Zobe
Zobe (Larabci:خاتَم) ko Hatimi wani ƙarfe ne da aka yi masa Ado da Dutse mai daraja da ake sanya shi a hannu, kan asasin abin da ya zo daga riwayoyi haƙiƙa sanya zobe yana daga cikin sunnar Annabi (S.A.W), cikin fiƙihu an yi bayanin hukunce-hukuncen zobe, kan asasin riwayar da aka naƙalto daga Imam Hassan Askari (A.S), haƙiƙa sanya zobe a hannun dama yana daga Alamomi guda biyar na gane Mumini, cikin riwayoyin Shi’a an yi wasicci da nau’in Zoben da za a sa haka kuma nau’in rubutun da zai kasance kan Zoben misalin Kalmar (Al-Mulku lillahi) da (Hasbiyallah), ƴan Shi’a suna sassaƙa rubutun kalmomi misalin (La’ilaha illallah) , (Muhammad Nabiyullahi) da (Ali waliyullah) a saman Zobunansu Ana amfani da Zobe domin yin Tambarin Hatimi a jikin wasiƙa, haƙiƙa Annabi (S.A.W) ya yi amfani da wannan hanya, hakama Malaman Shi’a sun yi amfani da ita matsayin hanya Hattama wasiƙa.
Matsayi Da Muhimmanci
Cikin littafin Farhang Fiƙhu Islami, zoben da aka yi bayani kansa yawancinsu zobe ne daga Ma’adani na ƙarfe ya kuma tattaro wanda aka yi masa ado da dutse mai daraja da wanda babu ado jikinsa. [1] a wasu ba’arin riwayoyi ya zo cewa sanya zobe yana daga sunnar Annabi (S.A.W) [2] kuma Alama ce ta ɗan Shi’a [3] da Alama ta Muminai [4] Malamai suna cewa sanya Zobe a hannun dama yana daga cikin alamomi da aka san ƴan Shi’a da su. [5] a cikin babukan daban-daban na fiƙihu Misalin babin sallah, [6] Hajji, [7] Jihadi, [8] magana dangane da sanya Zobe ta zo.
Imam Hassan Askari (A.S)
Alamomin Mumini abubuwa guda biyar ne:
- yin Sallolin Farilla na kowacce rana tareda Nafilfilin dare da rana.
- Ziyaratu Arba’in
- Sanya Zobe a hannun Dama.
- bayyanar da karatun Bismillah.
- ɗora Goshi kan ƙasa a Halin Sujjada.
Tusi, Tahzeeb Al-Ahkam, shekara ta 1407 h ƙamari, j 6 sh na 52
Samfuran Zobunan Da Imamai Suke Sanyawa
Kan asasin Riwayoyi daga litattafan Shi’a, [9] da Ahlus-Sunna, [10] an naƙalto cewa Imam Ali (A.S) a lokacin da yake halin Ruku’u cikin sallah ya yi kyautar Zobe ga wani Talaka, wannan Waki’a ta shahara da Waki’ar Kyautar Zobe, haka kuma kan asasin abin da ya zo cikin littafin Lahuf na Ibn ɗawus wanda ya mutu a shekara ta 664 h ƙamari, ya naƙalto cewa Imam Husaini (A.S) a lokacin da ya yi shahada ya kasance yana sanye da Zobe, sai Bajdalu Bn Sulaimi Kalabi daga Dakarun Umar Bn Sa’ad ya gutsire yatsan Imam Husaini (A.S) domin ya cire Zoben daga jikin yatsan Imam,. [11] cikin riwayar da aka naƙalto an tambayi Imam Kazim (A.S) kan dalilin da ya sa Imam Ali (A.S) sanya Zobe a hannun dama, sai ya bada amsa ya ce: dalilin shi ne kasancewar Imam Ali (A.S) Jagoran Madamaita (Ashabul Yamin) a bayan Annabi (S.A.W). [12]
Buga Tambari Kan Wasiƙu
Buga tambari kan wasiƙu da Zobe yana daga sunnonin Muslunci. [13] ana ce Annabi (S.A.W) a ƙarshe-ƙarshen shekara 6 ya bada umarnin ƙera Zobe domin amfani da shi cikin buga tambarin Hatimi kan wasiƙun da ake aikawa Manya-manyan Sarakuna. [14] aiki da sunnar tambarin Zobe kan wasiƙu an naƙalto shi daga Malaman Shi’a. [15] da wannan dalili ne ake kiran Zobe da sunan Hatimi. [16]
Jinsin Zobe Da Adon Rubutun Da Ake Yi A Kansa
Cikin riwayoyin Shi’a Magana ta zo dangane da Jinsin Zobe da nau’in Adon da ake masa da rubutun da ake sassaƙawa a kansa. [17] Jinsin Zobe: a cikin ba’arin wasu riwayoyi ya zo cewa jinsin Zoben Annabi (S.A.W) ya kasance daga ƙarfen Azurfa. [18] sannan cikin ba’arini wasu riwayoyi an yi wasicci da amfani da wasu nau’ukan Duwatsu masu daraja kamar misalin Aƙiƙ, [19] Fairuz, [20] Yaƙutu, [21] Zumrad. [22] haka kuma cikin littafin Wasa’ilul Al-Shi’a akwai riwaya da ta zo da ishara kan zagayen Zoben Annabi (S.A.W) da kasancewar Adon samansa Baƙi. [23] Zanen jikin Zobe: dangane da Zanen da ake sassaƙawa a saman Zobe an naƙalto riwaya daga A’imma (A.S) [24] a wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) ya zo cewa Zanen rubutun saman Zoben Annabi (S.A.W) ya kasance Kalmar (Muhammadur Rasulillahi). [25] zanen saman Zoben Imam Ali (A.S) ya kasance Kalmar (Al-Mulku Lillahi) zanen saman Zoben Imam Baƙir (A.S) ya kasance Kalmar (Al-Izzatu Lillahi), zanen saman Zoben Imam Kazim (A.S) ya kasance Kalmar (Hasbiyallah Hafizi) [26] da kuma Kalmar (Al-Mulku Lillah Wahadahu) [27] haka zalika an bada rahoton kan cewa kalmomin (Muhammadu Nabiyullahi) da (Ali Waliyullahi) suna daga kalmomin da aka yi wasicci da sassaƙa zanensu a saman Zobe. [28] ana samun Zubunan da suke da wannan zanen rubutu a hannayen ƴan Shi’a.
Hukunce-hukunce
Cikin babukan fiƙihu daban-daban akwai hukunce-hukunce da aka yi bayaninsu kan Zobe, ba’arin Hukunce-hukuncen sun kasance kamar haka: ɗahara: wasu ba’ari daga Malaman fiƙihu suna cewa Makaruhi ne amfani da Hannun da yake sanye da Zobe domin tsarkake Mahallin fitar fitsari ko kasha. [29] Zoben da a jikinsa an rubuta sunan Allah ko kuma wata kalma daga Alkur’ani. [30] Muhammad Hassan Najafi Marubucin littafin Jawahirul Al-Kalam ya rubuta cewa sunayen A’imma (A.S) da Hazrat Fatima (S) suma suna cikin wannan hukuncin. [31] Alwala: yayin Alwala, dole ruwa ya isa ga fatar da take ƙasan Zoben da aka sa a hannu, da wannan dalili ne ya zama mustahabbi a motsa zoben a jujjuya shi yayin Alwala domin ruwa ya samu isa zuwa ƙarƙashinsa. [32] Sallah: a fatawar Malaman fiƙihu, Mustahabbi ne sanya Zoben Aƙiƙ a yayin Sallah. [33] na’am yin sallah da zoben Zinare haramun ga Namiji kuma yana ɓata sallah. [34] haka zalika Makruhi sanya Zoben ƙarfe ga Maza da Mata a lokacin da suke sallah. [35] kan asasin ra’ayin ba’arin Malaman fuƙihu yin sallah sanye da Zoben kwace yana ɓata sallah. [36] Hajji: wasu ba’ari daga Malaman fiƙihu cikin bahasinsu kan Muƙaddimomin Hajji, sun ambaci sanya Zoben Aƙiƙ ruwan ɗorawa yana daga Mustahabbi a lokacin tafiya. [37] a ra’ayin Sayyid Abu ƙasim Kuyi daga Maraji’an Taƙlidi sanya Zobe ga Mai harami idan ya kasance da niyyar Ado to ya haramta, amma idan ba da niyyar Ado bane ya halasta, [38] hakama Imam Khomaini bisa Ihtiyaɗi wujubi yana ganin yin aiki Hajji sanye da Zoben Najasa yana ɓata aikin Hajji. [39] Jihadi: ana ƙidaya Zobe cikin Salbu a lokacin Jihadi, [40] Salbu yana daga dukiyar wanda aka kashe a lokacin Jihadi, wanda ya kashe shi ya cancanci ɗaukar wannan dukiya ta wanda ya kashe ba ta karkasashi misalin ganima. [41] Aure: a cewar Muhaddisul Bahrani, Makruhi ne yin jima sanye da Zoben da jikinsa akwai sunan Allah ko wata kalma daga Alkur’ani. [42] Gado: ana lissafa Zobe cikin Habwa (dukiyar da babban ɗa yake keɓantuwa da ita ) gabanin kasa gado tsakanin magada. [43] Zoben Zinare: Malaman fiƙihu sun bada fatawa kan cewa haramun ne Namiji ya sanya zoben zinare. [44]
Zoben Sulaiman
Asalin Maƙala: Zoben Sulaiman. Magana dangane da Zoben Annabi Sulaiman (A.S) ta zo a cikin riwayoyi, wanda ya kasance wata alama ta ƙarfin iko, [45] wannan Zobe ya kasance a hannun Imamai [46] kuma Hazrat Mahadi (A.F) zai kasance sanye da wannan Zobe a lokacin Bayyanarsa. [47]
Bayanin kula
- ↑ Muassaseh Dayiratu Almaref Fikh Islami, Farhang fikh Farsi, 1385, juzu'i na 1, shafi na 746.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407H, juzu'i na 6, shafi na 468.
- ↑ Hurrul Amili, Hidaya Al-Umma, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 137.
- ↑ Sheikh Mufid, Kitab Al-Mazar, 1413 AH, shafi na 53.
- ↑ Zarei, "Angushtar dar Islam", shafi na 15.
- ↑ Ameli, Miftah Al-Karamah, 1419 AH, juzu'i na 5, shafi na 444.
- ↑ Khoi, Mausou'ah Al-Imam Khoi, 1418 Hijira, juzu'i na 28, shafi na 452.
- ↑ Tusi, Al-Mabsut, 1387 AH, juzu'i na 2, shafi na 67.
- ↑ Sheikh Mufid, Masar Al-Shia, 1414 AH, shafi na 41.
- ↑ Hakim Haskani, Shawaheed Al-Tanzil, 1411 AH, Mujalladi na 1, shafi na 209-239.
- ↑ Ibn Tawos, Allahouf, 1348, shafi na 130.
- ↑ Hurrul Amili, Hidaya Al-Umma, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 137.
- ↑ Zarei, "Angushtar dar Islam", shafi na 15.
- ↑ Zarei, "Angushtar dar Islam", shafi na 15
- ↑ Zarei, "Angushtar dar Islam", shafi na 15
- ↑ Duba Dehkhoda,Luggatnameh, Zaile wajeh Angushtar".
- ↑ Misali, duba: Hurrul Ameli, wasa'ilul Al-Shi’ah, 1409 AH, Juzu’i na 5, shafi na 79, 94, 93 da Mujalladi na 1, shafi na 331.
- ↑ Tabarsi, Makarem Al-Akhlaƙ, 1412 AH, shafi na 85.
- ↑ Hurrul Amili, Wasa'il Al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 88
- ↑ Hurrul Ameli, Wasa'ilul Al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 94.
- ↑ Hurrul Amili, Wasa'il Al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 92
- ↑ Hurrul Amili, Wasa'il Al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 93
- ↑ Hurrul Amili, Wasa'il Al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 79
- ↑ Duba Hurrul Amili, wasa'ilul Al-Shia Tools, 1409 AH, Mujalladi na 5, shafi na 103-97 da Mujalladi na 1, shafi na 331 da Mujalladi na 5, shafi na 78 da Mujalladi na 5, shafi na 79 da Mujalladi na 5. shafi na 91 da Mujalladi na 5, shafi na 94.
- ↑ Hurrul Amili,Wasa'ilul Al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 99.
- ↑ Ɗabarasi, Makarem Al-Akhlaƙ, 1412 AH, shafi na 91.
- ↑ Majlesi, Bihar -Anwar, 1403 AH, juzu'i na 48, shafi na 11.
- ↑ Hurrul Amili, Wasa'ilul Al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 92.
- ↑ Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi na 12.
- ↑ Bahrani, Al-Hadaeƙ Al-Nadrah, 1405 AH, juzu'i na 2, shafi na 76.
- ↑ Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi.72
- ↑ Najafi, Jawahirul Al- Kalam, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi na 287.
- ↑ Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta (Mohashi), 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 361.
- ↑ Ameli, Miftahul Al-Karamah, 1419 AH, juzu'i na 5, shafi na 444
- ↑ Najafi, Jawahir Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 8, shafi na 264.
- ↑ Allama Hili, Tahrir Al-Ahkam, 1420 AH, juzu'i na 1, shafi na 196.
- ↑ Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuƙtha (Mohshi), 1419 AH, juzu'i na 4, shafi na 331.
- ↑ Khoi, Musouah Al-Imam Khoi, 1418 Hijira, juzu'i na 28, shafi na 452.
- ↑ خمینی، تحریر الوسیله، نشر دار العلم، ج۱، ص ۴۲۹-۴۳۰.
- ↑ Tusi, Al-Mabsud, 1387 AH, juzu'i na 2, shafi na 67.
- ↑ Tusi, Al-Mabsud, 1387 AH, juzu'i na 2, shafi na 67.
- ↑ Bahrani, Al-Hadaeƙ Al-Nadrah, 1405 AH, juzu'i na 23, shafi na 138
- ↑ Sayyid Murtada, Al-Intisar, 1415 Hijira, shafi na 582.
- ↑ Duba Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 41, shafi na 54.
- ↑ Majlisi, Bihar-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 14, shafi na 99.
- ↑ Misali, duba Saffar, Basai'rul Al-Darajat, 1404H, shafi na 208 da 198.
- ↑ Majlesi, Bihar-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 26, shafi na 222.
Nassoshi
- Ibn Taus, Ali Ibn Musa, Allahouf, Jahan Publications, Tehran, 1348.
- Bahrani, Yusuf bin Ahmed, Al-Hadaiƙ Al-Nadrah fi Haƙam Al-Etrah Al-Tahirah, tahkik Muhammad Taƙi Iraɓani-Syed Abd al-Razzaƙ Mokaram, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci da ke da alaƙa da ƙum Theological Seminary Society, bugun farko. , 1405 AH.
- Hakim Haskani, Obeidullah, SHawaheed Al-Tanzil, wanda Mohammad Baƙer Mahmoudi ya yi bincike, bugu na biyu, ƙum, Majalisar Al’adun Islama, 1411H.
- Hurrul Amili, Muhammad bin Hassan, Wasa'ilul Al-Shi'a ila Tahsil Masa'il Shari'ah, kungiyar bincike ta Cibiyar Al-Baiti, ƙum, Cibiyar Al-Baiti, bugu na 1, 1409 AH.
- Hurrul Amili, Muhammad bin Hassan, Hidayatul Al'ummah ila Ahkam A'imma - Muntakabul Al-Masa'il, bincike na sashin Hadisi a ƙungiyar bincike ta Musulunci, Mashhad, Al-Pakhuh al-Islamiyya, bugu na 1, 1412 Hijira.
- Khomeini, Sayyid Ruhollah, Tahrir al-Wasila, ƙom, Dar al-Alam Press Institute, bugu na farko, beta.
- Khoi, Sayyid Abu al-ƙasim, Mausu'atul Imam Khoi, Bincike da masu bincike na cibiyar farfado da ayyukan Ayatullahi Grand Khoi, ƙum, Cibiyar Farfado da Ayyukan Imam Al-Khoei, bugu na farko. 1418 AH.
- زارعی، محمد، «انگشتری در اسلام»، در مجله فرهنگ کوثر، شماره ۳۲، سال ۱۳۷۸ش.
- Seyyed Morteza, Ali bin Hossein, Al-Intisar fi Infiradat Al-Amamiyeh, Groupungiyar Bincike na Ofishin Daba'ar Musulunci, ƙum, Ofishin Harda Daba'ar Musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta ƙum. Bugu na farko, 1415 AH.
- Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Kitab Al-Mazar, wanda Seyyed Mohammad Baƙer Abtahi, ƙum, Sheikh Mofid World Hazara Congress ya yi bincike, bugu na farko, 1413 AH.
- Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Masar Al-Shia, Beirut, Dar Al-Mofid, 1414 AH/1993 Miladiyya.
- Safar, Muhammad bin Hasan, Basa'ir al-Drejad al-Kubari, muƙaddima da ƙarshen Mirzam Hassan Kochebaghi, Manuscripts of Al-A'lami for Press, 1362/1404 AH.
- Tabatabai Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-Urwa al-Wuƙtha Fi Ma Tam Beh Al-Balawi (Mohshi), bincike na Ahmad Mohseni Sabzeɓari, ƙum, Islamic Publications Office alaka da ƙum Seminary Society of Teachers, bugu na farko, 1419 AH. .
- Tabarsi, Hasan bin Fazl, Makarem Al-Akhlaƙ, ƙom, Al-Sharif al-Mortaza, 1412H.
- Tousi, Muhammad bin Hassan, Al-Mabsut fi fiƙhu Al-Imamiyyah, bincike na Sayyid Mohammad Taƙi Kashfi, Tehran, Al-Maktabeh al-Mortazawieh Lahiya al-Aƙti al-Jaafariyya, bugu na 3, 1387H.
- Ameli, Seyyed Jaɓad bin Muhammad, Miftah Al-Karamah fi Sharh Al-ƙa'wa'ed Al-Allamah, bincike da Mohammad Baƙer Khalasi, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci da ke da alaƙa da ƙum Theological Seminary Society, bugu na farko, 1419 AH.
- Alameh Hilli, Hasan bin Yusuf, Tahrir al-Ahkam al-Shari'a Ali Madhhab al-Umamiya, Ibrahim Bahadri, Kum, Cibiyar Imam Sadiƙ (AS), bugun farko, 1420H.
- Allameh Majlisi, Mohammad Bagher, Bihar Al-Anwar, Al-Wafa Foundation, 1403 AH.
- Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, al-Kafi, bincike da gyara na Ali Akbar Ghafari, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na 4, 1407H.
- Muassaseh Dayiratul Maref Fikh Islami, Farhang fikh Mutabik Mazhab Ahle Baiti (A.S), Muassaseh Dayiratul Maref Fikh Islamiƙom, bugu na biyu, 1385.
- Najafi, Mohammad Hasan, Jawaher Al-Kalam fi Sharh Shar'e al-Islam, Abbas ƙuchani da Ali Akhundi suka yi bincike a Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na 7, 1404H.