Shekara Ta 12 Hijira
Shekara 13 Hijira Ƙamari Shekara 11 Hijira Ƙamari | |
| 633 da 634m | |
|---|---|
| Imamanci | |
| Imam Ali (A.S) | |
| Hukumomin ƙasashen Muslunci | |
| Halifancin Abubakar Bin Abi Ƙuhafa | (Hukuma: 11-13H) |
| Muhimman abubuwan da suka faru | |
| Fara faɗaɗa ƙasa ta hannun halifofin Ahlus-Sunna | |
| Yaƙin Yamama | |
| Haihuwa da mutuwa | |
| Haihuwar Kumailu Bin Ziyad Nakha'i | |
| Wafati/Shahada | |
| Bashir Bin Sa'ad | |
| Abul Asi Bin Rabi'i | |
| Kannaz Bin Hosaini | |
| Abu Huzaifa | |
| Abu Dujana | |
| Musailamatul Kazzab | |
Shekara ta 12 hijira ƙamari, (Larabci: سنة 12 للهجرة) ita ce shekara ta goma sha biyu cikin lissafin hijira ƙamari. Rana ta farko a wannan shekata ta kasance 1 Muharram daidai da Panjeshanbe 1 ga watan Farwardin shekara ta 12 kalandar Farsi kuma daidai da 21 Maris 633M. Rana ta ƙarshe a wannan shekara ta kasance 29 Zil-Hijja, daidai da Yekshanbe 18 ga watan Isfandi shekara ta 12 kalandar Farsi kuma 9 Maris 634M.[1]farkon imamancin Imam Ali (A.S)
Daga cikin mafi muhimmanci abubuwan da suka faru a wannan shekara, fara futuhat na Musulmi wanda bayan wasu shekaru sun samu damar cin nasara da ƙwato manyan yankuna daga masarautun Iran da Rum, haihuwar Kumailu Bin Ziyad Nakha'i da rasuwar Bashir Bin Sa'ad da Abul Asi Bin Rabi'i suna daga cikin jumlar abubuwan da suka faru a wannan shekara
Abubuwan Da Suka Faru A Shekara Ta 12 Hijira
- Fara faɗaɗa ƙasa a zamanin halifofi wanda ake kira da futuhat.[2]
- Ƙwato garin Hira ta hannun Khalid Bin Walid a watan Safar.[3]
- Yaƙin Yamama a watan Rabi'ul Awwal.[4]
- Auren Umar Bin Khaɗɗab tare da Atika Ƴar Zaidu Bin Amru.[5]
Haihuwa
- Haihuwar Kumailu Bin Ziyad Nakha'i, daga tabi'ai kuma fitattun sahabban Imam Ali (A.S) da Imam Hassan (A.S).[6]
Wafati
- Rasuwar Bashir Bin Sa'ad, sahabin Annabi (S.A.W) kuma daga Ansar.[7]
- Rasuwar Abul Asi Bin Rabi'i ɗan ƴar uwar Sayyida Khadija (A.S) kuma mijin Zainab Ƴar Annabi (S.A.W) a watan Zil-Hijja.[8]
- Rasuwar Kannaz Bin Hosaini daga sahabban manzon Allah (S.A.W) a Madina.[9]
- Rasuwar Abu Huzaifa[10] da Abu Dujana Ansari[11] a yaƙin Yamama.
- Mutuwar Musailamatul Kazzab mai da'awar Annabta.[12]
Bayanin kula
- ↑ سایت تبدیل تاریخ هجری
- ↑ Dinawari, Akhbaruɗ Ɗiwal, shafi. 112.
- ↑ Balazuri, Futuhul Buldan, 243-244; Ɗabari, Tarikh Al-Umam wa al-Muluk, juzu'i. 3, shafi 344, 345, 348, 351, 353, 355, 358.
- ↑ Yaƙubi, Tarikhul Yaƙubi, juzu'i. 2, shafi. 131.
- ↑ Ibn Abdul-Barr, Al-Isti'ab, juzu’i. 4, shafi. 1878; Ibn Asir, Al-Kamil, juzu'i. 2, shafi. 400.
- ↑ Zarkali, Al-A'alam, juzu'i. 5, shafi. 234.
- ↑ Waƙidi, Al-Magazi,,juzu'i. 2, shafi. 165; Balazuri, Futuhl Buldan, shafi na 244, 248; Ibn Abdul-Barr, Al-Isti'ab, juzu'i. 1, shafi. 173; Zahabi, Tarikhul Islam, shafi. 78.
- ↑ Ibn Asir, Usdul Ghaba, juzu'i. 4, shafi. 222.
- ↑ Ibn Sa'ad, Attabaƙatul Kubra, juzu'i. 3, shafi. 35; Ibn Ƙutaiba, Al-Ma'arif, shafi. 327; Ɗabari, Tarikh Al-Umam wa al-Muluk, juzu'i. 3, shafi. 385.
- ↑ Ibn Sa'ad, Attabaƙatul Kubra, juzu'i. 3, shafi. 85.
- ↑ Waƙidi, Ar-Ridda, shafi. 74; Ibn Sa'ad, Attabaƙatul Kubra, juzu'i. 3, shafi. 557; Balazuri, Futuhl Buldan, juzu'i. 1, shafi. 110.
- ↑ Yaƙubi, Tarikhul Yaƙubi, juzu'i. 2, shafi. 131.
Nassoshi
سایت تبدیل تاریخ هجری, (Shafin sauya kwanan watan hijira), Ranar dubawa: 29 Yuli 2026M.
- Balazuri, Ahmad Bin Yahaya, Futuhl Buldan, tare da taimakon Radwan Muhammad Radwan, Beirut, 1398H.
- Ibn Abdul-Barr, Yusuf Bin Abdullah, Al-Isti'aab fi Ma'arifat Al-Ashab, wanda Ali Muhammad Bejawi ya yi bincike, Mawallafar Dar Al-Jil, Beirut, 1412H.
- Ibn Asir, Ali Bin Muhammad Jazari, Usdul Ghaba, Beirut, Mawallafar Darul Fikr, 1409H.
- Ibn Athir, Ali ibn Muhammad, Al-Kamil Fit Tarikh, Beirut, Mawallafar Dar Sadir, 1385H.
- Ibn Sa'ad, Muhammad Bin Sa'ad, Attabaƙatul Kubra, Muhammad Abdul-Ƙadir Atta, Beirut, Mawallafar Darul Kutubil Ilmiyya, ya yi bincike, 1410H.
- Ibn Ƙutaiba, Abdullahi Bin Muslim, Al-Ma'arif, tare da taimakon Tharwat Ukasha, Alkahira, 1960M.
- Ɗabari, Muhammad Bin Jarir, Tarikh Al-Umam wa al-Muluk, Beirut, Darul Turas, 1387H.
- Waƙidi, Muhammad, Al-Magazi, gyara Marsden Jones, London, 1966M.
- Yaƙubi, Ahmad Abi Yaƙub, Tarikhul Yaƙubi, Beirut, Mawallafar Dar Sadir, babu kwanan wata.
- Zahabi, Muhammad, Tarikhul Islam, Umar Abdul-Salam Tadmur, Beirut, Mawallafar Darul Kutubil Arabi, bugun na biyu, 1413H.
- Zarkali, Khairud-Din, Al-A'alam, Beirut, Datrul Ilimi Lil Malayin, bugu na takwas, 1989M.
- Dinawari, Ahmad Bin Dawud, Akhbaruɗ Ɗiwal, Abdul Mun'im Amir, Qom, Mawallafar Manshurat al-Radi, ya yi bincike, 1368SH.