Al-Ma'ul Kur
Wannan wani rubutu ne na siffantawa game da wata ma'ana ta fiƙihu, kuma ba za ta iya zama ma'auni ga ayyukan addini ba, domin ayyukan addini sai a koma zuwa ga wasu madogaran na daban. |
| Sashe dagaHukunce-hukuncen Aiki da na Fiƙihu |
|---|
Al-ma'ul Kur ko Ruwan Kur shi ne wani ƙayyadadden adadin ruwa mai tsarki wanda idan ya haɗu da najasa ba ya zama najasa. Haka kuma, ana iya amfani da shi wajen tsarkake abubuwan da suka gurɓata da najasa.
Adadin ruwan kur shi ne ruwan da girmansa ya kai zira'i uku da rabi a tsawo, zara'i uku da rabi a faɗi, da zara uku da rabi a zurfi. Malaman fikihu sun ƙiyasta nauyinsa tsakanin kilogiram 376 zuwa 480.
Idan wani abu mai najasa ya taɓa ruwan kur, ruwan ba ya zama najasa, sai dai idan launinsa, ƙamshinsa ko ɗanɗanonsa ya sauya saboda najasar.
Abubuwan da suka gurɓata da najasa suna tsarkaka ne da wankewa sau ɗaya a cikin ruwan kur.
Girma Da Nauyin Ruwan Kur
Bisa ga mashahurin ra'ayin malamai na fiƙihu, adadin ruwan kur shi ne ruwan da girmansa ya kai zara'i uku da rabi a tsawo, zara'i uku da rabi a faɗi, da zara'i uku da rabi a zurfi.[1]
Game da nauyin ruwan kur, akwai ra'ayoyi daban-daban, ciki har da: Kilogiram 376.740, kilogiram 377, da kilogiram 384.[2]
Haka kuma, an ce idan nauyin ruwan ya kai kilogiram 480, to bisa ra'ayin dukkan malamai wannan ruwa tabbas ruwan kur ne.[3]
Hukunce-hukuncensa
- Ana tabbatar da cewa ruwa kur ne ta hanyar: mutum ya sami tabbatacciyar masaniya (yaƙini), ko shaidar maza biyu masu adalci. Amma idan mutum guda ɗaya mai adalci ko amintacce ne kawai ya ba da labarin cewa ruwan kur ne, malamai sun yi saɓani kan ko hakan ya isa wajen tabbatar da kasancewarsa kur.[4]
- Ruwan kur yana daga cikin ruwa muɗlaƙ kuma yana daga cikin ruwan da ake yin tsarkakewa da shi.[5] Ba ya zama najasa idan ya haɗu da najasa, sai dai idan launinsa, ƙamshinsa ko ɗanɗanonsa ya canza sakamakon haɗuwar da najasar.[6] Idan hakan ta faru, ba zai sake zama mai tsarki ba sai idan canjin ya gushe kuma ya haɗu da wani ruwa mai yawa ya gaurayu da shi.[7]
- Ana tsarkake abubuwa masu najasa da wankewa sau ɗaya a cikin ruwan kur. Sai dai malamai sun yi saɓani kan ko:
wankewa sau ɗaya ya isa wajen tsarkake abin da fitsari ya gurɓata, da kuma wajen tsarkake kwano mai najasa. Haka kuma sun yi saɓani kan ko ya zama dole a matse abubuwan da ruwa ke shiga cikinsu, kamar tufafi, bayan an wanke su da ruwan kur.[8] Duk da haka, mashahurin ra'ayi shi ne cewa abin da fitsari ya gurɓata da kuma kwano mai najasa ba sa buƙatar a wanke su fiye da sau ɗaya.[9]
- Idan aka yi shakka ko ruwa yana nan a matsayin kur ko a'a, za a ɗauke shi a matsayin ruwan kur. Amma idan aka yi shakka ko ƙaramin ruwa ya kai adadin kur ko bai kai ba, to za a ci gaba da ɗaukarsa a matsayin ƙaramin ruwa.[10]
- Idan ƙaramin ruwa ya zama kur, sannan ya taɓa najasa, amma ba a san ko ya taɓa najasar ne bayan ya zama kur ko kafin ya zama kur ba, to wannan ruwan mai tsarki ne.[11]
- Haka kuma, idan ruwa ya kasance kur, daga baya ya ragu ya zama ƙaramin ruwa, sannan ya haɗu da najasa, amma ba a san ko haɗuwar ta faru kafin ya ragu ko bayan ya ragu ba, to wannan ruwan ma ana ɗaukarsa mai tsarki ne.[12]
Bayanin kula
- ↑ Najafi, Jawahirul Kalam fi Sharhi Shara'i'il Islam, juzu'i na 1, shafuka na 172–173.
- ↑ Bani-Hashimi Khomaini, Tawdih al-Masa'il Maraji', mas'ala ta 16, juzu'i na 1, shafuka na 38–39.
- ↑ Bani-Hashimi Khomaini, Tawdih al-Masa'il Maraji, mas'ala ta 16, juzu'i na 1, shafuka na 38–39.
- ↑ Tabataba'i Yazdi, al-Urwa al-Wusƙa, juzu'i na 1, shafi na 46.
- ↑ Tabataba'i Yazdi, al-Urwa al-Wusƙa, juzu'i na 1, shafi na 26.
- ↑ Najafi, Jawahirul Kalam fi Sharhi Shara'i'il Islam, juzu'i na 1, shafuka na 153–154.
- ↑ Tabataba'i Yazdi, al-Urwa al-Wusƙa, juzu'i na 1, shafi na 43.
- ↑ Najafi, Jawahirul Kalam fi Sharhi Shara'i'il Islam, juzu'i na 1, shafuka na 113–114.
- ↑ Musawi Sabzawari, Muhazzab al-Ahkam fi Bayan al-halal wa al-haram, juzu'i na 18, shafuka na 33 da 40.
- ↑ Tabataba'i Yazdi, al-Urwa al-Wusƙa, juzu'i na 1, shafuka na 36–37.
- ↑ Khomaini, Tahrir al-Wasila, juzu'i na 1, shafi na 14.
- ↑ Khomaini, Tahrir al-Wasila, juzu'i na 1, shafi na 14.
Nassoshi
- Bani-Hashimi Khumayni, Muhammad hasan, Tawdih al-Masa'il Maraji Muɗabiƙ Ba Fatawa Dowardah Nafar Az MaTaƙlid , wallafen Musulunci mai alaƙa da Ƙungiyar Malaman Makarantar Hauzar Ilimi ta Qum, 1378 Sh.
- Khomaini, Ruhullah, Tahrir al-Wasila, bincike da wallafar Cibiyar Tsarawa da Wallafa Ayyukan Imam Khomaini (q.s.), Tehran, Cibiyar Uruj, bugu na farko, 1392 Sh / 1434 AH.
- Tabataba'i Yazdi, Sayyid Kazim, al-Urwa al-Wusƙa fima Ta'ummu bih al-Balwa (Muhashi), Qum, Ƙungiyar Malaman Hauzar Ilimi ta Qum., 1419 AH.
- Musawi Sabzawari, Sayyid Abd al-A'la, Muhazzab al-Ahkam fi Bayan al-halal wa al-haram, Qum, Cibiyar al-Manar, 1413–1417 AH.
- Najafi, Muhammad Hassan, Jawahirul Kalam fi Sharhi Shara'i'il Islam, Beirut, Gidan Raya Gadon Larabawa, 1404 AH.
- Hashimi Shahrudi, Sayyid Mahmud, Farhang-e Fiqh Muɗabiƙ Mazhab Ahl al-Bayt (a.s.), Qum, Cibiyar Kundin Ilimin Fikhun Musulunci Bisa Mazhabar Ahlul Baiti (a.s.), 1382 Sh.