Maukibi

Daga wikishia
Maukibin Imam Rida (A.S), Hanyar Najaf zuwa Karbala, Amood 285.

Maukibi (Larabci:موكب)wani Tanti ne da ake kafa shi a ba’arin wasu wurare a lokutan bukukuwan Mazhabar Shi’a domin hidima ga Maziyarta cikin ba su abinci shayi da ruwa, duba lafiya, da dai sauransu, Wannan Isɗilahi ya yaɗu sosan gaske cikin Al’adun ƴan Shi’ar ƙasar Iraƙi, wannan Al’ada ta tsallaƙo ƙasar Iran cikin casa’iniyat na hijira shamsi, amma tun gabaninsa dama akwai wani abu mai kama da haka a ƙasar Iran. Kalmar Maukibi a Al’adun ƴan Shi’a Larabawa wata ishara ce da ake amfani ita zuwa ga wasu gungun masu Makoki, a ƙasar Iraƙi ana amfani da kalmomin misalin (Maukibul Aza’i, Maukibu Azadari) da kuma (Maukibu Kidmi, Maukibu Kadmati), a ƙasashen Fakistan da Indiya shirya Maukibi ya kasance cikin Al’adun ƴan Shi’arsu, galibin lokuta ƙungiyoyin Jin ƙai tare da ɗaiɗaikun mutane sune suke nɗaukar nauyin samar da kuɗaɗen da ake sarrafawa da amfani da su a Maukibi.

Sanin Mafhumi Da Kuma Takaitacen Tarihi

Maukibin Imam Rida (A.S) kan hanyar Tattaki daga Najaf zuwa Karbala Amudi Mai Lamba 285 Maukibi suna ne da ake amfani da shi kan Tantina da ake Hidima ga Maziyarta [1] wanda ake kafa su a wurare daban-daban [2] a lokutan bukukuwan Mazhabar Shi’a [3] ana yiwa Maziyarta Hidima kyauta, waɗannan Maukibobi sun kasance cikin Tantina da kuma Rumfuna ko kuma wasu gine-gine. [4]

Hemomin Maukibobi a Iraki

Tarihinsa

Kalmar Maukibi wata kalma ce a Al’adun ƴan Shi’a da take ishara zuwa ga Hai’a [5] ko wasu Gungun masu zaman makoki [6] ko Tattakin makoki, [7] [yadasht 1] cikin littafin Al-ɗaffi wanda aka rubuta shi tun kusan shekara 1374 h shamsi, bisa rahotan Hai’ar masu zaman makoki ana kakkafa Tantinan hidima a garuruwa daban-daban da suke geffan garin Karbala tun kafin kusantowar Tattakin Arba’in. [8] Kan asasin bayanan da suka zo a littafin Farhang Sauge Shi’i a da aka buga shi shekara ta 1395 h shamsi, ya kawo cewa a ƙasar Iraƙi ana kiran Tantina da sauran wuraren Hidima ga Masu Tattakin[9] ziyarar Arba’in da sunan Maukibi, 10 domin banbance masu zaman makoki da masu hidima ga masu makoki ana amfani da kalmar Maukib Aza ko Maukib Azadari, da kuma Maukib Kadmi ko Kadmati. [10] Anfara raya wannan Al’ada ne a ƙasar Iraƙi daga Gomomin Shekarun wannan ƙarni bayan nan kuma wanann al’ada ta tsallaka zuwa ƙasar Iran, [11] na’am tun kafin tsallakawarta dama can akwai wani abu mai kama da haka a ƙasar Iran da suke Kiransa da sunan (Istigahe Salawati) wurin Hidima na kyauta [yadasht 2] ko dai wani abu kwatankwacin Maukibi, [12] kalmomi biyu na Maukibi da istigahe salawati dukkaninsu ana amfani da su cikin harshen Farisanci. [13]

Hidima

Dukkanin hidimomin da ake yi a cikin Maukibobi sun kasance kyauta waɗanda suka tattaro daga bada abinci, wurin hutawa, [14] duba lafiya da bada magani da goge takalma, cikin kan hanoyin Tattakin Arba’in bayan abinci da ake bayarwa ana bada wuraren hutawa da kuma tausar jiki da ƙafafun Masu Tattaki da wanke musu tufafi. [15] Wasu ba’arin Maukibobi a lokutan faruwar bala’o’in ɗabi’a da ba a tsammaninsu misalin girgizar ƙasa ko ambaliyar ruwa, an tanadi kayayyakin buƙatuwa na larurra misalin kayan abinci, Tantina, Bargo da kuma raba ruwan sha, [16] kuɗaɗen da aka tanada domin sarrafa cikin wannan hali sun samu ne ta hanyar taimakon da mutane suke bayarwa, [17] wani lokacin kuma daga hannun Gwamnati ake samunsu. [18]

Lokacin Da Wuri

A ƙasar Iraƙi ake shirya Tattakin Tattakin Arba’in Maukibobi cikin bukukuwan Mazhabar Shi’a, daga cikinsu akwai Tattakin Arba’in [19] watan Muharram [20] Nisfu Sha’aban [21] zagayowar ranakun shahada da ranakun haihuwar Ma’asumai (A.S) [22] ana shirya tarurruka a garurun da ƴan Shi’a suke rayuwa ciki, haka kuma ana kafa Maukibobi a wurare masu tsarki misalin Haraman Imamai (A.S) domin bada hidima ga Masu zuwa ziyara. [23] Maukibobin Tattakin a lokacin Nisfu Sha’aban, cikin kowacce shekara yayin kusantowar Nisfu Sha’aban ana kafa Maukibobin hidima kan hanyar tsakanin Najaf da Karbala [24] haka kuma an shirya Maukibi ɗaiɗai har guda 350 a cikin garin Tehran na ƙasar Iran a lokacin Idil Ghadir a shekarar 2022 m, cikin wani Biki da ake kira da Mehmani Dahe kilomitri (Walimar Kilo mita goma) ana rabawa mutane abinci kyauta. [25]

Lokacin Tattakin Arba’in

Ku duba Maƙala: Tattakin Arba’in

Maukibobin Tattakin Arba’in ƙarƙashin kulawar Mutanen ƙasar Iraƙi, ƙabilu Mazauna ƙauyuka suna kafa Maukibobi kan kowacce hanya, [26] sannan gudanar da waɗanann Maukibobi yana kasance cikin hannaye masu yawa na mutanen ƙasar iraƙi ba tare da sa hannun hukuma ba. [27] Kan asasin rahotannin (Idare Sha’a’ir, Maukibha wa Husainiyeha dar Iraƙ) da ta kasance ƙarƙashin Hukumar kula da Haramin Imam Husaini, an bayyana cewa a lokacin Tattakin Arba’in na shekarar 2020 an kafa Maukibobi har guda dubu talatin da biyu. [28] da suke hidima ga masu Tattaki, kan asasin bayanan Hukumar kula da Hubbaren Abbas (A.S) a taron Arba’in na shekarar 2022 kan hanyar zuwa Karbala an kafa Maukibobi har guda 14500 cikinsu akwai Maukibi guda 300 da ya kasance na mutanen ƙasashen waje ciki kuwa har da Iran. [29] Hukumar kula da Hubbaren Abbas (A.S) sun bayyana cewa a shekarar 2022 adadin Abinci da aka rarraba a garin Karbala da kan hanyoyi zuwa Karbala su kai kusan adadi Miliyan huɗu. [30]

Maukibobi A Garuruwan ƴan Shi’a

Bayan Iraƙi da Iran a wasu ba’arin ƙasashen duniya da ƴan Shi’a suke zaune suke rayuwa a wurin nan ma ana samar da Maukibobi. [31] a ƙasar Fakistan da Indiya idan sun rarraba lemo waɗannan maukibobi suna kiransa “Sabil” [32] idan kuma abinci aka raba suna kiransa “Niyaze Husaini” [33] [yadasht 3] hatta Ahlus-sunna a ƙasar Fakistan kwanakin watan Muharram suna rarraba Sabil da Niyaze Husaini, [34] Dafadukan Shinkafa da nama tana cikin Jumlar abincin da Maukibobi suke rabawa a ƙasar Fakistan a watan Muharram. [35]

Bayanin kula

1. همه چیز در مورد موکب‌های اربعین
2. موکب‌داران سراسر کشور از زائران در جوار حرم مطهر امام رضا(ع) پذیرایی می‌کنند
3. برنامه‌های محرم و صفر در منطقه ۱۴
4. Ishaghi, "Piyadeh Rawi Arba'in", shafi na 100.
5. Ishaghi, "Maukib", shafi na 481.
6. بمشارکة أکثر من ۲۰۰ موکب عزاء.. عتبات کربلاء
7. Muhaddi, Farhang Ashura, 1376, shafi na 175.Esfandiari, Kitabe shinasi Tarikh Imam Husaini (A.S), 1380, shafi na 178.
8. Shabar, Adab al-Taf, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 42.
9. اسحاقی، «پیاده‌روی اربعین»، ص۱۰۰.
10. العتبةُ العبّاسیة المقدّسة ترفد مواکب الخدمة الحسینیة بموادّ غذائیة
11. راه‌اندازی ۱۰۰ موکب پذیرایی هیات‌های مذهبی ایلام در اربعین ۹۶
12. Misali, duba “ Saleh Ruze Rihlat Imam Khumaini” shafi na 199.
13. این موکب ۶۰ روز میزبان بی‌خانمان‌هاست
14. موکب‌های سرو غذا در پیاده‌روی اربعین
15. Ishaghi, Piyadeh Rawi Arbaeen", shafi na 100.
16. موکب‌های استان مرکزی در نقاط سیل زده فعال شد
17. من این تحصل المواکب الحسینیة علی التمویل؟
18. اسقرار موکب‌های جهاد کشاورزی استان در مرز میرجاوه برای زوار اربعین
19. اسحاقی، «پیاده‌روی اربعین»، ص۱۰۰.
20. برنامه‌های محرم و صفر در منطقه ۱۴
21. ۲۰۰ موکب مردمی ایام نیمه شعبان در قم به زائران خدمت‌رسانی می‌کنند
22. پذیرایی بیش از ۲۰ نفر در ایام شهادت امام صادق(ع)
23. موکب‌داران سراسر کشور از زائران در جوار حرم مطهر امام رضا(ع) پذیرایی می‌کنند
24. جزئیات میزبانی موکب ایرانی خدام‌الحسین از زائران پیاده‌روی نیمه شعبان
25. در مهمونی ۱۰ کیلومتری خیابان ولیعصر چه گذشت؟
26. Ishaghi, "Piyadeh rawi Arbaeen", shafi na 100.
27. Ishaghi, "Piyadeh rawi Arbaeen", shafi na 100.
28. إحصائیات حول عدد المواکب الخدمیة والعزائیة ووجبات الطعام والخدمات الطبیة وعدد المتطوعین بالأربعینیة
29. جزئیات خدمات ارائه شده از سوی آستان قدس عباسی در اربعین حسینی
30. جزئیات خدمات ارائه شده از سوی آستان قدس عباسی در اربعین حسینی
31. https://www.dawn.com/news/1577099
32. https://www.dawn.com/news/1577099
33. https://en.dailypakistan.com.pk/10-Sep-2019/trend-of-niaz-distribution-on-ashura-still-alive-across-country
34. https://theazb.com/swat-organized-a-sabeel-on-the-10th-of-muharram/
35. https://en.dailypakistan.com.pk/10-Sep-2019/trend-of-niaz-distribution-on-ashura-still-alive-across-country

Nassoshi