Jump to content

Juz'i (Alkur'ani)

Daga wikishia
(an turo daga Juzu'i)

Juzu'i (Larabci: الجزء (قرآن)) yana daga cikin ma'aunan rarraba Alkur'ani, ko wane juzu'i guda ɗaya yana daidai da kaso ɗaya bisa talatin na Alkur'ani, kusan shafuka ashirin kenan cikin rubutun Usman Ɗaha, duk juzu'i guda ɗaya yana matsayin hizbi biyu juzu'i talatin ya ƙunshi surorin 37 wanda shi ne ya ƙunshi mafi yawan surori, cikin ba'arin al'adu, ana karanta juzu'an Alkur'ani cikin ƙarƙashin ambaton lamba ko Kalmar farkon Juzu'in.

Nazarin Ma'ana

Juzu'i, yana cikin tsarin Alkur'ani, Musulmai sun kasa Alkur'ani zuwa juzu'i talatin, ma'ana ɓangarori talatin.[1] a wasu al'adu ana karanta juz'an Alkur'ani cikin hanyar amfani da lambar da take kansu ko kuma Kalmar take a farkon Juzu'in, misalin Juzu'in Amma, wanda yake da ma'anar Juzu'i na talatin wanda yake farawa da (Amma yatasa'alun)[2] kowanne Juzu'i yana kasuwa zuwa hizbi biyu sannan a Alkur'ani rubutun Usman Ɗaha ko wane Juzu'i yana da shafi ashirin.[3]


Takaitaccen Tarihin Juzu'in Kur'ani

Juzu'i na tara na Alkur'ani

Wasu ba'arin Malamai suna ganin asalin amfani da tsarin Juzu'i a Kur'ani ya samu daga wata riwaya daga Annabi (S.A.W) wanda cikinsa aka yi ishara kan karanta Alkur'ani a ko wane wata cikin watannin Muslunci.[4] Amma game da wane zamani ne aka fara kasa Kur'ani zuwa tsarin Juzu'i-Juzu'i zuwa juz'ai talatin, akwai mabambantan ra'ayoyi, an ce hakan ya faru ne a lokacin Hajjaju Bin Yusuf Saƙafi wanda ya mutu shekara ta 95 h ƙamari,[5] a kowacce rana cikin watan Ramadan ana karanta juzu' ɗaya.[6] wasu ba'ari kuma sun ce Sarki Ma'amun Abbasi wanda ya yi mulki tsakanin shekaru 198-218, shi ne wanda ya bada umarnin karkasa Kur'ani cikin tsarin Juzu'i,[7] Zarkashi daga Malaman tafsiri a ƙarni na takwas yana ganin yaɗuwar tsarin juz'antar Kur'ani zuwa Juzu'i talatin ya samu ne daga makarantun addini.[8]

Karatun Juzu'i-Juzu'i

Majalisin Karatun Kur'ani a Haramin Imam Husaini (A.S)[9]
Asalin Maƙala: Karatun Juzu'i

A ƙasar Iran da ba'arin wasu ƙasashen Muslunci, a cikin watan Ramadan Musulmi suna taruwa su karanta Kur'ani tun daga farko har ƙarshensa (Khatma), da wannan ne ya kasance suke karanta Juzu'i ɗaya a ko wace rana, ana kiran wannan al'ada da sunan karatun juzu'i, a ƙasar Iran karatun juzu'i da ake yi a wurare masu tsarki Tashoshin Talabishin suna ɗaukowa suna watsa wannan karatu kai tsaye.[10] Cikin ba'arin ƙasashen Musulmi misalin Iran, ana buga juz'an Kur'ani a ware daga cikin Alkur'ani, zai zama kenan kammalallensa cikin yanki guda talatin ana karantawa kan wannan tsarin a taron addu'ar zaman makoki.[11] na'am Sayyid Muhammad Husaini Tehrani wanda ya mutu shekara 1416 h shamsi,yana da sa ɓani da wannan al'ada, yana ganin wannan tsari na rarraba Kur''ani da junansa a khatma ya fara yaɗuwa ne a zamanin Mulkin Yazidu Bn Mu'awiya, Malamin yana ganin ya kamata ne ayi amfani da kammalallen Alkur'ani a lokacin Khatamarsa bawai wanda aka rarraba shi zuwa Juzu'i-Juzu'i ba.[12]

Fihirisar Karatun Juzu'in Kur'ani

Juzu'an Kur'ani
Juzu'i Ayar farkon juzu'i Surorin da ya tattaro
1 Aya ta 1 Fatiha: "Bismillahi..." Suratul Fatiha da Baƙara (farkon aya ta 141)
2 Aya ta 142 Suratul Baƙara:"sayaƙulu Alsufaha'u..." Baƙara (Ayoyi 142-253)
3 Aya ta 253 Suratul Baƙara: "tilkar Ar-rusulu..." Baƙara (Aya 253 zuwa ƙarshen sura) da kuma Alu Imran (farkon aya ta 92)
4 Aya ta 93 Alu Imran: "kulluɗ ɗa'ami..." [Alu Imran(Aya 93 zuwa ƙarshen sura) da kuma Nisa'i (farko aya ta 23)
5 Aya ta 24 Nisa'i:"Wal-muhsanat..." Nisa'i(Aya 24-148)
6 Aya ta 148 Suratul Nisa'i:"La yuhibbulahu..." Nisa'i(Aya 148 zuwa ƙarshen sura)
7 Aya ta 82 Ma'ida: " Latajidanna..." Ma'ida (Aya 82 zuwa ƙarshen sura)
8 Aya ta 112 An'am: "wa lau anna nazzalna..." An'am (Aya 112 zuwa ƙarshen sura)
9 Aya ta 89 A'araf "ƙalal Al-Mala'u..." A'araf (Aya 90 zuwa ƙarshen sura) da kuma Anfal (farkon Aya ta 40)
10 Aya ta 41 Anfal: "Wa'alamu..." Anfal (Aya ta 41 zuwa ƙarshen sura) da kuma Tauba (farkon aya ta 92)
11 Aya ta 93 Tauba"Innamas As-Sabil..." Tauba (Aya ata 93 zuwa ƙarshen sura)
12 Aya ta 6 Hud: "wama min da'batin..." Hudu (Aya ta 6 zuwa ƙarshen sura) da Yusuf (farkon aya ta 53)
13 Aya ta 54 Suratul Yusuf: Yusuf (Aya ta 54 zuwa ƙarshen sura) Ra'ad da Ibrahim
14 Aya ta 1 Hujurat: "ALif lamra" Hijri da Nahli
15 Aya ta 1 Isra'i: "Subhanallahi..." Isra'i da Kahafi (farkon Aya ta 74 zuwa ƙarshen sura)
16 Aya ta 75 Suratul Kahafi: "ƙala alam..." Kahafi, Maryam da Ɗaha
17 Aya ta 1 Anbiya: "Iƙtaraba lilnasi..." Anbiya da Hajji
1 Aya ta 1 Muminun: "ƙad Aflaha..." Muminun, Nur da Furƙan (farkon aya ta 20)
19 Aya ta 21 Furƙan : "Wa ƙala Allazina..." Furƙan, (Aya ta 21 zuwa ƙarsehn sura)
20 Aya ta 56 Namli: "Fama kana..." Namli, Ƙasas da Ankabut (farkon aya ta 45)
21 Aya ta 46 Ankabut: "Wa latujadilu..." Ankabut (Aya ta 46 zuwa ƙarshen sura) Rum, Luƙman, Sajada da Ahzab (ayoyi na 30 na farko)
22 Aya ta 31 Ahzab: "wa man yaƙnut..." Ahzab (Aya ta 31 zuwa ƙarshe), Saba'i, Faɗir da Yasin (farkon aya ta 27)
23 Aya ta 28 Yasin: "Wama Anzalna..." Yasin, Sa'fat, Sa'd da Zumar (farkon Aya ta 31)
24 Aya ta 32 Zumar: "Faman Azlama" Zumar, (Aya ta 32 zuwa ƙarshe), Gafir da Fussilat (farkon aya ta 46)
25 Aya ta 47 Fussilat: "Ilaihi yaruddu..." Fussilat, (Aya ta 47 zuwa ƙarshe), Shura, Zukhruf, Dukhan da Jasiya.
26 Aya ta 1 Ahƙaf: "Hemim...) Ahƙaf, Muhammad, Fathu, Ƙaf, Zariyat, (farkon aya ta 30)
27 Aya ta 31 Zariyat: "ƙala fama khaɗbukum..." Zariyat, (Aya ta 31 zuwa ƙarshe), Ɗur, Najmu, ƙamaru Ar-Rahman, Waƙi'a da Hadid
28 Aya ta Mujadala: "ƙad sami'a..." Hashar, Mumtahana, Saffi, Juma'a, Munafiƙun, Tagabun, Ɗalaƙ da Tahrim
29 Aya ta 1 Mulki: "Tabarakal lazi..." ƙalam, Ha'ƙati, Ma'arij, Nuhu, Jinni, Muzammil, Mudassir, Insan da Mursalat
30 Aya ta 1 naba'i: "Amma yatasa'alun...' Nazi'at, Abasa, Takwir, Infiɗar, Muɗaffifin, Inshiƙaƙ, Buruj, Ɗariƙ, A'ala, Gashiya, Fajar, Balad, Shamsu, Lailu, Dhuha, Inshirahu, Tiinu, Alaƙ, ƙadar, Bayyina, Zalzala, A'diyat, ƙari'a, Takasur, Asru, Humaza, Filu, ƙuraishi, ma'un, Kausar, Kafirun, Nasru, masad, Iklas, Falaƙi, Nasi

Ku Duba

Bayanin kula

  1. Moini, "Juz'u", shafi na 836.
  2. Moini, "Juz'u", shafi na 836.
  3. Reza Fur، دانستنی‌های قرآن، Iran Daweh.
  4. Ahmad bin Ahmad bin Muhammad Abdullah Al-Tawil, Fannun Al-Tartil wa Ulumehi, 1420 AH, shafi na 65.
  5. Faiz Kashani, Mahajjah Al-Bayda, 1428H, shafi na 224.
  6. Moini, "Juz'u", shafi na 836.
  7. Marfat, Tamhid, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 364.
  8. Zarakshi, Al-Burhan, 1408H, Mujalladi na 1, shafi na 250.
  9. «تصاویر/ مراسم جزءخوانی قرآن کریم در حرم امام حسین(ع)»]Hukumar Labarai Hauza.
  10. برنامه جزءخوانی صدا و سیما، Tawoos Bahesht.
  11. Dehkhoda, Luggat Nameh Dehkhoda, ƙarƙashin kalmar Si pareh.
  12. «دیدگاه علاّمه طهرانی نسبت به برگزاری محافل جشن و عروسی و ترحیم»، Maktab Wahayi.

Nassoshi