Ziyaratu Nahiya Muƙaddasa

Daga wikishia
wata gaba daga ziyarar nahiya mukaddasa

Ziyaratu Nahiya Mukaddasa (Larabci: زيارة الناحية المقدسة) tana daga cikin ziyarorin Imam Husaini (A.S) da aka yi wasicci da karanta su ranar Ashura, `Yan Shi’a suna karanta wannan ziyara a sauran ranaku, ana fara wannan ziyara tare da sallama ga Annabawa da A’imma (A.S) sai kuma a cigaba da karantawa tare da sallama ga Imam Husaini da Sahabbansa, bayan nan kuma sai a tsunduma cikin sharhin siffofi da ayyukan Imam (A.S) da fagen Mikewarsa, shahdarsa da kuma Makokin dukkanin halittu kan shahadarsa. Hakika Ibn Mashadi wanda ya mutu shakara ta 610 shi ne ya nakalto Ziyaratu Nahiya Mukaddasa, Allama Majlisi ya tabbatar da cewa Ibn Mashadi da Shaik Mufid wanda ya mutu shekara ta 413 sune suka nakaltota, sai dai cewa bayani bai zo karara cikin litattafan hadisi wanne Imami ne ya yi bayaninta, amma wasu ba’ari suna cewa ta fito ne daga Nahiyar Imam Mahadi (A.S)

Suna Da Kuma Muhimmanci Ziyaratu Nahiya Mukaddasa ziyara ce da ta tattaro Musibun Husaini da Sahabbansa [1] da wannan dalili ne ma Malamai masu Muhadara da Mawaka suke yawan dogara da ita. [2] Ibn Mashadi yana kirgata cikin ayyukan ranar Ashura, [3] sai dai cewa kuma `Yan Shi’a suna karantata cikin sauran ranaku. [4] Wannan ziyara ana kiranta da sunaye misalin Ziyaratu Nahiya Mashhur, [5] da kuma ZIyaratu Nahiya Ma’aruf, [6] kishiya ga Zyaratu Nahiya Gairu Mashhur. [7] Nahiya Mukaddasa wani Isdilahi ne da `Yan Shi’a suke amfani da shi tun zamanin Imam Hadi (A.S) har zuwa karshen Gaiba Sugra, matsayin ishara zuwa ga Imami Ma’asumi (A.S) [8]

Ku duba: Nahiya Mukaddasa

Ziyaratu Nahiya Mukaddasa Daga Wanne Imami Ta Fito? Bayani kan karara kan cewa daga wanne Imami ta fito bai zo ba karara cikin Masadir din Hadisi, kadai dai cikin littafin Al-Mazar Al-Kabir talifin Ibn Mashadi wanda ya mutu shekara ta 610 h kamari, ya zo cewa ta fito daga Nahiya Mukaddasa (A.S) [9] Allama Majlisi shima ya bada rahoto daga Mashadi da Shaik Mufid wanda ya mutu shekara ta 413, kan Ziyarar ba tare da ya yi bayani daga wanne Imami Ma’asumi aka samota ba. [10] Tare da dukkanin wadannan bayanai, Malamai sun fitar da Natija daga wani ba’arin daga Maganar Ibn Mashadi lokacin Nakaltota cewa wannan ziyara ce da Imam Mahadi (A.F) ya fadeta ga daya daga Na’ibansa guda hudu, [11] Maganar Ibn Mashadi ta kasance kamar haka: [12]

«وَ مِمَّا خَرَجَ مِنَ النَّاحِيَةِ عَلَيْهِ السَّلَامُ إِلَى أَحَدِ الْأَبْوَاب

Daga cikin abin da ya fito daga Nahiya Mukaddasa (A.S) zuwa ga daya daga Na’ibai

Abinda Ziyarar Ta Tattaro

Gabobin Ziyara

اَلسّلامُ عَلَی الشَّیبِ الخَضیبِ Aminci ya tabbata kan gemun da aka masa Kunshi da ruwan jini اَلسّلامُ عَلَی الخَدِّ التَّریبِ Aminci ya tabbata kan Kumaun da aka Tuburbuda shi da Kasa اَلسّلامُ عَلَی الثَّغرِ المَقروعِ بِالقَضیبِ Aminci ya tabbata kan Wushiyaryar da aka zungura Sanda cikinta. اَلسّلامُ عَلَی الرَّأسِ المَرفوعِ Aminci ya tabbata kan Kai da aka daga shi Sama yana Soke a kan Mashin Yaki اَلسّلامُ عَلَی الاَجسادِ العارِیةِ فِی الفَلَواتِ Aminci ya tabbata kan Jikkuna da aka yi wa Tsirara aka barsu yashe cikin Daji. Hakika wannan ziyara ana fara ta da yin Sallama ga Annabawa, Ahlil-Baiti, Imam Husaini (A.S) da kuma Sahabbansa na Filin Karbala, bayan nan kuma sai a shiga fara Sharhin Siffofi da Ayyukan Imam Husaini (A.S) gabanin Waki’ar Karbala, sharar fagen mikewa da yunkurin Ashura, Shahada da kuma wahalhalun da ya fuskanta shi da Sahabbansa, Makokin Halittu, daga karshe kuma aka hattama ta da Tawassuli da kuma Addu’a. [13] A farkon wannan ziyara anyi Sallama ga Annabawa guda 24 da kuma As’habul Kisa tare da ambaton shahararrun Siffofinsu, [14] aminci ya tabbata ga Husaini (A.S) wani lokaci kuma tare da ambaton suna da kuma Falaloli da ayyukansa, wani lokacin kuma ana sallama kan sashen sassan gabban jikinsa tare da bayanin Musibar da ta gangara kansu. [15]

Bayanin Hususiyoyin Imam Husaini

An yi bayanin wasu ba’arin Hususiyoyin Imam (A.S) Husaini cikin wannan Ziyara: Akwai samun waraka cikin Turbarsa. Ana amsa addu’a a karkashin kasan Kabarinsa. A’imma sun fito daga tsatsonsa. Ya kasance `da ga Annabi (S.A.W) Ali (A.S) da Fatima (A.S). [16]

Isnadin Ziyaratu Nahiya Mukaddasa

An nakalto Wannan Ziyara daga littafin Al-Mazar Al-Kabir na Ibn Mashadi wanda ya mutu shekara ta 610, [17] na’am Allama Majlisi cikin Bihar-Anwar tare da nakalinta daga littafin Al-Mazar talifin Shaik Mufi wanda ya mutu shekara ta 423 ya kawota, [18] sai dai cewa kuma cikin Kofin da yake hannu a yanzu daga wannan littafi nasa babu Ziyaratu Nahiya Mukaddasa a cikinsa. [19] Ibn Mashadi cikin littafinsa ya ce abin da na nakalto cikin wannan littafi na nakalto shi ne ta hanyar Sikatu zuwa Sadatu. [20] wasu cikin dogara da cewa abin da yake nufi daga sadatu shi ne Imamai Ma’sumai sun tafi kan cewa riwayoyin da suke cikin littafin riwayoyi ne masu inganci, duk da cewa akwai riwayoyi Mursalai. [21] haka kuma suna kirga wannan maganar da ya yi cikin gamammen tausiki, ma’ana baki dayan Marawaitan cikin Littafin nasa Sikatu ne. [22] Sabanin Ayatullahi Kuyi a cikin littafin Mujamu Rijalil Al-hadis, ya bayyana cewa bai yarda da ingancin Littafin Al-Mazar Al-Kabir da shi kansa ma Ibn Mashadi din ba saboda mutum ne da ba a san shi ba, [23] Muhammad Hadi Yusufi Garawi wanda aka Haifa a shekara ta 1327 h shamsi, Masanin Tarihi shima ya yi kokwanto kan Isnadin wannan ziyara, yana cewa ba’arin wasu abubuwa da suke cikin wannan ziyara basa dacewa da Musallamat din ingantaccen Tarihin Makatil. [24] amma tare da haka Najamud Addini Tabasi wanda aka Haifa shekara ta 1334 h shamsi, wanda ya kasance Masanin Hadisi ya bayyana cewa karbarta da Malamai suka yi da kuma dogara da ita kamar misalin Sayyid Ibn Tawus, Shahid Awwal, Allama Majlisi da Muhaddisul Nuri yana sanya samun nutsuwa kan Sikantuwar Ibn Mashadi. [25]

Ziyarar Da Aka Nakaltota Daga Sayyid Murtada

Sayyid Bn Tawus cikin littafin Misbahul Az-Za’ir ya nakalto wata ziyara daga Sayyid Murtada wanda ya mutu shekara ya 436 h kamari, wacce ake kira da Ziyaratu Sanawiyya Bi-Alfaz Shafiya, ana kuma kidayata cikin ayyukan ranar Ashura. [26] a cewar Muhammad Ihsani cikin Makala mai taken (Itibaru Sanadi Ziyarathaye Nahiya Mukaddasa) kaso biyu cikin ukun matanin ziyara Nahiya mukaddasa ya zo cikin wannan ziyara, [27] Allama Majlisi ya kawo tsammani cewa dalilin wannan banbanci da yake tsakanin ziyarorin biyu ya faru ne daga banbanci kofi da aka samu, ku kuma da cewa akwai tsammani mai karfi kan haka. Sayyid Murtada ya kara wasu kalmomin daga gare shi cikin Ziyaratu Nahiya Mukaddasa, [28] Ihsanfur bai jingina ziyarar da ya nakalto daga Sayyid Murtada zuwa ga Ma’asumi ba, ya ce wannan ziyara ta Sayyid Murtada tana banbanci daga asasi da Ziyara Mukaddasa, [29]

Kokwanto Kan Ingancin Gangarowar Wasu Gabobin Ziyarar Daga Ma’asumi

Wasu ba’arin Marubuta bisa la’akari da wasu gabobi daga ziyarar sun nuna shakku da kokwanto kan fitowar ziyarar daga Ma’asumi, daga jumla sun ce wannan gabar da yake cewa: (mata sun fito ta bayan labulen Haimomi, daidai lokacin da kitsonsu duk ya kwance, suna marin fuskokinsu,sun cire Nikabinsu daga fuskarsu) wannan Magana ba ta dacewa da Mabani na Shi’a, saboda ya zo a riwaya cewa an yi hani kan kwance gashi da marin fuska lokacin bakin ciki, haka kuma wannan aiki baya dacewa da Mukamin Hakurin matan Ahlil-Baiti musammam ma Hazrat Zainab (S) kan jarabbawar da Allah ya yi a kansu. [30] amsar kan wannan ishkali an ce wannan jumla da ta zo cikin wannan ziyara ta Sayyid Murtada ta zo ne a Mukamin Kinaya, ma’ana dai Matan sun shiga matsanancin bakin ciki. [31] Haka kuma wasu sun yi suka da ishkali kan jumlar( hakika Shimru ya zauna kan Kirjinka ya sara Takobinsa ta nutse cikin wuyanka ya kamo gashinka sannan ya yankaka da Takobinsa) wannan Jumla bata dacewa da wasu rahotannin daban da suka bayyana cewa Shimru ya yanka Imam Husaini (A.S) ne ta keya. [32]

Wasu Adadin Sharhi Da Aka Kan Ziyaratu Nahiya Mukaddasa

An rubuta Sharhi daban-daban kan Ziyaratu Nahiya Mukaddasa, jumlarsu wasunsu ta kasance kamar haka: Az-Zakiratul Al-Bakiyatu, talifin Muhammad Jafar Shamili, cikin Harshen Farisanci. Ash-shamsul Adh-Dhahiya, talifin wasu adadi daga Malamai, cikin harshen Farisanci. Tuhfatul Ka’imiyya. Talifin Shaik Muhammad Fakihu Imani, cikin harshen Farisanci. Kashful Dhahiya, wasu ba’arin Malaman Kasar Indiya, cikin harshen Urdu. Hamrahe Nur; Sharh Ziyarat Nahiya Mukaddasa, talifin Sayyid Hidayatullahi Talikani, cikin harshen Farisanci. Salam Mau’ud, Bayan wa Tahlili wa Tausifi Ziyarat Nahiya Mukaddasa, talifin Muhammad Rida Sangari. 33 cikin harshen farisanci.

Bayanin kula

1. Mohammadi Rishahri,Daneshnameh Imam Husaini (AS), 2008, juzu'i na 12, shafi na 271.
2. Mohammadi Rishahri,Daneshnameh Imam Husaini (AS), 2008, juzu'i na 12, shafi na 271
3. Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1378, shafi na 496.
4. «سیری در زیارت ناحیه مقدسه»
5. «زیارت ناحیه مقدسه»
6. Dubi Tabasi, “Ziyarat Nahiye Mukaddaseh”, shafi na 194.
7. «زیارت ناحیه مقدسه»
8. Mohammadi Rishahri, daneshnameh Imam Husaini (AS), juzu'i na 12, shafi na 271, shafi na 1.
9. Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1378, shafi na 496.
10. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 101, shafi na 317, 328.
11. Ehsanifar, "Itibar Sanadi zyarat Nameh Nahiye mukaddasseh", shafi na 56-57
12. Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1378, shafi na 496.
13. در محضر زیارت ناحیه
14. در محضر زیارت ناحیه
15. «سیری در زیارت ناحیه مقدسه»
16. در محضر زیارت ناحیه
17. Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1378, shafi na 519-496.
18. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 101, shafi na 317.
19. Mohammadi Rishahri,Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 7, shafi na 59.
20. Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1378, shafi na 27.
21. Ehsani Far, "Itibar Sanadi Ziyarat Nahiye Mukaddaseh", shafi na 53.
22. Mousavi Gharifi, Kawa'idul Al-Hadis, Beta, shafi na 188.
23. Khoi, Mujam Rijal al-Hadith, 1372, juzu'i na 1, shafi.51
24. بررسی تحلیلی سیر مقتل‌نگاری عاشورا
25. Tabasi, “ziyarat nahiye mukaddaseh”, shafi na 209.
26. Sayyid Ibn Tavus, Misbah al-Zaer, 1417H, shafi na 221.
27. Ehsani Far, "Itibar Sanadi ziyarat nahiye mukaddaseh", shafi na 66.
28. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 101, shafi na 328.
29. Ehsani Far, "Itibar Sanadi ziyarat nahiye mukaddaseh", shafi na 65-66.
30. Ranjbar, " Fajuheshi baraye do Ziyarat, Ziyarat Nahiye MUkaddaseh wa Ziyarat Rajbiyeh", shafi na 65-66..
31. Ihasanifar, "Itibar Sanadi ziyarat nahiye mukaddaseh", shafi na 54.
32. >Ranjbar, " Fajuheshi baraye do Ziyarat, Ziyarat Nahiye MUkaddaseh wa Ziyarat Rajbiyeh", shafi na 67

Nassoshi