Suratul Falaki

Daga wikishia
(an turo daga Falaƙi)
Error creating thumbnail:
Suratul Falaki

Suratul Falaki (Larabci: سورة الفلق) sura ce ta 113 cikin jerin surorin Kur’ani kuma ta sauka a Makka ne tana cikin juz’i 30, an ciro wannan suna nata na Falak wanda yake ba da ma’anar Asubahi da hudar Alfijir daga ayar farko na surar, suratu Falaki tana cikin jerin surori hudu da suka fara da Kalmar Kul, cikin wannan sura Ubangiji ya umarci Annabi (S.A.W) da ya nemi tsari da shi musammam sharrin duhun Dare da kuma Sharrin Matsafan Mata da sharrin Mahassada, wasu ba’arin Malaman tafisiri daga Ahlus-sunna suna cewa wannan sura ta sauka a lokacin da wani Bayahude ya shirya Sihiri wanda hakan ya sanya Annabi (S.A.W) yin rashin lafiya bayan dan wani lokaci sai Mala’ika Jibrilu ya zo wajensa da Suratul Falaki da Suratu Nasi ya kuma karanta wasu ayoyi kan Annabi (S.A.W) sai ya tashi da shimfidar rashin lafiya, wasu daga Malam Shi’a sun nuna rashin amincewarsu kan wannan Magana suna masu cewa Sihiri da tsafi basa tasiri kan Annabi (S.A.W) Suratul Falaki da Nasi ana kiransu da Ma’uzataini tsari guda biyu saboda ana karanta su ne domin kariya da neman tsari, cikin falalar wannan sura an nakalto cewa duk wanda ya karanta Falaki da Nasi misalin kamar wanda ya yi tilawar dukkanin littafan Annabawan Allah, haka kuma an nakalto cewa Annabi (S.A.W) yana ganin wadannan surori biyu matsayin surorin da Allah yafi so.

Gabatarwa

  • Sanya Suna

Wannan Sura ana kiranta da suratu Falak kuma an ciro wannan suna daga aya ta farkon surar [1] da ma’anar Asubahi da hudar Alfijir [2] wannan sura ce ta neman tsarin Allah wanda aka ciro haka daga farkon surar [3] Suratu Falaki da Nasi ana kiransu da Ma’uzataini haka kuma ana kiransu da Mushakshakataini sakamkon ana karantu a duk inda ake jin tsoro da razana [4]

  • Mahalli da kuma Jerantar Sauka

Suratu Falaki tana cikin jerin surorin da suka sauka a garin Makka kuma cikin sura ce ta Ashirin cikin jerin sauka a wurin Annabi (S.A.W) wannan sura a tsarin Kur’ani a yanzu sura ce ta 113. [5] kuma cikin juzu’i na 30, Allama Tabataba’i Marubucin Littafin Tafsirul Almizan yana cewa kan asasin riwayoyin da suka zo kan sha’anin saukarta sura ce da ta sauka Madina [6]

  • Adadin Ayoyi da wasu Hususiyoyi na Daban

Surar tana dauke da aya 5 da haruffa 73, wannan sura bisa la’akari da girma tana cikin surori Mufassalat (wanda aka faifaice bayani) hakika suratu Falaki tana cikin jerin surori hudu da suka fara da Kul [7]

Abin da Take Tattare da Shi

Cikin Suratu Falak Ubangiji ya umarci Annabi (S.A.W) ya nemi tsarin sa daga sharrri musammam sharrin Duhun Dare da sharrin Matsafan Mata da Sharrin Mahassada, a cewa Allama Tabataba’i cikin tafsirul Almizan abin da ake nufi da <centre>«النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ»</centre> Bawai kadia Matsafan Mata ne ba bari dai dukkanin mutumin da yake Tsafi da Sihiri [8] cikin Tafsir Namuneh ya zo cewa: Suratu Falak tana koyar da Annabi da Musulmai da su nemin tsarin Allah daga dukkanin wani sharri [9]

Dangane da Sha’anin Saukarta

Hotan SUratul Falaki a daya daga dakin nazari da yake Astan Kudus Razawi na shekera 1279 h.k.

dangane da sha'anin saukar ta wata riwaya ta zo cikin masadir din Ahlus-sunna sai dai cewa Malaman Shi’a basu karbeta ba [10] wannan riwaya tana na cikin tafsir Addurul Mansur cewa wani Bayahude yayiwa Annabi (S.A.W) Sihiri, sai Mala’ika Jibrilu ya sauka wurin Annabi da suratu Falaki da Nasi ya gaya masa cewa wani Bayahude yayi maka Sihiri wannan Sihiri nasa yana nan cikin wata Rijiya, sai Annabi (S.A.W) ya aiki Aliyu Bn Abu Talib ya dauko Sihirin, sannan ya ba da Umarni a kwance dukkanin wani Kulli na Sihirin sannan kan kowanne Kulli a a karanta Ma'uzataini, bayan gama kwance karanta su da budewar dukkanin Kullin sai Annabi (S.A.W) Ya samu lafiya [11] Allama Tabataba’i cikin Tafsirul Almizan ya rubuta cewa babu wani dalili cewa Annabi (S.A.W) da yake nuni cewa wannna Sihiri ya shiga jikinsa kuma wannan mutumi bai samu damar sanya masa ciwo a jiki ba, bari dai ayoyin Kur’ani sun nuna cewa Zuciyarsa da da Ransa da hankali da Tunaninsa sun aminta da tasirin Sihiri da Shaidanu. [12]

Ra’ayin Malaman Tafsiri Dangane da Sihiri da Tsafi

Sayyid Radiyu wanda ya bar duniya a shekara 406 h cikin tafisirin aya ta hudu cikin suratu Falak (daga sharrin masu hura cikin kulli) ya rubuta cewa wannan aya Isti’ara ce [13] (ma’ana anyi aron kalma) abin da ake nufi shi ne neman tsari daga Mata wanda suke warware karfaffan mataki da Maza ke dauka wanda saboda karfin sa aka kamanta da shi da Kulli, amma duk da haka Makiran Mata sai lalata shi su raunana karfin Mazaje ta hanyar Sihiri 15 wasu ba’arin Masu Tafsiri na Ahlus-sunna [14] su ma basu yarda da Sihiri da Kambun Baka [15] tare da haka Allama Tabataba’i Ya rubuta cewa wannan aya da kuma aya ta 102 cikin Suratul Bakara suna nuni karara cewa Sihiri da tsafi fa suna da samuwa [16]

Falala da Hususiya

Asalin Makala: Fada’ilu Suwari An nakalto daga Annabi (S.A.W) cewa duk wanda ya karanta Falaki da Nasi, misalinsa kamar wanda ya karanta dukkanin Litattafan Annabawan Allah [17] haka kuma an nakalto daga Imam Bakir (A.S) duk wanda ya karanta Falaki da Nasi da Iklas cikin sallolin dare da yake yi da kuma Shafa’I da Witiri Ubangiji zai Magana da shi: ya kai wannan Bawan Allah lada ya kasance gareka Allah ya karbi sallar Witirinka [18] haka kuma an nakalto cewa Annabi (S.A.W) ya ce: Suratu Falaki da Nasi sun e mafi soyuwar Surori wurin Allah [19] a wani nakalin kuma ya zo cewa duk wanda kowanne dare ya karanta Suratul Tauhid da Falaki da Nasi kafa goma, kamar ya karanta baki dayan Kur’ani kuma zai fita daga cikin zunubai da ya aikata zai zama fes kamar ranar da Mahaifiyarsa ta haife shi, idan kuma ya mutu a wannan rana ko wannan dare to ya yi shahada [20] sannan kuma dangane da Hususiyar suratu Falaki an nakalto daga Annabi (S.A.W) cewa ya kasance yana nemawa Imam Hassan (A.S) da Imam Husaini (A.S) tsarin Allah da karanta musu Falaki da Nasi [21]

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ ١ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ ٢ وَمِنْ شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ ٣ وَمِنْ شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ ٤ وَمِنْ شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ ٥﴾



(Quran: Suratul Falaki 23)


Bayanin kula

  1. ِDaneshnameh Quran wa-Quran Pajuhi 1377, juzu'i na 2, shafi 1271.
  2. Rajeb Esfahani, Al-Mufradat alfaz Kur'an, 1412 AH, karkashin lafazin Falaq.
  3. Daneshnameh Quran wa-Quran Pajuhi 1377, juzu'i na 2, shafi 1271.
  4. Daneshnameh Quran wa-Quran Pajuhi 1377, juzu'i na 2, shafi 1271. karkashin suratul Nasi
  5. Marafet,Amuzeshi Ulumi Kur’an, 1371, juzu’ina 2, shafi na 166.
  6. Tabatabaei, Al-Mizan, 1394 Hijira, juzu'i na 20, shafi na 392.
  7. Daneshnameh Quran wa-Quran Pajuhi 1377, juzu'i na 2, shafi 1271.
  8. Tabatabaei, Al-Mizan, 1394 Hijira, juzu'i na 20, shafi na 392.
  9. Makarem Shirazi, Tafsir al-Namuneh, 1374, juzu'i na 27, shafi na 454.
  10. Tabatabai, Al-Mizan, 2002, juzu'i na 20, shafi na 394.
  11. Siyuti, Durrul Al-Manthor, 1404 AH, juzu'i na 6, shafi na 417.
  12. طباطبایی، الميزان، ۱۳۸۲ش، ج۲۰، ص۳۹۴.
  13. Ma’anar Isti'ara a nan gamammiya ce kuma ta haɗa da kowane nau’i na Isti'ara, ishara, izni na hankali da kowane irin kamanceceniya domin ranar rubuta wannan littafi shekaru da dama ne kafin haɗar ilimin ma’ana da magana. (Duba: Sayyed Razi, Talkhis al-Bayan a cikin hukuncin Alqur'ani, 1407 AH, Gabatarwa na Muhammad Al-Husaini al-Mashkwa, shafi na 11.Sayyed Razi, Talkhis Al-Bayan a cikin Hukuncin Alqur'ani, 1407H, shafi na 280.
  14. Masal Zamakhshri
  15. Alqur'an Kareem, Tauzihat, Wajeh Nameh:<a href="/w/index.php?title=%D8%A8%D9%87%D8%A7%D8%A1%D8%A7%D9%84%D8%AF%DB%8C%D9%86_%D8%AE%D8%B1%D9%85%D8%B4%D8%A7%D9%87%DB%8C&action=edit&redlink=1" class="new" title="بهاءالدین خرمشاهی (صفحه وجود ندارد)">بهاءالدین خرمشاهی</a>
  16. Tabatabai, Al-Mizan, 2002, juzu'i na 20, shafi na 393.
  17. Tabarsi, Majma Al-Bayan, 1338 H., juzu'i na 10, shafi na 491
  18. Tabarsi, Majma Al-Bayan, 1338 AH, juzu'i na 10, shafi na 491.
  19. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 92, shafi na 368.
  20. Tabarsi, Majma Al-Bayan, 1338 H., juzu'i na 10, shafi na 491
  21. Duba:Daneshnameh Qur'an wa-Qur'an Pajuhi, 1377, juzu'i na 2, shafi na 1271-1272.

Nassoshi

  • Alqur'an Kareem, tarjamar Muhammad Mehdi Fouladvand, Tehran, Darul Qur'an al-Karim, 1418H/1376H.
  • Alqur'ani Kareem, Tauzihat Wajeh Nameh: Bahauddin Khorramshahi, Tehran, Jami, Nilofar, 1376.
  • Daneshnameh Qur'an wa-Qur'an Pajuhi, kokarin Bahauddin Khorramshahi, juzu'i na 2, Tehran, Dostane-Nahid, 1377.
  • Ragheb Esfahani, Hossein bin Muhammad, Al-Mufardat fi Gharib Al-Qur'an, bincike na Safwan Adnan Davoudi, Beirut, Dar al-Alam al-Dar al-Shamiya, bugu na farko, 1412 AH.
  • Sayyid Razi, Muhammad Bin Hussain, Talkhis Al-Bayan fi Ahkam Kur'an, Tehran, Al-Tabar da Mu'assasa Wallafa na Ma'aikatar Al'adu da Shiryar da Musulunci, 1407H.
  • Siyuti, Al-Darrul Al-Manthor, Qum, Ayatullah Murashi Najafi Public Library, 1404H.
  • Tabatabaei, Al-Mizan, Qom, Islamic Publication Office, 2013.
  • Tabarsi, Al Bayan Majma, Tehran, Makarantar Kimiyya, bugun farko, 1338H.
  • Majlesi, Bihar Al-Anwar, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, 1403 AH.
  • Marafet, Mohammad Hadi, Amuzeshi Ulum Kur'an, [ba a buga ba], Cibiyar Buga da Buga ta Islamic Propaganda, Ch. 1, 1371.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir al-Namuneh, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, bugun farko, 1374.