Jump to content

Alwalar Jabira

Daga wikishia

Alwalar Jabira (Larabci: وضوء الجبيرة) daya daga cikin nau'ukan Alwala ce, idan ya kasance cikin daya da sassan jikin mutum ciwo ko wata karaya za ta hana shi ya wanke wurin ko shafa, to ya zama dole ya yi Alwalar Jabira, wurin zai shafa ko wankewa sai ya wadatu da shafa kan bandejin ko kan kyalllen da aka lullube ciwon da shi.

Nazarin Ma'ana

Ana kiran duk wani abu da ake daure ciwo da shi sawa'un bandeji ne ko kyalle,[1] duk lokacin da daya daga sassan jikin Mai Alwala ya samu larura ta ciwo ko karaya wanda hakan ya hana shi wanke wurin ko shafa to a irin wannan hali zai shafa bandeji ko kyalle da kan ciwon da danshi ruwan Alwala da ya yi ragowa a[2] hannunsa bawai sai ya wanke ko shafa asalin kan fatar gabar ba, da wannan dalilin ne ake kiran wannan nau'in Alwala da sunan Alwalar Jabira (Alwalar mai larura) sakamakon Mai Alwala ya shafi kan bandeji da sauran danshin hannunsa ake kiran wannan Alwala da Alwalar Jabira.

Hukunce-hukunce

idan ya zamanto daya da sassan jikin Mai Alwala ya samu larurar ciwo ko karaya hakan ya hana shi wanke wurin ko shafa, wajibi kansa ya yi Alwalar Jabira wurin wankewa ko shafa gabar da ke da ciwo sai ya wadatu da shafa kyallen da yake lullube da ciwo,[3] ana yin Alwalar jabira ne idna ya kasance cire kyallen ko bandejin don wankewa ko shafa asalin gabar zai cutar da Mai Alwala, ko kuma kai tsaye ba zai iya kwarara ruwa ya kai ga fatarsa ba[4] A wasu wuraren Taimama na zama wajibi maimaikon Alawala, cikin su akwai idan ya zamanto babu ishashen lokacin da za ai Alwala ayi salla cikin lokaci[5] ba tareda rasa wata raka'a a salla ba, na biyu: idan ya zamana babu ruwan Alwala ko kuma amfani da ruwan zai cutar da jikin Mai Alwala, a wannan hali zai yi Taimama ne maimakon Alwala[6] wanda ya yi Wankan Janaba ba sai ya yi Alwala ba domin sallah wankan ya wadatar shi ne mayin Alwalar.[7]

Bayanin kula

  1. Fallahzadeh, Darasnameh Ahkam Mubtala be Hujjaj, 2009, shafi na 37.
  2. Darasnameh Ahkam Mubtala be Hujjaj, 2009, shafi na 37-38
  3. Darasnameh Ahkam Mubtala be Hujjaj, 2009, shafi na 37-38
  4. Fallah Zadeh Ahkam dini,1386. shafi na 47-48
  5. Fallah Zadeh Ahkam dini,1386. shafi na 46
  6. Ibn Idris Hali, Al-Sarair, 1410 ƙ., Kashi na 1, shafi na 135.
  7. Fallah Zadeh Ahkam dini,1386. shafi na 57

Nassoshi

  • Ibn Idris Hali, Muhammad Ibn Ahmad, Al-Saraer, ƙum, Al-Nashar al-Islami Foundation na Jama’ah al-Madrasin, bugu na biyu, 1410H.
  • Fallahzadeh, Mohammad Hossein, Akhmat Din, Tehran, Mashaar, 2013.
  • Fallahzadeh, Mohammad Hossein,Darasnameh Ahkam Mubtala ben Hujjaj, Tehran, Mashaar, 2009.