Jump to content

Daƙiƙa:Shirun Imam Ali (A.S) Na Tsawon Shekaru 25

Daga wikishia
Maƙalar Shirun Imam Ali (A.S) Na Tsawon Shekaru 25 tana da alaƙa tare da maƙalolin.
Jadawalin Rayuwar Imam Ali
Cikin Makka
599M Haihuwa
650M Fara zuwa gidan Annabi(S.A.W)
610M Farkon wanda ya fara karɓar da'awar Annabi(S.A.W) zuwa Muslunci
613M Goyan bayan Annabi aYaumud Dar
616M Halartar kewayar Shi'bi Abi Ɗalib
619M Rasuwar Abi Ɗalib (Mahaifi)
622M Lailatul Mabit: Kwantawa a gadon Annabi (S.A.W) Maimakonsa
A cikin Madina
622M Hijira Zuwa Madina
2H-624M Halartar Yaƙin Badar
2H-624M Aure tare da Faɗima (S)
3H-625M Halartar Yaƙin Uhudu
4H-626M Rasuwar Faɗima Bint Asad (Mahaifiya)
5H-627M Halartar Yaƙin Ahzab da kashe Amru Bn Abdi Wuddi
6H-628M rubuta takardarSulhu Hudaibiyya bisa umarnin Annabi(S.A.W)
7H-629M Buɗe ƙofar Khaibar Yaƙin Khaibar
8H-630M HalartarFatahu Makka da kakkarya gumaka bisa umarnin Annabi (S.A.W)
9H-631M halifantar Annabi A Madina a lokacinYaƙin Tabuk
9H-631M Umartarsa da Isar Da Ayoyin Bara'a ga Mushrikai
9H-631M HalartarTaron Mubahala
10H-632M Halartar Hajjin Bankwana
10H-632M Waƙi'ar Ghadir Khum
11H-632M Wafatin Annabi (S.A.W) Wanka da likkafi ta hannun Imam Ali (A.S)
Zamanin Halifofi Uku
Daga11-35H Shiga Zamanin shiru na shekaru 25
11H-632H Batun Saƙifatu Bani Sa'ida a fara halifancin Abubakar
11H-632M Harin kan gidan Ali (A.S.) Domin Karɓar mubaya’a daga gare Shi
11H-632M Wafatin Sayyida Zahra (S) (mata)
23H-644M HalartarMajalisar shura ta Umar mai mutane shida don ayyana Halifanci
35H-655M Aika Hasanaini don ba da kariya ga Usman
Zamanin Hukumar Imam Ali (A.S)
35H-655M Bai'ar mutane da fara daurar hukuma (Yana da kusan shekaru 57)
36H-656M Yaƙin Jamal
37H-657M Yaƙin Siffin
38H-658M Yaƙin Nahrawan
40H-661M Shahada (Yana da kusan shekaru 62)

Shirun Imam Ali (A.S) na tsawon shekaru 25, (Larabci: عزلة الإمام علي (ع) عن السياسة لمدة 25 سنة) ishara ce game da zaman gida da Sayyidina Ali (A.S) ya yi tun bayan wafatin Annabi (S.A.W) daga shekara ta 11 bayan hijira har zuwa zamanin halifancinsa a shekara ta 35 bayan hijira. A tsawon wannan shekaru Imam Ali (A.S) bai ɗauki mataki karɓo haƙƙinsa na halifancin Annabi ba, saboda kare muradun addini da haɗin kan Muslunci, kuma ya haƙura ya bada haɗin kai tare da halifofi uku.

Bayan wafatin Annabi (S.A.W), taron Saƙifatu Bani Sa'ida wanda cikinsa ne aka naɗa Abubakar matsayin halifa, Imam Ali (A.S) da wasu sahabbai ba su amince da shi ba, sai dai cewa Imam Ali (A.S) bai yi amfani da ƙarfi wajen ƙwaton haƙƙinsa na halifan Annabi ba, sakamakon wasu dalilai da suka haɗa da rashin cikakken tallafi da mataimaka, tsoro kan rayuwar Ahlul-baiti da Musulmi, da kuma gujewa rushewar al'ummar Musulmi. Da wannan dalili ne ya yi shiru na tsawon shekaru 25.

Tare da wannan, a cewar malaman tarihi da malaman hadisi, a gaban waɗannan sauye-sauye da abubuwan da suka dinga faruwa da al'ummar Musulmi, Imam Ali ya shagaltu da tattara Kur'ani da ba da shawarwari ga halifofi a fagen yaƙoƙi na faɗaɗa daular Muslunci, ya kuma ba su shawarwari cikin warware matsalolin siyasa a wani lokaci na wannan zamani

Matsayi Da Muhimmanci

Shiru na tsawon shekaru 25 wani ɓangare ne daga rayuwar Sayyidina Ali (A.S) a zamanin halifofi uku, wanda ya kau da kai daga ƙwatar haƙƙinsa na halifancin Annabi da ƙarfi. Wannan shiru ya fara tun bayan wafatin Annabi (S.A.W) har zuwa lokacin da ya karɓi halifanci a shekara ta 35 bayan hijira.[1] Wasu marubuta suna ɗaukar shirun tsawon shekaru 25 na Imam Ali (A.S) a matsayin misali daga taƙiyyar Imamai[2] kuma wani nau'i ne daga taƙiyya mudarati (Taƙiyya ta gudananarwa)[3] Duk da cewa a zamanin shiru na tsawon shekaru 25, an hana Imam Ali (A.S) kujerar halifanci, amma daidai da abin da ya zo a wani hadisi daga Imam Rida (A.S) cikin tsawon shekaru 25 na shiru bai gushe ba yana nan a matsayinsa na Imami.[4]

Jawad Muhaddisi, mawallafin littafin Farhange Ghadir, jumlar "Shiru na shekaru 25" baya ɗaukarta jumla da ta dace a yi amfani da ita, saboda Imam Ali (A.S) bai yi shiru ba, bari dai a lokuta da daman gaske Imam Ali (A.S) ya tashi ya kawo dalilai da hujjoji kan tabbatar da cewa halifanci haƙƙi ne nasa ya kuma yi suka kan tsarin gwamnatin halifofi uku tare da yi musu nasiha[5] A cewar Rasul Jafariyan, masanin tarihi, haƙiƙa rashin jituwar Imam Ali (A.S) da masu hamayyarsa yana ƙara bayyana a fili a kowace rana, har ta kai ga ya haifar da matsaloli da alaƙarsa da su, daga cikin abubuwa da suke nuni kan haka, akwai harin da aka kai kan gidan Imam Ali (A.S), da yanke alaƙar da Faɗima ta yi da Shehunai biyu da shahadarta.[6] Kasancewar Imam Ali (A.S) yana ganin cewa karɓo halifanci a irin wannan lokaci da yanayi ba ya dacewa da manufofinsa na kiyaye addinin Musulunci da aikin Annabi (S.A.W) sai ya zama bai da wani zaɓi sai na zuba idanu da kame bakinsa.[7]

A cikin huɗubar Shiƙshiƙiyya Imam Ali (A.S) ya fito fili ya yi bayani batutuwa da suke da dangantaka da halifancin Annabi (S.A.W).[8] ya nuna kokensa game da halifancin halifofi uku da suka gabace shi[9] cikin wannan huɗuba an bayyana cikakken tarihin halifanci halifofi uku na farko a mahangar Imam Ali (A.S), dalilin yin shirunsa da abin da ya sa ya yarda ya karɓi halifanci bayan an nemi hakan daga gare shi, duka suna daga sauran batutuwa na asali da ya yi maganarsu a cikin wannan huɗuba.[10] a cewar wasu marubuta, mutane sun gano daraja da ƙimar Imam Ali (A.S) bayan shaida aibobi da gazawar gwamnatin halifofi uku, da wannan dalili ne suka kafe suka nace lallai sai Imam Ali (A.S) ya karɓi ragamar halifanci bayan kashe Usman.[11]

Bin sawu da kwaikwayon salon yin shiru na tsawon shekaru 25 na Imam Ali (A.S) da niyyar tabbatar da haɗin kai na Musulunci, yana matsayin larura ga Musulmi, wanda ta hanyarsa ne za su iya hana maƙiyan Musulunci samun iko kan Musulmi.[12]

Mene ne Dalilin Yin Shiru

A ra'ayin Shi'a duk da cewa Ali bin Abi Ɗalib (A.S) shi ne ya kasance farkon halifan Annabi,[13] amma domin kare muradun al'ummar Musulmi da haɗin kan Muslunci sai ya haƙura ya ba da haɗin kai tare da halifofi.[14] A ra'ayin Muhammad Taƙiyyu Mishabu Yazdi, a tsawon shekaru 25 da ya zaɓi yin shiru, zai iya shugabanci da mulki kan mutane kuma mulkinsa halastacce ne, amma sakamakon mutane ba su yi masa bai'a ba, kuma mulkinsa bai samu karɓuwa ba a wurinsu, shi kuma bai son ya mulki mutane ta hanyar nuna fin ƙarfi da tilastawa a kansu.[15]

Akasin wannan mahanga, Mahadi Bazargan da Mahadi Ha'iri Yazdi, daga malamai na Shi'a ma'abota bincike suna da ra'ayin cewa haƙƙin yin mulki da shugabanci kaɗai ya dora ne da yarda da kuma amincewa mutane, ba wai naɗi daga Allah da Annabawa da Imaman Shi'a ba.[16] bisa wannan fahimta tasu sun fassara shirun Imam Ali (A.S) bisa cewa mutane ba su zaɓe shi matsayin shugabansu ba.[17] Ahlus-Sunna suma suna da ra'ayin cewa batun halifancin Annabi yana hannun mutane, duk wanda suka zaɓa shine ake la'akari da shi matsayin shugaba kuma halifa.[18] Suna da ra'ayin cewa hatta shi kansa Imam Ali (A.S) bai yi imani da cewa Annabi ya zaɓe shi ya ayyana shi a matsayin halifansa a bayansa ba. Da wannan dalili ne, lokacin da aka kashe Usman, mutane suka nemi Ali (A.S) ya karɓi ragamar halifanci, yaƙi yarda ya karɓa.[19]

Rashin Mataimaka

A cikin huɗuba ta 26 a Nahjul Balaga, Imam Ali (A.S) ya bayyana cewa ɗaya daga cikin dalilansa na yin shiru tsawon shekaru 25 ya kasance rashin samun mataimaka.[20] haka nan akan asasin wata riwaya da aka naƙalto a cikin littafin Al-Amali Shaik Ɗusi daga Imam Hassan (A.S), cikinta ya bayyana cewa dalilin hijirar Annabi daga Makka zuwa Madina da shirun mahaifinsa tsawon shekaru 25 da kuma sulhun da ya yi tare da Mu'awiya, shi ne rashin mataimaka.[21]

Tsoron Hatsari Ga Rayuwar Ahlul-Baiti Da Musulmi

Imam Ali:

أَفْلَحَ مَنْ نَهَضَ بِجَنَاحٍ أَوِ اسْتَسْلَمَ فَأَرَاحَ هَذَا مَاءٌ آجِنٌ‏ وَ لُقْمَةٌ يَغَصُّ بِهَا آكِلُهَا وَ مُجْتَنِي الثَّمَرَةِ لِغَيْرِ وَقْتِ إِينَاعِهَا كَالزَّارِعِ بِغَيْرِ أَرْضِهِ.‏

Tarjama: Duk wanda ya tashi tare da taimako (magoya baya), zai ga fuskar tsira; in ba haka ba, sai ya miƙa wuya ya zauna cikin hutu. Domin wannan halifanci a irin wannan yanayi kamar ruwa ne marar daɗi kuma mara armashi, da kuma kamar lomar abinci ce da ke makale a maƙogwaro. Wanda kuma ya tsinka ƴaƴan itace tun ba su nuna ba, kamar manomi ne da ya zaɓi gonar wani domin ya yi shuka a cikinta.

Nahjul Balaga. Gyaran Subhi Salih, shekara 1993–1994 Miladiyya, juzu'i 5 shafi 52

A cikin huɗuba ta 26 Nahjul Balaga[22] da huɗuba ta 217 Nahul Balaga[23] Tsoron jefa rayuwar Ahlul-Baiti da Musulmi cikin hatsari ya kasance daga dalilan yin shirun Imam Ali (A.S) tsawon shekaru 25.[24] A cikin wata riwaya da Ibn Abil Al-Hadid daga masu sharhi na Nahjul Balaga kuma Ahlus-Sunna, ya naƙalto daga Imam Ali (A.S), cewa jin tsoro jefa rayuwar Musulmi cikin hatsari ya sanya shi yin shiru tsawon wannan lokaci.[25]

Rashin Yanayi Mai Kyau

Ibn Maisam Bahrani, marubucin Kitabu Misbahus Salikin, tare da daogara da huɗuba ta 5 Nahjul Balaga yana da ra'ayin cewa Ali Bin Abi Ɗalib (A.S) bayan taron Saƙifa, bai samu yanayi da ya dace ba da cikinsa zai iya motsawa domin ƙwato haƙƙinsa na halifanci, da wannan dalili ne, yake ganin cewa wannan lokaci bai dace da lokacin neman haƙƙi ba, kamar dai yadda bishiyar kayan marmari ba ta yin ƴaƴa a lokacin da bai dace ba.[26] Muhammad Taƙiyyu Jafari, ɗaya daga cikin masu sharhi na Nahjul Balaga shima yana da ra'ayin cewa kyakkyawan zaton da mutane suka yi wa juna da yaɗuwar jita-jitan cewa Imam Ali (A.S) ya amince da sakamakon da ya fito daga taron Saƙifa, sun hana mutane shirya kansu da tanadin yanayi na karɓar gwamnatin Imam Ali (A.S).[27]

Hana Rusgewar Al'ummar Musulmi

Shaik Mufid a cikin littafin Al-Fusulul Mukhtara ya bayyana cewa hana rarrabuwar kan Musulmi yana daga dalilin da ya sa Imam Ali (A.S) yin shiru.[28] Daidai da abin da ya zo a wata riwaya da ya naƙalto a cikin littafin Al-Amali, ya bayyana cewa babban dalili da ya sanya Imam Ali (A.S) ya kau da idanu daga karɓar haƙƙinsa na halifanci shi ne gudun rarrabuwar kan al'ummar Musulmi da kuma tsoron dawowar kafirci,[29] Kamar yadda aka yi ishara da hakan cikin wasiƙa ta 62 a cikin Nahjul Balaga.[30] Haka nan, a lokacin da matarsa Sayyida Faɗima (S) ta ƙarfafa shi ta motsa shi kan ƙwato haƙƙinsa na halifanci, Imam Ali (A.S) tare da ishara da fara kiransa sallah, ya nuna cewa tabbatar da wanzuwar addinin Muslunci ne ya sanya shi kame baki da yin shiru.[31]

Barazanar Hare-hare Daga Rumawa

Mahadi Pishwayi, ɗanshi'a masanin tarihi, barazanar yiwuwar hari daga ɓangaren Rumawa kan Musulmi suna daga dalilan da suka sanya Imam Ali (A.S) ɗaukar matakin yin shiru tsawon shekaru 25.[32] Rumawa suna ɗaukar Musulmi matsayin babbar hatsari gare su, da wannan dalili ne suka kasance suna jira da dakon duk wata dama domin ƙaddamar da hare-hare kan Musulmi, rikice-rikice cikin gida na Musulmi na iya zama wata babbar dama ga Rumawa.[33] A zamanin Annabi (S.A.W) Rumawa sau uku suna fuskantar Musulmi.[34]

Bin Salo da Tsarin Annabawa

Daidai da wata riwaya da aka naƙalto daga Imam Ali (A.S),[35] cikin amsa ga tambayar da aka yi masa me yasa ya yaƙi A'isha da Ɗalha da Zubairu, amma kuma bai yaƙi halifofi uku ba, ya ba su amsa da cewa dalilinsa na yin shiru shi ne kwaikwayon salon Annabawa shida, ma'ana Ibrahim (A.S), Luɗ (A.S), Yusuf (A.S), Musa (A.S), Haruna (A.S) da Muhammad (S.A.W), Su ma, na ɗan lokaci, sun zama tilas su yi shiru a gaban mutanen ƙasarsu.[36]

Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Shekaru 25 Da Matsayar Imam Ali (A.S)

Musɗafa Delshad Tehrani, ɗanshi'a masanin tarihi, ba ya ɗaukar shirun Imam Ali (A.S) na tsawon shekaru 25 a matsayin shiru mara amfani, kuma yana da ra'ayin cewa Imam Ali (A.S) ya ɗauki mataki da dabaru masu tasirin gaske a gaban sauye-sauye da muhimman abubuwan da suka faru cikin al'umma Musulmi.[37]

Tattara Kur'ani

Bayan wafatin Annabi (S.A.W), Ali (A.S) ya shagaltu da tattara Kur'ani cikin mus'hafi guda ɗaya.[38] wasu daga sahabbai ba su karɓi wannan Mus'hafi da Sayyidina Ali (A.S) ya tattara ba, da wannan dalili ne ya ɗauke wannan Kur'ani da ya haɗa daga hannun mutane.[39] tare da haka, Imam Ali (A.S) ya ba da goyon baya kan yunƙurin Usman na tattara Kur'ani da mai da shi kwafi ɗaya kacal, kuma bayan Imam Ali (A.S) ya zama halifa sai ya ci gaba da riƙo da aiki da Mus'haf Usman ya tattara.[40]

Futuhatul Islamiyya (Nasarorin Musulmi Cikin Yaƙe-Yaƙe Bayan Annabi)

Samfuri:Futuhat Na Musulmi Bisa rahotan Mas'udi, marubucin tarihi a cikin littafinsa Murujuz Zahab, lokacin da Umar ya nemi Imam Ali (A.S) ya shiga yaƙin Fatahu Iran, Ali (A.S) bai amsa ba,[41] tare da haka, a lokacin halifancin Abubakar da Umar, a wasu lokuta ya kasance yana ba su shawarwari.[42]

Kashe Usman

Bore da rikice-rikice da suka faru a zamanin gwamnatin Usman Bin Affan suna daga abubuwan da suka yi tasiri a shekaru 25 na mulkin halifofi uku.[43] A faɗar Rasul Jafariyan, haƙiƙa Imam Ali (A.S) ya amince da yawancin suka da ƙorafi da ake yi a kan Usman, amma a siyasance ya kasance yana adawa da kashe Usman kuma yana ganin hakan zai zama wata dama ga Mu'awiya a siyasance.[44] Ya kasance yana nasiha ga masu bore kan Usman tare da faɗakar da su kan kurakuransu.[45]

Ayyukan Imam Ali A Zamanin Shiru

Jafar Subhani, marja'in taƙlidi na Shi'a, ya lissafa ayyuka da Imam Ali (A.S) ya shagaltu da su a tsawon mulkin halifofi uku kamar haka:

  1. .Tafsirin Kur'ani da tarbiyantar da almajiransa kamar Ibn Abbas
  2. .Amsa tambayoyi malamai na duniya, musamman malaman Yahudawa da Nasara
  3. .Bayanin hukunce-hukunce sabbin abubuwa da suke faruwa
  4. .Ba da shawarwari ga halifofi uku cikin matsaloli da matsaloli na siyasa
  5. .Tarbiyantar da tsaftatattun mutane masu tsaftar zukata
  6. .Aiki domin lamintar da buƙatun talakawa.[46]

Maƙaloli Masu Alaƙa

Bayanin kula

  1. Rafi'i, Zindagiy Imaman, Pajuheshkadeye Tahqiqate Islami, shafi na 34-35.
  2. Razwanfar, Farhange Ahlaghiye Masumin, 2008, shafi na 400.
  3. Musawi, Mabaneye Fiqhiye Taqiyaye Mudarati, 2013, shafi na 120; Kamali Ardakani, Pajuheshi Piramune Iqtidayi Amme, Sazmane Hajji da Ziyara, shafi na 43.
  4. Sheikh Saduq, Uyuni Akhbaril Rida, 1959, juzu'i na 2, shafi na 81-82.
  5. Muhaddisi, Farhange Ghadir, 2007, shafi na 313-314.
  6. Ja'fariyan, Hayati Fikri-Siyasiye Imamane Shi'e, 2011, shafi na 58.
  7. Pishwai, Sirate Pishwayan, 2018, shafi na 71.
  8. Makarem Shirazi, Payame Imam, 2007, juzu'i na 1, shafi na 318.
  9. Bahrani, Sharhu Nahjil Balagha, 1984, juzu'i na 1, shafi na 251.
  10. Ku duba, Khutuba ta 3, shafi na 48-50.
  11. Zamani, Nahjul Balagha, 1990, juzu'i na 1, shafi na 134.
  12. Jabbari, "Itihad da Insijam, Zarurati Tarikhi", shafi na 4.
  13. Don ganin wasu hujjoji, misali duba: Sayyid Murtad, Al-Dhakhira, 1991, shafi na 437-483; Ibn Nubakht, Al-Yaqut, 1993, shafi na 80-86; Himsi Razi, Al-Munqidh Mina Al-Taqlid, 1992, juzu'i na 2, shafi na 299-365; Muhaghigh Lahiji, Gauhare Murad, 2004, shafi na 485-538.
  14. Danish, "Mu'amalar Imam Ali da Khalifai domin Haɗin Kan Musulunci", shafi na 110.
  15. Misbah Yazdi, Amsa ga Tambayoyi, 2012, juzu'i na 1, shafi na 29.
  16. Bazargan, Baa'sat (2), 2008, shafi na 298; Ha'iri, Hikima da Mulki, 2009, shafi na 209-212.
  17. Bazargan, Baa'sat (2), 2008, shafi na 299.
  18. Taftazani, Sharhul Maqasid, 1992, juzu'i na 5, shafi na 262.
  19. Ibn Abil Hadid, Sharhin Nahjul Balagha, 1984, juzu'i na 7, shafi na 34.
  20. Nahjul Balagha, gyaran Subhi Salih, 1994, Khutuba ta 26, shafi na 68.
  21. Sheikh Tusi, Al-Amali, 1994, shafi na 560.
  22. Nahjul Balagha, gyaran Subhi Salih, 1994, Khutuba ta 26, shafi na 68.
  23. Nahjul Balagha, gyaran Subhi Salih, 1994, Khutuba ta 217, shafi na 336.
  24. Pishwai, Sirate Pishwayan, 2018, shafi na 72.
  25. Ibn Abil Hadid, Sharhu Nahjil Balagha, 1984, juzu'i na 1, shafi na 308.
  26. Bahrani, Sharhu Nahjil Balagha, 1984, juzu'i na 1, shafi na 278.
  27. Ja'fari, Sharhu Nahjil Balagha, 1997, Khutuba ta 5.
  28. Sheikh Mufid, Al-Fusulul Mukhtara, 1993, shafi na 258.
  29. Sheikh Mufid, Al-Amali, 1993, shafi na 155.
  30. Nahjul Balagha, gyaran Subhi Salih, 1994, wasika ta 62, shafi na 451.
  31. Ibn Abil Hadid, Sharhu Nahjil Balagha, 1984, juzu'i na 11, shafi na 113.
  32. Pishwai, Sirate Pishwayan, 2018, shafi na 77.
  33. Pishwai, Sirate Pishwayan, 2018, shafi na 77.
  34. Pishwai, Sirate Pishwayan, 2018, shafi na 77.
  35. Sheikh Saduq, Ilalush Sharayi', 2006, juzu'i na 1, shafi na 149.
  36. Al-Qatit, Waqfatu ma'ad Dukturil Buti fi Masa'ilih, 1997, shafi na 112-114.
  37. Delshad Tehrani, "Intisabe 25 Sale Sukut Imam Ali (A.S.) ishtibah Ast", Kamfanin Labari na Tasnim.
  38. Ibn Nadim, Al-Fihrist, 1997, shafi na 45; Sajistani, Kitabul Masahif, 2002, shafi na 59.
  39. Ma'rifat, Ulumul Qur'ani, 2002, shafi na 122.
  40. Ma'rifat, Ulumul Qur'ani, 2002, shafi na 138.
  41. Mas'udi, Murujuz Zahab, 1989, juzu'i na 2, shafi na 310.
  42. Ranjbar, "Mawazi'e Imam Ali Dar Barabare Fatuhati Khulafa", shafi na 62.
  43. Ja'fariyan, Tarikhu Khulafa, 2015, shafi na 185.
  44. Ja'fariyan, Tarikhu Khulafa, 2015, shafi na 180.
  45. Misali duba: Ibn Asir, Al-Kamil, 2006, juzu'i na 3, shafi na 173.
  46. Subhani, "Farazhaye Hassas Az Zindigani daga Amirul Muminin (A.S.): Bisto Fanje Sale Sukut Cera?", shafi na 52-53.

Nassoshi

  • «انتساب ۲۵ سال سکوت، به امام علی(ع) اشتباه است»Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, ranar bugawa: 5 Fabrairu 2014, ranar ziyara: 4 Nuwamba 2019.
  • Al-Qatit, Hashim, Waqfatu ma'ad Dukturil Buti fi Masa'ilih, Beirut, Darul Mahajjatil Baidha, 1997.
  • Bazargan, Mahdi, "Akhirat Wa Khoda, Hadafe Bi'isat", Mujallar Kiyaan, lamba ta 28, hunturu 1995.
  • Delshadi Tehrani, Mustafa
  • Ha'iri Yazdi, Mahdi, Hikimat Wa Hukumat, Landan,Nashere Mooje Azadi, 2009.
  • Himsi Razi, Sadiduddin, Al-Munqid Mina Al-Taqlid, Qom, Intisharate Islami, 1992.
  • Ibn Abil Hadid, Abdulhamid bin Hibatullah, Sharhu Nahjil Balagha, Qom, Laburaren Ayatullah Mar'ashi Najafi, 1984.
  • Ibn Asir, Ali bin Abil Karam, Al-Kamilu fit Tarikh, Beirut, Daru Sadir, 2006.
  • Ibn Maitham Bahrani, Maitham bin Ali, Sharhu Nahjil Balagha, Tehran, Ofishin Buga Littattafai, bugu na biyu, 1984.
  • Ibn Nadim, Muhammad bin Ishaq, Al-Fihrist, Beirut, Darul Ma'rifah, 1997.
  • Ibn Nubakht, Ibrahim, Al-Yaqutu fi Ilmil Kalam, Qom, Laburaren Ayatullah Mar'ashi Najafi, 1993.
  • Ja'fari, Muhammad Taqi, Sharhu Nahjil Balagha, Tehran, Ofishin Buga Al'adun Musulunci, 1997.
  • Ja'fariyan, Rasul, Hayate Fikri Imamane Shi'eh Shi'a, Tehran, Nashre Ilmiy, 2011.
  • Ja'fariyan, Rasul, Tarikh Khulifai Az Raehlat Payambar Ta Zawale Umawiyyan,
  • Jabbari, Muhammad Rida «Hadin kai da daidaito larura ce ta tarihi»،Cikin Mujallar Marifat, lamba ta 114, watan Yuni 2007, shafi na 27
  • Jafar Subhani «فرازهایی حساس از زندگانی امیرمومنان(ع): بیست و پنج سال سکوت چرا؟»،Mujallar Wata-wata: Darussa daga Makarantar Musulunci, Shekara ta 16, Lamba ta 8, Yuli/Agusta 1975.
  • Kamali Ardakani, Hamid, Pajuheshi Piramune Iqtidayi Amme, Tehran, Sazmane Hajji da Ziyara, babu kwanan wata.
  • Ma'rifat, Muhammad Hadi, Ulumul Qur'ani, Qom, Al-Tamhid, bugu na hudu, 2002.
  • Ma'rifat, Muhammad Hadi, Ulumul Qur'ani, Qom, Cibiyar Al'adu da Buga ta Al-Tamhid, 2002.
  • Makarem Shirazi, Nasir, Sakon Imam Amirul Muminai, Tehran, Darul Kutubil Islamiyyah, 2007.
  • Mas'udi, Ali bin Husain, Murujuz Zahab wa Ma'adinil Jawahir, Qom, Darul Hijrah, 1989.
  • Misbah Yazdi, Muhammad Taqi, Amsa ga Tambayoyi, Qom, Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini, 2012.
  • Muhaddisi, Javad, Farhange Ghadir, Qom, Nashri Ma'ruf, 2007.
  • Muhaghigh Lahiji, Abdulrazzaq bin Ali, Gauhare Murad, Tehran, Nashri Saye, 2004.
  • Muhsin Rajebar «مواضع امام علی در برابر فتوحات خلفا»،
  • Musawi, Sayyid Muhammad Ya'qub, Mabanaye Fiqhiye Taqiyaye Mudarati, Qom, Cibiyar Fikihu ta Imani Ahlulbait, 2013.
  • Pishwai, Mahdi, Sirate Pishwayan, Qom, Cibiyar Imam Sadiq, 2018.
  • Rafi'i, Ali, Zindagiy Imaman, Tehran, Cibiyar Bincike ta Ilimin Musulunci, babu kwanan wata.
  • Razwanfar, Ahmad, Farhange Ahlaghiye Masumin, Qom, Cibiyar Binciken Musulunci ta Murya da Talabijin, 2008.
  • Sajistani, Abdullah bin Suleman, Kitabul Masahif, Al-Qahira, Al-Farouq Al-Haditha, 2002.
  • Sayyid Murtada, Ali bin Husain, Al-Dhakhira fi Ilmil Kalam, Qom, Daftar Nashr Islami, 1991.
  • Sayyid Radi, Muhammad bin Husain, Nahjul Balagha, gyaran Subhi Salih, Qom, Hijrat, 1994.
  • Sheikh Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-Amali, Qom, Kungirar Sheikh Mufid, 1993.
  • Sheikh Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-Fusulul Mukhtara, Kungirar Sheikh Mufid, 1993.
  • Sheikh Saduq, Muhammad bin Ali, Ilalush Sharayi', Qom, Kitabfurushi Davari, 2006.
  • Sheikh Saduq, Muhammad bin Ali, Uyuni Akhbaril Rida, Tehran, Nashri Jahan, 1959.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hasan, Al-Amali, Qom, Darus Saqafah, 1994.
  • Taftazani, Mas'ud bin Umar, Sharhul Maqasid, Qom, Al-Sharif al-Radi, 1992.
  • Zamani, Mustafa, Nahjul Balagha, Qom, Al-Zahra, 1990.
  • Isma'il Danesh، «تعامل امام علی(ع) با خلفا در جهت وحدت اسلامی»، A cikin Mujallar Andishe-ye Taqrib, lamba ta 4, kaka 2005.