Yankan Ahlil-Kitabi
- Wannan rubutu ne mai bayyanawa game da ra'ayi na fikihu kuma ba zai iya zama ma'auni na ayyukan addini ba. Koma zuwa wasu tushe don ayyukan addini.
Yankan Ahlil-Kitabi, (Larabci: ذبيحة أهل الكتاب) ita ce Dabbar da Ahlil-Kitab (Mabiya Addinan da aka aikowa Annabinsu da littafi daga sama) suka yanka,[1] daidai da ra'ayin shaik baha'i, mafi yawan malaman fiƙihun shi'a misalin shaik ɗusi, shaik mufid, da sayyid murtada sun haramta cin naman dabbar da ahlil-kitab suka yanka,[2] ko da kuwa lokacin yankawa sun ambaci sunan Allah,[3] sun haramta ne sakamakon dogara da riwayoyi,[4] suna cewa abin nufi daga halascin abincin Ahlil-Kitab da ya zo a cikin aya ta biyar suratul ma'ida, yana nufin nau'ukan abincin misalin abincin da aka noma da ƴayan itaciya bawai naman dabbobin da suka yanka da hannunsa ba,[5] haka kuma a ra'ayin wasu ba'ari daga malaman fiƙihu sassan jikin dabbobin da suke da tsartuwar da kwararar da jini da ahlil-kitab suka yanka da hannunsu daga misalin fatar dabba ana musu hukunci da mushe kuma najasa ne, sannan ba za a iya amfani da ƙirgi da fatar Dabbobin ba.[6] Sai dai kuma an samu wasu ba'arin Malaman fiƙihu tare da kafa hujja da ba'arin wasu riwayoyi[7] suna ganin halascin Yankan Ahlil-Kitab, Allama Hilli ya danganta wannan magana ga Ibn abi Aƙil[8] da Ibn Junaid Iskafi ,[9] kan imanin Shaik Saduƙ[10] da Muhaƙƙiƙul Ardabili[11] Yanka yana halasta idan lokacin yanka shi an ambaci sunan Allah.[12]
An yi rubuce-rubuce daban-daban kan wannan Maudu'i daga jumlarsu akwai:
- littafin Tahrimu Zaba'ihi Alil Al-Kitab, rubutun Shaik Mufi wanda ya rasu[13] shekara ta 413, cikin wannan littafi ya yi amfani da ayoyin Alkur'ani, riwayoyi da Kuma Ijma'i, kan haramta Yanka Ahlil-Kitab,[14] ya kuma tattauna dalilin masu saɓawa da haramta Yankan Ahlil-Kitab.[15]
- littafin Hurmatu Zaba'ihi Ahlil-Kitab, rubutun Shaik Baha'i[16] wanda ya rasu a shekara ta 1031 h ƙamari,ya rubuta wannan littafi bisa buƙatar Sarki Abbas Safawi,[17] a farkon littafin ya yi bincike kan ra'ayoyin Malaman Shi'a da Ahlus-sunna,[18] marubucin ya bayyana shak.kunsa kan haramcin Yankan Ahlil-Kitab, cikin taka tsantsan cikin bada fatawa kan batun Yankan Ahlil-Kitab ya yi amfani da jumlar (Allah ne Masanin Haƙiƙanin al'murra)[19]
Bayanin kula
- ↑ Mu'assaseh Dayiratu Almaref Fikh Islami, Farhang Fiƙh, 1382, juzu'i na 3, shafi na 701.
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Nehaya, 1400H, Juzu'i na 1, shafi na 582
- ↑ Sheikh Mufid, Al-Muƙni'a, 1413 AH, shafi na 579
- ↑ Seyyed Morteza, Al-Intisar, 1415 AH, Mujalladi na 1, shafi na 403.
- ↑ Sheikh Baha'i, Hurmatu Zaba'ihi Ahlil Kitab, 1410H, shafi na 60.
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Nehaya, 1400 AH, Juzu'i na 1, shafi na 582; Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Al-Masa'il Maraji'u, 1392, juzu'i na 2, shafi na 745.
- ↑ Imam Khumaini, Tahrir Al-Wasila, 1392, juzu'i na 2, shafi na 156.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407, juzu'i na 6, shafi na 264.
- ↑ Golpayegani, Majma'ul Al-Masa'el, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 39.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Al-Masa'il Maraji'u, 1392, juzu'i na 2, shafi na 745.
- ↑ Sheikh Baha'i, Hurmatu Zaba'ihi Ahlul Kitab, 1410H, shafi na 60.
- ↑ Allama Hilli, Muktalaful Al-Shi'a, 1413 AH, Mujalladi na 8, shafi na 316.
- ↑ Allameh Hilli, Muktalaful Al-Shi'a, 1413 AH, Mujalladi na 8, shafi na 316.
- ↑ Sheikh Sadouƙ, Al-Muƙni'a, 1415 AH, shafi na 417.
- ↑ Mohagheƙ Ardabili, Majma'ul Al-Fa'edath wa Al-Burhan, Al-Nashar al-Islami Foundation, juzu'i na 11, shafi na 78.
- ↑ Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 36, shafi na 80.
- ↑ Sheikh Mofid, Hurmatu Zaba'ihi Ahlil-Katab, 1413H.
- ↑ Sheikh Mofid, Hurmatu Zaba'ihi Ahlul Kitab, 1413 AH, shafi na 20
- ↑ Sheikh Mofid, Hurmatu Zaba'ihi Ahlul Kitab, 1413 AH, shafi na 24
Nassoshi
- Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Tahrir al-Wasila, ƙum, Muassaseh Nazshar asar Imam Khumaini , 1392.
- Bani Hashemi Khomeini, Mohammad Hasan, tauzihul Al-Masa'il Maraji'ah, ƙum, Daftare Intisharatu Islami, 1392.
- Seyyed Morteza, Ali bin Hossein, Al-Intisar fi Infradat al-Imamiya, ƙum, Al-Nashar al-Islami Foundation, 1415H.
- Sheikh Baha'i, Muhammad bin Hossein, Hurmatu Zaba'ihi Ahlul Kitab, Beirut, Al-alami Foundation for Publications, 1410 AH.
- Sheikh Sadouƙ, Muhammad Bin Ali, Al-Muƙnia, ƙum, Imam Al-Hadi Foundation, 1415H.
- Sheikh Tusi, Muhammad bin Hasan, Al-Nehaya fi majarrad fiƙh wa al-fatawi, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, 1400 A.H.
- Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Maƙna'a, ƙum, World Hazara Congress of Sheikh Mofid, 1413 AH.
- Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Hurmatu Zaba'ihi Ahlul Kitabi, ƙum, buga taron duniya na Lalfiyya Al-Sheikh Al-Mofid, 1413H.
- Allameh Hilli, Hasan bin Yusuf, Muktalaf Shi'a Fi Ahkam al-Sharia , ƙom, Al-Nashar al-Islami Foundation, 1413 AH.
- Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, Al-Kafi,Tashihu: Ali Akbar Ghafari, Tehran, Darul Kutub al-Islami, 1407H.
- Golpaygani, Seyyed Mohammad Reza, Majma Al-Masail, ƙom, Darul ƙur'an al-Karim, 1409 AH.
- Mu'assaseh Dayiratul Alma'arif Fikh Islami, Farhang Fiƙh Mutabik Mazhab Ahlul-Baiti, Mu'assaseh Dayiratul Alma'arif Fikh Islami, 1382.
- Mohagheƙ Ardabili, Ahmed bin Muhammad, Majma Al-Fa'edat Al-Burhan fi Sharh Irshad Al-Azhan, tahkik: Mojtaba Iraƙi, ƙom, Al-Nashar al-Islami Foundation, B.T.A.
- Najafi, Mohammad Hasan, Jawaher Al-Kalam fi Sharh Sharae Al-Islam,tahkik: Mahmoud ƙochani, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1362.