Miƙewar Kurasani
Mikewar Kurasani (Larabci: خروج الخراساني) yana daga cikin Alamomin Bayyana, ishara ce zuwa ga Mikewar wani Mutumin garin Kurasan, kuma zai faru ne a daidai lokacin fitowar Sufyani da Mikewar Yamani, wasu Ba’ari daga Masu zurfafa bincike kansa sun bayyana cewa Kurasani shi ne Ma’abocin Bakaken Tutoci kuma Rundunarsa karkashin Kwamandanci Salihu Bn Shu’aibu za su samu nasara da galaba kan Sufyani. Na’am dangane da batun Bakaken Tutoci akwai sabanin Ra’ayoyi a tsakanin Masu bincike kan lamarin Bayyanar Imam Mahadi (A.F), wasu ba’ari suna ganin Abu Muslim Kurasani wanda ya yaki Banu Umayya shi ne Jagoran Bakaken Tutoci, wasu kuma suna ganin Bakaken Tutoci za su zo ne kafin Bayyanar Imam Mahadi (A.F).
Sayyid Kurasani
Cikin riwayoyin Alamomin Bayyana, an kawo rahoton mikewar wani Mutum daga Kurasan matsayin daya daga cikin Alamomin Bayyana [1] Taken Kurasani ya zo cikin riwayoyi da suke da alaka da Kurasan gabashin Duniya da kuma wani Mutum da zai Mike tare da Mutanen garin Kurasan [2] Cikin riwayoyin da aka kawo, hakika Hususiyoyi misalin Kurasani da kuma kasancewarsa Sharifi duka ba su zo ba [3] tare da haka a cewar Ali Kurani cikin littafin Asarul Az-Zuhur, a cikin litattafan Ahlus-sunna [4] da kuma Litaffan Shi’a na baya-bayan nan an bayyana cewa Kurasani daya ne daga tsatson Imam Hassan (A.S) ko kuma Imam Husaini (A.S), sunansa ya zo a riwayoyin da Unwanin Kurasani ko Hashimi [5] da wannan dalili ne zaka samu an ambace shi cikin riwaya da sunan Sayyid Kurasani [6] haka kuma cikin wadannan Masadir anyi bayanin Siffofinsa daga kasancewar samun wata Alama a kan hannun damansa [7]
Shin Mikewar Kurasani daya ce daga cikin Alamomin Bayyana ?
Mikewar Kurasani zata faru tare da Karajin Sama, Kashe Nafsuz Zakiyya, Fitowar Sufyani da kuma Kusuful Baida’u duka suna daga cikin Alamomin Bayyanar Imam Mahadi Mau’ud (A.F) [8] kan asasin wata riwaya da aka dangantata zuwa ga Imam Sadiƙ (A.S) Kurasani, Sufyani, da Yamani dukkaninsu za su mike cikin shekara daya wata daya lokacin daya [9] ya zo cikin riwayoyi cewa mikewar Kurasani zai kasance daga Gabas, (ma’ana gabashin duniyar Muslunci) zai dangane zuwa Irak [10] cikin Littafin Kundin Daneshnameh Imam Mahadi an kawo shakku da kokwanto cikin sanadin wannan riwaya [11]
Bakaken Tutoci da Sayyid Kurasani
Asalin Makala: Bakaken Tutoci Harkar Bakaken Tutoci ishara ce kan Mikewar wasu Gungun Jama’a daga Gabas wanda cikin ba’arin wasu riwayoyi aka bayyana su cikin Alamomin Bayyana [12] kan dogaro da wasu riwayoyi an bayyana cewa wadannan Tutoci suna da alaka da wani Matashi daga Banu Hashim wanda yake a garin Kurasan wanda a lokacin fitowarsa Shu’aibu Bn Salihu zai kasance cikin Rundunarsa [13] wasu ba’arin Masu bincike na Shi’a sun bayyana cewa abin da ake nufi daga Bakaken Tutoci shi ne Mikewar Abu Muslim Kurasani da ya yi yaki kan Banu Umayya wanda ya kare da kafa Daular Banul Abbas [14] wasu kuma suna ganin wannan Tutoci ishara ce zuwa ga wata Mikewa gabanin Bayyanar Imam Mahadi (A.F) [15] Marubucin Littafin Asarul Az-Zuhur ya ce: Sayyid Kurasani shi ne Ma’abocin Bakaken Tutoci sannan Shu’aibu Bn Salihu shi ne zai jagoranci Kwamandancin Rundunarsa, sannan za a gwabza yaki tsakanin wanann runduna da rundunar Sufyani, daga karshe Kurasani zai nasara kan Sufyani [16] kuma zai yi Mubaya’a ga Imam Mahadi (A.F) [17] sai dai cewa kuma wannan Magana da ta zo daga littafin Asarul Az-Zuhur ta samu suka bisa cewa mai littafin ya dogara ne da riwayoyin da suka zo cikin littafin Al-fitanu talifin Ibn Hammad, hakika Sunan Kurasani bai zo cikin ingantattun riwayoyi ba, sannan shi kansa littafin da ya dogara da shi littafi ne mara inganci a wurin `Yan Shi’a, kuma riwayoyin da littafi ya tattaro riwayoyi ne da ba a tabbatar da zuwansu daga Imamai Ma’asumai ba. [18]
Sabbin Tadbik
A shekarar 1389 h Shamsi an samu bullar wani Fim na Documentary mai suna (Zuhur Bisyar Nazdik) wanda ya shirya wannan Fim ya yi da’awar cewa Jagoran Jamhuriyar Muslunci ta Iran Ayatullahi Khamna’i shi ne Kurasani, kuma Babban Sakataren Kungiyar gwagwarmayar Hizbullahi Lubnani Sayyid Hassan Nasrullahi shi ne Shu’aibu Bn Salihu, sannan Kuma Shugaban Kasar Iran na wancan lokaci Mahmud Ahmadi Nejad shi ne Yamani, hakika wannan fim ya samu suka daga Bangarori daban-daban sannan Masana Batun Bayyanar Imam Mahadi (A.F) sun bayyana cewa wannan Magana da tadbiki basu da inganci kuma sun kawo cikakkun dalilai kan rashin ingancin [19]
Bayanin kula
- ↑ Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 290.
- ↑ Kurani, Asr al-Zhoor, 1408 AH, shafi na 243; Mohammadi Rayshahriwa Digaran. Daneshnameh Juzu'i na 7, 1393, shafi na 447.
- ↑ Kurani, Asr al-Zahur, 1408H, shafi na 242..
- ↑ Misali, duba Ibn Hamad, Kitab al-Fitan, Dar al-Katb al-Alamiya, Manuscripts na Muhammad Ali Bizoon, shafi na 214.
- ↑ Kurani, Asr al-Zahur, 1408H, shafi na 242.
- ↑ Misali, duba Kurani, Asr Zahor, 1408H, shafi na 234, 205, 147.
- ↑ Kurani, Asr al-Zahur, 1408H, shafi na 242.
- ↑ Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 290.
- ↑ Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 255-256; Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 446-447.
- ↑ Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 256-255.
- ↑ Duba Mohammadi Rishahri wa Digaran, daneshnameh Imam Mahdi (A.F), Juzu'i na 7, 2014, shafi na 445-447.
- ↑ Misali, duba Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 251.
- ↑ Ibn Hammad, Kitab al-Fetan, Dar al-Kitab al-Alamiya, Muhammad Ali Bizoon's pamplets,shafi na 214 da 216; Ibn Tavus, al-Tashrif Balmenan, 1416H, shafi na 120.
- ↑ Duba Mohammadi Rishahri wa Digaran, daneshnameh Imam Mahdi Juzu'i na 6, 2014, shafi na 64, 65; Sadr, Tarikh al-Ghaibah al-Kubari, 1412 AH, shafi na 453
- ↑ Duba Kurani, Asr al-Zuhur, 1408H, shafi na 242 da 243.
- ↑ Korani, Asr al-Zhohor, 1408H, shafi na 242.
- ↑ Korani, Asr al-Zhohor, 1408H, shafi na 137.
- ↑ Mohammadi Rishahri da sauransu, Daneshnameh, juzu'i na 7, 2014, shafi na 448.
- ↑ pishger Tibyan <a class="external text" href="http://www.tebyan.net/newindex.aspx?pid=172554">شعیب بن صالح کیست؟</a>
Nassoshi
- Ibn Hammad, Naim bin Hammad, Kitab al-Fetan, edita na Majdi bin Mansour Shuri, Beirut, Darul Kitab al-Alamiya, Muhammad Ali Bizoun, Bita.
- Ibn Tavus, Ali Ibn Musa, Al-Tashrif Balmanan Fi Al-Tafrif Balftan, Qum, Cibiyar Sahib Al-Amr, bugun farko, 1416 Hijira.
- Pishgere Ummid شعیب بن صالح کیست؟،Bayani, saka abun ciki: Yuli 22, 1390, Yuli 9, 1400.
- Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Ghaibah, Research, Tehrani Ebadullah, Naseh, Ali Ahmad, Qum, Dar al-Maarif al-Islamiya, bugu na farko, 1411H.
- Sadr, Sayyid Muhammad, Tarikh al-Ghaibah al-Kubari, Beirut, Dar al-Taqqin Lal-Mahabbat, Beirut, 1412H.
- Kourani, Ali, Asr al-Zahur, Cibiyar Buga Makarantar Al-Alam Al-Islami, bugun farko, 1408H.
- Mohammadi Rishahri, Mohammad, Daneshnameh Imam Mahdi (Aj), Kum, Darul Hadith, 2013.
- Nomani, Muhammad bin Ibrahim, Al-Ghaibah, bincike na Ali Akbar Ghafari, Tehran, gidan buga littattafai na Sadouq, bugun farko, 1397H.