Naman Da Ya Haramta A Ci

Daga wikishia
Wannan wani rubutu ne mai bayyanawa game da ra'ayi na fikihu kuma ba zai iya zama ma'auni na ayyukan addini ba. Koma zuwa wasu tushe don ayyukan addini.
Risala

Naman da ya haramta ko kuma dabb0bin da suke haram, (Larabci:اللحوم المحرمة)sune dabbubin da aka haramtawa musulmi yace namansu,a fiƙihun musulinci an haramta cin naman dabbubi da yawa, da wasu abubuwa masu rai na cikin ruwa da wasu daga cikin tsintsaye. A cikin nassosin Musulunci,an raba abubuwan da suke haramun zuwa kashi biyu: haramun ne a asali da wanda yake haramun ne sabo da wani dalili.daga cikin dabbubin da suke rayuwa a doran ƙasa,irin namin dajin suke cin mutane wato masu kaiwa mutane hari domin su cinyesu da dabbar da take jan ciki da duk babbar da take a asalinta takasance mutum,kamar biri da kwarika da tsintsayan da suke da farce,duk haramin ne cinsu.kazalika duk abububuwan da suke rayuwa a ruwa haramin ne musulmi yace banda kifi wanda yake da wata fata mai tauri a bayan shi,to shi ba haramin ba ne.

Duk abin da akayi daga dabbar da take haramin ne cin namnta,kamar su fata da abubuwan da likitoci suke anfani da shi a wajan aikin su,da kayan kwalliya idan yazama ita dabbara an yankata to suna sun zamo masu tsarki,za’iya anfani da su babu matsala a fikihu sai dai kawai baza’ayi sallah da suba.

Abin nufi da abin da aka haramta

Dabbobin da aka haramtawa musulmi ana kiransu da dabbobin da ba’a cin namansu,kuma a fiƙihu an kasasu gida biyu,waɗan da suka haramta a asali da waɗanda suka haramata sabo da wani dalili.[1] kashi na farko wanda yaƙunshi dabbobin da suka haramta a asali kamar su zumo,amma shi kashi na biyu wanda bai haramata ba a asali,a asali halas ne,amma ya haramta sakamakon wani dalili da ya faru, kamar idan dabba taci najasa ko kuma rashi yanka.[2] ƙur’ani yayi bayani dabbobin da suka haramta musulmi yaci,loƙacin da yake bayani kan abinci da ya haramata a cikin suratul Baƙara da Ma’ida da Nahal da An’am.[3] Ira-iran naman da suka haramta An haramta cin nama da dama daga namun daji da na ruwa da tsuntsaye a fikihun Shi'a.[4]

Dabbobin da suke rayuwa a doran ƙasa

Daga cikin dabbobin da suke rayuwa a doran ƙasa,an haramta duk dabbar da take cin mutane ko dabbar da take farautar abin da zataci,kamar Damusa da Dub da kuma duk dabbar da take jan ciki,kamar muciji babba da kwarika kamar ƙuda da gizo-gizo,da abubuwa kamar su beraye da kunama irin wacce take gida a ƙarƙashin ƙasa,duk dabbar da asalinta takasance mutum kamar giwaye.[5] Amma daga cikin kwarika an togace fara,ita fara ba haramin bace a musulinci,amma da sharaɗn akamata a raye takasance tamutu a hannu,amma da za’a sameta a mace,bai kamata acita ba.[6]

Dabbobin cikin ruwa

Ku duba: Kifaye Masu Ɓawo a Jiki A mahangar Shi’a, duk naman ruwa haramun ne in ban da kifayen da suke da wata fata a bayansu mai tauri.[7] Kuma wasu daga cikin Ahlus Sunna kamar Malikiyyah da Hannabali sunaganin dukkan abin da yake cikin ruwa naman shi ya halasta.[8]

Tsintsaye

Malaman fiƙihu na Shi’a sun kasa naman da ya haramta zuwa gida uku,abubuwa da suke da dogon farce da abubuwan da asalinsu mutane ne da Al-kaba’is su ne abubuwa da mutum a al-da bayacinsu,amma su masu dogon farce kamar hankaka da shaho.amma ɗawisu da jemage da turorowa ance da su a asalinsu mutane ne,amma su al-ka’is su ne a ɗabi’ar mutum baya cin irinsu kuma ya tsani yace ira-iransu.[9] kuma a wasu littatafai na fiƙihu an anbaci cewa guda da sauro suna daga cikin Al-kaab’is.[10]

Dabbobin da suka haramta sabo da wani dalili

Dabbobin da suke halas ne cinsu zaiyiiyu su zamo haramin idan wasu sharuɗɗa suka tabbata a gurin malaman Shi’a,sabo da haka dabbbobin da suke halal waɗanda ba’a yankasu ba kuma dabbar da tce najasa kuma dabbar da ɗan adam yasadu da ita,duk zasu zamo haramin a musulinci.[11] Haramcin anfani da wani abu daga dabbar data haramata, bisa fikihun Shi’a, cin naman dabbobin da aka haramta, da duk wani amfani da su wajen shirya abinci, haramun ne[12] haka nan cin ƙwai da shan madarar su haramun ne[13]

Halasci yin anfani da dabbobin da suke haramin

Malaman fiƙihu na Shi’a suan sun halasta yin anfani da wani ɓangare na dabbobin da namansu bai halasta ba,idan yazama ba ci za;ayi ba,amma da sharaɗin a yanka,wato yazamo anyankasu ta hanyar shari’a.

Tufafi

Ya halasta ayi anfani da wani yanki ko ɓarayi na dabbobin da bai halasta aci naman ba waja yin tufafi,amma banda Kare da Alade,amma yazama anyankasu kafin ayi anfani da su.kazalika za’iya anfani da duk wani abu da akayi daga garesu kamar buzu [14]amma fa duk da yahalat ayi anfani da abin da kayi daga jikinsu da sharaɗin yankasu,to ammafa bai halasta ba sanya fatar su ba yayin da mutum zai yi sallah,domin sanyasu a loƙacin sallah yana ɓata sallah.[15] Malamai suyi fatawa da cewa abin da akayi daga dabbobin da bai halasta aci naman su ba najasane,kuma bai halasta ba ayi anfani da su dabbobin da ba’aci ba batare da anyankasu ba.[16]

Anfani da dabbobin da bai halasta aci ba domin anfani a asbiti da kayan kwalliya

Malaman Shi’a sunyi fatawa ta halascin anfani da kayan da ake anfani da su a asibit da kayan kwalliya da mai na shafawa da abin da yayi kama da su, waɗanda akayisu daga dabbobin da bai halatta aci namansu mutiƙar an yankasu.[17] amma duk loƙacin da ba’a yanka irin waɗanna dabbobin da bai halasta aci namansu ba,to bai halasta a sasu ba ko anfani da su ba a yayin sallah,domin bai halasta ba,sabo da najasace,kuma dola ne idan mutum yaɓasu ko suka taɓa jikin shi ya tsarkake jikin shi kafin sallah.[18]

Wasu daga cikin malamai sun halasta abubuwan da ake anfani da su a asibiti ko kuma abin da akeci,waɗanda akayisu daga dabbobin da bai halasta ba aci namanasu kuma batare da anyankasu kamar ƙashi,duk ya halasta ayi anfani da su,amma idan yazamo su abubuwan yayin da ake yinsu sun canza zuwa wani abu daban,wanna shi ne a Fiƙihu ake kira da ɗahara ta hanyar Istihala,sabo da haka idan hakan yatabbata,to waɗanna abubuwan sun tsarkaka kuma ya halasta ayi anfani da su kuma ya halasta aci.[19]

Hukuncin tsarki da najasar gaɓoɓi dabbobin da bai halasta aci naman su ba.

Bisa abin da yake cikin litattafan Fikihu na Shi’a gaɓoɓi na dabbobin da bai halasta ba aci namansu zasu zamo masu tsarki idan yazamo anyankasu.[20] amma idan yazamo ba’a yankasu ba kuma yazamo suna daga cikin dabbobin da idan anyanka su jini yana kwarara da karfi,to zasu zamo najasa kuma bai halasta ba ayi anfani da su ba.[21]

Najasar fitsari da bayan gida

Fitsari da bayan gida na dabbobin da ba’a cin namansu kuma waɗanda suka zamo masu idan anyankasu jini yana kwarara najasa ne[22] Hani a loƙacin sallah Bai halasta ba asami wata gaɓa ta dabbar da bai halasta aci namanata ba,kuma idan aka yankata jini yana kwarara a tufafi na mutuman da yake sallah ba ko da anyankata kuwa,sabo da haka gashi dabbar da ba’aci idan mutum yayi sallah da shi yana ɓata sallah.[23]

Bayanin kula

  1. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqh, 2007, juzu'i na 2, shafi na 255.
  2. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqh, 2007, juzu'i na 2, shafi na 255.
  3. Suratul Baqarah, aya ta 173; Suratul Ma'idah, aya ta 3; Suratul An'am, aya ta 145; Suratul Nahl, aya ta:115.
  4. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqh, 2007, juzu'i na 2, shafi na 255.
  5. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqh, 2007, juzu'i na 3, shafi.408.
  6. Hali, Shar’i al-Islam, juzu’i na 4, shafi na 742; Najafi, Jawahirul Kalam, 1362https://makarem.ir/ahkam/ru/home/istifta/251495/
  7. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqh, 2007, juzu'i na 3, shafi.408.
  8. «حکم خوردن گوشت خرچنگ و ماهی مرکب»، سایت سنی آنلاین
  9. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqh, 2007, juzu'i na 3, shafi.422.
  10. Najafi, Jawahirul Kalam, 1404 AH, juzu'i na 36, ​​shafi na 319.
  11. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqh, 2007, juzu'i na 3, shafi.408.
  12. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqh, 2004, juzu'i na 2, shafi na 255;
  13. [http://portal.anhar.ir/node/17219/?ref=sbttl#gsc.tab=0
  14. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqh, 2004, juzu'i na 2, shafi.427.
  15. Imam Khumaini, Tauzihul Masa'il, 1426H, shafi na 184.
  16. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqh, 2004, juzu'i na 2, shafi na 280.
  17. «استفتاء از آیت‌الله سیستانی درباره استفاده از داروهای فراوری شده از حیوانات حرام‌گوشت»، پورتال انها
  18. «استفتاء از آیت الله مکارم شیرازی درباره استفاده از ژلاتین، مواد دارویی و آرایشی فراوری‌شده از حیوانات حرام‌گوشت تذکیه‌نشده»، پورتال انهار
  19. «حکم استفاده از مواد دارویی فراوری‌شده از حیوانات حرام‌گوشت تذکیه‌نشده»، پورتال انهار
  20. Hashemi Shahroudi, Farhang Fiqh, 2004, juzu'i na 2, 426 da 427.
  21. سیستانی، رساله توضیح المسائل، مسأله ۹۶، سایت آیت‌الله سیستانی

Nassoshi

* Hashemi Shahroudi, Sayyid Mahmoud, Farhang Fiqhu Kamar yadda mazhabar Ahlul Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Qum, Islamic Fiqh Encyclopaedia Institute, bugu na daya, 1387.