Dukiyar Shubuha

Daga wikishia
Wannan wata ƙasida ce ta siffanta wata mas'ala ta fiƙihu, ba ya halasta a dogara da ita domin ayyukan addini, ku koma zuwa ga risalolin fiƙihu domin ayyukan addini
Littafin Al-urwatul wuska na Sayyid Muhammad Khazim Tabataba'i Yazdi

Dukiyar shubuha (Larabci: مال الشبهة) Kuɗin ko dukiyar shubha, kuɗi ne ko dukiyar da ba a san mai halal ne ba ko haram, saboda shi kuɗin shubha ya sha banban da dukiya ko kuɗin da ya haɗu da na haram, saboda shi kuɗin da ya cakuɗa da haram mutum ya san cewa akwai haram a cikinshi, saɓanin kuɗin shubha ko dukiyar shubha mutum ba shi da masaniya kan cewa wannan ya cakuɗa da haram ko kuma cewa wannan haram ne.

Amma malamai sun tafi kan cewa kuɗin shubha kuɗi ne na halal kuma ba a fitar mi shi da Khumusi kuma idan mutum ya yi aikin hajji da shi ba matsala. Ya zo a cikin ruwayoyi cewa wajibi ne mutum ya yi taka tsantsan kan shubha, Muhammad Taƙiyu Majlisi wanda aka fi sani da Majalisi ya ce mafi alheri shi ne kada mutum ya yi amfani kuɗi ko dukiya ta shubha, shi kuma Imam Khomaini yana ganin cewa, ruwayoyin da suke cewa mu nisanci dukiyar shubuha, suna nusar da mu ne cewa mu nisanci haram, sannan ya kuma ce amfani da kuɗi ko dukiyar shubha makaruhi ne.

Bayani Kan Kuɗi Ko Dukiyar Shubha

Kuɗi ko dukiyar shubha a bincike na fiƙihu[1] da cikin ruwayoyi[2] shi ne kuɗi ko dukiyar da ba a san cewa halal ce ba ko haram[3] ana kiran shi da kuɗin shubha a ruwayoyi saboda kalmar shubha ko shubhohi a cikinsu.[4] daga cikn ruwayoyin da suka zo daga Annabi (S.A.W) akwai «حَلَالٌ بَيِّنٌ وَحَرَامٌ بَيِّنٌ وَشُبُهَاتٌ بَيْنَ ذَلِكَ...» halal a bayyane yake kuma shi ma haram a bayyane yake, amma shubhohi suna nan a tsakaninsu.[5] wasu su na ganin cewa abinci wanda ba a san cewa halal ne ko haram ba, yana ɗaukar sunan dukiyar shubha.[6]

Amma ita shubha a yaran larabci tana nufin abin da ba a san cewa halal ne ko kuma haram ba.[7] ya zo a cikin ruwaya cewa imam Ali (A.S) ya ce, ita shubha ana kiranta shubha ne saboda tana kama da gaskiya.[8]

Banbancin Dukiyar Shubha Da kuɗin Da Ya Haɗe Da haram

Kuɗin shubha ya sha banban da kuɗin da ya haɗu da haram, saboda kuɗin da ya haɗe da haramin mutum ya san cewa akwai haramin a cikinshi, amma kuɗin shubha mutum ya na shakka shin wannan haram ne ko halal.[9]

Hukunce-hukunce

Akwai wasu hukunce-hukunce kan kuɗin shubha: • Halacci: ana ganin cewa kuɗin shubha, kuɗi ne na halal.[10] bisa dogaro kan ruwaya da aka rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S), ya yin da yake cewa; ko wane abu gareka halal ne har sai kasan cewa wannan abun haramun ne.[11] wannan ruwaya tana nuni kan halacci ne da Ibaha.[12]

• Kuɗin shubha ba a fitar mi shi da Khumusi; kuɗin shubha ba shi da Khumusi saboda kuɗi ne na shubha,[13] saɓanin kuɗin da ya haɗe da haram akwai khumusi a cikinshi, saboda haɗewarshi da haram.[14]

• Ana hajji da kuɗin shubha: malaman fiƙihu sun tafi kan cewa babu matsala a yi aikin hajji da kuɗin shubha,[15] amma malam Makarim Sirazi ya na ganin sharaɗi ne samun kuɗin aikin hajji ta hanyar halal.[16]

Yin Taka Tsan-tsan Kan Shubha

Ruwayoyi da dama sun zo a cikin littafan hadisi waɗanda suke nuni da yin taka tsantsan kan shubha, ga wasu daga ciki; «دَعْ مَا يُرِيبُكَ إلى مَا لَا يُرِيبُكَ.»[١٧] Ma'ana, ka bar abin da ake shakka zuwa abin da baka shakka.[17]

«...فَمَنْ تَرَكَ اَلشُّبُهَاتِ نَجَا مِنَ اَلْمُحَرَّمَاتِ وَمَنْ أَخَذَ بِالشُّبُهَاتِ اِرْتَكَبَ اَلْمُحَرَّمَاتِ.»[١٨]

Ma'ana; Duk wanda ya bar shubha ya tsira daga haramun, duk wanda ba ya nesantar shubha, to lalle zai kai ga aikata haramin.[18]

«الْوُقُوفَ عِنْدَ الشُّبْهَةِ خَيْرٌ مِنَ الِاقْتِحَامِ فِي الْهَلَكَةِ.»

ma'ana; Tsayawa kan shubha ko rashin amfani da ita, ya fi alheri kan mutum ya faɗa halaka.[19]

Amma Imam Khomaini ya fassara wannan ruwaya da cewa, tana nusar da mu kan cewa mu guji haramun, kuma makaruhi ne mutum ya yi amfani da kuɗin shubha.[20] Muhammad Taƙiyu Majalisi ya na daga cikin malaman Shi'a a ƙarni na sha ɗaya, ya ce duk da cewa kuɗin shubha halal ne bisa abin da ya zo a ruwayoyi, amma abin da ya fi shi ne a nisance shi gudun kar a faɗa haramin[21] amma wasu sun tafi kan cewa, bisa ruwayoyin da suka zo idan mutum yana da kuɗin shubha wajibi ne mutum ya bar amfani da su har sai ya sami tabbas cewa na halal ne.[22]

Kuma ya zo cewa nisantar kuɗi da abincin shubha ya na daga cikin matakai na tsoran Allah,[23] kuma an naƙalto daga wasu malamai cewa, su na taka tsantsan kan abincin shubha, idan suka ci ba tare da sun lura ba sai daga baya, to su na ƙoƙarin su dawo da shi idan hakan zai yiwu.[24]

Bayanin kula

  1. Al-Shaheed al-Thani, Masalak al-Afham, juzu'i na 4, shafi na 334; Al-Bahrani, al-Hadaiq al-Nadrah, juzu'i na 21, shafi na 197; Al-Naraghi, Awaed al-Ayyam, shafi na 144; Al-Najafi, Jawaharlal Kalam, juzu'i na 26, shafi na 328.
  2. Al-Tusi, Al-Amali, shafi na 381; Varam, Majmueh Varam, juzu'i 1, shafi na 6 da v. 2, shafi na 267.
  3. Al-Imam Al-Khomaini, Al-Makasab al-Muharramah, juzu'i na 2, shafi na 343; Al-Mazandrani, Sharh al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 415; Al-Majlisi, Mir'atul oqol, juzu'i na 1, shafi na 225.
  4. Kulaini, Kafi, juzu'i na 1, shafi na 68; Al-Harr al-Amili, Wasail al-Shia, Juzu'i na 27, shafi na 157-158.
  5. Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 1, shafi na 68.
  6. Malik Ahmadi, Darsnama Rizq Halal, shafi na 178.
  7. Al-Jurjani, Kitab Attarifat, shafi na 103.
  8. Nahj al-Balagha, Tas'hihu Subhi Saleh, na 28, shafi na 81.
  9. Montazeri,Mabani Fikhi Hukumate Islami, juzu'i na 6, shafi na 184.
  10. Al-Ansari, Faraed al-Usul, juzu'i na 2, shafi na 201; Al-Naraghi, Awaed al-Ayyam, shafi na 144; Al-Majlisi, Rawda Al-Mutaqiin, juzu'i na 6, shafi na 489.
  11. Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 5, shafi na 313; Al-Ansari, Faraid Al-Usul, juzu'i na 2, shafi na 200-201; Al-Majlisi, Rawdat al-Muttaqin, juzu'i na 6, shafi na 489.
  12. Al-Ansari, Fara’id Al-Usul, juzu’i na 2, shafi na 219.
  13. Al-Muntazari, Mabanī Fiqh Hukomat-Islami, juzu'i na 6, shafi na 180 da na 184
  14. Al-Tabatabai Al-Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, juzu'i na 4, shafi na 256-257.
  15. Mahmoudi, Manasik Hajji (Mahshi), shafi na 36.
  16. Makarem Al-Shirazi, Manasik Hajji, shafi na 395.
  17. Al-Hurrul Al-Amili, Wasa’il Al-Shi’a, juzu’i na 27, shafi na 167.
  18. Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 1, shafi na 68; Al-Hurrul Al-Amili, juzu'i na 27, shafi na 157.
  19. Al-Kafi, Al-Kulayni, juzu'i na 1, shafi na 50; Al-Hurr Al-Amili, Wasa’il Al-Shi’a, juzu’i na 27; shafi na 157-158.
  20. Al-Imam Al-Khomaini, Al-Makasab al-Muharramah, juzu'i na 2, shafi na 343-344.
  21. Al-Majlisi, Rawda Al-Muttaqiin, juzu'i na 6, shafi na 489.
  22. Malik Ahmadi, Darsenameh Rizk Halal, shafi na 179.
  23. Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i na 67, shafi na 100.
  24. Malik Ahmadi, Darsnama Rizq Halal, shafi na 179-180.

Nassoshi

  • Ibn Abi Firas, Waram, “Majmueh Waraam (Tanbih al-Khawatir wa Nuzhat al-Nawazir),” Qom, Laburaren Faqih, bugu na 1, 1410H.
  • Imam Khumaini, Ruhollah, Al-makasibul Muharrama Qum, Mu'assasa Tsara Da Buga Ayyukan Imam Khumaini, bugu na 1, 1415 Hijira.
  • Al-Ansari, Murtada, Fara'id al-Usul, Qum, Islamic Thought Academy, bugu na 12, 1431H.
  • Al-Bahrani, Yusuf bin Ahmed, Hadaiqun Nazra fi Ahkame Al-itra Tahira, Qum, Mu'assasa Buga Musulunci, bugu na daya, 1405H.
  • Al-Jurjani, Ali bin Muhammad, Kitabe Attarifat', Beirut, Gidan Rayar da Al'adun Larabawa, bugu na 1, 1431H/2010 Miladiyya.
  • Al-Hurr Al-Amili, Muhammad bin Al-Hasan, Wasa'il Al-Shi'a, Qum, Mu'assasa Al-Baiti Template:A.s don farfado da gado, na daya. shekara, 1409 AH.
  • Al-Sharif Al-Radi, Muhammad bin Hussein, Nahj al-Balagha, Tas'hihu: Subhi Saleh, Kum, Hajrat, bugun 1st, 1414.

Shahidus Sani, Zainul-Din bin Ali Al-Amili, Masalik al-Afham, Qum, Mu'assasa Ilimin Musulunci, bugu na 1, 1413H.

  • Al-Tabatabai Al-Yazdi, Muhammad Kazem, Al-Urwah Al-Wuthqa, Qum, Islamic Publishing Foundation, bugu na daya, 1419 AH.
  • Al-Tusi, Muhammad bn Al-Hasan, Al-Amali, bugun: Mu'assasar Al-Ba'athah, Qum, Gidan Al'adu, bugu na 1, 1414H.
  • Al-Kulayni, Muhammad bin Yaqoub, Al-Kafi, bugun: Ali Akbar Al-Ghafari da Muhammad Al-Akhundi, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, bugu na 4, 1407H.
  • Al-Mazandarani, Muhammad Salih, ' Sharhu Al-Kafi (Al-Usul wal-Rawdah) , edita kuma ya inganta shi: Abu Al-Hasan Al-Shaarani, Tehran, Laburaren Musulunci, bugun farko, 1382 AH.
  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Mir'atul oqool edita kuma ya gyara shi: Sayyed Hashim Rasul Mahallati, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, bugu na biyu. 1404 AH.
  • Al-Majlisi, Muhammad Taqi, 'Rawdat al-Muttaqin, Qom, Farhangi Islami Foundation, bugu na 2, 1406H.
  • Al-Najafi, Muhammad Hassan, Jawahir Al-Kalam fi Sharh Al-Islam', Beirut, Dar Ihya Al-Tarath Al-Arabi, bugu na 7, 1404H.
  • Al-Naraqi, Ahmed bin Muhammad Mahdi, ' Awaedul Ayyam, Qum, Mu'assasar Ilimin Musulunci, bugu na 1, 1417 Hijira.
  • Mahmoudi, Muhammad Reda, 'Hajj Rituals (Stuffed), Tehran, bugun Mash'ar, 1429 AH.
  • Makarem Al-Shirazi, Nasser, Manasikul Hajji Qum, Mazhabar Imam Ali bin Abi Talib, bugu na daya, 1426 Hijira.
  • Malik Ahmadi, Ali Asghar, 'Darsnamah Rizq Halal, Mashhad, Mu'assasa Karatun Ilimin Rahbardi da Ilimin Musulunci, bugu na daya, 1392H.
  • Montazeri, Hussein Ali, ' Mabani Fikhi Hukumate Islami, wanda: Mahmoud Salawati da Abul-Fadl Shukuri, suka fassara shi, Qum, Mu'assasa Kayhan, bugu na 1, 1409H.