Jump to content

Babban shafi

Daga wikishia
Encyclopedia na mazahabar Shi'a, Majma'a Ahlul-baiti (A S) na Dunya
540 Labari / 13,829 gyara cikin Hausa

Maƙalar da aka zaba

Falalolin Imam Ali (A.S) sun kasu rukuni biyu: keɓantattun falaloli da kuma falaloli da ya yi tarayya da Ahlul-baiti (A.S) cikinsu: ayar wilaya, ayar shira'u (ayar lailatul mabit), ayar infaƙ, hadisul ghadir, hadisul ɗairil mashwiyyi, hadisul manzilat da kyautar zobe suna daga cikin keɓantattun falaloli da Imam Ali (A.S) da ya keɓantu da su, ayar taɗhir, ayar zikri, ayar mawadda da hadis saƙlaini su kuma sun kasance daga falaloli da ya yi tarayya cikinsu da Ahlul-baiti (A.S) cikinsu.

Lokacin mulkin bani umayya sun hana faɗar falalolin Imam Ali (A.S) da yaɗa su. A lokacin wannnan gwamnati ana kashe masu naƙalto duk wata falala ta Imam Ali (A.S) ko kuma mafi ƙarancin abin da za yi musu shi ne jefa su a kurkuku. Haka nan bisa umarnin Mu'awiya ana ƙarfafa masu ƙirƙirar falalolin halifofi uku don kishiyantar falalolin Imam Ali (A.S), ba'arin malaman ahlus-sunna misalin Ibn Taimiyya shugaban ƴan salafiyya da almajiransa Ibn Kasir da Ibn ƙayyim Jauzi sun raunana ma'anonin ayoyi da hadisai da suke magana kan falalolin Imam Ali (A.S) ko kuma dai suna ma ganin cewa wannan magana ce kawai ta ƙarya. Tare da dukkanin da maƙiya suka yi cikin hana yaɗuwar falalolin Imam Ali (A.S), cikin litattafan hadisi na shi'a da ahlus-sunna an naƙalto falalolin Imam Ali (A.S) masu tarin yawa, malaman mazhabobi biyu, sun wallafa litattafai masu cin gashin kansu game da falalolin Ali ɗan Abi ɗalibi (A.S). Fada'ilul Amirul Al-muminin na Ahmad ɗan Hanbal, Khasa'isu Amirul Al-muminin na Nasa'i da Umdatul Uyuni Sihahil Al-Akhbar Fi Manaƙib Imamil Al-abrar na Ibn Biɗriƙ suna daga cikin jumlar litattafan da aka rubuta kan falalolin Imam Ali (A.S)

Full article ...

Other featured articles: Ayar Ulul amriَAyatul KursiyuAyar Ikmal

Shin kasani ...
  • ... Ko ka san Mu'ujizozin Annabi (S.A.W) abubuwa ne da suka saɓa da yadda ɗan Adam ya saba rayuwa, Allah yake gudanar da su ta hanyar Manzonsa (S.A.W)?
  • ...Sallar jam'i, sallah ce wace ake yinta cikin tsarin adadin wasu rukunin jama'a?
Labarin da aka Shawarar


  • Ƙa'idar Nafyis Sabil «(Larabci: قاعدة نفي السبيل) shi ne kore duk wani abu da zai fifita kafiri kan musulmi.»
  • Ƙa'idar Luɗufi « Larabci: قاعدة اللطف) ƙa'ida ce sananiya a cikin ilimin aƙida wato tauhidi, Luɗufi shi ne wani aiki da Allah ta'ala ya wajabatawa kanshi, ba tare da wannan Luɗufi ya yi tasiri a kan iyawar mukallafi ko tilasta masa ba..»
  • Ƙa'idar Kasuwar Musulmi «(Larabci: قاعدة سوق المسلمين) wata ƙa'ida ce ta fiƙihu wace take nufin halarcin sayo fata da naman dabbobin da aka yanka daga kasuwar musulmi tare da hukunci da tsarki waɗannan dabbobin...»
  • Ƙa'idar Jabbi «(Larabci: قاعدة الجَبّ) wata ka'ida ce ta fikihu wace ta keɓantu kafiran da suka musulunta, don haka abin da ya faru a baya bai shafi makomarsu ba»
  • Naman da ya halast aci «(Larabci: اللحوم المحللة) nama ne na wasu dabbobi da fikihun muslunci ya halasta aci, cikin kowanne daga nau’uka uku na dabbobin uku wanda suke kamar haka: dabbobin da suke rayuwa kan doran kasa, dabbobin cikin ruwa, tsuntsaye»
  • Kifi Mai Ɓawo «Larabci: الأسماك ذوات الفلس) shi ne kifin da yake halal a ci shi a mahangar Shi'a, kasancewar kifi yana da ma'auni to wannan ɓawon na jikin sa ne abin da yake halar ta cinsa»
  • Naman Da Ya Haramta A Ci «Larabci:اللحوم المحرمة)sune dabbubin da aka haramtawa musulmi yace namansu,a fiƙihun musulinci an haramta cin naman dabbubi da yawa, da wasu abubuwa masu rai na cikin ruwa da wasu daga cikin tsintsaye»
  • Assalatu Kairun Minan Naumi «ma'ana sallah ita ce mafi alheri daga bacci, wata jumla ce da ahlus-sunna suke faɗar ta lokacin kiran sallar asubahi bayan faɗin hayyu alal fala»
  • Nahjul Al-balaga (Littafi) « wani littafi ne da cikinsa aka tattaro wasu adadin huɗubobi, wasiƙu da gajejjerun maganganun Imam Ali (A.S).»
  • Sayyidina Abbas (A.S) «wanda ya rayu tsakanin shekaru 26-61 bayan hijira, ya shahara da Abul Fadli na biyar cikin jerin maza ƴaƴan Imam Ali (A.S).»
Babban Rukuni
Category Beliefs‎ not found
Category Culture‎ not found
Category Geography‎ not found
Category History‎ not found
Category People‎ not found
Category Politics‎ not found
Category Religion‎ not found
Category Sciences‎ not found
Category Works‎ not found