Waɗanda Ba Muharramai Ba

Daga wikishia
Wannan labarin labari ne mai bayyanawa game da ra'ayi na fikihu kuma ba zai iya zama ma'auni na ayyukan addini ba. Koma zuwa wasu tushe don ayyukan addini.
Risala Ilmiyya

Waɗanda ba Muharramai ba, (Larabci: غير المحارم) kishiyar Muharramai, ana faɗin wannan kalma ga mutumin da dole Mace ta sanya Hijabi a gabansa sannan kuma aure ya halasta tsakaninta da shi. A ra'ayin Malaman Fiƙihu kallon macen da ba Muharrama ba ya halasta in banda fuskarta da hannunta (daga tsintsiyar hannunta zuwa yatsunta) haka kuma kallon fuskarta da hannayenta da jin sautinta ba ya halasta idan ya kasance zai haifar da fitina (jin daɗi) da aikata zunubi, bisa fatawar Malaman Fiƙihu wajibi ne kan Mace ta suturce baki ɗayan jikinta a gaban wanda ba Muharraminta ba, na'am cikin batun lulluɓe zagayen fuska da hannun daga tsintsiyar hannu zuwa geffan yatsu akwai saɓanin ra'ayi tsakanin Malamai, Aksarin Malamai ba sa ganin wajabcin lulluɓe su, haka kuma ba ya halasta ita ma Macen ta Kalli Namiji wanda ba Muharraminta ba. Shafar wanda Muharrami bai halasta ba haka ma keɓancewa da shi tsakanin Mace da Namiji waɗanda ba Muharramai ba saboda tsoron afkawa cikin Saɓo, a fiƙhun Muslunci ya halasta mace ta auri wanda ba Muharraminta ba, na'am auren wanda ba Muharrami a wani lokacin yana zama haramun.

Sanin Mafhumi Da Matsayi

Ana kiran wanda baya daga cikin Muharramai da sunan wanda ba Muharrami ba, abinda ake nufi da Muharramai su ne waɗanda cikin wasiɗa da tsanin ɗaya daga cikin hanyoyin Aure da Shayarwa, Nasaba suke haɗewa da juna da samun ƙarfaffar Alaƙa. [1] an yi amfani da wannan Isɗilahi cikin babukan Fiƙihu misalin babin Aure da Haddodi. [2] Cikin ayoyi 3—31 Suratul Nur Ubangiji ya yi Umarni da kau da idanu daga barin kallon waɗanda ba Muharramai da kuma abin da ya kasance ya haramta. [3] cikin riwayoyi masu tarin yawa da aka nakaƙalto su daga Imamai Ma'asumai (A.S) [4] Imam Baƙir (A.S) ya bayyana cewa magana da waɗanda ba Muharramai ba tarko ne na Shaiɗan. [5] haka ma cikin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) ya ce: Kallon Waɗanda ba Muharramai Kibiya ce mai guba daga Kibiyoyin Shaiɗan. [6] haka kan asasin wata riwaya daga Imam Ali (A.S) yin Magana tare da Mace da ba muharrama yana zama sababin saukar bala’i da karkacewar zukata, [7] Faizul Kashani cikin littafin Mahajjatul Al-Baida [8] da Mulla Muhammad Mahadi Naraƙi cikin littafin Jami’ul As-Sa’adat [9] sun tafi kan cewa kallon waɗanda ba Muharramai ba Kafircewa ni’imar Idanu da Allah ya baka kyauta. Murtada Mutahhari cikin littafin Mas’aleh Hijab, yana ganin Falsafa da Hikimar wajabta kiyaye sanya Hijabi kan Mace da sanya suturar da ta dace a Addinin Muslunci wasu al’amura ne da suke da alaƙa da kiyaye lafiya da kare lafiyar Ruhi da lafiya zamantakewar Al’umma, da kuma ƙarfafa tsarin zamantakewar iyali tare da ƙololuwar girmama Mace, da kare Al’umma daga fajirci. [10]

Hukunce-hukunce Masu Alaƙa Da Waɗanda Ba Muharramai ba

A Fiƙihun Muslunci an tanadi hukunce-hukunce ga waɗanda ba Muharramai ba: Haramcin kallon waɗanda ba Muharramai ba. Kallon Macen da ba Muharrama ba haramun ne in banda zagayen Fuskarta da Hannunta daga tsintsiyar hannu zuwa yatsu.[11] haka kuma hatta kallon zagayen fuskarta da hannayenta idan ya kasance da niyyar jin daɗi sannan akwai tsoran za a iya afkawa cikin Saɓo to shima wannan kallo ya haramta. [12] Haka zalika ita ma Mace baya Halasta ta kalli jikin Namiji wanda ba Muharraminta ba , in banda gabobin da ba a saba lulluɓe su ba daga jikin Namiji misalin ƙwauri, Kai, Hannaye da ƙafafu da sharaɗin ba zata ji sha’awa ba idan da ta kalle su tare da aminci daga afkawa cikin haramun. [13] Bisa fatawar Malaman Fiƙihun Shi’a babu matsala a kallon zagayen fuskar Mace da niyyar aurenta. [14] ba’arin Malaman Fiƙihu suna ganin halascin kallon wani Miƙdarin jikinta misalin wuyanta wani sashe daga ƙirjinta idan ya je da niyyar aure tare kuma da sharaɗin rashin jin daɗi daga kallon. [15] Haka kallon Fim da Hotunan Matan da basa sa Hijabi idan ya kasance babu sha’awa kuma ba a san su ba to babu matsala, amma idan ya kasance an sansu to baya halasta a kalli Hotunansu da Fim ɗinsu. [16] Kallon da likita yake yi ga jikin waɗanda ba Muharramansa ba idan ya kasance sakamakon larura ta yi musu magani, babu matsala ya halasta. [17] Kallon Hotunan Mata da ba Musulmai ba tare da Hijabi a jikinsu ba idan ya kasance babu niyyar jin daɗi kuma ba zai haifar da ɓarna ba to babu matsala. [18]

Wajabcin Suturce Jiki A Gaban Waɗanda Ba Muharramai Ba

Wajibi kan Mata su suturce jikinsu daga idanun Namijin da ba Muharraminsu ba. [19] na’am akwai saɓanin Fatawowin Malamai kan wajabcin lulluɓe Fuska da hanneyensu (daga tsintsiyar hannu zuwa yatsu). [20] bisa ra’ayin wasu Malamai misalin Shaik Ɗusi, [21] Sahibul Hada’iƙ, [22] Shaik Ansari, [23] Sayyid Kazim Ɗabaɗaba’i Yazdi [24] Sayyid Hakim, [25] Imam Khomaini, [26] Sayyid Ali Khamna’i [27] lulluɓe Fuska da Hannaye daga tsintsiyar hannu zuwa geffan yatsu ba wajibi bane kan Mata, amma wasu ba’ari daga Malaman Fiƙihu kamar misalin Allama Hilli cikin littafin Tazkiratul Al-Fuƙaha, [28] Fadil Miƙdad [29] da Sayyid Abdul-A’ala Sabzawari [30] suna ganin wajabcin lulluɓe fuska da hannaye ga Mace. Haka kuma kan asasin ra’ayin baki ɗayan Malaman Fiƙihu idan ya zamana akwai tsoron faɗawa saɓo ko kuma jarrabtuwar Namiji da Haramun sakamakon buɗe ido fuska da hannu daga Mata, a irin wannan yanayi wajibi ne su rufe fuskarsu da hannunsu. [31]

Haramcin Taɓa Waɗanda Ba Muharramai Ba

Kan asasin fatawar Malaman Fiƙihu taɓa wanda ba Muharramai ba haramun ne, na’am idan ya kasance halin larura kamar misalin Halin magani da ko ceto rai mutum to a irin wannan hali yana halasta. [32] haka kuma taɓa jikin waɗanda ba Muharramai cikin tufafi ko saman wani shinge idan ya zama babu sha’awa babu kuma niyyar jin daɗi, to babu matsala, [33] ba’arin Malaman Fiƙihu suna ganin babu Haramci cikin gaisawa da Matar da ba Muharrama idan ya kasance tana sanye da kyalle ko safar hannu tsakani ko babu wata mummunar aniya sannan kuma ba a matsa hannun ba, [34]

Hukunci Jin Muryar Macen Da Muharrama Ba

Kan asasin ra’ayin Malaman Fiƙihu aza Kunnuwa domin jin muryar Mace da ba Muharrama idan ya kasance babu jin daɗi kuma babu tsoron afkawa saɓo, ya halasta, amma idan ya kasance akwai tsoron afkawa saɓo da kuma niyyar jin daɗi, a irin wannan yanayi ya haramta. [35] ɗaga muryar Mace yayin da take sallah a wurin da wanda ba Muharraminta ba zai iya jin muryarta. A ra’ayin wasu Malamai misalin Shahidul Awwal haramun ne kuma sallarta ta ɓaci, [36] Sahibul Jawahir tare da cewa ya yarda da haramcin wannan aiki amma bai yarda da cewa sallarta ta ɓaci ba. [37]

Hukuncin Keɓancewa Tare da Wanda Ba Muharrami Ba

a ra’ayin wasu daga cikin Malaman Fiƙihu suna ganin Haramcin kebancewar Macen da ba Muharrama ba, [38] wasu ba’arin Malaman Fiƙihu suna ganin Haramcin hakan kaɗai cikin surar tsammanin afkawa cikin Saɓo, [39] a fatawar Ayatullahi Kuyi wanda ya mutu shekara 1371 h shamsi, keɓancewa da Matar da ba Muharrama ba yana kasancewa haramun a babin Muƙaddimar afkawa cikin saɓo, [40] bisa ra’ayin Muhammad Hassan Najafi Marubucin littafin Aljawahirul Kalam, kebancewa da Matar da ba Muharrama ba Makruhi ne. [41]

Magana

Magana Tare da Wanda Ba Muharrami Ba Kan asasin Fatawar Malaman fiƙihu idan Magana da wanda ba Muharrami baya kasance babu jin daɗi kuma babu tsoran afkawa aikata saɓo, to ya halasta. [42] A ra’ayin Mirza Jawad Tabrizi ya kamata a ƙauracewa Magana tsakanin Saurayi da Budurwa ko da babu jin daɗi kuma babu tsoron afkawa saɓo. [43] Musayen saƙo tsakanin waɗanda ba Muharraman juna (ma’ana chartin da email) idan ya kasance zai haifar da ɓarna da afkawa saɓo to ya haramta. [44]

Halascin Auren Wanda Ba Muharrami Ba

A fiƙhun Muslunci aure kaɗai yana halasta da wanda ba Muharrami ba, sannan kuma yana haramta tsakanin waɗanda suke Muharramai. [45] na’am ƴar’uwar Matarka duk da cewa ba Muharramarka ba ce, sai dai cewa tare da haka ba zaka iya aurenta ba matukar Matarka tana raye baka sake ta ba. [46] Auren wasu ba’arin waɗanda ba Muharramai bisa wasu sharuɗɗa yana iya zama haramun na dindin har abda: Matar da ka sake ta sau tara, babu aure tsakaninku har abada. [47] Babu har abada tsakanin mutumin da ya yi zina da Mahaifiyar Mace kafin aurenta. [48] Babu aure har abada tsakanin Wanda ya yi zina da Mace alhalin tana da aure [49] babu aure har abada tsakanin Mutumin da ya aikata luwaɗi da ɗan Matar da yake son aure ko Mahaifinta ko ɗan’uwanta kafin aurenta. [50]

Bayanin kula

  1. Mojtahedi Tehrani: seh resaleh, Gunahane Kabireh, Mahram Na Mahram,Manyan, Haƙam al-Ghaibah, 2013, shafi na 10.
  2. Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 29, shafi na 237; Muassaseh Dayiratul Almaref Alfikh Al-islami , Farhang Farsi, 1387, juzu'i na 5, shafi na 405.
  3. ƙaraati, Tafsir Noor, 2007, juzu'i na 6, shafi na 171-173.
  4. Noori, Mostadrak al-Wasail, 1408H, juzu'i na 14, shafi na 272.
  5. Noori, Mostadrak Al-Wasa'il, 1408H, juzu'i na 14, shafi na 272.
  6. Sheikh Sadouƙ, Man La Yahzara Al-Faƙih, 1413 AH, juzu'i na 4, shafi na 18.
  7. Ibn Shu'uba Harrani, Tohaf Al-Uƙool, 1404H, shafi na 151.
  8. Faizul Kashani, Mahja Al Bayda, 1417 AH, juzu'i na 7, shafi na 161.
  9. Naraghi, Jame Al-Saadat, Al-Alami Publishing House, Juzu'i na 3, shafi na 245.
  10. Motahari, Mas'aleh Hijab, 2006, shafi na 76.
  11. Najafi, Jawaher Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 29, shafi na 75.
  12. Najafi, Jaɓwaher Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 29, shafi na 75; Sistani,tauzihul Al-masa’il, 1415H, shafi na 508.
  13. Sistani, tauzihul Al-Masa'il, 1415 AH, shafi na 508; Makarem Shirazi,Ahkam Khanuwade, 2009, shafi na 22.
  14. Shahid Thani, Masalik Al-Afham, 1412 AH, juzu'i na 7, shafi na 40.
  15. Shahid Thani, Al-Rawda Al-Bahiya, 1410 AH, Juzu'i na 5, shafi na 97-98; Tabrizi, Estifta'at Jadid, 1385, juzu'i na 1, shafi na 355.
  16. تبریزی، استفتائات جدید، ۱۳۸۵ش، ج۱، ص۳۵۶.
  17. Khoei, Estifta'at, shafi na 299; Makarem Shirazi, Ahkam Khanuwade, 2009, shafi na 25.
  18. Makarem Shirazi, Ahkam Khanuwadei, 2009, shafi na 31.
  19. Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi na 4.
  20. Mu'assaseh Dayiratul Al-maref Alfikh Al-Islami,, Farhng Fikh Farsi, 1387, juzu'i na 2, shafi na 283.
  21. Sheikh Tusi, Al-Mabsut, 1387H, juzu'i na 4, shafi na 160.
  22. Bahrani, Hadaeƙ Al-Nadrah, Al-Nashar al-Islami Foundation of Jamaat al-Madrasin, juzu'i na 23, shafi na 56.
  23. Sheikh Ansari, Kitab Al-Nikah, 1415H, shafi na 48.
  24. Yazdi Tabatabai, Al-Urwa Al-Wughta, 1430 AH, juzu'i na 6, shafi na 206.
  25. Hakim, Mustamsak Al-Urwa, 1391 AH, juzu'i na 5, shafi na 241-242.
  26. Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila, 1434H, juzu'i na 2, shafi na 261.
  27. <a class="eɗternal teɗt" href="https://b2n.ir/e64369">«پوشش و نگاه کردن»</a>سایت Khamenei.ir
  28. Allameh Hilli, Tazkirah Al-Fuƙaha, Al-Razwiyyah Library, Lahiya Al-Aƙti al-Jaafriya, juzu'i na 2, shafi na 573
  29. Fazel Miƙdad, Kanzul Al-Irfan, 1373, juzu'i na 2, shafi.222
  30. Sabzeɓari, Mahezzab Al-Ahkam, 1413 AH, juzu'i na 5, shafi na 230-237.
  31. Bahrani, Hadaeƙ Al-Nadrah, Al-Nashar al-Islami Est. Sistani, tauzihul Almasa'il, 1415H, shafi na 508.
  32. Najafi, Jawahir Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 29, shafi na 100.
  33. Najafi, Jawaher Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 29, shafi na 99; Fiƙh *islami, Al-Masu'a al-Fiƙhiyyah, 1423 AH, juzu'i na 5, shafi na 381.
  34. Imam Khumaini,Risaleh Najat al-Abad, 1409H, shafi na 363.
  35. Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Waghta, 1415 AH, juzu'i na 5, shafi na 490.
  36. Shahidi na farko, Zikra Al-Shia, 1419 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 322.
  37. Najafi, Jawaher Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 9, shafi na 383-384.
  38. Shahid Sani, Masalik Al-Afham, 1412 AH, juzu'i na 9, shafi na 323-325.
  39. Mu'assaseh Dayiratul Al-maref Alfikh Al-Islami, musu'atul Alfikhiyya, 1423 AH, juzu'i na 5, shafi na 185.
  40. Tawhidi, Misbah Al-Faƙahah, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 350.
  41. Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 32, shafi na 344.
  42. Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 29, shafi na 99.
  43. Tabrizi, Estgifta'at Jadid, 2005, shafi na 362.
  44. <a class="eɗternal teɗt" href="https://b2n.ir/ɗ39095">«ارتباط با نامحرم از طریق پیامک، چت و ایمیل»، سایت پایگاه اطلاع‌رسانی دفتر آیت الله العظمی مکارم شیرازی.</a>
  45. Misali, duba Mohaghegh Hilli, Shara’i Al-Islam, 1408 AH, juzu’i na 2, shafi na 224; Najafi, Jawahir Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 29, shafi na 237.
  46. Bani Hashemi Khumaini, Tauzihul Al-masa'il Sizda Maraji'u, 1385, Ahkam Nikah, shafi na 2390.
  47. Mofid, Al-Muƙni'a, Islamic Publishing House, juzu'i na 1, shafi na 501.
  48. Shahid Sani, Masalak Al-Afham, 1412 AH, juzu'i na 7, shafi na 297-298.
  49. Najafi, Jawahir Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 29, shafi na 446.
  50. Mohaghegh Hilli, Shara’i Al-Islam, 1408H, juzu’i na 2, shafi na 233.

Nassoshi

  • Ibn Shuba Harrani, Hassan bin Ali, Tahf al-Aƙool, Kum, Mu’assasa Nashar al-Islami, bugu na biyu, 1404H.
  • Imam Khomeini, Sayyid Ruhollah, Tahrir al-Wasila, Kum, Al-Aruj Foundation Press, bugun farko, 1434H.
  • Imam Khomeini, Sayyid Ruhollah, Risalah Najat al-Abad, Tehran, Imam Khumaini Aiyuka Editing and Publishing Institute, bugu na farko, 1422H.
  • Bahrani, Youssef, Hadaiƙ Al-Nadrah fi Haƙam Al-Atrah al-Tahira, ƙom, Al-Nashar al-Islami Foundation of Jamaat al-Madrasin, Bita.
  • Bani Hashemi Khomeini, Seyyed Mohammad Hasan, sharhin bayani kan magana ta goma sha uku, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, 1385.
  • Tabrizi, Mirzajaɓad, Estifta'at Jadid, ƙom, Sarwar Publications, bugu na uku, 2005.
  • Tawhidi, Mohammad Ali, Misbah Al-Faƙaha, ƙum, Ansariyya Publishing House, 1417H.
  • Hakim, Seyyed Mohsen, Mustamsak Al-Arwa al-Wathaghi, ƙom, Dar al-Tafsir, 1391H.
  • Khoei, Seyyed Abulƙasem, Estifta'at jadid, Najaf, Al-Khoei Islamic Foundation, Bita.
  • «پوشش و نگاه کردن»، سایت Khamenei.ir، تاریخ درج مطلب: ۱۴ مهرماه ۱۳۹۳ش، تاریخ بازدید: ۴ اردیبهشت ۱۴۰۰ش.
  • Sabzwari, Sayyid Abdul A'Ala, Mahazzeb Al-Ahkam, ƙom, Dar al-Tafsir Publications, 1413 AH.
  • Sistani, Sayyid Ali, Tauzihul Al-Masa'il, ƙum, Mehr Publications, 1415H.
  • شهید اول، محمد بن مکی، ذکری‌الشیعه فی احکام الشریعة، قم، ‌‌مؤسسه آل البیت علیهم السلام‌، چاپ اول، ۱۴۱۹ق.
  • شهید ثانی، زین‌‎الدین بن علی، مسالک الافهام، قم، مؤسسة المعارف الإسلامیة، ۱۴۱۳ق.
  • Shaheed Thani, Zain Al-Din Makki, Al-Rawda Al-Bahiya fi Sharh Al-Luma' Al-Damashƙiya, ƙom, Daɓari Publications, 1410 AH.
  • شیخ انصاری، مرتضی، کتاب‌النکاح، قم، تراث الشيخ الأعظم، ۱۴۱۵ق.
  • شیخ صدوق، محمد بن علی، من لا یحضره الفقیه، قم، دفتر انتشارات اسلامی وابسته به جامعه مدرسین حوزه علمیه قم‌، چاپ دوم، ۱۴۱۳ق.
  • شیخ طوسی، محمد بن حسن، المبسوط فی فقه الامامیة، تهران، المكتبة المرتضویة لإحیاء الآثار الجعفریة، چاپ سوم، ۱۳۸۷ق.
  • طباطبایی یزدی، سید محمدکاظم، العروة الوثقی، قم، مؤسسه جهانی سبطین (علیهماالسلام)، ۱۴۳۰ق.
  • علامه حلی، حسن بن یوسف، تذکرة‌الفقها، قم، منشورات المكتبة المرتضویة لإحیاء الآثار الجعفریة، بی‌تا.
  • فاضل مقداد، مقداد بن عبدالله، کنزالعرفان فی فقه القرآن، قم، انتشارات مرتضوی، ۱۳۷۳ش.
  • فیض کاشانی، محمد بن شاه‌مرتضی، محجة البیضاء، قم، موسسه النشر الاسلامی، چاپ چهارم، ۱۴۱۷ق.
  • ƙaraeti, Mohsen, Tafsir Noor, Tehran, Cibiyar Al'adu ta Darussan Kur'ani, 2007.

Muassaseh Dayitarul Almaref Alfikh Al-Islami, Al-Musua'at Al-Fiƙhiyyah, ƙum, Cibiyar Ilimin Fikihu ta Musulunci, 1423H.

  • Mu'assasatu Dayiratul Al-maref Alfikh Al-Islami, Farhang Fikih Farsi, ƙum, Mu'assasatu Dayiratul Al-maref Alfikh Al-Islami, 1387.
  • Mojtahedi Tehrani, Ahmad, Seh Risaleh: Gunahane Kabireh, Mahram wa Na Mahram, Ahkam Al-Ghibah, ƙum, Cibiyar Dar Rah Haƙ, 2013.
  • Mohaghegh Hilli, Jafar bin Hasan, Sharia al-Islam, ƙum, Cibiyar Ismailiya, bugu na biyu, 1408H.
  • محقق کرکی، جامع‌المقاصد، قم، مؤسسه آل البیت علیهم السلام‌، چاپ دوم، ۱۴۱۴ق.
  • Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Muƙna, ƙum, Sheikh Mofid Hazara World Congress, 1413 AH.
  • Motahari, Morteza, Mas'aleh Hijab, ƙum, Sadra Publications, 2006.
  • مکارم شیرازی، ناصر، احکام خانواده، قم، امام علی بن ابی طالب علیه السلام‌، چاپ دوم، ۱۳۸۹ش.
  • Najafi, Mohammad Hasan, Jawaher Al-Kalam fi Sharh Shariah al-Islam, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1404 AH.
  • نراقی، ملامحمد مهدی، جامع السعادات، بیروت، مؤسسة الأعلمی للمطبوعات، چاپ چهارم، بی‌تا.
  • نوری، میرزاحسین، مستدرک الوسائل، قم، مؤسسة آل البيت عليهم السلام لإحياء التراث، ۱۴۰۸ق.