Kashe Tsarkakakken Rai

Daga wikishia

Kashe tsarkakakke rai, (Larabci: قتل النفس الزكية) Yana daga alamomin bayyanar Imam Mahadi kashe rayukan da basu jiba basu gani ba, za'a kashe ɗaya daga magoya bayan Imam a kusa da Ka'aba, shi wannan da za a kashe yana daga jikokin Imam Husaini (A.S) za a kashe shi a gefan ɗakin Ka'aba a Haramin Makka.

Ruwayoyi da yawa sun kawo hakan a matsayin manyan alamomin bayyanar Imam Mahadi (A.J). Mula Salihu Mazandarani ya kawo a littafinsa cewa akwai yiwuwar cewa wannan mutumin da za a kashe ya zamanto sunansa Sayyid Hasani.

Wanene Wannan Mutumin

Nafsuz zakiyya (Rai mai tsarki) mutum ne da ya zo a ruwayoyi cewa ,yana da taƙawa da zuhudu ga tsoran Allah,[1] kuma kasha shi yana daga alamomin bayyanar Imam Mahadi,[2] yana daga jikokin Imam Husaini kaman yadda ya zo a ruwayoyi,[3] sunansa Muhammad Bn Hasan.[4]

Nafsuz zakiyya yana daga manyan mataimakan Imam Mahadi, wanda shi Imam yake turawa zuwa garin makka ga magoya bayan Imam ɗin, Imam zai cewa magoya bayansa: Shin ku Ahlu makka makwa nemana, Sai dai ni zan turo wani zuwa gare ku saboda cika umarnin Allah da tabbatar da hujja akan ku, Lokacin da Nafsuz Zakiyya zai bayyana kansa a matsayin ɗan aiken Imam, mutane za su afka masa da duka har su yanke kansa a tsakanin Rukuni da maƙam[5]

Tabbbatattun Alamomin Bayyanar Imam Mahadi (A.F)

Imam Sadiƙ (A.S):

قَبْلَ قِيَامِ الْقَائِمِ خَمْسُ عَلَامَاتٍ مَحْتُومَاتٍ الْيَمَانِيُّ وَ السُّفْيَانِيُّ وَ الصَّيْحَةُ وَ قَتْلُ النَّفْسِ الزَّكِيَّةِ وَ الْخَسْفُ بِالْبَيْدَاءِ؛

Kafin miƙewar ƙa'im akwai wasu tabbatattun alamomi guda biyar: Yamani, Sufyani, karajin sama, kashe nafsuz zakiyya da kisfewar ƙasa a baida'u

Tarikh Bayigani, Sadouq, Kamaluddin, 2014, juzu'i na 2, shafi na 650, H7.

kaman yadda ya zo a wannan ruwayar ta Imam Sadik as kashe Nafsuz zakiyya da kira daga sama da fitowar Sufyani da ruftawar ƙasa suna daga alamomin bayyanar Imam na ba makawa.[6] ya zo a Kamaluddin, ruwaya daga Imam Sadiƙ ya ce tsakanin kashe Nafsuz zakiyya da bayyanar Imam dare goma sha biyar ne kawai,[7] a wani hadisin daga Imam Baƙir as yana cewa : inda za a kashe Nafsuz zakiyya a haramin Makka zai kasance tsakanin maƙamu Ibrahim da rukuni.[8]

Mulla Salihu Mazandarani mai sharhin littafin; Alkafi a sharhin wannan hadisin ya kawo yiwuwar wannan Nafsuz Zakiyya ya kasance Sayyid Hasani, wanda yana daga alamomin bayyanar Imam Mahadi (A.F).[9] dalilin wannan maganar tasa ruwayace da take cewa za a kashe Sayyid Hasani a hannun mutanan Makka kuma za su tura da kansa zuwa gun Sufyani, a daidai lokacin bayyanar Imam Mahadi (A.F).[10]

Taɗbiƙi Na Tarihi

Ya zo a littattafan tarihi cewa wasu daga magoya bayan Muhammad bin Abdullahi (ya mutu a 145h) suna ganin cewa shi ne wannan Nafsuz zakiyya ɗin.[11] bayan Yahaya bin Zaid ya yi shahada sai suka yi masa bai'a a matsayin Imam Mahadi.[12] a shekara ta 145h ya yi wa Mansur Abbasi tawaye, an kasheshi a wani guri da ake kira Ahjaruzzait kusa da Madina.[13]

Wasu ruwayoyin sun kawo cewa Nafsuz zakiyya mutum biyune ɗayan za'a kasheshi a makka ɗayan kuma tare da mutanansa su saba'in a Kufa[14] Kurani a littafin a na Asru Azzhur ya ce , akwai yiwuwar, Sayyid Muhammad Baƙir Sadr( shahada 1359h) shi ne ɗaya Nafsuz Zakiyya da akace za'a kashe shi a bayan garin Kufa.[15]

Bayanin kula

  1. Mohammadi-ri Shahri, Danesnameh Imam Mahdi, 1393, juzu’i na 7, shafi na 438.
  2. Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 264.
  3. Ayashi, Tafsir al-Ayashi, 1380 AH, juzu'i na 1, shafi na 65.
  4. Sheikh Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 1, shafi na 331, h16.
  5. Allameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 52, shafi na 307.
  6. Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi 264, h. Sheikh Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 649, h1.
  7. Sheikh Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 649, h2.
  8. Sheikh Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 1, shafi na 331, h16.
  9. Mazandarani, Sharh al-Kafi, 1380 AH, juzu'i na 12, shafi 414.
  10. Dubi Salimian, Farhangnameh Mahdaviyat, 2008, shafi na 208.
  11. Abul Faraj Esfahani, Muqatil al-Talbeyin, Dar al-Marafa, shafi na 207.
  12. Abul Faraj Esfahani, Muqatil al-Talbeyin, Dar al-Marafa, shafi na 207.
  13. Abul Faraj Esfahani, Muqatil al-Talbeyin, Dar al-Marafa, shafi na 207.
  14. Duba Allameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 52, shafi na 273.
  15. Korani, Asr al-Zhohor, 1408H, shafi na 126.

Nassoshi

  • Abul Faraj Esfahani, Ali bin Hossein, Muqatil al-Talbeyin, bincike na Sayyid Ahmad Saqr, Beirut, Dar al-Marafah, Bita.
  • Salimian, Khodamorad,Farhananmeh Mahawiyat, Qum, Hazrat Mahdi Mououd Cultural Foundation, bugu na biyu, 2008.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Kamal al-Din da Tamma Al-Naimah, Ali Akbar Ghafari, Tehran, Islamia, bugu na biyu, 1395H.
  • Allameh Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Dar Ahya al-Trath al-Arabi, Beirut, bugu na biyu, 1403H.
  • Ayashi, Muhammad Bin Mas'ud, Tafsir Al-Ayashi, Sahih Rasouli Mahalati, Tehran, Al-Muttaba Al-Alamiya-Islamiyya, 1390H.
  • Korani, Ali, Asr al-Zahur, markaz nashare Maktab Al-Alam, bugu na farko, 1408H.
  • Mazandarani, Mulla Mohammad Saleh bin Ahmad, Sharh Al-Kafi - Al-Asul da Al-Rawzah, Abul Hasan Shearani ya inganta shi, Tehran, Al-Maktaba al-Islami, 1382H.
  • Mohammadi Rishahri, Muhammad, Ilimin Imam Mahdi (Aj), Kum, Dar Al Hadith, 2013.
  • Nomani, Mohammad bin Ibrahim, Al-Ghaibah, Ali Akbar Ghafari, Tehran, Publishing Sadouq, 1397 AH.