Hadasul Asgar

Daga wikishia
Risala Ilmiyya
Wannan ƙasida ce mai bayyanawa game da mafhumin fiƙihu. ba zai iya zama ma'auni na ayyukan addini ba. Koma zuwa wasu tushe don ayyukan addini.

Hadasul Asgar (ƙaramin Kari) (arabic: الحدث الأصغر) shi ne abin da yake karya Alwala, ko wani hali wanda kan kufansa ne alwalar mutum take karyewa yake kuma hana mutum yin wasu ayyuka da dole sai da ɗahara da alwala ake yinsu. [1] Malaman fiƙihu sun kasa hadasi zuwa gida biyu, Hadasul Akbar da Hadasul Asgar, (ƙaramin Kari) shi ne abin da yake karya Alwala, abubuwan da suke karya Alwala sune: fitowar fitasri, fitowar kashi, fitowar iska daga babban hanji daga cikin mutum, bacci da yake hana gani da ji, abubuwan da suke tafiyar da hankalin mutum, misalin tabuwar hankali, buguwa da maye, suma da kuma ƙaramar istihada, [2] Hadasi, shi ne abin da yake zama sababin karyewar ɗahara, [3] ƙari kan haka, hadasi a cikin zantukan Malaman fiƙihu ana amfani da kalmar kan wani hali da yake zuwa sakamakon wasu sabubba misalin fitar fitsari, kashi, maniyyi, haila, da kuma taɓa gawa, da yake zama sababin hana yin wasu ayyuka da ba a yinsu dole sai tare da ɗahara, daga jumlarsu alwala da wanka. [4] cikin risalolin fiƙihu na ibada an yi magana dangane da hadas, [5] ana kiran wanda hadasi ya faru da shi da suna Muhdis. [6]

Bayanin kula

  1. Mu'assaseh Da'iratul Alm-Marif Fikh, Farhang Fiqh, 2007, juzu'i na 3, shafi na 246-248.
  2. Faiz Kashani, Rasa'il, 1429 AH, Juzu'i na 2, Rasalah 4, shafi na 22
  3. Mu'assaseh Da'iratul Alm-Marif Fikh, Farhang Fiqh, 2007, juzu'i na 3, shafi na 246
  4. Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 63; Muassaseh farhang Fikh, 2007, juzu'i na 3, shafi na 246.
  5. Misali duba: Sheikh Ansari, Kitabul Tahara, 1415 Hijira, juzu'i na 4, shafi:43.
  6. Mu'assaseh Da'iratul Alm-Marif Fikh, Farhang Fiqh, 2007, juzu'i na 3, shafi na 246

Nassoshi

  • Faiz Kashani, Mohammad Mohsen, Rasa'il Faiz Kashani, Binciken Behzad Jafari, Tehran, Makarantar Shahid Motahari, 1429 AH.
  • Muassaseh Da'iratul Al-marif Mutabik Mazhab Ahlul-baiti, karkashin kulawar Sayyid Mahmoud Hashemi Shahroudi, Qum, Mu'assasar Shari'a ta Musulunci, kan Mazhabar Ahlul-Baiti, 1426H.
  • Najafi, Mohammad Hasan, Jawaher al-Kalam fi Sharh Shar'e al-Islam, Abbas Quchani da Ali Akhundi suka gyara, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1404H.
  • Sheikh Ansari, Morteza, Kitab al-Tahara, Qum, World Congress of Honoring Sheikh Azam Ansari, Qom, 1415 AH.