Baƙaƙen Tutoci
Baƙaƙen Tutoci (Larabci: الرّايات السود) nuni ne ga wasu mutane da suka ɓullo daga gabas waɗanda suke ɗaga baƙaƙen tutoci bisa abin da ya zo a ruwayoyi, kuma wasu sun fassara su da ɓullowar Abu Muslim khurasani wanda ya kasance maƙiyin gwamnatin umayyawa. da kuma jagorantar kafa gwamnatin Abbasiyawa, amma ta gefe ɗaya akwai wasu ruwayoyi da suke nuna cewa su waɗannan tutocin alama ce ta mai ceto a ƙarshen zamani.
Masu bincike a ilimin hadisi suna ganin cewa Ahlus-sunna sun tafi kan cewa baƙaƙen tutoci suna daga cikin alamomi na bayyanar Imam Mahadi (A.F) amma ruwayoyin da ƴan shi'a suka rawaito sun fassara baƙaƙen tutoci a matsayin ɓullowar Abu Muslim khurasani domin kawar da gwamnatin umayyawa, sai dai cewa wasu malaman shi'a suna ganin baƙaƙen tutoci a matsayin ɗaya daga cikin alamomi na bayyanar Imam Mahadi (A.F)
Abun da Ake Nufi Da Su
Kalmar baƙaƙen tutoci ta zo a cikin riwayoyi kuma tana nuni ne kan wasu mutane da za su fito daga yankin khurasan suna ɗaga tutoci masu kalar baƙi.[1] abin da ake nufi da Khurasan a zamanin da yanki ne babba wanda a yau ya kunshi wasu yankuna na ƙasar Iran da Afganistan da Turkuministan da Tajikistan da Uzubikistan.[2]
Litattafan Da Wannan Ruwayoyi Suka Zo
Bisa abin da Ya zo a Da'iratul Ma'arif ta Imam Mahadi (A.F) cewa mafi yawanci ruwayoyin da suka yi magana kan baƙaƙen tutoci sun zo ne a cikin litattafai na Ahlus-sunna, kuma duk abin da Ya zo na wannan ruwayoyin a litattafan shi'a ya zo ne daga litattafan Ahlus-sunna, zakalika wasu kaɗan daga cikinsu an rawaito su daga Imaman shi'a (A.S).[3]
Abin da Ruwayoyin Suke Ɗauke Da Shi
Ya zo a cikin wasu hadisai a litattafan ƴan shi'a cewa tutoci baƙaƙe suna daga cikin alamomi na bayyanar imamul Mahadi A S,misali abin da Ya zo a hadisi daga imamu Ali A S,cewa rarrabuwar mutanan Sham da bayyanar baƙaƙen tutoci a yankin Kurasan da kuma hargizi da tarzoma a watan ramadana suna daga cikin alamomi na bayyanar imamu Mahadi.[4] amma wasu ruwayoyi sun bayyana baƙaƙen tutoci a matsayin wani nuni na gushewar gwamnatin Umayyawa da bayyanar Abi Muslim Alkurasani, daga cikin ruwayoyin akwai wacce aka rawaito daga imamu Baƙir A S a littafin Gaiba na Annu'umani,[5] kazalika Ya zo ƙarara a cikin wasu cewa Aba Muslim Alkurasani shi ne mai tutoci baƙaƙe.[6]
Amma dangane da abin da Ya zo a ruwayoyin Ahlussunna kan baƙaƙen tutoci ga shi a dunƙule; • Gushewar Umayyawa bayan motsawar masu baƙaƙen tutoci.[7] • Tuhuma ga waɗanda suke biyayya ga gwamnati bayan motsawar masu baƙaƙen tutoci.[8] • Samun saɓani a tsakanin masu baƙaƙen tutoci.[9] • Bayyanar Sufyani.[10] • Tashi ko motsawar Shu'aibu ɗan Salih.[11] • Bayyanar Imam Mahadi wanda Allah ya yi alƙawarin bayyanar shi a ƙarshan zamani.[12]
Shin Baƙaƙen Tutoci Suna Daga Cikin Alamomin Bayyanar Imam Mahadi?
Wasu malamai da masu bincike na shi'a sun tafi kan cewa abin da ake nufi da baƙaƙen tutoci, shi ne motsi da gwagwarmayar da Abu Muslim khurasani zai yi domin kifar da gwamnatin Umayyawa da ya kai ga kafa gwamnatin Abbasiyawa.[13] saboda ruwayoyin da Shi'a suka rawaito su kaɗai waɗan duk waɗanda suka rawaitosu ƴan shi'a ne basu anbaci baƙaƙen tutoci a matsayin alamar bayyanar imamul Mahadi ba A S,amma litattafan shi'ar da suke ganin baƙaƙen tutoci alama ce ta bayyanar Imam Mahadi sun dogara da ruwayoyi ne waɗanda suka zo ta hanyar Ahlus-sunna.[14] kuma Sayyid Muhammad Sadar ya ce an rawaito ruwayoyi da yawa a lokacin mulikin Abbasiyawa, kuma da yawasu ƙirƙirarsu aka yi wato basu da asali, kamar yadda Abbasiyawa sun yi amfani da salo na ƙirƙirar ruwayuyi domin binne shari'a.[15]
Duk da faruwar abin da ya gabata kan baƙaƙen tutoci akwai waɗanda suka yi imani da cewa su baƙaƙen tutoci alama ce ta bayyanar Imam Mahadi (A.F) kuma suna nuni kan motsin da zai faru kafin bayyanar Imam Mahadi (A.F)[16] marucin littafi na Asaruz Zuhur yana gani cewa mai baƙaƙen tutoci shi ne Assayyid Alkurasani kuma shugaban sujojin shi shi ne Shuaibu ɗan Salihu wanda zai yaƙi Sufyani kuma ya yi galaba a kanshi,[17] kuma daga nan ne zai yiwa Imam Mahaidi (A.F) bai'a.[18] wasu masu bincike sun ce abin da Ya zo a cikin litttafin Asaruz Zuhur ya samo asali ne daga ruwayoyin da suka zo a cikin littafin Alfitan na ɗan Hamda,kuma shi wannan littafin bashi da asali a gun ƴan shi'a, saboda ruwayoyin da suke cikin shi ba su gangaro daga Ma'asumai ba.
Ƴan Isis Da Alaƙarsu Da Baƙaƙen Tutoci
Masu goyan bayan ƴan da'ish suna ganin abin da ruwayoyin da suke magana kan baƙaƙen tutoci suke nufi, shi ne abin da ƙungiyar da'ish take yi, wanda take ganin jahadi ne.[19] amma Rasul Jafariyan mai bincike a tarihi yana ganin cewa ruwayoyin da suke magana kan baƙaƙen tutoci basu da ingancine kuma ƙirƙirarsu akayi, kamar yadda wasu daga cikin mlaman Ahlus-sunna suma sun tafi kan cewa waɗannan ruwayoyin basu inganta ba, kuma sun ce ko dawaɗannan ruwayoyin sun inganta to bai kamata a ɗabbaƙasu a kan ƴan da'ish ba.[20]
Bayanin kula
- ↑ Soleyman, Farhangama Mahdavit, shafi na 136.
- ↑ Soleyman, Farhangama Mahdavit, shafi na 136.
- ↑ Al-Muhammadi Al-Rai Shehri et al., Danishnameh Imam Mahdi, juzu'i na 6, shafi na 60 da 61.
- ↑ Nomani, Al-Ghaibah, 2017, p. 256, h. 13.
- ↑ Tabari, Dalai al-imamah, 1413 AH, shafi 294, H. 248; Tabarsi, Alwari, 1417 AH, juzu’i na 1, shafi 528.
- ↑ Ibn Hammad, Al-Fitan, 1414, Juzu'i na 1, shafi na 207, AH 566.
- ↑ Ibn Hammad, Al-Fitan, 1414 BC, juzu'i na 1, shafi na 210, h.
- ↑ Ibn Hammad, Al-Fitan, 1414, Juzu'i na 1, shafi na 216, AH 595 da shafi na 288, AH 841.
- ↑ Ibn Hammad, Al-Fitan, 1414, Juzu'i na 1, shafi na 288, AH 1841 da shafi 289, AH 1845.
- ↑ Ibn Hammad, Al-Fitan, 1, shafi na 314, h.
- ↑ Ibn Hammad, Al-Fitan, 1414 BC, juzu'i na 1, shafi na 322, h.
- ↑ Duba Mohammadi Rishahri wa digaran, Imam Mahdi Daneshnameh, 1393, juzu'i na 6, shafi na 64, 65; Sadr, Tarikh al-Ghaibah al-Kubari, 1412 AH, shafi 453.
- ↑ Mohammadi Rishahri wa digaran, littafin Imam Mahdi, 2014, juzu’i na 6, shafi na 63.
- ↑ Sadr, Tarikh al-Ghaibah al-Kubari, 1412 AH, shafi 453.
- ↑ Salimian, Farhange Mahdaviyat, 2008, shafi na 137; Duba Kurani, Asr al-Zuhur, 1408 AH, shafi na 242 da 243.
- ↑ Kurani, Asr al-Zahur, 1408Q, p.
- ↑ Kurani, Asr al-Zahur, 1408H, shafi.
- ↑ Mohammadi Rishahri wa digaran, littafin Imam Mahdi, juzu'i na 7, 2014, shafi na 448.
- ↑ جعفریان، «موج جدید استفاده از گفتمان مهدوی در برآمدن داعش»، وبگاه کتابخانه تخصصی تاریخ اسلام و ایران.
- ↑ جعفریان، «موج جدید استفاده از گفتمان مهدوی در برآمدن داعش»، وبگاه کتابخانه تخصصی تاریخ اسلام و ایران.
Nassoshi
- Ibn Hammad, Naim, Al-Fatan, Beirut, Darul Fikr, 1414H.
- Salimian, Khudamorad, Farhange Mahdaviyat , Tehran, Hazrat Mououd Cultural Foundation, 2008. * Sadr, Sayyid Muhammad, Tarikh al-Ghaibah al-Kubari, Beirut, Dar al-Taqqin Lal-Mahabbat, Beirut, 1412H. * Tabarsi, Fazl bin Hasan, I'lamul Al-Wara, bi Alamul Al-huda, Qum, Cibiyar Al-Baiti, 1417H. *Tabari, Mohammad Bin Jarir, Dalai al-Imamah, bincike na Cibiyar Al Ba'ath, Tehran, 1413H. * Korani, Ali, Asr al-Zahur, Cibiyar Buga Makarantar Al-Alam Al-Islami, bugun farko, 1408H. *Mohammadi Rayshahri, Muhammad wa digaran, Daneshnameh Imam Mahdi bar paye qur'an wa hadis wa tarikh, Qum, Darul Hadith, bugun farko, 1393.
- Nomani, Mohammad bin Ibrahim, Al-Ghaibah, Ali Akbar Ghafari, Tehran, Publishing Sadouq, ya yi bincike kuma ya gyara shi, 1397.
- جعفریان، رسول، «موج جدید استفاده از گفتمان مهدوی در برآمدن داعش»، وبگاه کتابخانه تخصصی تاریخ اسلام و ایران، نشر: ۵ مرداد ۱۳۹۳ش، بازدید: ۲ خرداد ۱۴۰۰ش.