Daƙiƙa:Khumusin Ribar Sana'o'i Da Kasuwanci
Wannan wani rubutu ne na siffantawa game da wata ma'ana ta fiƙihu, kuma ba za ta iya zama ma'auni ga ayyukan addini ba, domin ayyukan addini sai a koma zuwa ga wasu madogaran na daban. |
| Sashe dagaHukunce-hukuncen Aiki da na Fiƙihu |
|---|
Khumusin ribar sana'o'i da kasuwanci shi ne fitar kashi ɗaya bisa biyar na ribar da aka samu daga kasuwanci da sauran hanyoyin samun kuɗi.[1] A fiƙihun Shi'a, biyan wannan khumusi wajibi ne bayan an cire kuɗaɗen buƙatun rayuwa na shekara da aka saba yi (mu'una).[2]Wannan hukunci ya shafi kuɗaɗen shiga da aka samu daga: Kasuwanci, noma, masana'antu, rubuce-rubuce, ɗinki, hayar dukiya, da sauran sana'o'i da ayyukan samun kuɗi.[3] Sai dai malamai sun sami saɓanin ra'ayi kan ko khumusi ya wajaba a kan abubuwa kamar: sadaki, kyauta, lambar yabo ko kyautar gasa, da gado.[4]
Malaman fiƙihu na Ahlus-Sunna ba sa ɗaukar ribar sana'o'i da kasuwanci a matsayin abin da khumusi ya wajaba a kansa.[5] A gefe guda kuma, malaman Shi'a suna kafa hujjar wajibcin khumusi ne da ruwayoyin Ahlul-Baiti (A.S)[6] da kuma ayar khumusi. Suna ganin cewa kalmar ghanima da ta zo a cikin ayar tana da ma'ana mai faɗi, wadda ta ƙunshi kowane irin riba da kuɗin shiga.[7]
A cewar wasu masu bincike, duk da cewa babu wani rahoto a cikin littattafan tarihi da ya nuna cewa an karɓi khumusin ribar sana'o'i da kasuwanci a zamanin Annabi Muhammad (S.A.W) da Imam Ali (A.S),[8] malaman Shi'a suna ganin cewa wajibcin khumusi ya tabbata tun farkon Musulunci, amma an jinkirta aiwatar da shi saboda talaucin da Musulmi suke ciki a lokacin.[9]
Bisa ra'ayin malaman fikihu, ana biyan khumusin ribar sana'o'i da kasuwanci ne bayan shekara guda ta cika daga farkon shekarar khumusi.[10] Ita kuma shekarar khumusi tana farawa ne daga lokacin da mutum ya samu kuɗin shiga na farko ko kuma ya fara harkar tattalin arzikinsa.[11]
Bayanin kula
- ↑ Mu'assase Da'iratul Ma'arifil Fiƙhil Islami, Farhange Fiƙh Mutabiƙ Mazhab Ahli al-Bait (A.S), juzu'i na 1, shafi na 364.
- ↑ Ƙummi, Al-Gayatul Ƙuswa, juzu'i na 2, shafi na 258; Makarim Shirazi, Anwarul Faƙaha, Kitab al-Khums wa al-Anfal shafi na 290.
- ↑ Hasanpur, «Muta'allaƙ Khums Arbah al-Makasib ta Mutlaƙ Fa'ida,» shafi na 56; Bani Hashimi Khomaini, Taudih al-Masa'il Maraji, shafuffuka na 7–125; Bani Hashimi Khomaini, Risalaye Taudih al-Masa'il Maraji, shafuffuka na 468–498.
- ↑ Bani Hashim Khomaini, Taudih al-Masa'il Maraji, shafi na 7–125.
- ↑ Ƙurɗubi, Al-Jami' li Ahkamil Kur'an, juzu'i na 8, shafi na 1.
- ↑ Muntaziri Najafabadi, Mabani Fiƙhi Hukumate Islami, fassarar Salati da Shukuri, juzu'i na 6, shafi na 197.
- ↑ Ɗabrisi, Majma'ul Bayan, juzu'i na 4, shafi na 468; Musawi Golpaigani, Majma al-Masa'il, juzu'i na 1, shafi na 390.
- ↑ Muntaziri Najafabadi, Mabani Fiƙhi Hukumate Islami, fassarar Salati da Shukuri, juzu'i na 6, shafi na 142.
- ↑ Makarim Shirazi, Anwarul Faƙaha, Kitab al-Khums wa al-Anfal, shafi na 291.
- ↑ Bani Hashimi Khomaini, Risalaye Tawdih al-Masa'il Maraji, shafuffuka na 468–498.
- ↑ Bani Hashimi Khomaini, Risalaye Taudih al-Masa'il Maraji, shafuffuka na 468–498.
Nassoshi
- Bani Hashimi Khomaini, Sayyid Muhammad Hasan, Taudih al-Masa'il Maraji, Qom, Daftare Intisharate Islami wabaste bi Jami'ah-ye Mudarrisin-i Hauzeye Ilmiyya Qom, 1392Sh.
- Hasanpur, Dawud, Muta'allaƙ Khums Arbah al-Makasib ta Mutlaƙ Fa'ida, a cikin Mujallar wata uku-uku ta Pajuheshi dini (Binciken Addini,) lamba ta 33, kaka da hunturun 1395Sh.
- Makarim Shirazi, Nasir, Anwarul Faƙaha, Kitab al-Khums wa al-Anfal, Qom, Madrase Imam Ali bin Abi Ɗalib, 1416H.
- Mu'assase Da'iratul Ma'arifil Fiƙhil Islami, Farhange Fiƙh Mutabiƙ Mazhab Ahli al-Bait (A.S), ƙarƙashin kulawar Sayyid Mahmud Hashimi Shahrudi, Qom, Cibiyar Da'iratul Ma'arifil Fiƙhil Islami, 1382Sh.
- Muntaziri Najafabadi, Husain Ali, Mabani Fiƙhi Hukumate Islami, fassarar Mahmud Salawati da Abul Fadl Shukuri, Qom, Cibiyar Kayhan, 1409H.
- Musawi Golpaigani, Sayyid Muhammad Rida, Majma'ul Masa'il, Qom, Darul Kur'anil Kareem, 1409H.
- Ƙummi, Shaik Abbas, Al-Gayatul Ƙuswa Fi Sharhi Al-Urwatul Wusƙa, Qom, Cibiyar Subh Piruzi, 1423Sh.
- Ƙurɗubi, Muhammad Bin Ahmad, Al-Jami' li Ahkamil Kur'an, Tehran, Mabugar Nasir Khusraw, 1364Sh.
- Ɗabrisi, Fadlu Bin Hassan, Majma'ul Bayan Fi Tafsiril Kur'an, Beirut, Cibiyar Al-A'lami Lil Maɗbu'at, 1415H.