Hizbi (Alkur'ani)

Daga wikishia

Hizbi (Larabci:حِزب)ɗaya ne daga sassan tsarin Alkur’ani, [1] kowanne juzu’in Alkur’ani ya na kasuwa zuwa wasu adadin hizbi, [2] cikin ba’arin rubutun Ku’ranai kowanne juzu’i ana kasa zuwa hizbi biyu, [3] kan asasin wannan karkasawa zai zama yana da hizbi Sittin, [4] amma wasu ba’ari sun kasa kowanne juzu’i zuwa hizbi huɗu wanda kan asasinsa Kur’ani zai zama yana da hizbi 120, kenan [5] sannan kuma kowanne hizbin ana kasa shi zuwa kashi huɗu kowanne kashi ɗaya ana kiransa da rubu’i, [6] wannan tsarin karkasawa an yi shi kan asasin ayoyi [7] bisa dogara da wata riwaya da litattafan hadisi na Ahlus-sunna suka naƙaltota daga Umar Bn Khaɗɗab, 8 da take bayyana cewa Isɗilahin hizbi ya kasance tun lokacin Annabi (S.A.W) kuma ya zo cikin maganarsa, sannan kuma Musulmai suna karanta hizbi ɗaya a kowacce rana, [8] na’am cikin wannan riwaya ba ayi Magana. kan miƙdarin hizbi ba.

Alamar Farkon Hizbi

Alamomin Farkon Hizbi A Cikin Kur’ani

A wasu ƙasashe misalin Iran ana buga kowanne hizbi guda shi kaɗai sai ya zamana a buga hizbi 120 cikin kammalallen Kur’ani, ana amfani da wannan Kur’anai a taron addu’a ga jana’izar mamaci, [9] sai dai cewa Sayyid Muhammad Husaini Tehrani wanda ya rasu shekara ta 1416 h ƙamari, yana da saɓani da wannan al’ada ta warware Kur’ani da junansa a khatamarsa a zaman makoki da addu’a ga mamaci, yana ganin wannan al’ada ta samo asali ne a zamanin Yazid Bn Mu’awiya, Malamin yana ganin idan za a yi khatmar Kur’ani to ayi amfani da cikakken Kur’ani da yake kammale da junansa. [10] Manufar tsarin rarraba Kur’ani zuwa Juzu’ai daban-daban, shi ne kwaɗaitar da mai karatu zuwa ga tilawarsa, [11] sauƙaƙe haddace shi, [12] da kuma koyar da ilimin Kur’anin. [13] ana jingina tsarin raba Kur’ani zuwa Juzu’ai da hizbai zuwa ga Sarki Mamun Abbasi wanda ya mutu shekara ta 218 h ƙamari; duk da cewa wasu ba’ari su na jingina wannan aiki zuwa ga Hajjaju Bn Yusuf Saƙafi wanda ya mutu shekara ta 95 h ƙamari, [14] daga cikin illolin da ke tattare da rarraba Alkur’ani juzu'i-juzu'i da hizbi, an ambaci kawo karshen karatun a lokacin magana ko fara karatu daga tsakiyar maudu’i. [15] A cewar Marubucin littafin Al-Ziyadatu wal Al-Ihsan fi Ulumil Al-kur’an, Sahabban Annabi (S.A.W) sun kasance suna ɗaukar sati guda don Khatmar Alkur’ani suna rarraba shi zuwa gida bakwai, suna kiran kowanne kashi guda da sunan hizbi. [16] wannan rarabawa ya kasance kan asasin surori. [17] daidai da nau’in rarrabawar, hizbi na farko ya tattaro surori uku farko tare da kau da ido da suratul Hamdu, Hizbi na biyu ya tataro surori biyar, hizbi na uku ya tattaro surori bakwai, hizbi na huɗu ya tattaro surori tara, hizbi na biyar ya tattaro surori goma sha ɗaya, hizbi na shida ya tattaro surori goma sha uku, hizbi na bakwai wanda ake kira hizbi da yafi faifaicewa ya tattaro ragowar surorin, daga suratul ƙafu har zuwa ƙarshen Alkur’ani. [18] Kuma an ruwaito wani rabawar zuwa wasu gida bakwai daga wasu Sahabbai [19] A kan haka ne ake cewa duk wani ɓangare na Alƙur’ani da mutum ya wajabtawa kansa karanta shi da sunan hizbi. [20]

Hizban cikin Kur'ani
Lambar Hizbi Juzu'i- Hizbi Daga Farkon aya Zuwa ƙarshen aya
1 1-1 Aya 1 Suratul Hamdu Aya 43 Suratul Baƙara
2 1-2 Aya 44 Suratul Baƙara Aya 74 Suratul Baƙara
3 1-3 Aya 75 Suratul Baƙara Aya 105 Suratul Baƙara
4 1-4 106 Suratul Baƙara Aya 141 SUratul Baƙara
5 2-1 Aya 142 Suratul Baƙara Aya 176 Suratul Baƙara
6 2-2 Aya 177 Suratul Baƙara 202 Suratul Baƙara
7 2-3 Aya 203 Suratul Baƙara Aya 232 Suratul Baƙara
8 2-4 Aya 233 Suratul Baƙara Aya 252 Suratul Baƙara
9 3-1 Aya 253 Suratul Baƙara Aya 271 Suratul Baƙara
10 3-2 Aya 272 Suratul Baƙara Aya 14 Suratul Alu Imran
11 3-3 Aya 15 Suratul Alu Imran Aya 51 Suratul Alu Imran
12 3-4 Aya 52 Suratul Alu Imran Aya 92 Suratul Alu Imran
13 4-1 Aya 93 Suratul Alu Imran Aya 132 Suratul Alu Imran
14 4-2 Aya 133 Suratul Alu Imran Aya 170 Suratul Alu Imran
15 4-3 Aya 171 Suratul Alu Imran Aya 200 Suratul Alu Imran
16 4-4 Aya 1 Suratul Nisa'i Aya 23 Suratul Nisa'i
17 5-1 Aya 24 Suratul Nisa'i Aya 57 Suratul Nisa'i
18 5-2 Aya 58 Aya 87 Suratul Nisa'i
19 5-3 Aya 88 Suratul Nisa'i Aya 113 Suratul Nisa'i
20 5-4 Aya 114 Suratul Nisa'i Aya 147 Suratul Nisa'i
21 6-1 Aya 148 Suratul Nisa'i Aya 176 Suratul Nisa'i
22 6-2 Aya 1 Suratul Ma'ida Aya 26 Suratul Ma'ida
23 6-3 Aya 27 Suratul Ma'ida Aya 50 Suratul Ma'ida
24 6-4 Aya 51 Suratul Ma'ida Aya 81 Suratul Ma'ida
25 7-1 Aya 82 Suratul Ma'ida Aya 108 Suratul Ma'ida
26 7-2 Aya 109 Suratul Ma'ida Aya 35 Suratul An'am
27 7-3 Aya 36 Suratul An'am Aya 73 Suratul An'am
28 7-4 Aya 74 Suratul An'am Aya 110 Suratul An'am
29 8-1 Aya 111 Suratul An'am Aya 140 Suratul An'am
30 8-2 Aya 141 Suratul An'am Aya 165 Suratul An'am
31 8-3 Aya 1 Suratul A'araf Aya 46 Suratul A'araf
32 8-4 Aya 47 Suratul A'araf Aya 87 Suratul A'araf
33 9-1 Aya 88 Suratul A'araf Aya 141 Suratul A'araf
34 9-2 Aya 142 Suratul A'araf Aya 170 Suratul A'araf
35 9-3 Aya 171 Suratul A'araf 206 Suratul A'araf
36 9-4 Aya 1 Suratul Anfal Aya 40 Suratul Anfal
37 10-1 Aya 41 Suratul Anfal Aya 75 Suratul Anfal
38 10-2 Aya 1 Suratul Tauba Aya 33 Suratul Tauba
39 10-3 Aya 34 Suratul Tauba Aya 59 Suratul Tauba
40 10-4 Aya 60 Suratul Tauba Aya 92 Suratul Tauba
41 11-1 Aya 93 Suratul Tauba Aya 121 Suratul Tauba
42 11-2 Aya 122 Suratul Tauba Aya 25 Suratul Yunus
43 11-3 Aya 26 Suratul Yunus Aya 70 Suratul Yunus
44 11-4 Aya 71 Suratul Yunus Aya 5 Suratul Hudu
45 12-1 Aya 6 Suratul Hudu Aya 40 Suratul Hudu
46 12-2 Aya 41 Suratul Hudu Aya 83 Suratul Hudu
47 12-3 Aya 84 Suratul Hudu Aya 6 Suratul Yusuf
48 12-4 Aya 7 Suratul Yusuf Aya 52 Suratul Yusuf
49 13-1 Aya 53 Suratul Yusuf Aya 100 Suratul Yusuf
50 13-2 Aya 101 Aya 18 Suratul Ra'ad
51 13-3 Aya 19 Suratul Ra'ad Aya 9 Suratul Ibrahim
52 13-4 Aya 10 Suratul Ibrahim Aya 52 Suratul Ibrahim
53 14-1 Aya 1 Suratul Hajari Aya 99 Suratul Hajari
54 14-2 Aya 1 Suratul Nahali Aya 50 Suratul Nahali
55 14-3 Aya 51 Suratul Nahali Aya 89 Suratul Nahali
56 14-4 Aya 90 Suratul Nahali Aya 128 Suratul Nahali
57 15-1 Aya 1 Suratul Isra'i Aya 49 Suratul Isra'i
58 15-2 Aya 50 Suratul Isra'i Aya 98 Suratul Isra'i
59 15-3 Aya 99 Suratul Isra'i Aya 31 Suratul Kahafi
60 15-4 Aya 32 Suratul Isra'i Aya 74 Suratul Kahafi
61 16-1 Aya 75 Suratul Kahafi Aya 21 Suratul Maryam
62 16-2 Aya 22 Suratul Maryam Aya 98 Suratul Maryam
63 16-3 Aya 1 Suratul Ɗaha Aya 82 Suratul Ɗaha
64 16-4 Aya 83 Suratul Ɗaha Aya 135 Suratul Ɗaha
65 17-1 Aya 1 Suratul Ambiya Aya 50 Suratul Anbiya
66 17-2 Aya 51 Suratul Ambiya Aya 112 Suratul Anbiya
67 17-3 Aya 1 Suratul Hajji Aya 37 Suratul Hajji
68 17-4 Aya 38 Suratul Hajji 78 Suratul Hajji
69 18-1 Aya 1 Suratul Muminun Aya 74 Suratul Muminun
70 18-2 Aya 75 Suratul Muminun Aya 20 Suratul Nur
71 18-3 Aya 21 Suratul Nur Aya 52 Suratul Nur
72 18-4 Aya 53 Suratul Nur Aya 20 Suratul Furƙan
73 19-1 Aya 21 Suratul Furƙan Aya 77 Suratul Furƙan
74 19-2 Aya 1 Suratul Shu'ara Aya 110 Suratul Shu'ara
75 19-3 Aya 111 Suratul Shu'ara Aya 227 Suratul Shu'ara
76 19-4 Aya 1 Suratul Namli Aya 55 Suratul Namli
77 20-1 Aya 56 Suratul Namli Aya 11 Suratul Ƙasas
78 20-2 Aya 12 Suratul Ƙasas Aya 50 Suratul Ƙasas
79 20-3 Aya 51 Suratul Ƙasas 88 Suratul Ƙasas
80 20-4 Aya 1 Suratul Ankabut Aya 45 Suratul Ankabut
81 21-1 Aya 46 Suratul Ankabut Aya 30 Suratul Rum
82 21-2 Aya 31 Suratul Rum Aya 21 Suratul Luƙman
83 21-3 Aya 22 Suratul Luƙman Aya 30 Suratul Sajada
84 21-4 Aya 1 Suratul Ahzab Aya 30 Suratul Ahzab
85 22-1 Aya 31 Suratul Ahzab Aya 59 Ahzab
86 22-2 Aya 60 Suratul Ahzab Aya 23 Suratul Saba'i
87 22-3 Aya 24 Suratul Saba'i Aya 14 Suratul Faɗir
88 22-4 Aya 15 Suratul Faɗir Aya 27 Suratul Yasin
89 23-1 Aya 28 Suratul Yasin Aya 21 Suratul Safat
90 23-2 Aya 22 Suratul Safat Aya 144 Safat
91 23-3 Aya 145 Suratul Safat Aya 51 Suratul Sad
92 23-4 Aya 52 Suratul Sad Aya 31 Suratul Zumar
93 24-1 Aya 32 Suratul Zumar Aya 75 Suratul Zumar
94 24-2 Aya 1 Suratul Gafir Aya 40 Suratul Gafir
95 24-3 Aya 41 Suratul Gafir Aya 8 Suratul Fussilat
96 24-4 Aya 9 Suratul Fussilat Aya 46 Suratul Fussilat
97 25-1 Aya 47 Suratul Fussilat Aya 26 Suratul Shura
98 25-2 Aya 27 Suratul Shura Aya 23 Suratul Zukruf
99 25-3 Aya 24 Suratul Zukruf Aya 16 Suratul Dukhan
100 25-4 Aya 17 Suratul Dukhan Aya 37 Suratul Jasiya
101 26-1 Aya 1 Suratul Ahƙaf Aya 9 Suratul Muhammad
102 26-2 Aya 10 Suratul Muhammad Aya 17 Suratul Fathu
103 26-3 Aya 18 Suratul Fathu Aya 13 Suratul Hujurat
104 26-4 Aya 14 Suratul Hujurat Aya 30 Suratul Zariyat
105 27-1 Aya 31 Suratul Zariyat Aya 25 Suratul Najamu
106 27-2 Aya 26 Suratul Najamu Aya 55 Suratul Ƙamar
107 27-3 Aya 1 Suratul Rahman Aya 74 Suratul Waƙi'a
108 27-4 Aya 75 Suratul Waƙi'a Aya 29 Suratul Hadid
109 28-1 Aya 1 Suratul Mujadala Aya 10 Suratul Hashar
110 28-2 Aya 11 Suratul Hashar Aya 14 Suratul Saffi
111 28-3 Aya 1 Suratul Juma'ati Aya 18 Suratul Tagabun
112 28-4 Aya 1 Suratul Ɗalaƙ Aya 12 Suratul Tahrim
113 29-1 Aya 1 Suratul Malak Aya 52 Suratul Ƙalam
114 29-2 Aya 1 Suratul Haƙƙatu Aya 28 Suratul Nuhu
115 29-3 Aya 1 Suratul Jinni Aya 56 Suratul Mudassir
116 29-4 Aya 1 Suratul Ƙiyamati Aya 50 Mursalat
117 30-1 Aya 1 Suratul Naba'i Aya 29 Suratul Takwir
118 30-2 Aya 1 Suratul Infiɗar Aya 17 Suratul Ɗariƙ
119 30-3 Aya 1 Suratul A'ala Aya 11 Suratul Dhuha
120 30-4 Aya 1 Suratul Sharh Aya 6 Suratul Nasi

Bayanin kula

  1. Tayar, Al-Muhrar fi Ulum al-Qur'an, 1429 AH, shafi na 249.
  2. Saleh, "Mabahis fi Ulumi Qur'an", 1372, shafi na 97.
  3. Zarqani, Manahel al-Irfan, 1424 AH, juzu'i na 1, shafi na 403.
  4. Jeremi,Mujam Ulumi Al-Qur'an, 1422 AH, shafi na 14.
  5. Mustafid, taksimat Kur’an, 2004, shafi na 41.
  6. Zarqani, Manahel al-Irfan, 1424 AH, juzu'i na 1, shafi na 403.
  7. دخیل، اقراء القران الکریم، ۱۴۲۹ق، ص۱۲۰-۱۲۱.
  8. Malik, Al-Muwatta, 1425 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 280.
  9. Dehkhoda, Luggat nameh, zaile wajeh sado bisti.
  10. <a class="external text" href="https://maktabevahy.org/Document/Article/Details/97/%D8%AF%DB%8C%D8%AF%DA%AF%D8%A7%D9%87-%D8%B9%D9%84%D8%A7%D9%85%D9%87-%D8%B7%D9%87%D8%B1%D8%A7%D9%86%DB%8C-%D9%86%D8%B3%D8%A8%D8%AA-%D8%A8%D9%87-%D8%A8%D8%B1%DA%AF%D8%B2%D8%A7%D8%B1%DB%8C-%D9%85%D8%AD%D8%A">«دیدگاه علاّمه طهرانی نسبت به برگزاری محافل جشن و عروسی و ترحیم»</a>
  11. Siyuti, Al-Iqtan fi Ulumi al-Qur’an, 1394 AH, juzu’i na 1, shafi na 222; Masri, Fiqh qira'ati alqur'ani, 1418 AH, shafi na 15
  12. Khadiri, Tafsir al-Tabi'in, 1420H, juzu'i na 2, shafi 1145.
  13. Mustafid, Taksimat Kur’an, 2004, shafi na 41.
  14. Marifat, Tamhid, 2008, juzu'i na 1, shafi na 360.
  15. Tayar, Al-Muhrar fi Ulum al-Qur'an, 1429 AH, shafi na 249.
  16. Aqilah, Al-Ziyadeh wa Al-Ihsan, 1427H, Juzu'i na 2, shafi na 253.
  17. Dakhil, Iqra Al-Qur'an al-Karim, 1429 AH, shafi na 121-120. Dakheel, Iqra Alqur’an al-Karim, 1429 AH, shafi na 120-121.
  18. Haddad, al-Tahdid fi al-Itqan wa al-Tajwid, 1424H, shafi na 65.
  19. Mostafid, taksimat Kur'an, 2004, shafi na 30-32.
  20. Majidi, Izhabul Al-Huzni, Dar al-Ayman, shafi na 429.

Nassoshi

  • Jeremi, Ibrahim, Ma'jam Ulum Al-Qur'a* Aqilah, Muhammad bin Ahmad, Al-Ziyadeh wa Al-Ihsan fi Ulum al-Qur'an, Sharqa, Cibiyar Bincike da Nazarin Jami'ar Sharqa, bugun farko, 1427 Hijira.
  • Dakheel, Abdullah, Ikra Alkur'an Al-Kareem, Jiddah, Cibiyar Nazarin Kur'ani da Bayani a Cibiyar Imam Al-Shatabi, 1429H.
  • Dehkhoda, Ali Akbar, ƙamus.
  • Fazel Mohadi Lankarani, Mohammad, Mukaddimat Bunyadin Ilimi Kur'an, Tehran, Mu'assasar Quran, 2008.
  • Haddad, Muhammad bin Ali, Al-Tajdid fi al-Itqan wa Al-Tajwid, Beirut, Darul Katb al-Alamiya, 1424H.
  • Khadiri, Muhammad bin Abdullah, Tafsir al-Tabi'in, Riyad, Dar Al-Watan, 1420H.
  • Majidi, Abdulsalam, Izhab Al-Huzni wa Shafa al-Sadr al-Saqim, Alexandria, Dar al-Ayman, Bita.
  • Malik bin Anas, al-Muwatta, bincike: Muhammad Mustafa al-Azami, Zayed bin Sultan Al Nahyan Foundation for Charritable and Humanitarian Services - Abu Dhabi - Emirates, bugun farko, 1425 AH.
  • Marafet, Mohammad Hadi, Tamhid fi
  • Masri, Said, Fikh Qira'atil Qur'ani, Alkahira, Makarantar Qudsi, bugu na farko, 1418H.
  • Mustafid, Mohammadreza, Taksimat Kur'an wa suware Makki wa Madani, Tehran, Ma'aikatar Al'adu da Jagorar Musulunci, 2004.
  • Saleh, Sobhi, Mabahis fi Ulumi Alqur'an, Qum, Al-Sharif al-Razi, 1372.
  • Siyuti, Abd al-Rahman bin Abi Bakr, mai bincike: Muhammad Abu al-Fazl Ibrahim, mawallafi: Al-Masriy Al-Aae Al-Katab, bugun: 1394 AH 1974
  • Tayar, Masa'ed bin Suleiman, Almuharar fi Ulumi Alkur'an, Cibiyar Nazarin Kur'ani da Bayani a Cibiyar Imam al-Shatabi, bugu na biyu, 1429 Hijira.
  • Zarqani, Muhammad Abd al-Azeem, Manahl al-Irfan fi Ulum al-Qur'an, Beirut, Darul Katb al-Ulamiya, 1424H.
  • «دیدگاه علاّمه طهرانی نسبت به برگزاری محافل جشن و عروسی و ترحیم»، مکتب وحی، بازدید: ۹ آبان ۱۴۰۲ش.n, Damascus, Darul Qalam, bugun farko, 1422H. Ulum al-Qur'an, Qum, Tamhid Publishing Cultural Institute, 2008.