Daƙiƙa:Taƙlidi Da Mujtahidi
Kada a yi kuskure da Taƙlidi (Hajji)
Wannan wani rubutu ne na siffantawa game da wata ma'ana ta fiƙihu, kuma ba za ta iya zama ma'auni ga ayyukan addini ba, domin ayyukan addini sai a koma zuwa ga wasu madogaran na daban. |
Taƙlidi Da Mujtahidi, ko kuma a taƙaice, taƙlidi, wata kalma ce ta fiƙihu da take nufin bin fatawar mujtahidi da mukallafi (mutumin da aka ɗora wa nauyin shari'a) yake yi a cikin hukunce-hukuncen aikace-aikace na addini.
Bisa fatawar malaman fikihu, wajibi ne a yi taƙlidi da mujtahidin da yake da dukkan sharuɗɗan cancanta. Ma'ana, ya kasance namiji, ɗan Shi'a, halastaccen ɗa, kuma adali.
Mafi yawan malaman fikihun Shi'a suna ganin cewa a cikin mas'alolin fiƙihu da aka samu saɓanin ra'ayi tsakanin mujtahidai, wajibi ne mutane su bi fatawar mujtahidin da ya fi sauran zurfin ilimi.
| Sashe dagaHukunce-hukuncen Aiki da na Fiƙihu |
|---|
Batun wajabcin yin taƙlidi ya kasance sananne a tsakanin ƴan Shi'a tun zamanin Imamai. Tun daga zamanin Sayyid Murtada (ƙarni na biyar bayan Hijira), aka fara tattauna batun a cikin littattafan ilimin Usulul Fiƙhi. Daga ƙarni na goma kuma, ana tattauna shi a cikin littattafan fiƙihu mai dogaro da hujjoji, sannan daga baya a cikin littattafan Risala Amaliyya (bayanin hukunce-hukuncen shari'a).
Ana kiran Mujtahidi wanda mutane suke yin taƙlidi da shi da Marji'in Taƙlidi, yayin da ake kiran mutumin da yake yin taƙlidi da Mujtahidi da "Muƙallidi".
Bisa fatawar malaman fiƙihu, bai kamata a yi taƙlidi a cikin muhimman abubuwan da aka sani na addini da kuma Asalan addini ba. A maimakon haka, dole ne mutum ya kai ga sakamako da kansa ta hanyar bincike da nazari.
Wasu malaman fiƙihun Shi'a, kamar Akhbariyyawa, basu yarda da yin taƙlidi a addini ba.
Matsayin Taƙlidi A Fiƙihun Shi'a
A Isɗilahin fiƙihu, yin taƙlidi da Mujtahidi yana nufin bin Mujtahidi a cikin hukunce-hukuncen addini. Bin Mujtahidi yana nufin aikata ayyuka bisa ra'ayinsa da fahimtarsa ta fikihu a cikin hukunce-hukuncen rassan addini, kamar sallah, hajji da sauransu.[1]
A fiƙihun Shi'a, yin taƙlidi da Mujtahidi wajibi ne domin sanin hukunce-hukuncen aikace-aikace.[2] Bisa wannan bayani, mashahurin ra'ayin malaman Shi'a shi ne cewa wajibi ne kowane mutum ya zaɓi ɗaya daga cikin hanyoyi uku domin sanin ayyukan addini da suka rataya a kansa: ijtihadi, yin ihtiyaɗi ko yin taƙlidi da Mujtahidi. Ma'ana, ko dai mutum ya kasance Mujtahidi da kansa, ya fitar da hukunci daga madogaran fiƙihu, ko kuma idan ba Mujtahidi ba ne, ya yi aiki bisa ihtiyaɗi, ko kuma ya koma ga Mujtahidi mai cika dukkan sharuɗɗan cancanta, ya kuma yi aiki bisa ra'ayinsa.[3]
Hukunci Ayyuka Ba Tare da Taƙlidi Ba
Game da ayyukan addini da mutumin da ba Mujtahidi ba ya aikata ba tare da yin taƙlidi da Mujtahidi ba, akwai manyan ra'ayoyi guda biyu a tsakanin malaman fiƙihun Shi'a: Wasu daga cikinsu suna ganin cewa ayyukan da aka aikata ba tare da taƙlidi ko kuma ihtiyaɗi (yin taka-tsantsan ba), ba su inganta ba. Wasu kuma suna ganin cewa waɗannan ayyuka sun inganta idan an cika wasu sharuɗɗa.[4]
Kamar yadda aka ruwaito, Agha Ziya Iraƙi da Luɗfullah Safi Gulfaigani suna ganin cewa ayyukan da aka aikata ba tare da taƙlidi ba, za su inganta ne kawai idan sun dace da ainihin hukuncin Allah ko kuma sun dace da fatawar Mujtahidin da ya kamata mutum ya yi taƙlidi da shi.[5]
Faɗaɗuwar Taƙlidi
Abin da ake magana a kai game da yin taƙlidi da Mujtahidi shi ne taƙlidi a cikin rassan addini, wato hukunce-hukuncen aikace-aikace na fikihu. A cikin rassan addini ma, ba a yin taƙlidi a cikin muhimman abubuwan da aka sani na addini; taƙlidi ya shafi mas'alolin da hujjojinsu suke bisa zato.[6] A ra'ayin wasu malaman fiƙihu, an haramta yin taƙlidi ga mutumin da yake Mujtahidi, wanda ya fitar da hukuncin shari'a ta hanyar ijtihadi.[7]
A fagen tushen aƙidu da imani, mafi yawan Mujtahidan Shi'a ba sa halatta yin taƙlidi.[8] Haka kuma, a fannin gano abubuwan da suke faruwa a Zuhairi, taƙlidi yana da wasu iyakoki. Game da tantance ainihin abin da hukunce-hukuncen shari'a suka shafa, dole ne mutane su tantance da kansu su kai ga sakamako, domin maganar Mujtahidi ba ta zama hujja a wannan fanni.[9]
Masu Adawa Da Taƙlidi
A cikin mabiya Shi'a, malaman tafarkin Akhbariyya suna adawa da yin taƙlidi da Mujtahidi. Tun asali, suna kallon ijtihadi na zato da taƙlidi a matsayin abubuwan da Ahlus-Sunna suka ƙirƙiro, waɗanda daga baya suka shiga al'adun mabiya Shi'a.[10] Kamar yadda aka rawaito, wasu malaman kuma, irin su Abus Salah Halabi, Ibn Zuhra da Ibn Hamza, ba sa ganin halaccin yin taƙlidi ga Mujtahidi.[11]
Suna ganin cewa wajibi ne mutane su koma ga malami kuma faƙihi wanda yake dogaro da dalilai tabbatattu da hadisai daga Imamai kawai, ba tare da yin istinbaɗi (Fito da hukunci) da dalilan hankali ko ijma'i ba.[12] A fahimtar Akhbariyyawa, wannan aiki a Zuhairi taƙlidi ne ga Imamai Ma'asumai, ba taƙlidi ga wani malami ba.[13]
Yin Taƙlidi Da Malamin Fiƙihu Mai Cika Dukkan Sharuɗɗan Cancanta
A ra'ayin malaman Shi'a, ba wanda ya halatta ya bayar da fatawa sai Mujtahidi mai cika dukkan sharuɗɗan cancanta. Haka kuma, mutanen da ba Mujtahidai ba, ba za su iya yin taƙlidi ba sai ga malamin fiƙihu mai cika dukkan waɗannan sharuɗɗa.[14]
Malamin fiƙihu mai cika dukkan sharuɗɗan cancanta shi ne cikakken Mujtahidi wanda yake namiji, halastaccen ɗa kuma ɗan Shi'a. Haka kuma, dole ne ya kasance yana da cikakken hankali, Musulunci da imani, adalci, ƙwarewa da iya tafiyar da al'amura yadda ya kamata. Sannan dole ne ya nisanci munanan ɗabi'u kamar rowa da kwaɗayi.[15]
A cewar Sahibul Jawahir da Shaik Ansari, malamin fiƙihun da yake da ƙwarewar fitar da hukunce-hukuncen shari'a daga dalilan shari'a, kuma yake da sharuɗɗan da ake buƙata na kasancewarsa ɗan Shi'a, tare da adalci, zuhudu da tsoron Allah, shi ne malamin fiƙihu mai cika dukkan sharuɗɗan cancanta domin riƙe matsayin Marja'in Taƙlidi.[16]
Taƙlidi Da Mujtahidi Mafi Zurfin Ilimi (A'alam)
A cikin littattafan bayanin hukunce-hukuncen shari'a (Risala Amaliyya), an bayyana cewa idan Mujtahidan Shi'a suka sami saɓanin ra'ayi a kan wani hukunci, wajibi ne waɗanda aka ɗora wa nauyin shari'a su yi aiki da ra'ayin Mujtahidin da ya fi sauran zurfin ilimi.[17] Mafi yawan malaman fiƙihu suna ɗaukar wannan sharaɗi a matsayin wajibi wajen zaɓen Marja'in Taƙlidi.[18]
Bisa rahoton Jannati Shahrudi, malamin fikihun Shi'a, manyan Mujtahidan Shi'a suna ganin cewa Mujtahidin da ya fi sauran zurfin ilimi shi ne wanda ya fi dukkan Mujtahidan zamaninsa ƙwarewa wajen fahimtar hukuncin Allah.[19]Wasu malaman fiƙihu suna ganin cewa ko da mutumin da aka ɗora wa nauyin shari'a yana da zato cewa wani Mujtahidi ya fi sauran zurfin ilimi, wajibi ne ya yi taƙlidi da shi.[20] A ɗaya ɓangaren kuma, wasu malaman fiƙihu, ciki har da Mirzayi Ƙummi da Sahibul Fusul, sun halatta yin taƙlidi da Mujtahidi wanda ba shi ne mafi zurfin ilimi ba.[21]
Tarihin Taƙlidi A Mazhabar Shi'a
Bisa hadisai, yin taƙlidi a mazhabar Shi'a ya samo asali ne tun zamanin Imamai. Suna nuna wa mabiyansu su koma ga masu ruwayar hadisai[22] ko kuma amintattun almajiransu na kusa, kamar Zurara Bin A'ayan, Yunus Bin Abdur-Rahman, Aban Bin Taglib, Zakariyya Bin Adam, Muhammad Bin Muslim da Abu Basir.[23] Haka kuma, a wasu lokuta suna ƙarfafa sahabbansu da su riƙa zuwa masallatai da wuraren taruwar jama'a domin bayar da fatawa da shiryar da mutane.[24]
Samuwar taƙlidi a zamanin Imamai da kuma ƙarfafa mutane su yi hakan ya samo asali ne daga wasu dalilai: nisan da ke tsakanin garuruwa, rashin samun kayan aikin da ake buƙata domin mutane su yi tafiya, wanda hakan ya sa samun damar zuwa wajen Imam ya zama mai wahala; taƙiyya; da kuma tsananin wahala da ƙunci da zai sami Imamai idan mutane za su riƙa zuwa wajensu kai tsaye.[25]
A zamanin Gaiba Sugra (ƙaramin ɓoyuwa), an ƙara jin buƙatar yin taƙlidi a cikin hukunce-hukuncen shari'a.[26] Haka kuma, a zamanin Gaiba Kubra (babban ɓoyuwa), batun taƙlidi ya ci gaba da kasancewa abin da ake tattaunawa a tsakanin ƴan Shi'a.[27]
Gabatar Da Hukunce-hukuncen Taƙlidi A Littattafan Hukunce-hukuncen Aiki
Tarihin tattaunawa game da ijtihadi da taƙlidi ya samo asali ne tun lokacin da aka fara rubuta ilimin Usulul Fiƙhi. A cikin littattafan Usulul Fiƙhi na Imamiyya, an ci gaba da nazarin wannan batu tun daga lokacin da aka rubuta littafin Az-Zari'a Ila Usulish Shari'a, wanda Sayyid Murtada (355–436H) ya wallafa, har zuwa ƙarni na goma sha biyar bayan Hijira.[28]
A cikin littattafan fiƙihu mai dogaro da hujjoji, a wasu lokuta ana gabatar da wasu batutuwan da suka shafi taƙlidi a yayin nazarin sharuɗɗan malamin fiƙihu mai cika dukkan sharuɗɗan cancanta. Ana kuma tattauna waɗannan batutuwa a babukan umarni da aikata alheri da hana aikata mummuna, da kuma alƙalanci.[29][30]
Daga ƙarni na goma bayan Hijira, aka fara rubuta littattafai na musamman game da wannan batu, ƙarƙashin taken Al-Ijtihadu wat Taƙlid ko wasu sunaye daban-daban. Bayan zamanin Shaik Murtada Ansari (ƙarni na goma sha uku bayan Hijira), al'adar gabatar da hukunce-hukuncen taƙlidi a farkon littattafan hukunce-hukuncen aiki ta yaɗu. A zamanin yanzu ma, batu na farko da ake gabatarwa a cikin waɗannan littattafai shi ne hukunce-hukuncen taƙlidi da sharuɗɗan Marja'in Taƙlidi.[31]
Dalilan Halaccin Taƙlidi
Malaman fiƙihu na Shi'a sun dogara da dalilai huɗu na fiƙihu wajen tabbatar da wajibcin yin taƙlidi ga Mujtahidi. Waɗannan daliali su ne: Alƙur'ani, Sunna, hankali da ijma'i.[32]
Dalilan Hankali
Ta fuskar hankali, idan wanda aka ɗora wa nauyin bin shari'a ya aikata abin da aka haramta ko ya ƙyale abin da aka wajabta, zai cancanci azabar lahira. Saboda haka, dole ne ya kasance yana da madogara da hujjar da za ta kare shi daga wannan azaba. Ana samun wannan hujja ta ɗaya daga cikin hanyoyi uku: ijtihadi, Ihtiyaɗi (taka-tsantsan) ko taƙlidi.[33]
Ta haka ne, taƙlidi yake zama Wajib Takhyiri (wajibi na zaɓi) tare da sauran hanyoyi biyun. Idan mutum ba zai iya yin ijtihadi ba, kuma ba ya son bin hanyar taka-tsantsan, to taƙlidi zai zama Wajib Ta'ayini (wajibi a kansa kai tsaye).[34]
Dalili Na Alƙur'ani
Malaman tafsiri da malaman fiƙihu sun kafa hujja da aya ta 122 Suratut Tauba wajen tabbatar da halaccin yin taƙlidi ga malaman addini. Wannan aya an fi saninta da Ayar Nafru. A ganinsu, ayar tana nuna wajabcin yin tafiya domin zurfafa fahimtar addini, koyon koyarwar Musulunci da isar da ita ga sauran mutane. Daga wajabcin isar da koyarwar addini ga wasu, sun fahimci cewa wajibi ne sauran mutane su yi taƙlidi gare su.[35]
Haka kuma, malaman tafsiri sun fahimci wajabcin yin taƙlidi da komawa ga malamai da Mujtahidi daga ayoyi na 43 Suratun Nahli da ta 7 Suratul Anbiya, waɗanda aka sani da Ayar Ahluz Zikri. Alal misali, Allama Ɗabaɗaba'i ya rubuta cewa wannan aya tana ishara zuwa ga wata ƙa'ida ta bai ɗaya wadda hankali ya yarda da ita, wato komawar wanda bai da ilimi ga wanda yake da ilimi.[36]
Dalili Na Hadisi
An rarraba hadisai da malaman fiƙihu na Imamiyya suke amfani da su a wasu lokuta wajen tabbatar da halaccin taƙlidi zuwa rukuni-rukuni kamar haka:[37]
- . Hadisan da Imamai (A.S) suka umurci Shi'a da komawa ga masu riwayar hadisai, kamar wasiƙar Imam na Goma Sha Biyu (A.S);[38]
- . Hadisan da suka nuna cewa Imamai (A.S) sun umurci mabiyansu da komawa ga wasu mutane da suka ambata sunayensu, domin neman sanin hukunce-hukuncen addini;[39]
- . Hadisan da suka nuna cewa Imamai (A.S) sun ƙarfafa sahabbansu da su riƙa bayar da fatawa ga mutane, ko kuma sun amince da fatawoyin da suke bayarwa;[40]
- . Hadisan da suka hana bayar da fatawa ba tare da ilimi ba, ko kuma bayar da fatawa bisa hanyoyi irin su ra'ayi da ƙiyasi.[41] Ma'anar waɗannan hadisai ita ce halaccin bayar da fatawa bisa ingantacciyar hujjar shari'a;[42]
- . Hadisan da suka nuna cewa Imaman Shi'a sun halatta yin taƙlidi ga waɗanda suke bayar da fatawa bisa ƙa'idojin shari'a.[43] Misali, akwai wani hadisi daga Imam Hassan Askari (A.S) mai wannan ma'ana: "Duk wani malamin fiƙihu da yake kula da kansa, yake kiyaye addininsa, yake saɓa wa son zuciyarsa, kuma yake bin umarnin Ubangijinsa, to talakawan Shi'a za su iya yin taƙlidi gare shi".[44]
Ijma'i
Ijma'i, wato "haɗuwar ra'ayin malaman fiƙihu", yana daga cikin sauran hujjojin da ake amfani da su wajen tabbatar da halaccin taƙlidi a hukunce-hukuncen shari'a.[45] Ma'anarsa ita ce, dukkan malaman fiƙihu na Shi'a sun yi imanin cewa wanda aka ɗora wa nauyin bin shari'a yana da zaɓi tsakanin ya kai matsayin ijtihadi da kansa, ko kuma ya karɓi hukunce-hukuncen shari'a daga wanda ya kai wannan matsayi, ba tare da sanin hujjojin fiƙihu da aka gina waɗannan hukunce-hukuncen a kansu ba.[46]
Taƙlidi A Mazhabar Ahlus-Sunna
A cewar masana masu bincike, batun taƙlidi a tsakanin Ahlus-Sunna ya fuskanci sauye-sauye da dama a tsawon tarihi. A wani lokaci, mazhabobi daban-daban sun bayyana, kuma yawaitar waɗannan mazhabobi ta haifar da saɓanin ra'ayoyi. A ƙarshe, waɗannan saɓani suka jawo tasowar ra'ayin rufe ƙofar ijtihadi da taƙaita mazhabobin fiƙihu. Daga ƙarshe, a ƙarni na bakwai bayan Hijira, mazhabobi huɗu daga cikin mazhabobin Ahlus-Sunna suka samu amincewa a hukumance, sannan aka haramta bin sauran mazhabobi.[47]
Wasu daga cikin malaman Ahlus-Sunna na farko, kamar Abul Fathi Shahrastani (wanda ya rasu a shekara ta 548H) da Abu Ish'aƙ Shaɗibi (wanda ya rasu a shekara ta 790H), sun nuna rashin amincewarsu da rufe ƙofar ijtihadi da bayar da fatawa, kuma sun yi kira da a sake buɗe ta.[48] A cikin ƙarni na baya-bayan nan ma, wasu malaman Ahlus-Sunna da malaman jami'ar Al-Azhar sun yi amfani da ijma'in Musulmi a farkon Musulunci, wanda ya tabbatar da halaccin yin taƙlidi ga kowane Sahabi, wajen ƙin yarda da taƙaita ijtihadi ga mazhabobi huɗu kawai.[49]
Batutuwa Masu Alaƙa
Bayanin kula
- ↑ Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwatul Wusƙa, juzu'i na 1, shafi na 4; Rahman Sitayesh, «تقلید»،shafi na 789.
- ↑ Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwatul Wusƙa, juzu'i na 1, shafi na 11.
- ↑ Khamna'i, «احکام تقلید»، Ofishin Hifze Wa Nashre Asare Ayatullahi Khamna'i.
- ↑ Nazri da wasu, «بطلان عمل مکلف بدون تقلید و احتیاط، در بوته نقد»، shafi na 74.
- ↑ Nazri da wasu, «بطلان عمل مکلف بدون تقلید و احتیاط، در بوته نقد»، shafi na 74.
- ↑ Beheshti, Akhbarigeri, shafi na 395.
- ↑ Subhani, «موضوع: اجتهاد و تقلید»، gidan yanar gizo na Madrase Faƙahat.
- ↑ Berenjakar da Nusratiyan Ahur, «تقلید در اعتقادات؛ از انکار تا پذیرش»، shafi na 83.
- ↑ Alidust, «نظرات کارشناسانه فقیه در موضوعات احکام»، shafi na 49.
- ↑ Beheshti, Akhbarigeri, shafi na 353.
- ↑ Beheshti, Akhbarigeri, shafi na 379.
- ↑ Beheshti, Akhbarigeri, shafi na 380.
- ↑ Beheshti, Akhbarigeri, shafi na 380-383.
- ↑ Mahamid, Mabani Qur'ani Hukumat Dini, shafi 199.
- ↑ Muntaziri, Dirasat Fi Wilayatil Faƙih, juzu'i na 1, shafi na 407.
- ↑ Najafi, Jawahirul Kalam, juzu'i na 21, shafi na 399, Shaik Ansari, Al-ƙada'u Wash Shahadat, shafi na 229-331.
- ↑ Bani Hashim, Taudihul Masa'il Maraji, juzu'i 1, shafi na 13-15.
- ↑ Jannati, «سیر تاریخی تقلید از اعلم»، shafi na 20.
- ↑ Jannati, «سیر تاریخی تقلید از اعلم»، shafi na 101.
- ↑ Bani Hashim, Taudihul Masa'il Maraji, juzu'i 1, shafi na 15-17, Mas'ala 4.
- ↑ Zuhairi, «نقد نظریه عدم تعین تقلید از اعلم»، shafi na 56.
- ↑ Misali ku duba: Hurru Amili, Wasa'ilus Shi'a, juzu'i na 27, shafi na 137, 140, 142, 149, 150.
- ↑ Misali ku duba: Hurru Amili, Wasa'ilus Shi'a, juzu'i na 27, shafi na 140, 142, 145, 147, 148.
- ↑ Najashi, Rijal Najashi, shafi na 10.
- ↑ Rahman Sitayesh, «تقلید»، shafi na 789.
- ↑ Rahman Sitayesh, «تقلید»، shafi na 789.
- ↑ Rahman Sitayesh, «تقلید»، shafi na 789.
- ↑ Rahman Sitayesh, «تقلید»، shafi na 789.
- ↑ Misali ku duba: Allama Hilli, Ƙawa'idul Ahkam, juzu'i na , shafi na 525-526; Shahidus Sani, Ar-Raudatul Bahiyya Fi Sharhil Lum'atil Dimashƙiyya, juzu'i na 1, shafi na 236-237.
- ↑ Rahman Sitayesh, «تقلید»، shafi na 789.
- ↑ Rahman Sitayesh, «تقلید»، shafi na 789.
- ↑ Zuhairi, «تقلید در بوته تحقیق»، shafi na 61.
- ↑ Bahrul Ulum, At-Taƙlid Fish Shari'atil Islamiyya, shafi na 46; Khuyi, At-Tanƙihu Fi Sharhil Urwatil Wusƙa, juzu'i na 1, shafi na 64.
- ↑ Hakim, Mustamsakul Urwatil Wusƙa, juzu'i na 1, shafi na 6; Khuyi, At-Tanƙihu Fi Sharhil Urwatil Wusƙa, juzu na , shafi na 65.
- ↑ Khuyi, At-Tanƙihu Fi Sharhil Urwatil Wusƙa, juzu na , shafi na 66; Makarim Shirazi, Tafsir Namuna, juzu'i na 8, shafi na 193.
- ↑ Ɗabaɗaba'i, Almizan, juzu'i na 12, shafi 259.
- ↑ Beheshti, Akhbarigeri, shafi na 369.
- ↑ Hurru Amili, Was'ilush Shi'a, juzu'i na 27, shafi na 140.
- ↑ Hurru Amili, Was'ilush Shi'a, juzu'i na 27, shafi na 142, 144, 146.
- ↑ Hurru Amili, Was'ilush Shi'a, juzu'i na 27, shafi na 148, 149.
- ↑ Hurru Amili, Was'ilush Shi'a, juzu'i na 27, shafi na 20, 31, 35, 62.
- ↑ Akhund Khurasani, Kifayatul Usul, shafi na 473.
- ↑ Hurru Amili, Was'ilush Shi'a, juzu'i na 2, shafi na 382, 386.
- ↑ Hurru Amili, Was'ilush Shi'a, juzu'i na 27, shafi na 131.
- ↑ Beheshti, Akhbarigeri, shafi na 377.
- ↑ Shahidul Awwal, Zikra Ash-Shi'a Fi Ahkamish Shari'a, juzu'i na 1, shafi na 41.
- ↑ Haidar, Al-Imam As-Sadiƙ Wal Mazahibul Arba'a, juzu'i na 1, shafi na 170-173; Agha Buzurg Tehrani, Tarikh Hasril Ijtihad, shafi na 25.
- ↑ Agha Buzurg Tehrani, Tarikh Hasril Ijtihad, shafi na 26.
- ↑ Shaukani, Irshadil Fuhul Ila Tahƙiƙil Haƙƙi Min Ilmil Usul, shfai na 231 da 240.
Nassoshi
- Agha Buzurg Tehrani, Muhammad Muhsin, Tarikh Hasril Ijtihad, Qom, Matba'atu Khayyam, 1401H.
- Akhund Khurasani, Muhammad Kazim Bin Husain, Kifayatul Usul, Qom, Cibiyar Ali Bait (A.S) Li Ihya'it Turas, 1409H.
- Allama Hilli, Hassan Bin Yusuf, Ƙawa'idul Ahkam, Qom, Cibiyar An-Nashril Islami, 1413H.
- Ansari, Murtada, Al-ƙada'u Wash Shahadat, Qom, Babban Taron Duniya na Tunawa da Shaikh A'azam Ansari, 1415H.
- Alidust, Abul Ƙasim,«نظرات کارشناسانه فقیه در موضوعات احکام»، (Ra'ayoyin ƙwararru na malamin fiƙihu game da batutuwan hukunce-hukuncen shari'a), Mujallar wata uku-uku ta Fiƙhe Wa Usul, lamgba ta uku, Hunturu, 2004M.
- Bahrul Ulum, Izzuddin, At-Taƙlid Fish Shari'atil Islamiyya, Beirut, Daruz Zahra Lit Tibaa wan Nashr wat Tawzi', 1398H/1978M.
- Bani Hashimi, Sayyid Muhammad Hassan, Taudihul Masa'il Maraji Taƙlid, Ofishin Intisharate Islami, Qom, 1381Sh.
- Beheshti, Ibrahim, Akhbarigeri: Tarikh Wa Aƙa'id, Cibiyar Farhangi Darul Hadis, Qom, 1391Sh.
- - Baranjakar, Reza, da Nusratian Ahur, Mahdi, «تقلید در اعتقادات؛ از انکار تا پذیرش»، (Taƙlidi a Akidu: Daga Ƙin Yarda zuwa Amincewa), Mujallar Ma'rifat Kalami, Lamba ta 11, Kaka da Hunturu 2013/2014M.
- Haidar, Asad, Al-Imam As-Sadiƙ Wal Mazahibul Arba'a, Beirut, Darut Ta'aruf Lil Matbu'at, 1422H/2001M.
- Ɗabaɗaba'i Yazdi, Sayyid Muhammad Kazim, Al-Urwatul Wusƙa, Beirut, Cibiyar A'alami Lil Matbu'at, 1409H.
- Ɗabaɗaba'i, Muhammad Husain, Tafsir Almizan, Beirut, Cibiyar A'alami Lil Matbu'at, 1352Sh/1393H.
- Hakim, Muhsin, Mustamsakul Urwatil Wusƙa, Qom, Darut Tafsir, 1374Sh/1416H.
- Hurru Amili, Muhammad Bin Hassan, Wasa'ilush Shi'a, Qom, Cibiyar Ali Bait (A.S) Li Ihya'it Turas, 1374Sh/1416H.
- Jannati, Muhammad Ibrahim, «نظریه تعین تقلید از اعلم», (Ra'ayin Wajabcin Taƙlidi ga Mujtahidi Mafi Zurfin Ilimi,) Mujallar Kayhan Andisha ta fitowa sau biyu a kowane wata, lamba ta 51,22 ga Nuwamba, 1993M.
- Jannati, Muhammad Ibrahim, «سیر تاریخی تقلید از اعلم»، (Tarihin Taƙlidi ga Mujtahidi Mafi Zurfin Ilimi,) Mujallar Kayhan Andisha ta fitowa sau biyu a kowane wata, lamba ta 6, Mayu da Yuni, 1986M.
- Khamna'i, Sayyid Ali، «احکام تقلید»، (Hukunce-hukuncen Taƙlidi), Ofishin Hifze Wa Nashre Asare Ayatullahi Khamna'i. Ranar shigar da labari 16 ga Satumba, 2014M. Ranar duabwa 5 Nuwamba 2026M.
- Khuyi, Abul Ƙasim, At-Tanƙihu Fi Sharhil Urwatil Wusƙa, wanda Ali Gharawi Tabrizi ya rubuta, Qom, Lutfi, 1407H.
- Mahamid, Ali, Mabani Qur'ani Hukumat Dini, Ustane Muƙaddas Hazrate Fatima Ma'asuma (A.S), Qom, 1389Sh.
- Makarim Shirazi, Nasir, Tafsirul Namuna, Qom, Darul Kutubil Islamiyya, 1374Sh.
- Muntaziri, Husain Ali, Dirasat Fi Wilayatil Faƙih Wa Fiƙhid Daulatil Islamiyya, Qom, Nashr Tafakkur, 1409H.
- Najafi, Muhammad Hassan, Jawahirul Kalam fi Sharai'il Islam, Beirut, Daru Ihya'it Turasil Arabi, 1404H.
- Najashi, Ahmad Bin Ali, Rijal Najashi, Qom, Cibiyar An-Nashril Islami, 1365 Sh.
- Nazari, Ihsan da wasu، «بطلان عمل مکلف بدون تقلید و احتیاط در بوته نقد»، (Soke ingancin aikin wanda aka ɗora wa nauyin bin shari'a idan bai yi taƙlidi ko taka-tsantsan ba, a ƙarƙashin bincike da suka), Mujallar wata uku-uku ta Fiƙhe Wa Mabani Huƙuƙ, daura ta 57, lamba ta 1, Satumba 2024M.
- Rahman Sitayesh, Muhammad Kazim, «تقلید»، (Taƙlidi,) Daneshname Jahane Islami (Juzu'i na 7), Tehran, Gidauniyar Da'iratul Ma'arif ta Musulunci, 2014M.
- Shahidul Awwal, Muhammad bn Makki, Zikra Ash-Shi'a fi Ahkamish Shari'a, Qom, Cibiyar Ali Bait (A.S) Li Ihya'i Turas, 1377Sh/1419H.
- Shahidus Sani, Zainuddin Bin Ali, Ar-Raudatul Bahiyya Fi Sharhil Lum'atil Dimashƙiyya, Qom, Ofishin Tabligate Islami Hauze Ilmiyye Qom, bugun farko, 1412H.
- Subhani, Ja'afar، «موضوع: اجتهاد و تقلید»، (Maudu'i: Ijtihadi da Taƙlidi), gidan yanar gizo na Madrase Faƙahat. 23 Samtuba 2019M. Ranar duabwa 5 Nuwamba 2026M.
- Shaik Saduƙ, Muhammad Bin Ali, Kamalud Din Wa Tamamum Ni'ima, wanda Ali Akbar Ghaffari ya gyara, Tehran, Nashr Islamiyya, 1395H.
- Shaukani, Muhammad, Irshadil Fuhul Ila Tahƙiƙil Haƙƙi Min Ilmil Usul, Beirut, Darul Ma'arifa, ba tare da kwanan wata ba.
- Zuhairi, Abbas, «نقد نظریه عدم تقین تقلید از اعلم»، (Sukar Ra'ayin Rashin Tabbatar da Wajabcin Taƙlidi ga Mujtahidi Mafi Zurfin Ilimi,) Mujallar Kayhan Andisha ta fitowa sau biyu a kowane wata, lamba ta 55, Yuli da Satumba 1993M.
- Zuhairi, Abbas, «تقلید در بوته تحقیق» (Taƙlidi a Ma'aunin Bincike,) Mujallar Kayhan Andisha ta fitowa sau biyu a kowane wata, lamba ta 61,Yuli da Satumba 1994M.