Jump to content

Saddam Husaini

Daga wikishia
Saddam Husaini
Shugaban ƙasa kuma babban sakataren jam'iyyar ba'as Iraƙ
Haihuwa20 Mayu 1937 miladiyya
Rasuwa30 Disamba 2006, an kashe shi ta hanyar rataya ta hannun sojojin Amurka
AddiniMuslunci, Ahlus-Sunna
MuƙamiBabban sakataren jam'iyyar ba'as Iraƙ. shugaban jamhuriyar Iraƙ. Babban kwamandan dukkanin rundunonin soja na Iraƙ
Farkon mulki1979 miladiyya
Ƙarshen mulki2006 miladiyya
Muhimman matakaiHana tarukan addini. korar Iraniyawa da suke zaune a Iraƙ. kisan kiyashi kan masu adawa da shi. yaƙin shekaru takwas kan Iran. kai farmaki kan ƙasar Kuwait. kisan kiyashin Dujaili. Intifazatul Sha'aban Iraƙ
KafinHassan Albakar


Saddam Husaini 1936-2006 miladiyya, shugaban ƙasar Iraƙi a tsakanin shekaru 1979-2003 miladiyya. Har ila yau, ya kasance memba a cikin jam'iyyar ba'as Iraƙ. A shekarar 1968 miladiyya bayan juyin mulki da jam'iyyar ba'as ta yi ya zama mataimakin shugaban ƙasa sannan a shekarar 1979 ya zama shugaban ƙasa.

Saddam Husaini ya kasance mutum mai ra'ayin kishin ƙabilar Larabawa, ya kasance yana matuƙar muhimmantar da kishin ƙabilarsa, yana da ra'ayin cewa wajibi ne kishin ƙabila ya zama yana sama da kishin addini domin hakan ya zama shimfiɗa da share fage ga juyin mulki a nan gaba, lokacin mulkinsa ya sanya takura da matsin lamba kan makokin Shi'a da tattakin arba'in ta yadda ta kai ga ya hana gudanar da waɗannan munasabobi. Har ila yau, ya yi bakin ƙoƙarinsa cikin raunana ƙungiyoyin addini da hauzozin ilimi. Sayyid Muhsin Hakim yana ganin membobin jam'iyyar ba'as daga jumlarsu hadda Saddam Husaini a matsayin mushrikai.

Saddam Husaini ya kashe dubunnan masu adawa da shi, ya kuma kasance yana ɗaukar tsauraran matakai da tarwatsa duk wani bore da nuna rashin aminta da salon mulkinSa da ya faru a lokacin shugabancinSa. A lokacin yaƙin Iran da Iraƙ ya yi amfani da bamabamai masu guba kan al'ummar Iran lamarin da ya kai ga hallaka dubban fararen hula wasu kuma suka ji munanan raunuka, majiyar jaridar NewYork Times ta siffanta Saddam Husaini cikin mutane mafi zalunci da rashin tausayi a wannan ƙarni.

Shekarar 1980 miladiyya ne ya ƙaddamar da kallafaffen yaƙi kan Iran, wannan yaƙi ya ja lokaci har zuwa shekaru takwas, kusan mutane dubu 400 suka rasa rayukansu daga ɓangarori biyu, tare da asarar ɗaruruwan bilyoyin daloli daga ɓangarori biyu. A watan Yuli 1990 ne Saddam Husaini ya ƙaddamar da farmaki kan ƙasar Kuwait, bayan watanni da ƙaddamar da wannan hari, sojojin Amurka da ƙawayenta suka kai hari kan sojojin Saddam Husaini tare da tilasta musu janyewa daga Kuwait.

A ranar 20 Maris 2003 miladiyya, Amurka ta ƙaddamar da hare-hare kan ƙasar Iraƙ, a shekarar 2004 miladiyya ne sojojin Amurka suka kama Saddam Husaini, sannan a shekarar 2006 ne aka zartar da hukuncin rataya kansa bisa samunsa da aikata lefin kisan kiyashi kan mutanen garin Dujaili.

Tarihin Rayuwa

An haifi Saddam Husaini a ranar 28 Afrilu 1937 miladiyya[1] a garin Al-auja da yake ƙarƙashin jihar Tikrit.[2] A lokacin ƙuruciyarsa ya kasance makiyayi da yake yawon kiwo tare da mijin babarsa.[3] A wani yanki na rayuwarsa ya kasance tare da babarsa da mijinta. Bayan nan sai ya koma garin Bagdad wurin kawunsa Khairullah Tulfa.[4] Ya shiga jarrabawar shiga jami'ar soja, sai dai kuma bai samu nasarar shi ga wannan jami'a sabo da bai samu maki mai kyau ba.[5]

Iyali

A shekarar 1963 Saddam Husaini Ya Auri Sajida ɗiyar kawunsa, ya samu ƴaƴa biyu maza da ake kiransu da Udai da Ƙusai, da ƴaƴa mata uku.[6]] Husaini Kamil da ɗan uwansa Saddam Kamil sun kasance surukan Saddam Husaini waɗanda a shekarar 1996 bayan wani saɓani da suka yi da dangin Saddam sai suka gudu ƙasar Jodan, a kan hanyarsu ta dawo Iraƙi ne aka kashe su. An hallaka Udai da Ƙusai bayan Amurka ta shiga Iraƙi ta karɓe iko, sannan sauran ƴaƴa mata uku na Saddam sun yi gudun hijira tare da mahaifiyarsu zuwa Jodan[7] Har ila yau, Saddam Husaini ya auri Samira Shah Bandar, kuma ta haifa masa ɗa guda ɗaya da ake kira da suna Ali.[8]

Saddam Da Jam'iyyar Ba'as

Saddam Husaini a lokacin samartakarsa ya shiga jam'iyyar ba'as. a garin Al-auja da yake ƙarƙashin jihar Tikrit.[9] A ranar 7 Afrilu 1947 miladiyya, aka kafa Jam'iyyar ba'as a Siriya ta hannun Mishal Aflaƙ mutumin Siriya[Tsokaci 1] da Salahud-dini Biɗar, an kafa wannan jam'iya kan aƙidar kishin Larabawa, wannan take ya ja hankulan matasa a ƙasashen Larabawa zuwa shiga wannan jam'iyya.[10]

Jam'iyyar ba'as ta yanke shawarar kashe Abdul-Karim ƙasim firaministan Iraƙi a ranar 7 Oktoba 1959, kuma cikin da aka zaɓa waɗanda za su zarta da wannan kisa har da Saddam Husaini, wannan kisan bai samu nasara ba, Saddam Husaini ya ji rauni a yunƙurinsu na kisan gilla kan Abdul-Karim Ƙasim wanda ba su yi nasara ba, sai ya gudu Siriya daga nan ya ƙara guduwa ƙasar Misra. Kotun Iraƙi ta yanke hukuncin kisa kan Saddam ba tare da halartarsa a gaban kotun.[11] A ƙarshe dai shekarar 1963 miladiyya, Saddam ya dawo Iraƙi.[12] A shekarar 1964 miladiyya an jefa Saddam gidan kurkuku sakamakon samunsa da hannun cikin yunƙurin juyin mulki da kifar da gwamnatin Abdus-Salam Arif da ba su yi nasara ba, sai dai kuma a shekarar 1966 miladiyya ya samu nasarar tserewa daga kurkuku, ya koma yana rayuwa a ɓoye.[13]

Saddam Husaini a lokacin ƙuruciya

A shekarar 1968 miladiyya, jam'iyyar ba'as ƙarƙashin jagorancin Ahmad Hassan Albakar ta samu nasarar juyin mulki tare da kifar da gwamnati mai ci a lokacin.[14] Daga shekarar 1968 ne aka naɗa Saddam Husaini matsayin mataimakin shugaban ƙasa.[15] A shekarar 1979 miladiyya Ahmad Hassan Albakar ya yi murabus daga muƙamin shugaban ƙasar Iraƙi sakamakon tilasta shi da aka yi kan yin haka, Saddam Husaini ya karɓe shugabancin ƙasar da kwamandancin dukkanin rundunonin soja gaba ɗaya, da kuma muƙamin babban sakataren jam'iyyar ba'as.[16] Mayar da fetur ɗin Iraƙi mallakar al'ummar ƙasar ya faru a lokacin shugabancin Ahmad Hassan Albakar da mataimakinsa Saddam Husaini.[17]

Rawar Da Addini Da ƙabila Ya Taka

Jam'iyyar ba'as da kuma Saddam Husaini sun zaɓi taken siyasa guda uku a matsayin tushe da ginshiƙan manufofinsu: haɗin kai, ƴanci, da gurguzu (Tsarin raba arziƙin ƙasa bai ɗaya tsakanin al'umma).[18] Ƙabilanci da kishin ƙasa sun taka muhimmiyar rawa cikin aƙidun membobin jam'iyyar ba'as, da wannan dalili ne masana suka yi imani da cewa shugabannin ƙasar Iraƙi ba su damu da muhimmantar da addini da mazhaba ba, kuma cikin samar da dokoki, haƙƙoƙi da shugabancin Iraƙi, addini da malaman addini ba su da wani tasiri ko taka rawa.[19]

Saddam cikin shigar Larabawa

Jam'iyyar gurguzu ta ba'as, kafin samun karɓe ikon shugabancia a Iraƙi, sun kasance suna yabon addini tare da girmama shi, amma bayan kafa gwamnati sai suka koma suna yaƙar addini.[20]

Wannan jam'iyyar tana la'akari da Muslunci matsayin wani motsi da yunƙuri na Larabawa wanda manufarsa shi ne sabunta da kammala aƙidar Larabci.[21] Saddam Husaini ya kasance kan tafarkin Ahlus-sunna.,[22] Duk da cewa ya kasance yana ƙoƙarin nuna cewa shi mutum ne mai riƙo da addini.[23] Amma kuma tare da hakan yana da ra'ayin cewa ya kamata a faɗaɗa kallo sama da addini domin haɓɓaƙa aƙidar juyi.[24]Saddam ya yi imani da cewa matuƙar ana son daidaita tafiyar kishin ƙasa to bai kamata a yaɗa manufofin ko mazhaba ta addini ba.[25]

Saddam ya yi imani da cewa falsafar jam'iyyar ba'as, falsafa ce ta rayuwar gidan duniya ba wai addini ba. Amma kuma tare da haka yana da ra'ayin cewa bai kamata jam'iyya ta zama mai korar aƙidun addini ba.[26]

Bayan rasuwar Sayyid Muhsin Hakim shugaban hauzar ilimi ta Najaf, Saddam ya yi iya yinsa cikin raunana wannan hauza da rusa ta.[27]Imam Khomaini ya yi imani Saddam Husaini ya kasance mutum da ya yi ƙoƙarin rusa addini da hauzar karatun addini ta Najaf.[28]

Sayyid Mushin Hakim babban marja'in taƙlidi na Shi'a a zamaninsa, ya bayyana cewa shugabannin jam'iyyar ba'as da Saddam mutane ne Mushrikai.[29] Imam Khomaini shi ma ya yi ishara da wannan fatawa.[30]

Hana Tarurrukan Addini

Sayyid Muhammad Baƙir Sadar:
Wannan shugaba (Saddam) da ke mulki da karfin tsiya, yana hana jama'a ‘yancinsu na farko—na gudanar da tarukan addini—ba zai iya ci gaba da mulki ba. Ba za ka iya mulki da karfi da tsorotarwa ba har abada ba

[31]

Bayan ɗan wani lokaci kaɗan da karɓe iko da jam'iyyar ba'as ta yi a Iraƙi, tarurrukan addini na Shi'a sun fuskanci matsaloli da takura wasu lokuta har da rikici tsakaninsu da masu mulki.[32] Gwamnatin Iraƙi a shekarar 1977 a lokacin mulkin Ahmad Hassan Albakar da mataimakinsa Saddam Husaini, ta fitar da wasu umarnai da suka ci gaba da aiki har zuwa ƙarshen mulkin jam'iyyar ba'as, waɗannan umarnai su ne iyakance ba'arin ayyukan tunawa da shahadar Imam Husaini (A.S) wani lokaci hanawa kacokan, kuma duk wani taron maukibi ko tattakin arba'in zuwa Karbala to an shelanta hana yinsa. Haka nan an iyakance shirya majalisin makoki Imam Husaini (A.S) kaɗai za a bari ne a yi kan wasu sharuɗɗa.[33]

Rashin lamincewar hukuma da shirya waɗannan tarurruka daidai lokacin da su kuma ƴanshi'a ana su ɓangare suka kafe kan shirya tarurrukansu kamar yadda suka saba, wanda hakan ya haifar da rikici da bore, mafi muhimmancin bore da ya faru a wancan lokaci shi ne Intifazatul Safar Shekara 1977 miladiyya.[34]

Korar Iraniyawa

Gwamnatin ba'as ƙarƙashin shugabancin Hassan Albakar da mataimakinsa Saddam Husaini cikin yunƙurinsu na ƙarfafa siyasar kishin Larabci, tare da rattaba hannu kan wasu dokoki, sun iyakance hallara da tasirin Iraniyawa a cikin Iraƙi.[35] A lokacin hunturu na shekarar 1971 miladiyya, an kori ɗaruruwan Iraniyawa a suke zaune a Iraƙi, jigon mutanen da aka kora sun kasance daga ɗalibai da malaman addini na Iran, a shekarar 1975 an sake korar wani sashe daga Iraniyawa.[36]

Har ila yau, a shekarar 1980 miladiyya nan ma an ci gaba da korar iraƙawa wanda asalinsu yake komawa Iran.[37] Galibinsu ƴan kasuwa ne masu kuɗi da tarin dukiyam gwamnatin Iraƙi bayan korarsu ta kwace dukiyarsu, ta tattara kusan fiye da dala biliyan uku daga kadarori daga dukiyarsu da ta kwace.[38]

Ba'arin masana masu zurfafa bincike a wannan zamani, sun bayyana cewa irin wannan mu'amala da hukumar Iraƙi ta yi wa Iraniyawa ba komai ba ne sai zalunci kan marasa rinjaye waɗanda suke zaune a Iraƙi tsawom shekaru, har wasu nasaba masu yawa daga cikinsu sun taka rawa da ba da gudummawa cikin gina ƙasar Iraƙi.[39]

Saddam Husaini Da Falasɗinu

Saddam cikin jaddada aƙidar jam'iyyarsu kan kishin Larabawa, ya dinga yawaita bijiro da batun ƴancin ƙasar Falasɗinu.[40] Ya yi imani cewa Falasɗinu ƙasa ce ta Larabawa, kuma alƙibla ce ta farko ga Musulmi wuri na uku cikin jerin wurare masu tsarki a imanin Musulmi.u.[41] Saddam ya kasance yana da'awar cewa wane ne zai iya tabbatar da imaninsa da kuma cewa sallarsa tana karɓuwa a daidai lokacin da har zuwa yanzu birnin ƙudus yana nan a ƙarƙashin ikon Sahayoniyya.[42] A lokacin ya yake yaƙar Kuwait da Amurka da ƙawayenta suka tilasta masa janyewa. Saddam ya harba gomomin makamai masu linzami kan Isra'ila, wanda haka ya samar masa farin jini da yabo daga wasu mutane a duniya da ma cikin Larabawa.[43] Adadin masana sun tafi kan cewa manufar Saddam kan wannan aiki, shi ne amfana da ƙiyayya da ƙyamatar da Larabawa suke yi wa Isra'ila domin samawa kansa da hukumarsa halasci a wurin Larabawa ta yadda daulolin Larabawa za su mara masa baya a yaƙin da yake da Amurka.[44] Saddam Husaini ya yi alƙawari cewa sai ya ƙone rabin Isra'ila da wuta, Na'am wasu sun zarge shi a daidai lokacin da ya ɗauki alƙawari ƙone rabin Isra'ila da wuta, sai ya juya alƙawarin kan yankin Arbil na ƙurdawa ya ƙone su da wuta, har ila yau, ya yi alƙawarin ganin bayan Isra'ila amma sai ya ɓige da ƙoƙarin haɗiye Kuwait.[45] Haka nan Saddam Husaini ya kai hari kan jerin gwanon bayan Falasɗinu na ranar ƙudus ta duniya, tare da kashe mutum 80.[46]

Bore Da Kashe-Kashe

A lokacin mulkin Saddam Husaini shugaban ƙasar Iraƙi, Iraƙi ta shaida kisan kiyashi mai yawan gaske. Mujallar New York Times, ta bayyana Saddam matsayin mutum mafi zalunci da rashin tausayi a ƙarni na 20 miladiyya.[47] Saddam ya sa an kama Sayyid Muhammad Baƙir Sadar da ƴar uwarSa Bintul Huda ya kuma kashe su.[48] Haka nan ya dinga kashe ɗaiɗaikun membobin Hizbud Da'awa.[49]

Kisan Kiyashi Da Bom Mai Ɗauke Da Sinadarai Masu Guba

Harin makami mai guba kan mutanen garin Halabjce

Hukumar Iraƙi ta yi amfani da bom mai ɗauke da sinadarai masu guba kan Iraƙawa da Iraniyawa, soja da fararen hula. Sojojin Iraƙi sun yi amfani gas mai guba akan fararen hula daga jumlarsu akwai mutanen garin Halabjce na Iraƙi da kan ƙauyen Zarde na Iran. Haka nan sun yi amfani da iskar guba mai sa rauni da ciwo a kan mutanen garin Mariwan, Sardashte da wasu adadin ƙauyukan Iran.[50]

Gwamnatin ƴan ba'as a cikin rikici na soja ta yi amfani da bom mai guba, ta kai hari kan yankunan da aka yi ofireshin ɗin badar, khaibar, alfajar 8 da yanki Fawe .[51] Gwamnatin ba'as ta Iraƙi ta himmatu da fara kai hare-hare na bom mai guba daga shekarar 1983 lokacin kallafaffen yaƙi da ta ƙaddamar kan Iran.[52] Sun ci gaba da kai irin waɗannan hare-hare har zuwa ƙarsheh yaƙin a shekarar 1988 miladiyya.[53] Kusan mutum dubu 100 ne suka rasa rayukansu da masu raunuka daga soja da fararen hula sakamakon wannan hare-hare.[54]

Har ila yau, gwamnatin Iraƙi daɗi kan umarni amfani da makamai masu guba da ta bayar umarni ayi amfani da makamai masu guba kan garuruwa da ƙauyuka da suke kusa da iyakarta da ƙasar Iran, tare da haka ta ƙirƙiri wani motsi na tasirin tunani (Psychological operation) don ƙara matsin lamba kan shuwagabannin Iran, da kuma barazanar ruwan bamabamai na makamai rokoki masu guba kan garuruwa da jihohi da manyan cibiyoyin gwamnatin Iran; a ra'ayin masana masu bincike wannan barazana ba za a iya nesanta zartar da ita, kuma ta yi tasiri da taimakawa cikin karɓar ƙuduri mai lamba 598.[55]

Intifazatul Safar (Boren Safar)

Jam'iyyar ba'as ta iyakance shirya tarurrukan addini, haka zalika ta hana duk wani shirya taron maukibi da tattakin arba'in zuwa Karbala[56] Tare da haka mutanen garin Najaf 15 ga watan Safar da ya kasance a shekarar 1977 miladiyya sun shirya gudanar da tattakin arba'in.[57] Ayari da yake tare da mutane dubu 30 sun taso daga Najaf zuwa Karbala. Tunda farko wannan tattaki na su ya fuskanci hari daga hukuma, wasu adadin mutane sun yi shahada, daga ƙarshe dai a hanyar Najaf zuwa Karbala, sojojin Saddam sun kai farmaki, tare da kame dubban mutane.[58] da kuma kashe wasu adadi, cikin waɗanda aka kama, hakan nan an yankewa wasu hukuncin kisa, wasu kuma ɗauri na har abada a kurkuku.[59]] Sayyid Muhammad Baƙir Sadar da Sayyid Muhammad Baƙir Hakim sun taka muhimmiyar rawa a lokacin wannan bore na infazatul Sha'aban.[60]

Imam Khomaini shi ma ya goyi bayan bore mutanen Iraƙi.[61]

Kisan Kiyashin Dujaili

Dujaili yana daga cikin garuruwan Iraƙi da Shi'a suke da rinjaye.[62] wanda a watan Ramadan shekarar 1402 hijira ƙamari, Saddam ya je garin, shigarSa ke da wuya sai wasu adadi daga membobin jam'iyyar Hizbud Da'awa suka yi yunƙurin hallaka shi, sai dai kuma wannan yunƙuri bai yi nasara ba, bayan nan fa sai sojojin ba'as tare da taimakon sojojin sama masu yawan gaske suka dinga kai farmaki kan wannan gari, inda suka kame ɗaruruwan mutane daga maza da mata manya da yara, da kuma azabtar da wasu da kashe wani adadi mai yawan gaske daga cikinsu.[63] cikin wannan kisan kiyashi an kashe mutane 148[64] Wasu ba'ari daga cikinsu mata ne da ƙananan yara.[65] Sannan aka lalata fiye hekta dubu ɗari da ake noma.[66]

A shekarar 2006 miladiyya ne kotu ta sami Saddam Husaini da aikata lefin kisan kiyashi a garin Dujaili, da wannan dalili kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.[67]

Intifaza Sha'abaniyya

Bayan shan kashin gwamnatin Saddam a yaƙin Kuwait, mutanen Iraƙi sun yi bore wanda ake kira da sunan boren Sha'aban a shekarar 1411 wanda ya yi daidai da 1991 miladiyya.[68]

Yaƙin shekaru takwas tsakanin Iraƙi da Iran, da kuma mummunan shank aye a yaƙinsa da Kuwait, munanar yanayin tattalinn arziƙi da lalacewar da yawa-yawan manyan gine-gine na tattalin arziƙi da kasuwanni ya haifar boren mutane kan gwamnatin Saddam a faɗin ƙasar Iraƙi, wannan bore ya fara ne daga garin Basara, ya ci gaba da cinye garuruwa kamar misalin wutar daji.[69] Jihohi goma sha huɗu ne daga cikin jihohi sha takwas na ƙasar Iraƙi suka faɗa hannu masu bore.[70] Wannan yunƙuri ko a ce bore ya ci gaba har tsawon kwanaki goma sha biyar.[71] Sojojin Iraƙi cikin yunƙurinsu na tarwatsa masu bore sun fara da kisan kiyashi ta yadda suka kashe dubunnan mutane, sannan kusan mutane miliyan biyu ne suka rasa mahallansu.[72] Gine-ginen Haramin Imam Ali (A.S) da Haramin Imam Husaini (A.S) sun taɓu, lamarin ta kai ga rufe su na tsawon watanni shida.[73] Sojojin ba'as sun rusa gomomin makarantun addini a Najaf da Karbala.[74]

Yaƙoƙi

Iraƙi a zamanin Saddam bisa umarninsa ta ƙaddamar wasu yaƙoƙi:

Yaƙin Iran Da Iraƙi

A ranar 22 Satumba 1980 miladiyya, sojojin Iraƙi bisa umarnin Saddam Husaini suka fara ƙaddamar da hare-hare kan ƙasar Iran.[75] Cikin Wannan yaƙi Saddam Husaini ya yi yunƙurin cimma wasu buruka da manufofi na sa kamar haka:

  • Gwamnatin Iraƙi ta nemi soke yarjejeniyar Aljeriya da haɗe kogin Albandurud da yankinta. Wasu sun yi la'akari da salon ayyukan sojan Iraƙi bayan karɓe iko a garin Khorramshahar da wasu yankunan jihar Khuzestan matsayin alama da take nuni cewa suna da shiryayyen Shirin haɗe Khuzestan da Iraƙi.[76]

da kuma karkasa ƙasar Iran zuwa wasu ƙasashe.[77]

  • Saddam Husaini ya shelanta cewa dole ne Iran ta haƙura da jazirorinta guda huku watau: "Tanbe kucek" da"Abu Musa" da Tanbe Buzurge".[78]

Wannan yaƙi ya ci gaba har tsawon kwanaki 2888, ana la'akari da shi ɗaya daga cikin mafi girman yaƙi da ya faru a ƙarni na ashirin miladiyya..[79] Wannan yaƙi ya haifar da asara mai nauyin gaske kan dukkan ɓangarori biyu, rayuwa ta yi masifar tsananta ga mutanen ƙasashen guda biyu, ya haifar da rushewar cibiyoyin gina ƙasa da masana'antu, da lalacewa yankuna da mutane ke zaune daga birane da ƙauyuka na kan iyakokin ƙasashen biyu, da kuma taɓarɓarewar ma'adanai da dukiyar ƙasashen biyu da kayan gado na tarihi da al'adu.[80] Ƙashasen Iran da Iraƙi sun kashe dala biliyan ɗari biyu cikin wannan yaƙi, sannan kuma ya jawo musu asarar kusan dala biliyan 1500, Iran tana shahidai dubu 188 da masu rauni dubu 519 da fursunoni dubu 42.[81]] Haka nan ita ma Iraƙi ana ɓangaren an kashe mata kusan mutane dubu 200, sannan dubu 600 sun samu raunuka, da kuma fursunoni dubu 60.[82]

Saddam bayan kama shi

Yaƙin Iraƙ Da Kuwait

Sojojin Iraƙi a ranar 2 Agusta 1990 miladiyya, sun tsallaka kan iyakarsu da Kuwait sun kutsa cikin ƙasar Kuwait tare da mamaye wannan yanki har tsawo awa uku.[83] Bayan wani ɗan lokaci sai gwamnatin Iraƙi ta shelanta cewa ƙasar Kuwait ta zama jiha cikin jihohin ƙasarta.[84] Dangane wannan mamaya, an ambaci adadi wasu dalilai misalin rigimar kan iyaka da take tsakanin Iraƙi da Kuwai, Faɗuwar Iraƙi a ɓangaren siyasa da soja da dabarun yaƙi a cikin shekaru takwas da ta yi tana yaƙi da Iran, basussuka masu nauyi da taci sakamakon yaƙin da ta yi da Iran, suna daga cikin dalilin da ya sa ta kwaɗayin mamaye Kuwait.[85]

A ranar 17 Janairu 1991 miladiyya ne sojojin ƙawance ƙarƙashin jagoranci Amurka, suka fara ƙaddamar da hare-hare kan sojojin Iraƙi domin korar su daga Kuwait, wannan hare-hare sun ƙunshi faɗaɗa ruwan bamabamai da makamai masu linzami..[86] Bayan kwanaki 38 da ƙaddamar da wannan hari ne tare da lalata cibiyoyin soja da na tattalin arziƙi na Iraƙi , daga ƙarshe sai suka fara ƙaddamar da hari da sojojin ƙasa, cikin kwanaki huɗu kacal suka samu nasara kan sojojin Iraƙi tare da tilasta musu ficewa daga ƙasar Kuwait.[87] Sojojin Iraƙi a lokacin wannan yaƙi sun harba rokoki guda 39 har karo goma sha bakwai kan Isra'ila.[88]

Harin Amurka Kan Iraƙ

Bayan harin 11 Satumba ne da ya faru a birnin New York, Amurkawa tare da zargin hannun Saddam cikin wannan hari, da kuma zargin alaƙa ta kusa-kusa tsakanin alƙa'ida da gwamnatin ba'as da zargin cewa Iraƙi tana da makaman kisan ƙare dangi, ta gamsar da wasu kan shirinta na fara ƙaddamar da hare-hare kan Iraƙi.[89] Daga ƙarshe a shekarar 2003 Amurka da ƙawayenta.[90] sun ƙaddamar da hare-hare kan Iraƙi tare da kwace iko a ƙasar.[91]

Kama Saddam Da Zartar Masa Da Hukuncin Kisa

Zartar da hukunci rataya kan Saddam

A watan Disamba 2003 miladiyya, sojojin Amurka suka sanar da kama Saddam Husaini a cikin wata gona kusa da garin Tikrit.[92]

A shekarar 2005 miladiyya ne aka fara zaman kotu, bayan dogon zama da aka yi ta yi kan tuhumar Saddam Husaini kan kisan kiyashi da ya aikata a garin Dujaili.[93] da ya halakar da mutane 148, daga ƙarshe dai alƙalin wannan kotu ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.[94] A safiyar ranar Idin babbar sallah ne wanda ya yi daidai da 30 Disamba 2006 miladiyya.Khizr, I'idam Ra'is Bidaya Wa Nihaya Saddam Hussein, 2007, shafi. 317. a wani sansani da yake garin Kazimaini aka zartar masa da hukuncin rataya, wanda a wannan wuri ne dai shekarun baya Saddam ya zartar da hukuncin kisa kan Sayid Muhammad Baƙir Sadar[95]

Bayanin kula

  1. Al-Marsoumi, Dirasat Fi Fikri Al-Qa'id Saddam Hussein, 2000, shafi. 14.
  2. Willy, Nahzat Islami Iraq, 1994, shafi. 69.
  3. Khizr, I'idame Ra'isi Bidaya Wa Nihaya Saddam Hussein, 2007, shafi na 70.
  4. Willy, Nahzat Islami Iraq, 1994, shafi. 69.
  5. Tabraian, Intifada Sha'baniyah , 1391, shafi. 76.
  6. Tabraian, Intifada Sha'baniyah , 1391, shafi. 78.
  7. صدام از تولد تا چوبه دار، shafin yanar gizo na jaridar Iran.
  8. «حیاة صدام حسین فی سطور»
  9. Willy, Nahzat Islami Iraq, 1994, shafi. 70.
  10. صدام از تولد تا چوبه دار، Shafin Jaridar Iran.
  11. Mar, Tarikh Nowin Iraq, 1380, shafi 329
  12. صدام از تولد تا چوبه دار،Gidan yanar gizo na jaridar Iran.
  13. صدام از تولد تا چوبه دار،Gidan yanar gizo na jaridar Iran.
  14. Willy, Nahzat Shi'ayan Iraq, 1994, shafi. 70.
  15. صدام از تولد تا چوبه دار،Shafin Jaridar Iran.
  16. Tabraian, Intifada Sha'baniyah, 1391, shafi. 76
  17. «حیاة صدام حسین فی سطور»
  18. Al-Abasi, Safhat Sauda'i Min Ba'as Al-Iraq, 1361, shafi. 49.
  19. Afshun, "Din Wa Amaliyate Dar Sakhtare Huquqi -Kamimiyati Iraki," shafi. 48
  20. Foladzadeh, Idiyoloji Hizbe Sosiyalisti Ba'as Iraqi, 1410 AH, shafi. 26.
  21. Ardestan, "Saddam Wa Hezbe Baath; Mahiyat Wakneshehi", 2011, shafi. 40.
  22. «حقایقی ناگفته از دیکتاتور سابق عراق»
  23. Ardestan, "Saddam Wa Hezbe Baath; Mahiyat Wakneshehi", 2011, shafi. 40.
  24. Foladzadeh, Idiyoloji Hizbe Sosiyalisti Ba'as Iraqi, 1410 AH, shafi. 29.
  25. Foladzadeh, Idiyoloji Hizbe Sosiyalisti Ba'as Iraqi, 1410 AH, shafi. 30.
  26. Ashour, Al-Din Wa Al-turathul Al-fikri Arra'is Alqa'id Saddam Hussein, 1988, shafi. 186.
  27. الطالقانی، «دراسة حول انتفاضة صفر المجیدة عام ۱۹۷۷ میلادیة»،Barasa News
  28. Markaze Tanzim Wa Nashre Asare Imam Khumaini, Sahifeh Imam, 1999, Vol. 12, ku. 233
  29. Markaze Tanzim Wa Nashre Asare Imam Khumaini, Sahifeh Imam, 1999, Vol. 12, ku. 244
  30. Markaze Tanzim Wa Nashre Asare Imam Khumaini, Sahifeh Imam, 1999, Vol. 12, ku. 244
  31. Kazem, Arqame Wa Ara Haula Nizamil Ba'as Fil Irak, 1982, shafi. 266.
  32. Al-Momin, Sanawat al-Jamar, 2004, shafi. 164.
  33. Kazem, Arqame Wa Ara Haula Nizamil Ba'as Fil Irak, 1982, shafi. 158.
  34. Mazaheri, Farhange Sauge Shi'i, 2016, shafi 101-102.
  35. Pahlevan, "Taharrukate Jam'iyati Dar mantike", shafi, 147.
  36. Jafarian, "Tashayyu Dar Irak wa Munasabat Ba Iran,"shafi. 203.
  37. Al-Momin, Sanawat al-Jamar, 2004, shafi. 272.
  38. Al-Momin, Sanawat al-Jamar, 2004, shafi. 278.
  39. Jafarian, "Tashayyu Dar Irak wa Munasabat Ba Iran,"shafi. 204.
  40. Al-Marsoumi, Dirasat Fi Fikril Al-qa'id Saddam Hussein, 2000, shafi. 190.
  41. Al-Marsoumi, Dirasat Fi Fikril Al-qa'id Saddam Hussein, 2000, shafi. 192.
  42. Al-Marsoumi, Dirasat Fi Fikril Al-qa'id Saddam Hussein, 2000, shafi. 192.
  43. Al-Ani, "30 Aman .. Yaqsifu Isra'ila Raddan Ala Asifatil Sahra".
  44. Al-Ani, "30 Aman .. Yaqsifu Isra'ila Raddan Ala Asifatil Sahra".
  45. Khizr, I'idam Ra'is Bidaya Wa Nihaya Saddam Hussein, 2007, shafi na 60.
  46. “Binciken wata iƙirari na tarihi: Shin Saddam Hussein ya kasance mai adawa da Isra’ila?
  47. MacFARQUHAR, Saddam Hussein.
  48. Nomani, Ayatullah Uzma Shahid Sayyid Muhammad Baqir Sadr, 2009, shafi. 560.
  49. Willy, Nahzet Islami Shi'ayan Irak, 1994, shafi. 88.
  50. «خسارات و تلفات ۸ سال جنگ (بخش اول: عراق)»، shafin yanar gizo na Difa'i Muqaddas.
  51. یکتا، «کاربرد سلاحهای شیمیایی در جنگ ایران و عراق»، Portal Jami'i Ulum Insani.
  52. عملیات خیبر؛ آغاز استفاده تاکتیکی رژیم عراق از جنگ‌افزارهای شیمیایی،،shafin yanar gizo na Difa'i Muqaddas
  53. آخرین جنایت شیمیایی عراق در مناطق غیرنظامی ایران، shafin yanar gizo na Difa'i Muqaddas
  54. «خسارات و تلفات ۸ سال جنگ (بخش اول: عراق)»، ، shafin yanar gizo na Difa'i Muqaddas.
  55. «حمله شیمیایی عراق به ایران و مهمترین قطعنامه سازمان ملل»،Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA.
  56. Al-Momin, Sanawat al-Jamar, 2004, shafi na 165.
  57. Asadi, Mujaz Tarikh Al-iraq Assiyasi Al-hadis, 2001, shafi. 101.
  58. Willy, Nahzat Islami Shi'ayan Irak, 1994, shafi. 81.
  59. Asadi, Mujaz Tarikh Al-Iraq Assiyasi Al-Hadis, 2001, shafi. 103.
  60. Al-Momin, Sanawat al-Jamar, 2004, shafi. 169.
  61. Al-Momin, Sanawat al-Jamar, 2004, shafi. 170.
  62. «صدام یتحدث عن قضیة الدجیل التی أعدم بسببها».
  63. «مذبحة الدجیل»،Shafin yanar gizo na Tarasiyat.
  64. Al-Asadi, Mojar Tarikh al-Iraq al-Siyasi al-Hadith, 2001, shafi. 173.
  65. «صدام یتحدث عن قضیة الدجیل التی أعدم بسببها»، Shafin yanar gizo na Magras
  66. «مذبحة الدجیل»،Shafin yanar gizo na Tarasiyat.
  67. Khizr, KI'idame Ra'is Bidaya Wa Nihaya Saddam Hussein, 2007, shafi na 317
  68. Tabraian, Intifada Sha'baniyah , 1391, shafi. 223.
  69. Al-Asadi, Mujaz Tarikh Al-iraq Assiyasi al-Hadith, 2001, shafi na 200.
  70. Tabraian, Intifada Sha'baniyah , 1391, shafi. 230.
  71. Al-Tameh, Al-Intifada Shabaniyaha Fi Karbala, 1433H, shafi na. 17.
  72. «ماجرای انتفاضه شعبانیه چیست؟», Shafin labarai na gobe.
  73. Al-Tameh, Al-Intifada Shabaniyaha Fi Karbala, 1433H, shafi na. 47.
  74. Al-Tameh, Al-Intifada Shabaniyaha Fi Karbala, 1433H, shafi na. 149-156.
  75. «۸ «سال جنگ تحمیلی علیه ایران چگونه آغاز شد؟»، Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
  76. «آمده بودند بمانند...»، Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA.
  77. Jafari, Atlas Nabardehaye Mundigar, 2010, shafi. 14
  78. «حیاة صدام حسین فی سطور»
  79. «خسارات و تلفات ۸ سال جنگ (بخش دوم: ایران)»، Shafin yanar gizo na Difa'i Muqaddas.
  80. «خسارات و تلفات ۸ سال جنگ (بخش دوم: ایران)»،Shafin yanar gizo na Difa'i Muqaddas
  81. «خسارات و تلفات ۸ سال جنگ (بخش دوم: ایران)»، Shafin yanar gizo na Difa'i Muqaddas..
  82. «خسارات و تلفات ۸ سال جنگ (بخش اول: عراق)»، Shafin yanar gizo na Difa'i Muqaddas<.
  83. Tabraian, Al-Intifada Sha'baniyah , 2012, shafi na 157.
  84. Tabraian, Al-Intifada Sha'baniyah , 2012, shafi na 160-161
  85. Karimi, "Jange Iraki Wa Kuwait", Juz. 11, shafi. 140.
  86. Tabraian, Al-Intifada Sha'baniyah , 2012, shafi na 183.
  87. Karimi, "Jange Iraki Wa Kuwait", Juz. 11, shafi. 140.
  88. Tabraian, Al-Intifada Sha'baniyah , 2012, shafi na 187.
  89. Amini,“Rasanehaye Wa Amaliyat Rawani, Nabardehaye Itilafe Bar Zidde Iraq(Maris 2003)”, shafi. 151.
  90. Haeri, Ruzeshumari Shamsi, 2007, shafi 894.
  91. «حیاة صدام حسین فی سطور»
  92. Khizr, I"idame Ra'is, Bidaya Wa Nihaya Saddam Hussein, 2007, shafi. 314;«تبدیل تاریخ از میلادی به شمسی»، Ba Hisabe.
  93. «حیاة صدام حسین فی سطور»
  94. Khizr, I"idame Ra'is, Bidaya Wa Nihaya Saddam Hussein, 2007, shafi. 317
  95. تقدسی، «گفت و گوی «ایران» با منیر حداد قاضی دادگاه صدام: ناگفته‌های اعدام دیكتاتور», Gidan Jaridar Iran.

Tsokaci

  1. Michel Aflaq (a Larabci: ميشيل عفلَق), an haife shi ranar 9 ga Janairu, 1910 a garin Damashqi, kuma ya rasu a ranar 23 ga Yuni, 1989 a Paris. Ya kasance masanin Falsafa, masanin zamantakewa, mai sharhi kan harkokin siyasa, da mai kishin Larabawa na Syria.

Nassoshi

Qom, Daftar Aql, bugu na biyu, 2007.

an.com/npview.asp?ID=1255733 «صدام از تولد تا چوبه‌دار»، سایت روزنامه ایران،‌ تاریخ درج مطلب: ۱۷ آبان۱۳۸۵ش، تاریخ بازدید: ۶ خرداد ۱۳۹۷ش.]