Kifi Mai Ɓawo
Kifi mai ɓawo (Larabci: الأسماك ذوات الفلس) shi ne kifin da yake halal a ci shi a mahangar Shi'a, kasancewar kifi yana da ma'auni to wannan ɓawon na jikin sa ne abin da yake halar ta cinsa, wasu malaman fiƙihu suna ɗaukar wannan hukunci a matsayin ɗaya daga cikin keɓantattun hukunce-hukuncen Imamiyya,yazo a cikin hadisain bisa wannan hukuncin, inda aka ambaci wasu kifaye da wasu naman halal da naman haram. Malaman fiƙihu suna ganin saye da sayar da kifi mara ɓawo don ci bai inganta ba kuma haramun ne. A fatawarsu, idan wani bangare na jikin kifi yana da ɓawo ya wadatar kuma ya halatta a ci shi. Akwai saɓani tsakanin malamai dangane da hukuncin kifin da yake da ɓawo amma ba'a iya ganin su da ido saboda ƙanƙanta.
Gabatarwa
Kifi mai ɓawo a fatarsa, wanda shine murfin jikin fatar kifi.[1] A cikin shari’ar musulunci an ambaci kifaye da ma’auni a cikin babin farauta da yanka, da ci da sha (abin ci da abin sha)[2] kasancewar kifi yana da ma’auni to wannan ɓawon na fatarsa shine yake ma'aunin cewa wannan kifin halal ne[3] An kawo ruwayoyi a Shi’a da suke nuni da hukuncin kifin da yake da ɓawo.[4]
Hukuncinsa a Fiƙihu
Malaman fiƙihun Imamiyya suna ganin cin kifi mai ɓawo halal ne, hakanan cin kifin da ba shida ɓawo haramun.[5] abin da ake nufi da kifi mara vawo shgi ne kifin da tun asalinsa bashi da vawo,[6] da wannan dalili ne kifayen da suka kasance suna da vawo daga baya vawon ya zube ba a lissafa su cikin kifaye marasa vawo da suka haramta a ci.[7]
Game da dalilin da ya sa aka haramta cin naman kifi mara ɓawo, malamai sun ce waɗannan kifayen suna cin naman dabbobi ne wasun su kuma suna cin abubuwa marasa kyau don haka naman jikinsu ya gurɓace saboda rashin wannan ɓawon a fatarsu[8]
Hukuncin Kwan Kifi (CAVIAR)
A cewar fatawoyin mafi yawan malaman fiƙihu, hukuncin cin ƙwai (caviar) yana bin hukuncin kifin ne. Don haka idan cin kifi halal ne, cin caviar shima halal ne,[9] Wasu malaman sun bayar da wasu hanyoyin Misali, idan shi ƙwan kifin yana da ƙarfi ko yayi kaushi, halal ne, idan kuma ya yi laushi haram ne;[10] amma wasu sun ɗauki wannan ƙa'idar a wurin da aka kasa gane shin wannan kifin halal ne ko kuwa haram ne.[11]
Halascin Cin Kifi Mai Ɓawo
Wasu malaman fiƙihun Shi’a, irin su Sheikh Ɗusi da Sayyid Murtada, sun ɗauki halaccin wasu kifaye da haramcin sauran dabbobin ruwa a matsayin wasu hukunce-hukunce da suka kevanci fikihun Imamiyya,[12] san nan sun yi ijma’i a kansa[13] kuma suna ganinsa ɗaya daga cikin hukunce-hukuncen shari’a na ka’idojin maz'habar Shi’a,[14] Malaman fiƙihu waɗanda ba imamiyya ba, ba su ɗaukar halaccin kifi mai ɓawo da haramcin mara ɓawo ba . Abu Hanifa ya ɗauki dukkan kifaye a matsayin halal. Haka nan Shafi'i da Malik bin Anas sun gabatar da dukkan dabbobin cikin ruwa a matsayin halal,[15] Don haka masana fiƙihu da dama basu ɗauki kifi mai ɓawo a matsayin halal ba mara ɓawo kuma haram, don haka wannan abune da ya tsaya ga iya malaman Imamiyya.[16]
Misalai Daga Riwayoyi
Wasu malaman fiƙihu sun kawo hadisai daban-daban da suka ambaci wasu sunaye na kifayen halal dana haram.[17] haka kuma sun tattara hukunce-hukuncen malamai a wannan fage.[18] Sulhafaat (kunkuru), dafdea (kwaɗi) da Sarɗan (ƙaguwa) dabbobi ne na ruwa da aka haramtasu saboda ba kifaye bane kuma basu da ɓawo ajikinsu.[19] An ambaci kifayen teku, da ƙananan kifi mai ƙananan ɓawo , farar ruwa, kifin Ɗamrani daga kifayen halal.[20]
Malaman fiƙihu irin su Sheikh Ɗusi[21] Mohaghegh Hilli,[22] da Kidari mawallafin littafin Asbahul-Shia,[23] sun kawo hadisai, da suke ganin cin naman wasu dabbobin teku kamar jeri (eel) da kifin zahur da zimar makruhine, wasu kuma suna ganin tin da basu da ɓawo haramun ne,[24] Wannan ƙungiyar malaman na farko suna ganin waɗannan hadisan a matsayin hadisan zamanin taƙiyya,[25] Hakanan akwai sabanin ra'ayi kan yawan kifayen da aka halarta a Hadisai.[26]
Girma Da Nau'in Ɓawon Fatar Kifi
A fatawar wasu mujtahidai, ba lallai ba ne dukkan jikin kifin ya kasance yana da ɓawo ba, idan wani ɓangare na jikin kifin yana da shi ya wadatar,[27] gane jikin kifin yana da shi ko a'a yana hannun mutum[28] ko kuma masana a naimi taimakon masana kifi wajan ganewa.[29] Wasu suna ganin idan mutum ya yi shakkar kifi yana da ɓawo ko baida to gara ya haƙura da cinsa,[30] sai dai idan ya siya a kasuwannin musulmai. ko kuma wani mutum adili ya shaida cewa yana da ɓawo,[31] Don haka kifin da ake sayar da shi a kasuwan nin waɗanda ba musulmi ba,[32] idan akayi shakka yanada ɓawo ko baidashi, to a nisanci cinsa.[33]
Daga cikin malaman fiƙihu, akwai bambancin ra'ayi a kan hukuncin kifin da ke da ɓawo da ba'a iya gani da ido , Ezonbron, kifin giwa, kifin dice,[34] shark[35] da caviarfish,[36] na daga cikin kifin da aka tambayi malaman fiƙihu game da hukuncinsu. Wasu maraja'an suna ganin cewa ɓawon kifi ya kamata a ganshi da ido ba tare da wani gilashin ƙara girman abu ba,[37] ko kuma a ra'ayin mutane wannan kifin ana kiransa da mai ɓawo.[38] Wasu kuma kamar Ayatullah Bahjat suna ganin ya wadatar gani mudubin ƙara girman abu[39] Ayatullah Makarim Shirazi, a yayin da yake amsa tambaya kan hukuncin cin sharks, yace ra'ayin yawancin mutane ya wadatar wajan a fahimci yanada ɓawo ko kuwa[40] ko kuma faɗin masu ilimin abun.[41] Kungiyar masu bincike suna ganin cewa ya halatta a ci kifi idan yana da ɓawo, ana iya ganinsa da ido ko kuma da madubin ƙara girman abu.[42]
Bayanin kula
- ↑ Jam'i aza Mu'allifan, Mujallar Ahlul Baiti Fiqh, Qum, juzu'i na 9, shafi na 268.
- ↑ Muassaseh Dayirati Marif fikihu bar mazhab Ahlul-baiti,(A.S) Farhang fikihu mutabik mazahab Ahlul-baiti (AS), 1426 AH, juzu'i na 2, shafi na 291.
- ↑ Duba Khumaini, Tahrir al-Wasila, Qum, juzu'i na 2, shafi na 155.
- ↑ Misali, duba: Sadouq, Man la Yahdrah al-Faqih, 1413 AH, juzu'i na 3, shafi na 323; Har Ameli, Vasal al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 24, shafi 129; Tusi, Tahzeeb al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 9, shafi na 2.
- ↑ Misali, duba: Sharif Morteza, Al-Intisar, 1415 AH, shafi 400; Mohagheq Hilli, Shara'iu al-Islam, 1408H, juzu'i na 3, shafi na 169.
- ↑ Ghaffari, tarjameh wa sharh La Yahdrah al-Faqih, 1409 AH, juzu'i na 4, shafi na 444.
- ↑ Allameh Hali, Dokokin Al-Ahkam, 1413 AH, juzu'i na 3, shafi na 324; Ghaffari, tarjama da sharh La Yahdrah al-Faqih, 1409 AH, juzu'i na 4, shafi 444; Shahid Sani, al-Rawda al-Bahiya, 1410 AH, juzu'i na 7, shafi na 263.
- ↑ علت حرام گوشت بودن ماهیان بدون پولک چیست؟، سایت مشرق.
- ↑ Misali, duba: Allameh Hilli, Tahrir Al-Ahkam al-Sharia, Mashhad, juzu'i na 2, shafi na 160; Shahidi na farko, Al-Lama' Al-Damashqiya, 1410H, shafi na 235.
- ↑ Dilmi, al-Marasim al-Alawiyya, 1404H, shafi na 207.
- ↑ Allameh Hilli, Tahrir al-Ahkam al-Sharia, Mashhad, juzu'i na 2, shafi na 160; Shahidi na farko, Al-Lama' Al-Damashqiya, 1410H, shafi na 235.
- ↑ Tusi, Al-Mabsut, 1378 AH, Juzu'i na 6, shafi na 276; Sharif Morteza, Al-Intisar, 1415 AH, shafi 400.
- ↑ Rawandi, Fiqhu al-Qur’an, 1405 Hijira, juzu’i na 2, shafi 249.
- ↑ Ibn Idris Hilli, Al-saraer, 1410 AH, juzu'i na 3, shafi na 99
- ↑ Fazel Moqdad, Kenz al-Irfan, 1425 AH, juzu'i na 1, shafi na 328.
- ↑ Ardabili, Majma al-Fa'edat, 1403 AH, juzu'i na 11, shafi 187.
- ↑ Fazel Moqdad, Kenz al-Irfan, 1425 AH, juzu'i na 1, shafi na 328
- ↑ Fazel Abhi, Kashf al-rumoz, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 361
- ↑ Shahidi awol, Al-Lama' Al-Damashqiya, 1410H, shafi na 235.
- ↑ Sheikh Baha'i, Jame Abbasi, 1429H, shafi na 754.
- ↑ Tusi, Al-Nihaya, 1400 AH, shafi 576.
- ↑ Mohagheq Hilli, Shara'iu Al-Islam, 1408H, juzu'i na 3, shafi na 169.
- ↑ Kidari, Isbah al-Shia, 1416H, shafi na 387
- ↑ Ibn Idris Hilli, Al-saraer, 1410H, juzu'i na 3, shafi na 99
- ↑ Shahid Awol, al-Duros al-Sharia, 1417 AH, juzu'i na 3, shafi na 8
- ↑ Duba: ShaaraniTarjameh wa sharh Tabsiratul Al-muta'allimin, 1416 AH, juzu'i na 2, shafi na 634.
- ↑ Muassaseh Dayiratul Marif fikihu bar mazhab Ahlul-baiti, Farhang fikihu mutabik Ahlul-baiti (AS), 1426 AH, juzu'i na 2, shafi na 291.
- ↑ Golpayegani, Majumul Masael, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 63.
- ↑ Behjat, Esfatataat, 1428 AH, juzu'i na 4, shafi na 376.
- ↑ Hakim, Minhaj al-Salehin, 1410 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 367.
- ↑ Tabrizi, Isftatayat jadid, Qom, juzu'i na 2, shafi na 393
- ↑ Khoei, Sarat al-Najat, 1416 AH, juzu'i na 2, shafi 406; Bojunordi, al-Qasas al-Fiqhiyyah, 1419 AH, juzu'i na 3, shafi na 41.
- ↑ Tabrizi, Sarat al-Najat, 1427 AH, juzu'i na 5, shafi na 406.
- ↑ Golpayegani, Majam al-Masal, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 63-64.
- ↑ Tabrizi, Isftatayat al-Jadid, Qum, juzu'i na 1, shafi na 402; Behjat, Esfatataat, 1428 AH, juzu'i na 4, shafi na 376; Makarem Shirazi, Eftatayat jadid 1427 AH, juzu'i na 1, shafi.286; Safi Golpayegani, Jame al-Ahkam, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 286
- ↑ Tabrizi, Sarat al-Najat, 1427 AH, juzu'i na 5, shafi na 406; Golpayegani, Majumul Masael, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 63.
- ↑ Tabrizi, Isftatayat jadid, Qom, juzu'i na 2, shafi na 390.
- ↑ Tabrizi, Sarat al-Najat, 1427 AH, juzu'i na 5, shafi na 406.
- ↑ Behjat, Esfatataat, 1428 AH, juzu'i na 4, shafi na 376.
- ↑ Makarem, Istifta'at jadid juzu'i na 1, shafi na 282
- ↑ Makarem Shirazi, Esfatatayat jadid, 1427 AH, Juzu’i na 1, shafi 286.
- ↑ Jam'i az muallifan, Fiqhu Ahlul-Baiti (AS), juzu’i na 43, shafi na 237
Nassoshi
- Allameh Hali, Hasan bin Yusuf, Qa'aab al-Ahkam fi Marafah al-Halal wa Haram, Qom, Islamic Publications Office, 1413 AH.
- Allameh Hilli, Hasan bin Yusuf, Commentary of the Learned in Ahkam al-Din, researched by Mohammad Hadi Yousefi Gharavi, Tehran, Printing and Publishing Institute, 1411 AH.
- Allameh Hilli, Hasan bin Yusuf, Tahrir al-Ahkam al-Sharia Ali Madhhab al-Imamiyah, Mashhad, Al-Al-Bayt Institute (A.S.), Beta.
- Behjat, Mohammad Taqi, Istftatayat, Qom, office of Hazrat Ayatollah Behjat, 1428 AH.
- Makarem Shirazi, Nasser Esfattayat jadid, Qom, Imam Ali Ibn Abi Talib (a.s.) School Publications, 1427 AH.
- Mofid, Muhammad bin Muhammad bin Nu'man, Al-Maqna, Qom, Sheikh Mofid World Congress, 1413 AH.
- Mohaghegh Hilli, Jafar bin Hasan, Islamic Laws in Halal and Haram Issues, Qom, Ismailian Institute, 1408 AH.
- Rawandi, Qutbuddin, Fiqh al-Qur'an by Rawandi, Qom, Ayatollah Marashi Library Publications, 1405 AH.
- Shaarani, Abul Hasan, Note of the learned fi Ahkam al-Din, translation and description, Tehran, Islamic Manifesto, fifth edition, 1419 AH.
- Shaheed Thani, Zain al-Din bin Ali, Masalak al-Afham ili Tankih Shaaree al-Islam, Qom, Islamic Encyclopaedia Foundation, 1413 AH.
- Shaheed Thani, Zain al-Din bin Ali, al-Rawda al-Bahiya fi Sharh al-Lama' al-Damashqiya, Qom, Davari bookstore, 1410 AH.
- Sharif Morteza, Ali bin Hossein Mousavi, Al-Intisar fi Infradat al-Imamiya, Qom, Islamic Publications Office, 1415 AH
- Tabrizi, Javad, Isftatayat jadid, Qom, Bija, Bita.
- Tabrizi, Javad, Sarat al-Najat, Qom, Dar al-Sadiqa al-Shahida, 1427 AH.
- The first martyr, Muhammad Bin Makki, al-Dros al-Sharia fi Fiqh al-Imamiyah, Qom, Islamic Publications Office, second edition, 1417 AH.
- shahid Awol, Muhammad Ibn Makki, Al-Lama' Al-Damashqiyyah in Fiqh al-Imamiyah, Muhammad Taqi and Ali Asghar Marwarid, Beirut, Dar al-Trath, 1410 AH.
- Ardabili, Ahmed bin Ali, Majma al-Fa'edat wa al-Burhan fi Sharh Irshad al-Azhan, researched by Agha Mojtaba Iraqi and Alipanah Eshtredi, Qom, Islamic Publications Office, 1403 AH.
- Bojnoordi, Seyyed Hasan, Al-Qasea al-Fiqhiyah, researched by Mehdi Mehrizi and Mohammad Hasan Daraiti, Qom, Al-Hadi publication, 1419 AH.
- Dilmi, Selar, al-Marasim al-Alawiyya and al-Ahkam al-Nabawiyyah, researched by Mahmoud Bostani, Qom, Charters of Al-Haramain, 1404 AH.
- Fazel Abhi, Hasan bin Abi Talib, Kashf Al-rumuz. Qom, Islamic Publications Office, third edition, 1417 AH.
- Fazel Moqdad, Moqdad bin Abdallah Siyuri, Al-Tanqeeh Al-Whafir al-Makhtasar al-Shari'a, Qom, Ayatollah Murashi Najafi Library Publications, 1404 AH.
- Fazel Moqdad, Moqdad bin Abdullah, Kanz al-Irfan Fi Fiqh al-Qur'an, Qom, Mortazavi Publications, 1425 AH.
- Ghaffari, Ali Akbar wa Mohammad Javad Sadr Balaghi, Tarjame wa sharh man La Yahzara al-Faqih, Tehran, Sadouq Publishing House, 1409 AH.
- Golpaygani, Seyyed Mohammad Reza, Majmam al-Masail for Golbaygani, Qom, Dar al-Qur'an al-Karim, second edition, 1409 AH..
- Hakim, Seyyed Mohsen, Minhaj al-Salehin (Al-Mahshi), Beirut, Dar al-Taraif for publications, 1410 AH.
- Hurru Amili, Muhammad bin Hasan, Wasa'il al-Shi'a, Qom, Al-Al-Bayt Institute (AS), 1409 AH.
- Ibn Idris Hali, Muhammad Bin Mansour, Al-Sara'er al-Hawili Tahrir al-Fatawi, Qom, Islamic Publications Office, second edition, 1410 AH.
- Jam'i az muallifan, Mujallaeh fikh Ahl al-Bayt (a.s.), Farsi, Qom, Islamic Ahl al-Bayt (a.s.), Bita.
- Khoei, Seyyed Abul Qasim, Sarat al-Najat (Al-Mahshi), Qom, El-Elect Publishing School, 1416 AH.
- Khomeini, Seyyed Ruhollah, Tahrir al-Wasila, Qom, Dar al-Alam Press Institute, Beta.
- Kidari, Muhammad bin Hossein, Isbah al-Shia in Masbah al-Sharia, Qom, Institute of Imam Sadiq (pbuh), 1416 AH.
- Majlesi, Mohammad Baqir, Bihar al-Anwar al-Jamaeh Lederer Akhbar al-Aima al-Athar, Beirut, Institute of Al-Tabar and Al-Nashr, 1410 AH.
- Sadooq, Muhammad Bin Ali, Man Lai Hazara Al-Faqih, Qom, Islamic Publications Office, second edition, 1413 AH.
- Safi Golpayegani, Lotfollah, Jame Al-Ahkam, Qom, Hazrat Masoumeh (PBUH) Publications, 1417 AH.
- Sheikh Baha'i, Baha'uddin, Jame Abbasi and its completion by Mohshi, Qom, Islamic Publications Office, new edition, 1429 AH.
- Tusi, Mohammad Bin Hasan, Al-Mabsut fi Fiqh al-Imamiyah, research by Seyyed Mohammad Taqi Kashfi, Tehran, Al-Mortazawieh School, third edition, 1387 AH.
- Tusi, Muhammad bin Hasan, Al-Nihaya fi Majdar al-Fiqh and al-Fatawi, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, second edition, 1400 A.H.
- Tusi, Muhammad bin Hasan, Tahzeeb al-Ahkam, research by Hasan al-Mousavi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1407 AH.