Daƙiƙa:Ramadan
| Wata na tara cikin kalandar hijira ƙamari | |
|---|---|
| Bayanai na gaba ɗaya | |
| Wasu sunaye daban | Ramadan Al-Mubarak, Ramadan Al-Mu'azzam |
| Watan da ya gabata | Sha'aban |
| Watan da ya biyo baya | Shawwal |
| Ayyuka da al'adu | Nafilolin watan Ramadan, Itikafi, Raya dararen lailatul ƙadri |
| Cikin al'adu na addini | |
| Addu'o'i | Addu'ar shiga wata Ramadan, gajerun addu'o'i na yau da kullun, Du'a'u Iftitahi, Du'a'u Sahar, Du'a'u Abu Hamza Sumali, Du'a'u Mujir, Du'a'u Al-jaushanul Kabir |
| Hukunce-hukuncen shari'a | Azumin wajibi, duba jinjirin wata, Kaffaratul jam'i, Kaffarar azumi |
| Watanni masu alfarma | Baya ciki |
| Abubuwa da suka faru da munasabobi | Saukar Kur'ani, Yaƙin Badar, Fatahu Makka, Wilayat Ahad Imam Rida (A.S), Daren da aka sari Imam Ali (A.S), Mi'irajin Annabi, Ranar Ƙudus |
| Al'adun gargajiya | Raba abincin buɗa baki, Sahur, Girki da kuma kayan zaki na musamman na wannan watan, Sanar da lokacin Sahur |
Ramadan, (Larabc: رمضان) ma'ana wata na tara cikin jerin watannin hijira ƙamari, wata ne wanda cikinsa aka wajabta yin azumi kan Musulmi, cikin riwayoyin Musulunci an yi bayanin falaloli masu yawan game da wannan wata, kuma wata ne na liyafar Allah, wata ne na rahama da gafara da albarka, haka kuma ana kiransa da bazaran Kur'ani. Bisa abin da ya zo a cikin wasu hadisai, a cikin wannan wata ana buɗe ƙofofin aljanna kuma ana rufe ƙofofin jahannama. Cikin wannan wata lailatul Ƙadri da saukar Kur'ani suka kasance. Haka kuma wasu daga litattafan sama kamar Attaura da Injila suma an saukar da su a cikin wannan wata. Ramadan shi kaɗai ne watan da sunansa ya zo cikin Kurani. Watan Ramadan wata ne da yake da matsayi na musamman da girma da daraja a wurin Musulmi, A wannan wata al'ummar Musulmi suna himmatuwa sosai da ibada. A cikin litattafan addu'a an naƙalto ayyuka da ibada daban-daban. Daga cikin mafi muhimmancin ayyukan wannan wata akwai karatun Kur'ani, raya lailatul ƙadri, addu'a, sallah, istigfari, raba buɗa baki da kuma taimakon mabuƙata.
Daga muhimman abubuwan da suka faru a wannan wata akwai misalin saukar da Kur'ani a lailatul ƙadri da yaƙin Badar, wanda shi ne yaƙi na farko da ya fara faruwa tsakanin Musulmi da mushrikan ƙuraishawa ƙarƙashin kwamandancin Annabi (S.A.W), bugu da ƙari a dai cikin wannan wata ne Imam Ali (A.S) ya yi shahada, wanda ya kasance Imami na farko a wurin ƴanshi'a an shahadantar shi a rana ta 21 Ramadan. Imam Hassan Mujtaba (A.S) shima an haife shi 15 ga wannan wata.
Ibada da ɗaukar azumi wani ɓangare ne daga siffofi da alamomi na Musulmi, a cikin alumomin Musulmi, akwai wasu ladubba da ala'du daban-daban da ake yi a cikin wannan wata kamar shirya walima da taron jama'a, tsaftace masallatai da wuraren addini, da tarukan sulhu, da shirya nau'uka daban-daban na abincin buɗa baki.
Haka nan daga cikin hukunce-hukuncen watan Ramadan akwai cewa ba ya inganta a ɗauki azumi a halin tafiya da ta wajaba a yi ƙasaru.
Daya daga cikin manyan ibadu da bisa al'ada aka saba yi a wannan lokaci, shi ne shiga Itikafi domin neman aminci da yardar Allah.
Matsayi
Watan Ramadan, shi ne wata na tara cikin jerin watannin hijira ƙamariyya.[1] An wajabta azumi kan Musulmi a wannan wata.[2]
Kurani mai girma[3] da baarin litattafan sama kamar suhufu Ibrahim, Injila, Attaura da Zabura an saukar da su ga Annabawa a cikin wannan wata.[4]
Sau ɗaya aka ambaci kalmar Ramadan a cikin Kurani[5] Kuma shi kaɗai ne watan da sunansa ya zo a cikin Kurani:[6]
"Watan Ramadan shi ne watan da aka saukar da Kur'ani a cikinsa, a matsayin shiriya ga mutane, tare da bayyanannun hujjojin shiriya da kuma ma'aunin rarrabe gaskiya da ƙarya. Don haka duk wanda ya halarci wannan wata daga cikinku, to ya wajaba ya yi azumi a cikinsa. Amma wanda yake da rashin lafiya ko yana tafiya, to [ya rama] da adadin wasu kwanaki daban."
Suratul Baƙara aya ta 185
Haka kuma lailatul ƙadri da saukar da Kurani[7] Bisa abin da ya zo a riwayoyi[8] da tafsirai[9] sun faru ne a cikin watan Ramadan[10] Bisa mafi shaharar naƙali, Badar, yaƙi na farko a Muslunci da ya faru tsakanin Musulmai da maƙiyansu ƙarƙashin jagorancin Manzon Allah (S.A.W) da asubar ranar Jumaa 17 ga Ramadan[11] a wani naƙalin kuma an ce ya faru a ranar Litinin 17 ko 19 ga watan Ramadan[12]
Kalmar "Ramadan" a harshen Larabci tana nufin zafin rana.[13] an naƙalto cewa da wannan dalili ne ake kiran wannan wata da suna Ramadan saboda yana ƙone zunubai.[14] Haka kuma cikin madogaran riwayoyi, an bayyana cewa Ramadan ɗaya ne daga cikin sunayen Allah.[15]
Siffofi
Manzon Allah (S.A.W) cikin huɗubar watan Sha'aban ya yi bayanin wasu falaloli da watan Ramadan yake da su, daga cikinsu akwai:
- Cikin wannan wata an gayyaci mutane liyafar Allah.
- A wannan wata ne aka sanya lailatul ƙadri daren da ya fi watanni dubu alheri.
- Raya ko wane dare daga dararen wannan wata da sallah daidai yake da sallah guda sabain a cikin sauran watanni
- Wata ne na haƙuri, kuma aljanna ce ladan haƙuri.
- Wata ne na taimako da tausayawa mabuƙata.
- Wata ne da arziƙin muminai yake ƙaruwa.
Annabi (S.A.W) ya ce: watan Ramadan wata ne da ace za a san darajar da yake tare da ita, da mutum ya yi buri da fatan ace baki ɗayan shekara ta kasance Ramadan.[16] Bisa wata riwaya daga Annabi (S.A.W) yana cewa watan Ramadan, wata ne da ake ƙulle ƙofofin Jahannama kuma ana buɗe ƙofofin aljanna, kuma wata ne da ake ɗaure shaiɗanu da sasari da sarƙa.[17]
- A zamanin Annabi (S.A.W) an kasance ana kiran da watan Ramadan da sunan Marzuƙ (Azurtacce)[18][Tsokaci 1]
Haka kuma ya zo cikin riwayoyin maasumai cewa watan Ramadan wata ne da aka siffanta shi da watan Allah,[19] watan rahama da afuwar Allah,[20] watan albarka da ninka ladan ayyuka da goge zunubai[21] wata ne da idan har ba a yi wa mutum gafara a cikinsa ba to babu fatan samun gafara gare shi cikinsa sauran watanni.[22]
Wajabcin Azumi
A cikin watan Ramadan an wajabta yin azumi kan Musulmi[23] Azumi na nufin kaucewa yin wasu ayyuka daga jumla ci da sha tun daga farkon kiran sallar asubahi har zuwa kiran sallar magariba.[24] Umarni kan ɗaukar azumi da kuma bayanin hukunce-hukuncensa ya zo a cikin Kurani[25] da litatttafan fiƙihu. Bisa fatawar malaman fiƙihu idan mutum ya zamanto an masa afuwa daga ɗaukar azumi to bai kamata ya fito cikin mutane yana cin abinci ba.[26]
Karanta Addu'a
Karatun adduoin Sahur, daga jumla Duau Baha da Duau Abi Hamza Simali.[27] Kazalika Duaul Iftitahi cikin dararen wannan wata[28] da Duau Ya Ali Ya Azim, Allahumma Adkhil Ala Ahlil ƙuburis surura da “Allahumma arzuƙni Hajja baitikal harami” bayan sallolin farilla[29] sun kasance daga cikin gama-garin ayyuka a wannan wata.
Karatun Kur'ani
Cikin baarin riwayoyi, an bayyana watan Ramadan da bazaran Kurani[30] Hakazalika ladan karanta aya ɗaya a cikin watan Ramadan daidai yake da ladan kammala karatun Kurani a cikin sauran watanni.[31] A Wasu ƙasashen Musulunci, Musulmi tun daga farkon wannnan wata har zuwa ƙarshensa a ko wace rana suna karanta juzui guda na Kurani wanda zuwa ƙarshen watan suna kammala karanta baki ɗayan Kurani, wannan khatama da kammala karatun Kurani mafi yawan lokutan tana kasancewa ne a masallatai da sauran wuraren addini cikin tsarin adadin wasu jamaa. Haka kuma a ƙasar Iran ana watsa shirin karatun juzui tashoshin tabajizin da radiyo..[32]
Raya Lailatul Ƙadri

Bisa abin da ya zo a riwayoyi, lailatul ƙadri ya kasance ɗaya daga cikin dararen 19, 21, ko kuma 23 a watan Ramadan.[33] Cikin wasu riwayoyi, an ayyana daren 23 Ramadan matsayin lailatul ƙadri.[34] Shaik Saduƙ ya ce malamanmu sun yi ittifaƙi da cewa daren 23 Ramadan shi ne lailatul ƙadri.[35] A cewar Allama Ɗabaɗabai, maganar da ta shahara tsakankanin Ahlus-Sunna daren 27 Ramadan shi ne lailatul ƙadri.[36] Shia a ko wace dararen 19, 21 da 23 a wuraren addini ko gidajensu, suna raya waɗannan darare da ibada har zuwa lokacin sahur.[37] Daga cikin mafi alherin ayyuka da ake buƙatar yi cikin lailatul akwai misalin karanta adduar Al-Jaushanil Al-Kabir da ɗora Kurani aka.[38]
Sallolin Mustahabbi
Sallolin Mustahabbi suna daga cikin ayyukan watan Ramadan; Wasu daga cikin waɗannan nafiloli gama-gari ne da ake yin su cikin baki ɗayan dararen Ramadan, wasu kuma ana yinsu a wasu keɓantattun darare da ko wasu keɓantattun ranaku.[39]
Daga cikin ayyuka da suka shahara akwai umarni da yin sallah rakaa dubu da ake yi a cikin dararen Ramadan[40] An bayyana tsarinta kamar haka: daga dare na farkon Ramadan zuwa dare na 20, a ko wane dare za a yi rakaa 20. Daga dare na 20 har zuwa ƙarshen Ramadan, cikin ko wane za a yi rakaa 30, sannan cikin dararen da ake sa ran dacewa da lailatul ƙadri banda waɗannan rakaoi da aka ambata ana ƙara rakaa 100[41] Ahlus-Sunna a cikin ko wane dare suna yin sallar mustahabbi raka'a 20 wace suke kira da suna salatul tarawihi.[42] Ahlus-Sunna bisa biyayya da bin sawun halifa na biyu suna yin wannan sallah cikin tsarin jami, wanda yin haka bidia ne a wurin Shia.[43]
I'itikafi A Goman Ƙarshe
Daga cikin manyan ibadu da Musulmai suka saba yi a wannan lokaci, shi ne shiga Itikafi, domin neman tsaro da yardar Allah Maɗaukakin sarki. Wannan al'ada ce da aka gudanar a cikin addinin Musulunci tun farkon saukar Wahayi har zuwa yau, kuma Annabi Muhammad (S.A.W) ya tabbatar da ita, kamar yadda Allah ya ƙaddara.[44]
Itikafi a goman ƙarshen yana daga ayyuka na mustahabbi da suke tattare da tarin falaloli.[45] Goman ƙarshe, shi ne mafi kyawun lokaci na yin iitikafi wanda ladan yin iitikafi a cikinsa ana ɗauƙarsa daidai da ladan hajji guda biyu da umara guda biyu.[46] Annabi Akram (S.A.W) a farko ya fara zaɓar goman farkon watan Ramadan, sai kuma goma ta biyu, sai kuma goma ta uku domin yin iitikafi, bayan nan sa ya ci gaba da yin iitikafi a goman ƙarshe har zuwa ƙarshen rayuwarsa.[47]
Ladubba Da Aladu
Cikin alummun Musulunci akwai ladubba da alada da suka yaɗu a watan Ramadan.
Teburin Iftɗar
A ƙasashe daban-daban Musulmi kan shirya taron buɗa baki a wurare addini.[48] Haka kuma a ƙasar Iran mutane suna gayyatar juna zuwa gidajensu domin buɗa baki, haka nan a wuaren addini a lokacin buɗa baki ana raba abincin bakance..[49] Bisa wata riwaya daga Annabi (S.A.W) ladan duk wanda ya yi sadakar abincin buɗa baki ga mumini ko da gwargwadon ɗigon ruwa ko ɗanyen dabino yana daidai da ƴanta bawa.[50] A wasu yankuna, kai tsaye bayan kiran sallah ana tsayawa a yi buɗa baki, a wasu yankuna kuma sai bayan idar da sallar magariba da Isha.[akwai buƙatar kawo madogara]

Tashin Mutane Domin Sahur
A wasu birane ana sanar da lokacin sahur da tashin mutane daga bacci ta hanyoyi daban-daban kamar zagayawar mai sanarwa da masu shela loko-loko da saƙo-saƙo unguwanni da tituna domin sanar da lokacin sahur. Haka kuma ana Kunna fitilu a hasumiyoyin masallatai, kaɗa ganga da busa ƙahom buga ƙofofin gidaje da harba bindiga duka domin sanar da mutane lokacin sahur.[51] Haka kuma a gidajen radiyo da talabijin da bututun lasifiƙar masallatai a ƙasar Iran kafin kiran sallar asubahi ana karanta adduoin sahur, haka kuma gabanin magariba ana karanta munajati rabbana.


Aika Muballigai
Malaman Shia, a watan Ramadan suna zuwa birane da ƙauyuka domin wayar da kanmu mutane da koyar da su hukunce-hukuncen sharia da shirya laccoci da kuma limanci sallar jami.[52] Haka kuma cibiyoyin tabligi suna aika muballigai yankuna daban-daban na cikin ƙasar Iran da wasu ƙasashe domin tabligi.[53]
Karatun Adduoin Yau Da Kullum Cikin Taron Jama'a
Ƴanshia bayan idar da sallolin jami na yau da kullun, suna karanta adduar “Ya Aliyu Ya Azim” cikin taron jamaa, haka kuma mafi yawan lokuta ɗaya daga cikin masallata yana ɗaga sauti ya karanta adduar “Allahumma Adkhil ala ahlil ƙuburis surara” da adduar da ake karantawa a ko wace rana a watan Ramadan, sauran masu saurarensa kuma a ko wace gaɓa suna faɗin amin-amin. [akwai buƙatar kawo madogara]
Muzaharar Ranar Ƙudus
Imam Khomaini domin nuna goyan baya ga mutanen Falasɗinu a shekarar 1978m, ya sanya wa ranar Jumaa ta ƙarshen Ramadan cikin ko wace shekara da suna rana ranar ƙudus.[54] Musulmi a ƙasashe daban-daban na duniya a wannan rana cikin ko wace shekara suna shirya zanga-zanga nuna goyan baya ga mutane Falasɗinu da kuma ƴanto masallacin Al-Aƙsa.[55]
Sauran Ladubba Da Aladu
- Goge-goge da tsaftace gida, karkaɗe ƙura da share masallatai, wuraren ibada, unguwanni da kasuwanni a cikin kwanaki da suka rage kafin shiga watan Ramadan
- A Iran suna da wata alada da ake kira da suna Kuluk-andazan wace ake yi a ƙarshen watan Shaaban, mutane suna taruwa a manyan gidaje ko lambuna da wuraren shaƙatawa domin murna da walwala.
- Sulhunta mutane; mutanen da suka yi faɗa da juna suka yanke alaƙa, suna sulhun da juna.
- Azumin tarbar Ramadan: Ana yin azumi rana ɗaya zuwa uku kafin Ramadan a matsayin azumin tarbar Ramadan.[56]
- Aladar rigar muradi da zoɓen muradi
- Dafa gurasar ranar ashirin da bakwai
- Aladar bikin masoyi masoyi, Ali masoyi.[57]
Ayyana Farko Da Ƙarshen Ramadan
Ana tabbatar da farko da ƙarshen Ramadan ƙarƙashin ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi kamar haka:
- .Ganin jaririn wata: tabbatar da ganin jaririn wata a farko da ƙarshe
- .Samun yaƙini daga maganar wasu adadin mutane.
- .Shaidar adalan maza guda biyu da maganarsu ba ta ci karo da juna ba.
- .Cika kwanaki talatin da shigar wata.
- .Hukuncin shugaban sharia.[58]
Wasu hadisai, sun bayyana cewa watan Ramadan kwanaki talatin ne.[59] Wasu jamaa daga malaman Shia sun yi imani da wannan magana;[60] Akasin haka, bisa abin da ya zo cikin wasu riwayoyi, haƙiƙa watan Ramadan kamar dai sauran watanni yana yawo ne tsakanin kwanaki 29 ko 30.[61] Kuma mafi yawan malaman fiƙihu sun tafi kan wannan raayi.[62]
Watan Ramadan yana zuwa ƙarshe bayan shigar watan Shawwal da kuma sanar da ranar idin fiɗri, daga cikin ayyuka idul fiɗri akwai ba da zakkar fidda kai da sallar idi.[63]
Abubuwan Da Suka Faru Da Kuma Muhimman Ranaku
- Shelar Wilayatu Ahadi Imam Rida (A.S) (7 Ramadan shekara 201H)[64]
- Wafatin Sayyida Khadija (10 Ramadan da shekara 10 ga Biisa)[65]
- Taron ƙulla ƴan uwantaka tsakanin sahabban Annabi (S.A.W) da kuma tsakanin Manzon Allah (S.A.W) da Imam Ali (A.S) (12 Ramadan shekara 1 H)[66]
- Haihuwar Imam Hassan Mujtaba (A.S)(15 Ramadan 3H)[67]
- Yaƙin Badar (17 Ramadan shekara 2H)[68]
- Lailatul ƙadri da saukar da Kurani (Daren 19 Ramadan ko 21 ko 23 shekara 1H)
- Fatahu Makka (20 Ramadan shekara 8H)[69]
- Shahadar Imam Ali (A.S) (21 Ramadan shekara 40H)[70]
Bayanin kula
- ↑ Qureshi, Qamus al-Qur'an, 1412 H., juz 3, safa 123.
- ↑ Bustani, Farhang-e Abjadi, 1375 S., safa 443.
- ↑ Surat al-Baqarah, ayat 185.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1407 H., juz 2, safa 629.
- ↑ Al-Baqarah, ayat 185.
- ↑ Qara'ati, Tafsir-e Nur, 1388 S., juz 1, safa 285.
- ↑ Surat al-Qadr, ayat 1.
- ↑ Baraye nemune negah konid be: Kulayni, Al-Kafi, 1407 H., juz 4, safaha 66, 157 va 158.
- ↑ Negah konid be: Tabarsi, Majma' al-Bayan, 1372 S., juz 10, safa 786.
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, 1390 H., juz 20, safa 334.
- ↑ Ibn Sa'd, Al-Tabaqat al-Kubra, 1968 M., juz 2, safaha 14-15; Ya'qubi, Tarikh al-Ya'qubi, Dar Sadir, juz 2, safa 45.
- ↑ Ibn Sa'd, Al-Tabaqat al-Kubra, 1968 M., juz 2, safaha 14-15.
- ↑ Raghib, Mufradat Alfaz al-Qur'an, 1412 H., safa 366.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 H., juz 55, safa 341.
- ↑ Mazandarani, Sharh al-Kafi, 1382 H., juz 6, safa 110.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 H., juz 93, safa 346.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 H., juz 93, safa 348.
- ↑ Shaikh Saduq, Man La Yahduruhu al-Faqih, 1413 H., juz 2, safa 160.
- ↑ Saduq, Al-Amali, 1376 S., safa 19, hadith 1.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 H., juz 93, safa 342.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 H., juz 93, safa 340.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1407 H., juz 4, safa 66.
- ↑ Tabatabai Yazdi, Al-Urwat al-Wuthqa (Muhashi), 1419 H., juz 3, safa 521.
- ↑ Allama Hilli, Tadhkirat al-Fuqaha, 1414 H., juz 6, safa 5.
- ↑ Surat al-Baqarah, ayat 183-185 va 187.
- ↑ Negah konid be: Mousavi Golpayegani, Majma' al-Masa'il, 1409 H., juz 3, safa 215.
- ↑ Sayyid Ibn Tawus, Al-Iqbal bil A'mal al-Hasanah, 1376 S., juz 1, safaha 156–185.
- ↑ Sayyid Ibn Tawus, Al-Iqbal bil A'mal al-Hasanah, 1376 S., juz 1, safa 138.
- ↑ Sayyid Ibn Tawus, Al-Iqbal bil A'mal al-Hasanah, 1376 S., juz 1, safaha 79 va 80.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1407 H., juz 2, safa 630.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 H., juz 93, safa 341.
- ↑ «زمان پخش ترتیل جزءخوانی قرآن کریم در تلویزیون + جدول»، ISNA
- ↑ Duba: Al-Kulayni, Al-Kafi, shekara ta 1407 Hijiriyya, juzu'i na 4, shafi na 156–160
- ↑ Duba: Al-Kulayni, Al-Kafi, shekara ta 1407 Hijiriyya, juzu'i na 4, shafi na 158, hadisi na 8; Al-Saduq, Al-Khisal, shekara ta 1362 Hijiriyya ta Shawa, juzu'i na 2, shafi na 508, hadisi na 1.
- ↑ Al-Saduq, Al-Khisal, shekara ta 1362 Hijiriyya ta Shawa, juzu'i na 2, shafi na 519.
- ↑ Al-Tabataba'i, Al-Mizan, shekara ta 1390 Hijiriyya, juzu'i na 20, shafi na 334.
- ↑ Majidi Khameneh, "Dare-dare Mai Girma a Iran", shafi na 21.
- ↑ Majidi Khameneh, "Dare-dare Mai Girma a Iran", shafi na 22.
- ↑ Duba: Al-Qummi, Mafatih al-Jinan, bugu na Asowah, shafi na 183 da 238 da 239.
- ↑ Al-Qummi, Mafatih al-Jinan, bugu na Asowah, shafi na 183 da 184.
- ↑ Al-Najafi, Jawahir al-Kalam, Dar Ihya' al-Turath al-Arabi, juzu'i na 12, shafi na 187–190.
- ↑ «چرا شیعیان نماز تراویح نمیخوانند؟»، Shafin yanar gizo na wakilin Waliyyi Faqih a harkokin Hajji da Ziyara.
- ↑ صادقی فدکی، «تراویح»، Kundin sani (Encyclopedia) na Hajji da Haramai biyu masu tsarki (Makkah da Madinah).
- ↑ https://hausa.legit.ng/1330201-falalar-kwanaki-goman-karshe-na-watan-ramadan.html
- ↑ Al-Qummi, Mafatih al-Jinan, Buga na Asowah, Shafi na 234.
- ↑ Al-Qummi, Mafatih al-Jinan, Buga na Asowah, Shafi na 234.
- ↑ Al-Kulayni, Al-Kafi, shekara ta 1407 bayan Hijira, juzu'i na huɗu, shafi na ɗari saba'in da biyar, hadisi na uku.
- ↑ «رمضـان در کشورهای مختلف جهان»،Shafin Kehan.
- ↑ «افطاری»،Cibiyar Babban Kundin Sani na Musulunci (The Center for the Great Islamic Encyclopedia).
- ↑ Al-Saduq, Uyun Akhbar al-Rida (SAW), shekara ta 1378 Hijiriyya, juzu'i na 1, shafi na 295-297, hadisi na 53.
- ↑ Duba: Rahimi, "Ramadan."
- ↑ «تبلیغ، قلب دین»،Kamfanin Labarai na Fars
- ↑ «آغاز ثبتنام مبلغان در خارج از كشور».، Kamfanin dillancin labarai Hauza
- ↑ Imam Khomeini, Safihah Imam (Rubutun Imam), shekara ta 1389 Shamsiyya (Hijiriyya ta Shawa), juzu'i na 9, shafi na 267.
- ↑ «جهان و روز جهانی قدس»،Kamfanin dillancin labarai na Tasnim.
- ↑ Ku duba Rahimi«رمضان»، Kundin sanin duniyar Muslunci.
- ↑ «مراسم سنتی دوست، دوست و پیراهن مراد در شب بیست و هفتم ماه رمضان یزد»، Kamfanin dillancin labarai na Jamhuriyar Musulunci.
- ↑ Imam Khomeini, Taudihin Masail (mahashi), shekara ta 1424 Hijiriyya, juzu'i na 1, shafi na 959.
- ↑ Al-Hurr al-Amili, Wasail al-Shia, shekara ta 1409 Hijiriyya, juzu'i na 10, shafi na 268–274.
- ↑ Sayyid Ibn Tawus, Al-Iqbal, shekara ta 1376 Shamsiyya, juzu'i na 1, shafi na 33–35.
- ↑ Al-Hurr al-Amili, Wasail al-Shia, shekara ta 1409 Hijiriyya, juzu'i na 10, shafi na 261–268.
- ↑ Duba: Al-Bahrani, Al-Hada'iq al-Nadira, shekara ta 1405 Hijiriyya, juzu'i na 13, shafi na 270–271; Al-Amili, Misbah al-Huda, shekara ta 1380 Hijiriyya, juzu'i na 8, shafi na 384.
- ↑ Al-Najafi, Jawahir al-Kalam, shekara ta 1404 Hijiriyya, juzu'i na 11, shafi na 332-333.
- ↑ Al-Ya'qubi, Tarikh al-Ya'qubi, shekara ta 1378 Shamsiyya, juzu'i na 2, shafi na 465.
- ↑ Ibn Sa'd, Al-Tabaqat al-Kubra, shekara ta 1410 Hijiriyya, juzu'i na 8, shafi na 14.
- ↑ Al-Qummi, Waqai al-Ayyam, shekara ta 1389 Shamsiyya, shafi na 58.
- ↑ Sheikh al-Mufid, Al-Irshad, shekara ta 1413 Hijiriyya, juzu'i na 2, shafi na 5; Al-Tabari, Tarikh al-Tabari, shekara ta 1387 Hijiriyya, juzu'i na 2, shafi na 537.
- ↑ Al-Ya'qubi, Tarikh al-Ya'qubi, Dar al-Sadir, juzu'i na 2, shafi na 45.
- ↑ Al-Tabari, Tarikh al-Tabari, shekara ta 1387 Hijiriyya, juzu'i na 2, shafi na 343.
- ↑ Al-Mufid, Al-Irshad, shekara ta 1413 Hijiriyya, juzu'i na 1, shafi na 9.
Tsokaci
- ↑ Bisa ga rahotanni, abin da aka ƙaddara wa mutane kamar abubuwan da suka faru, masĩfu, da arziki, ana ƙayyade su a cikin wannan dare. A haƙiƙa, duk arziki da rabon su na zahiri da na ruhani ana rubuta su.
Nassoshi
- «ماه مبارک رمضان نمادی از هویت دینی جامعه اسلامی است»،Kamfanin labarai na Ƙur’ani na ƙasa da ƙasa, ranar wallafa bayani: 8 Khordad 1395 SH, ranar dubawa: 18 Farvardin 1401 SH.
- Majidi Khameneh, Farideh، «شبهای قدر در ایران»A cikin mujallar Golestan-e Qur’an, lamba ta 37, Azar 1379 SH.
- Al-Hurr al-Amili, Muhammad bin al-Hasan, Wasail al-Shi'a, Qum, Mu'assasah Al al-Bayt (A.S.), 1409 H.
- Al-Raghib, Al-Husayn bin Muhammad, Mufradat Alfaz al-Qur'an, Beirut - Dimashq, Dar al-Qalam - Dar al-Shamiyah, bugu na farko, 1412 H.
- Amoli, Mirza Muhammad Taqi, Misbah al-Huda fi Sharh al-'Urwat al-Wuthqa, Tehran, Nashr al-Mu'allif, 1380 H.
- Fatima Rahimi «رمضان»Kundin Ilimin Duniya na Musulunci (juzu’i na 20), ranar dubawa: 18 Farvardin 1401 SH.
- Kulayni, Muhammad ibn Ya'qub, Al-Kafi, Tahqiq wa Tas-hih Ali Akbar Ghaffari wa Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyah, Chap-e Chaharum, 1407 H.
- Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar al-Jami'ah li Durar Akhbar al-A'immah al-Athar (A.S.), Beirut, Dar Ihya' al-Turath al-'Arabi, bugu na biyu, 1403 H.
- Mazandarani, Sharh al-Kafi (Al-Usul wa al-Rawdah), Tahqiq wa Tas-hih Abul Hasan Sha'rani, Tehran, Al-Maktabah al-Islamiyah, Chap-e Aval, 1382 H.
- Mousavi Golpayegani, Sayyid Muhammad Reza, Majma' al-Masa'il, Tahqiq wa Tas-hih: Ali Karimi Jihromi, Ali Thabeti Hamedani, wa Ali Niri Hamedani, Dar al-Qur'an al-Karim, Qum, bugu na biyu, 1409 H.
- Mufid, Muhammad ibn Muhammad, Al-Irshad fi Ma'rifat Hujaj Allah 'ala al-'Ibad, Tas-hih Mu'assasah Al al-Bayt, Qum, Kungirah Shaykh Mufid, bugu na farko, 1413 H.
- Legit Hausahttps://hausa.legit.ng/1330201-falalar-kwanaki-goman-karshe-na-watan-ramadan.html
- Najafi, Muhammad Hasan, Jawahir al-Kalam fi Sharh Shara'i' al-Islam, Beirut, Dar Ihya' al-Turath al-'Arabi, bugu na bakwai, babu tarihin shekara
- Qara'ati, Mohsen, Tafsir-e Nur, Tehran, Markaz-e Farhangi-ye Darsha-ye az Qur'an, Chap-e Aval, 1388 Sh.
- Qummi, Shaykh Abbas, Fayz al-'Alam fi 'Amal al-Shuhur wa Waqayi' al-Ayyam, Entesharat-e Sobh-e Pirouzi, Bi Ta.
- Qummi, Shaykh Abbas, Mafatih al-Jinan, Qum, Nashr-e Osve, Bi Ta.
- Saduq, Muhammad ibn Ali, Al-Amali, Tehran, Kitabchi, bugu na shida, 1376 S.
- Saduq, Muhammad ibn Ali, Al-Khisal, Tahqiq wa Tas-hih Ali Akbar Ghaffari, Qum, Jami'ah Mudarrisin, bugu na farko, 1362 S.
- Saduq, Muhammad ibn Ali, Uyun Akhbar al-Rida (A.S.), Tahqiq wa Tas-hih Mahdi Lajvardi, Tehran, Nashr Jahan, bugu na farko, 1378 H.
- Sayyid Ibn Tawus, Ali ibn Musa, Al-Iqbal bil A'mal al-Hasanah Fima Yu'mal Marratan fil Sanah, Tahqiq wa Tas-hih Jawad Qayyumi Isfahani, Qum, Daftar Tablighat Islami, bugu na farko, 1376 S.
- Tabari, Tarikh al-Umam wal Muluk, Tahqiq Muhammad Abu al-Fadl Ibrahim, Beirut, Dar al-Turath, tab'a ta biyu, 1387 H.
- Tabarsi, Fadl ibn Hasan, Majma' al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Nasir Khusraw, bugu na uku, 1372 S.
- Tabatabai Yazdi, Sayyid Muhammad Kazim, Al-'Urwat al-Wuthqa (Muhashi), Qum, Daftar Nashr al-Islami, bugu na farko, 1419 H.
- Tabatabai, Sayyid Muhammad Husayn, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Mu'assasah al-A'lami lil Matbu'at, bugu na biyu, 1390 H.
- «چرا شیعیان نماز تراویح نمیخوانند؟»، Ofishin wakilcin Waliyyul-Faqih a harkokin Hajji da Ziyara, ranar wallafa bayani: 24 Dey 1391 SH, ranar dubawa: 18 Farvardin 1401 SH.
- «فرهنگ غذایی جهان در ماه رمضان+ تصاویر»، Shafin yanar gizo na Al-Kawthar, ranar dubawa: 18 Farvardin 1401 SH.
- «رمضـان در کشورهای مختلف جهان»،Shafin yanar gizo na Kayhan, ranar wallafawa: 25 Farvardin 1402 SH, ranar dubawa: 10 Ordibehesht 1402 SH.
- «افطاری»،Shafin yanar gizo na Cibiyar Babbar Da’irar Ilimin Musulunci, ranar wallafawa: 22 Ordibehesht 1400 SH, ranar dubawa: 10 Ordibehesht 1402 SH.
- «تبلیغ، قلب دین»،Kamfanin labarai na Fars, ranar wallafawa: 8 Tir 1398 SH, ranar dubawa: 10 Ordibehesht 1402 SH.
- «آغاز ثبتنام مبلغان در خارج از كشور»،Kamfanin labarai na hukuma na Hauza, an wallafa labarin a ranar 9 Khordad 1390 SH, an duba a ranar 29 Farvardin 1402 SH.