Alwalar Irtimasi

Daga wikishia

Alwalar Irtimasi daya daga cikin hanyoyin yin Alwala ne bayan an daura niyya [1] za a fara da tsoma fuska a ruwa [2] sai kuma hannuwa duka da niyyar Alwala, haka kuma ya halasta Mai Alwala ya fara shigar da fuskarsa a ruwa daga baya sai ya kulla niyya shigarwa amma ba zai fito da ita sai bayan kulla niyya, [3] a cikin Alwalar Irtimasi bayan an fito da fuska da hannuwa daga cikin ruwa sai ayi shafar kai[4]

Irtimasi Isdilahi ne na fikihu da yake dauke da ma’anar nutsar da kai ko wani sassan jiki cikin ruwa [5] kiyaye jerantawa a Alwalar Irtimasi bai da banbanci da na Alwala wacce ba ta Irtimasi ba, ana farwa da fuska sai a tsallaka hannun dama sai kuma na hagu 1. Cikin Alwalar Irtimasi ana farawa nitsar da saman fuska saman goshi zuwa kasan fuska, haka hannuwa ma ana fara da saman hannu zuwa geffan yatsu [6] a fatwar Imam Komaini a Alwalar Irtimasi sau biyu kadai zaka nutsar da fuska da hannuwa cikin ruwa, na farko wajibi na biyu halas, baya halasta ayi fiye da sau biyu [7] wanke wasu ba’arin gabbai ta hanyar Irtimasi tareda kiyaye jerantawa ya halasta. [8] Wasu Malaman Fikihu sun ce amfani da sauran danshin ruwa wanke hannuwa don shafar kai sharadi ne wanda rashin kiyaye shi na bawa Alwalar Irtimasi.

 • Imam Komaini ya tafi kan cewa da ruwan Alwalar ne za a shafi kai a iya yanayin kulla niyya lokacin da aka shigar da hannuwa a ruwa bayan nan sai a kuduri niyya sannan a jawo su waje.[9]

Assayid Abu Kasim Kuyi da Mirza Jawad Tabrizi daga Masana fikihun Shi’a sun tafi kan cewa ba zai yiwu a wanke hannun hagu ta hanyar Irtimasi ba.[10]

 • Assayid Sistani daga Maraji’an Taklidi ya tafi kan cewa shafa da danshin hannu bai da wata matsala, sai dai cewa hakan ya sabawa aiki da Ihtiyadi.[11]
 • Shaik Nasir Mukarim Shirazi daga Maraji’an Taklidi ya tafi kan cewa Mai Alwala bayan ya fito da hannunsa daga ruwa dole ya kudurci niyya matukar dai akwai sauran ruwa a hannunsa ta yana cikin yankin Alwala [12]

Bayanin kula

 1. Mirzai Qomi, Jame al-Shatt, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 32.
 2. Behjat, Tauzihul Masa'il, 1428H, shafi na 53.
 3. Imam Khumaini, Tauzihul Masa'il, 1426H, shafi na 61
 4. Khamenei, Ajuba al-Istaftaat, 1424H, shafi na 21.
 5. Muassashe Maref Islami Fiqh, Farhang Fiqh, 1426 AH, juzu'i na 1, shafi na 346.
 6. Makarem Shirazi, Resalhe Tauzihul Masa'il, 1429H, shafi na 60.
 7. Imam Khumaini, Tauzihul Masa'il (Mohshi), 1424H, juzu'i na 1, shafi na 199.
 8. Muassaseh Maref Islami Fiqh, Farhang Fiqh, 1426 AH, juzu'i na 1, shafi na 347.
 9. Imam Khumaini. Risalatu Najat al-Abad, 2005, shafi na 20.
 10. Imam Khumaini, Tauzihul Masa’il (Mohshi), 1424H, juzu’i na 1, shafi na 160.
 11. Imam Khumaini, Tauzihul Masa’il (Mohshi), 1424H, juzu’i na 1, shafi na 160
 12. Imam Khumaini, Tauzihul Masa’il (Mohshi), 1424H, juzu’i na 1, shafi na 161

Nassoshi

 • Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Tauzihu Masa'il (Mohshi), (tare da fatawowin manyan malaman fikihu), Kum, Jamia Madrasin, 1424H.
 • Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Tauzihu Masa'il, Mohaghegh, Muslim Qolipour Gilani, Bija, Bina, 1426H.
 • Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Risala Najat al-Abad, Tehran, Imam Khumaini Editing and Publishing Institute, bugu na biyu, 1385.
 • Behjat, Mohammad Taqi, Tauzihu Masa'il , Qum, Shafaq Publications, 1428H.
 • Khamenei, Ali, Ajwaida Istifta'at, Qum, Cibiyar Buga Ayatullah Khamenei, 1424H.
 • Makarem Shirazi, Nasser, Tauzihu Masa'il, Qum, wallafe-wallafen makarantar Imam Ali Ibn Abi Talib, 1429H.
 • Mirzai Qomi, Abu al-Qasim bin Mohammad Hasan, Jami al-Shatt fi Ajuba al-Asthalat, Tehran, Kayhan, 1413 AH.
 • Mu'assaseh Fikihi Islami, farhang Fiqh Ahlul-Baiti ta ruwaito, karkashin kulawar: Mahmoud Hashemi Shahroudi, Qum, Cibiyar Encyclopaedia Musulunci, 1426 Hijira.