Mikewar Assayid Hasani

Daga wikishia

Mikewar Assayid Hasani (Larabci: قيام السيد الحسني) na daga Alamomin bayyanar Imamul Mahadi (A.F) kan asasin riwayoyi, hakika Assayid Hasani zai kasance wani matashi daga garin Dailama da zai mike ya `daga sauti domin amsa kiran Imam Mahadi (A.S), za a samu mutane daga garin Talakan sun taimaka masa, hakika motsin Assayid Hasani ya cudanya da bayyanar Imam Mahadi (A.F) a garin Kufa ko kuma kusa da garin zai yiwa Imam Mahadi (A.F) mubaya’a Kan asasin wasu riwayoyin daban, na bayyana cewa zai mike ne a garin Makka kuma mutanen garin za su kashe shi, wasu ba’arin Malamai da jingina da wannan riwayoyi sun rinjayar da tsammanin cewa ba wani Assayid Hasani ba face Kashe Nafsuz Zakiyya da kashe a garin Makka ya kasance alamomin bayyanar Imam (A.F) na yankan shakku, wasu kuma sun yi shakku kan ingancin wadannan riwayoyi.

Alamomin bayyana

A cikin ba’arin wasu riwayoyi an hakaito mikewar wani mutum me suna Assayid Hasani da cewa yana daga Alamomin bayyana [1] daga cikin jumlarsu akwai abinda ya zo cikin hudubar Albayan ba’arinta yayi bayani kan alamomin bayyanarsa, Assayid Hasani mu’amalarsa da Imam Mahadi (A.F) an hakaito maganarsa [2] ta bakin Najamuddini Attabasi Masani Muhakkiki daga shi’a akwai kusan hadisi bakwai zuwa takwas kan maudu’in Assayid Hasani, [3] za a fa’idantu daga garesu kan cewa mikewar Assayid Hasani tana daga alamomin bayyanar Imam Mahadi (A.F) cikin fadinsa wadannan riwayoyi sun kai haddin istifaza a ilimin hadisi, kuma za a iya samun nutsuwa kan cewa ba’arin wasu cikin hadisan lallai daga Imamai Ma’asumai (A.S) [4] suka zo, duk da cewa cikin abinda kowannensu ya kunsa akwai dan banbance-banbance. [5] Kan asasin riwayoyin da Malam Kadi Nurullahi Shushtari a littafinsa Ihkakul Hakki ya nakalto cewa Assayid Hasani yana daga cikin `ya`yan Imam Hassan Mujtaba (A.S) [6] a lokacin bayyanar Imamul Mahadi (A.F) zai motsazai yi mubaya’a ga Imam Mahadi (A.F) tareda rundunar Sojoji [7]

Yaya motsin ya kasance

Kamar yanda Najamud dini Attabasi yake fada: hakika riwayoyin da suka hakaito motsin Assayid Hasani mabanbanta juna ne [8] wasu cikinsu sun hakaita cewa motsin nasa zai fara ne daga garin Dailamaa Kufa ko kuma dai kusa da garin Kufa, zai yi ma Imam Mahadi (A.F) mubaya’a [9] amma kuwa wasu adadin riwayoyin daban sun hakaito cewa za a kasha shi a garin Makka. [10] Wani Hadisi da aka daganta shi ga Imam Sadik (A.S) hakika Assayid Hasani wani matashi ne mai kyawun fuska da zai fito daga garin Dailama ya yi yekuwayaku iyalan Ahmad kuma amsa kiran wannan mutumin da kuka yi takaici da bakin cikin fakuwarsa, za a samu wasu mutane daga garin Talikan da suke karfin imani makasa Azzalumai zasu shiga garin Kufa, a wannan lokaci zasu tsarkake yankunan Kufa daga marasa addini, zasu maida kufa matsuguninsu masaukinsu, lokacin da labarin bayyanar Imam Mahadi (A.F) ya isu kunnen Assayid Hasani da Sahabbansa, zai nemi a nuna masa alamomin bayyana, bayan ganin karamomi daga Imamul Mahadi (A.S) sai shi da rundunarsa su yi Imam mubaya’a illa mutum dubu arba’in daga Zaidiyya da suka ki yin mubaya’a. [11] Kan asasin wata riwayar a lokacin bayyanarsa (A.S) a Makka Assayid Hasani zai motsa sai mutanen garin su kashe shi su aika da kansa wurin Shami, sai dai kuma cikin wadannan riwayoyi sun kunshi cewa fitiwar Assayid Hasani na daga alamomin farajin Imam bawai alamomin bayyanarsa ba, haka kuma cikinsu anyi Magana kan sabani da zai kasance ckin `ya`yan Abbas da raunanar hukumarsu, akwai shakku kan ingancin isnadi da abinda hadisin yake kunshe da shi.[12]

Shin Assayid Hasani shine dai Nafsuz Zakiyya?

Mulla Salihu Mazandarani Ma’abocin Sharhin Kitabu Alkafi cikin Sharhin Hadisi daga alamomin bayyana ya kawo tsammani cewa akwai yiwuwar Assayid Hasani ya zamanto shine dai Nafsuz Zakiyya,[13] dalili kan haa=kan shine riwayar da hakaito kan cewa mutanen garin Makka za su kashe Assayid Hasani da kuma aikawa da kansa zuwa ga Shami Sufyani a kokacin bayyanar Imam (A.F),[14] Nafsuz Zakiya wani mutum ne daga tsatson Imam Husanini (A.S), [15] da a kashe shi a garin Makka kusa da Rukunu da Mukam Ibrahim da Masallacin Harami,[16] kuma kashe shi yana daga alamomi bayyanarsa na yankan shakku [17]

Bayanin kula

  1. Duba Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 53, shafi na 16; Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Juzu'i na 8, shafi na 225, H. 285; Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 270.
  2. Tabasi, “Sayyid Hosni dar hudubar Al-Bayan az Sanjad ta Matan” shafi na 52.
  3. Tabesi, "Nagareshi dar riwayat Hassani", shafi na 26
  4. Tabesi, "Nagareshi dar riwayat Hassani", shafi na
  5. Tabesi, "Nagareshi dar riwayat Hassani", shafi na 47
  6. Shushtri, Ahqaq al-Haq, 1409 AH, juzu'i na 29, shafi na 448.
  7. Shushtri, Ahqaq al-Haq, 1409 AH, juzu'i na 29, shafi na 448.
  8. Tabasi, “Halaye a cikin hadisai Hassani”, shafi na 47.
  9. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 53, shafi na 15-16.
  10. Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Juzu'i na 8, shafi na 225, H. 285; Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 270.
  11. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 53, shafi na 16; Yazdi Haeri, Elzam al-Nasib, 1422 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 218.
  12. Duba Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 1393, juzu'i na 7, shafi na 439-441.
  13. Mazandarani, Sharh al-Kafi, 1380 AH, juzu'i na 12, shafi na 414.
  14. ,Dubi Salimian, FarhangNameh Mahdavit , 2008, shafi na 208.
  15. Duba Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 52, shafi na 223.
  16. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 1, shafi na 331.
  17. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi 650, h7.

Nassoshi

  • Salimian, Khodamorad, FarhangNameh Mahdawiyya, Qum, Hazrat Mahdi Mououd Cultural Foundation, bugu na biyu, 2008.
  • Shushtri, Qazi Noorullah, Ahqaq al-Haq da Izhaq al-Batil, Gabatarwa na Shahab al-Din Marashi, Qum, Hazrat Ayatullah Azami Marashi Marashi Najafi Public Library, 1409 AH.
  • Saduk Muhammad Bn Ali کمال‌الدین و تمام النعمة، علی‌اکبر غفاری
  • طبسی، نجم‌الدین، «نگرشی در روایات سید حسنی»، انتظار موعود، ش۳۱، زمستان ۱۳۸۸ش.
  • طبسی، نجم‌الدین، «سید حسنی در خطبه البیان»، انتظار موعود، ش ۳۲، بهار و تابستان ۱۳۸۹ش.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, al-kafi, Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya, bugun 4, 1407H.
  • Mazandrani, Mulla Mohammad Saleh bin Ahmad, Sharh al-Kafi - Al-Asul da al-Rawzah, Abul Hasan Shearani ya inganta shi, Tehran, Al-Maktaba al-Islami, 1382H.
  • مجلسی، محمدباقر، بحار الانوار، بیروت، دار احیاء التراث العربی، ۱۴۰۳ق.
  • محمدی ری‌شهری، محمد، دانشنامه امام مهدی(عج)، قم، دار الحدیث، ۱۳۹۳ش.
  • Nomani, Muhammad bin Ibrahim, Al-Ghaibah, bugun Ali Akbar Ghafari, Tehran, Publishing Sadouq, 1397H.
  • یزدی حائری، علی، الزام الناصب فی اثبات الحجة الغائب، تصحیح علی عاشور، بیروت، مؤسسه الاعلمی، ۱۴۲۲ق.