilami Lalfiya Al-Sheikh Al-Mofid, bugu na farko, 1413H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Man La Yahdrah al-Faqih, Qum, Ofishin Daba'ar Musulunci, bugu na biyu, 1413H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Al-Hassan, Al-Amali, Kum, Darul Taqwa, bugun farko, 1414H.
  • بازوند، رضا، «بازخوانی سندی و دلالی حدیث سیدا شباب اهل الجنة»، مرکز حقایق اسلامی، تاریخ بازدید: ۲۰ دی ۱۴۰۲ش.

Sendi, Nour al-Din, Hashiya al-Sandi Ali Sunan Ibn Majah, Beirut, Dar al-Jeil, Bita.