Ziyaratu Shuhada
Ziyaratu Shuhada (Larabci: زيارة الشهداء) ko Kuma Ziyaratu Nahiye Gairu Mash’hur, wata ziyara ce da ta kebanci Shahidan Karbala wacce ake kidayata cikin ayyukan Ranar Ashura da a ka yi Wasicci a kansu, Muhammad Bn Jafar Mashadi wanda ya mutu shekara ta 610 h Kamari cikin Al-Mazar Al-Kabir da Sayyid Ibn Tawus wanda ya mutu shekara ta 664 h Kamari, cikin littafin Al-Ikbal, dukkaninsu sun rawaito wannan ziayara. Cikin wannan ziyara an ambaci sunan kowanne Shahidi tare da Gaisuwa a gare shi, da kuma la’antar Makasan kowanne daya daga cikinsu tare da Ambato sunayensu. ba a bayyana isnadin Ziyaratu Shuhada ba da cewa wanne Imami ne ya yi bayaninta, kadai dai ya zo cewa an sameta daga Nahiya Mukaddasa. Nahiya Mukaddasa: wani Isdilahi ne da`Yan Shi’a suke amfani da shi domin ishara zuwa ga Imam Hadi (A.S) da Imam Mahadi (A.F).
Ziyaratu Shuhada Wata Ziyara ce Domin Shahidan Karbala
kuma ana kidayata cikin ayyukan Ranar Ashura. [1] cikin wannan ziyara bayan yin sallama da gaisuwa ga Imam Husaini (A.S) ana sallama ga Shahidan Karbala daya bayan daya tare da ambaton sunayensu, haka kuma ana la’antar Makasansu daya bayan daya tare da Ambato sunayensu. [2] Ziyaratu Shuhada ana kiranta da sunan Ziyaratu Nahiya Mukaddasa Gairu Mash’hura. [3] kishiya ga Ziyaratu Mukaddasa Mash’hura, [4] haka kuma ana kiranta da Ziyaratu Nahiya Ma’arufa. [5]
Danganta Ziyaratu Shuhada Zuwa Ga Nahiya Mukaddasa
Cikin Masadir din Hadisi bayani kan Ziyaratu Shuhada bai zo karara a fili ba da cewa wanne Imami Ne ya yi bayaninta, kadai a shekara ta 252 ta fito daga Nahiya Mukaddasa [6] Nahiya Mukaddasa wani Isdilahi ne da `Yan Shi’a suke amfani da shi domin ishara zuwa ga Imam Hadi (A.S) ko Imam Mahadi (A.F) zuwa karshen Gaiba Sugra. [7] Abdullahi Mamakani Masanin Ilmin Rijal na Shi’a wanda ya mutu shekara ta 1351 h kamari ya danganta wannan ziyara zuwa ga Imam Hadi (A.S) [8] Na’am Imam (A.F) shekaru bayan wannan kwanan tarihi a shekara ta 255. [9] ko 256, [10] ya zo duniya ma’ana aka haife shi (A.S) [11] da wannan dalili neya sanya wasu suka tafi kan cewa abin da ake nufi da Nahiya Mukaddasa cikin sanadin ziyarar ishara ce zuwa ga Imam Hadi (A.S) da Imam Hassan Askari (A.S) [12] Allama Majlisi ya kawo tsammanin Fuskoki biyu, ta farko akwai yiwuwar faruwar kuskure cikin ambaton kwanan tarihi wanda a Asali a shekara ta 262 ya kasance amma suka rubuta 252, na biyu abin nufi da Nahiya Mukaddasa shi ne Imam Hassan Askari (A.S). [13]
Ingancin Sanadin Ziyara
Muhammad Bn Jafar Mashadi wanda ya mutu shekara ta 610, ya rawaito Ziyaratu Shuhada cikin Littafin Al-Mazar Al-Kabir, [14] haka Sayyid Ibn Tawus wanda ya mutu a shekara ta 664 shima ya rawaitota cikin littafin Al-Ikbal, [15] a cewar Muhammad Shamsud Addini wanda ya mutu shekara ta 1379 h shamsi cikin littafin Ansarul Al-Husaini, wasu ba’arin Marawaita da aka samu sunansu cikin wannan ziyara Marawaita ne Majhulai, kuma sunansu bai zo cikin litattafan Ilimin Rijal in banda littafin Kamus Ar-Rijal wanda aka rubuta a shekara ta 1360 h Kamari, kuma tare da haka ba’arinsu raunana ne. [16] Ayatullahi Kuyi wanda ya mutu shekara 1413 h Kamari cikin littafin Mujamu Rijalil Al-hadis, ya ce ba zamu iya samun yakini da cewa wannan ziyara daga Nahiya Mukaddasa ta fito, [17] Muhammad Mahadi Shamsud Addini yana ganin danganta wannan ziyara ga Imam Mahadi Magana ce mai rauni, tare da haka ya yi Imani kan cewa bisa duba da Matanin tarihi za a iya dogara da ita. [18] Kishiyantar wancan magana, Najamud Addini Tabasi Masanin Hadisi, shi bai karbi ishkalai da sukan da akayi kan sanadin wannan ziyara ba. [19] shi yana ganin ingancin wannan ziyara bisa dogaro da abin da ta kunsa da kuma dacewarsa da Addu’o’i da matanin sauran ziyarori da kuma dabbakuwarta da rahotannin tarihi. [20]
Adadin Shahidai Da Sunansu Ya Zo Cikin Ziyarar
A cewar Muhammad Mahadi Shamsud Addini, hakika ziyaratu Shuhada wacce ta zo cikin littafin Al-Ikbal na Sayyid Ibn Tawus ta kunshi sunayen Shahidai 63, [21] amma Muhammad Ibrahim Ayati shi ya ce a a ba haka bane hakika ta kunshi sunayen Shahidai 72 na Karbala kuma an yi sallama a gare su, kuma mutane 17 cikin sun kasance daga Banu Hashim sauran 55 daga Kabilu daban-daban. [22] tare da haka wasu ba’arin Kofin Littafin Al-Mazar ya tattaro sunayen mutane 74, [23] daga Shahidan Karbala tare da Sallama a gare su, a ba’arin kofin littafin Al-Ikbal ya ambaci sunayen Shahidai 81, [24]
Sukan kan Abin Da Ziyarar Ta Tattaro
Malam Muhsin Ranjibar cikin Kasida mai Taken (Fajuheshi Darbaraye Do Ziyarat Nahiye Mukaddasa Wa Ziyarat Rajabiyya) hakika wannan ziyara ta kunshi wasu kalmomi da aka danganta su ga Ma’sumai, danganta wadannan kalmomi ga Ma’asumi akwai alamomin tambaya a kai: Babu a kawo sunan Burairatu Bn Khudair cikin gayyar Shahidan Karbala ba, alhali yana cikinsu; Kawo sunan Kaisu Bn Mus’hir cikin jerin sunayen Shahidin Karbala, daidai lokacin ya rigaya ya yi shahada tun kafin Ranar Ashura; Sanya sunan Muslim Bn Ausaja matsayin farkon Shahidi a Karbala, daidai lokacin litattafan tarihi suka ba da rahoto kan cewa Burairatu Bn Khudair shi ne farkon shahidin Karbala. [25]
Bayanin kula
- ↑ Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419 AH, shafi na 485; Sayyed bin Tavus, Al-Iqbal, 1416 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 73.
- ↑ Duba Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419 AH, shafi na 485-496; Sayyid Ibn Tavus, Al-Iqbal, 1416 AH, Juzu'i na 3, shafi na 73-80.
- ↑ <a class="external text" href="https://fa.alkawthartv.ir/news/290323">«زیارت ناحیه مقدسه»</a>
- ↑ <a class="external text" href="https://fa.alkawthartv.ir/news/290323">«زیارت ناحیه مقدسه»</a>
- ↑ Dubi Tabasi, “ziyarat nahiye mukaddaseh”, shafi na 194.
- ↑ Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419 AH, shafi na 485; Sayyed bin Tavus, Al-Iqbal, 1416 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 73.
- ↑ Mohammadi Rishahri,Daneshnameh Imam Husaini (AS), juzu'i na 12, shafi na 271, qafa na 1.
- ↑ Duba Mamqani, Tanghih al-Maqal, Beta, Mujalladi na 1, shafi na 453.
- ↑ Mofid, Al-Ershad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 339.
- ↑ Kulaini, al-Kafi, 1407H, juzu'i na 1, shafi na 514.
- ↑ Mahdipur, Nebras al-Za'ir fi Ziyarat al-Hayer, 1419 AH, shafi na 134.
- ↑ Testri, Kamus Al-Rajal, Juzu'i na 9, shafi na 504; Ayiti, Barasi tarikh Ashura, 1383, shafi na 141.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 101, shafi na 274.
- ↑ Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419 Hijira, shafi na 485-496.
- ↑ Sayyed bin Tavus, Al-Iqbal, 1416 AH, juzu'i na 3, shafi na 73-80.
- ↑ Shams al-Din, Ansar al-Husain, 1429 AH, shafi na 207-209.
- ↑ Khoi, Majam Rijal al-Hadith, 1413 AH, juzu'i na 18, shafi na 220.
- ↑ Shams al-Din, Ansar al-Husayn, 1429H, shafi na 215.
- ↑ Dubi Tabasi, "Hajji zuwa Wuri Mai Tsarki", shafi na 195-197.
- ↑ Dubi Tabasi, "Ziayarat Nayihe Mukaddaseh", shafi na 196-197.
- ↑ Shams al-Din, Ansar al-Husain, 1429H, shafi na 216.
- ↑ Ayiti, Barasi tarijh Ashura, 1383, shafi na 141.
- ↑ Duba Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419 AH, shafi na 485-496.
- ↑ Duba Sayyid Ibn Tavus, Al-Iqbal, 1416H, Mujalladi na 3, shafi na 73-80.
- ↑ Ranjbar, “Bincike kan mahajjata biyu na yankin da hajjin Rajbiya” shafi na 61.
Nassoshi
- Ayiti, Mohammad Ibrahim, Bincike kan tarihin Ashura, da kokarin Mehdi Ansari, Qum, Imam Asr Publishing House (AJ), 2003.
- Ibn Mashhadi, Muhammad bin Jafar, Al-Mazar al-Kabir, Javad Qayyumi, Qum, Al-Nashar al-Islami Foundation, ya yi bincike, 1419H.
- Tastri, Mohammad Taqi, Qamoos al-Rajal, bincike na Cibiyar Al-Nashar al-Islami, Qum, al-Nashar al-Islami, 1428H.
- Khoei, Sayyid Abul Qasim, Majam Rizal al-Hadith, Kum, Al-Adab Press, 1413 AH/1372 AH.
- رنجبر، محسن، «پژوهشی درباره دو زیارت ناحیه و زیارت رجبیّه»، در مطالعات تاریخ اسلام، شماره ۲۶، پاییز ۱۳۹۴ش.
- «زیارت ناحیه مقدسه»، وبگاه الکوثر، تاریخ درج مطلب: ۵ آذر ۱۴۰۰ش، تاریخ بازدید: ۱۲ مهر ۱۴۰۲ش.
- Sayyed Ibn Tavus, Ali Ibn Musa, Al-Iqbal Balaamal Al-Hasan, Bincike na Javad Qayyumi, Qum, Makarantar Nazarin Musulunci, 1416 Hijira.
- Shams al-Din, Mohammad Mahdi, Ansar al-Hussein, bincike na Sami Ghariri, Qum, Dar al-Kitab al-Islami, 1429 AH/2008 AD.
- Tabasi, Najmuddin, "Ziyarat Nahiye Mukaddaseh", a cikin littafi mai lamba 20, Mayu 2006.
- Kilini, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, bincike na Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na 4, 1407H.
- Mamghani, Abdullah, Tanqih Al-Maqal Fi Alam al-Rajal, Najaf, Bita.
- Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, Beirut, Al-Wafa Institute, 1403 AH.
- Mohammadi Rishahri, Muhammad, Daneshnameh Imam Hossein (AS) a kan Alqur'ani, Hadisi da Tarihi, Qum, Wallafar Dar Al Hadith, 2008.
- Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-Arshad fi Mafarah Hajjullah Ali al-Abad, edita ta Mu'assasar Al-Bait, Qum, Sheikh Mufid Congress, 1413H.
- Mehdipour, Ali Akbar, Nebras al-Za'ir fi Ziyarat al-Ha'er, Qom, Risala Institute, 1429 AH.