Istihara

Daga wikishia

Istihara, (Larabci: الإستخارة) ma'ana neman abin da yafi alheri tare da sallamawa Allah zaɓi a yayin da mutum yake cikin shakku da kokwanto game da rashin sanin alherin wata buƙata ta sa ko sharrinta, tare da cewa ya yi shawara da wasu amma duk da haka ya gaza tantance alheri ko sharrin wannan buƙata. Ana yin istihara ta hanyoyi daban-daban, daga jumlarsu ana yi ta hanyar addu'a, sallah, kur'ani, takarda da carbi. Malaman addini sun jingina da riwayoyi cikin halasta istihara. Shaik Abbas ƙummi ya kawo ba'arin hanyoyin yin istihara a littafin Mafatihul jinan. Ba'arin ladubban istihara su ne misalin: karanta surorin kur'ani, yin salatin ga Annabi (S.A.W) da iyalansa da yin wasu keɓantattun azkar.

A cewar Allama Majlisi, asali shi ne kowa ya yi istihara da kansa; duk da cewa ba'arin malamai sun halasta zuwa wurin wani mutum domin ya maka istihara, kamar yadda a wannan yake faruwa zaka samu yawanci mutane suna zuwa wurin wasu su yi musu istihara. An naƙalto shahararrun istihara daga malamai da sauran mutane, Shaik Abdul-karim ha'iri wanda ya kafa hauza ilimiyya ta ƙum. Lokacin da yake da niyyar zaunawa a garin ƙum ya yi istihara, haka nan Muhammad Ali Shah shi ma ya yi istihara kan rufe majalisar shura.

Ma'ana

A harshen larabci kalmar استخاره tana da ma'anar neman alheri.[1] amma a isɗilahi tana da ma'anar neman alheri daga Allah.[2] Sahibul Jawahir malamin fiƙihu a shi'a a ƙarni na 13. Yana cewa istihara tana ɗauke da ma'ana guda biyu, 1- Allah ya masa zaɓi na alheri cikin abin da ya yanke shawara yinsa. 2-roƙon Allah ya taufiƙi da dacewa cikin aikisa, wanda me yi wuwa ta hanyar istiharar ayi dace da samun zaɓi na alheri, ko kuma Allah ya gudanar da wannan zaɓi na alheri kan harshen mutumin da ake nemi shawararsa kan zaɓin.[3]

Hanyoyin Istihara

Istihara ta hanyar sallah ta na kasancewa cikin wannan sura: yinsa sallah raka'a biyu bayan sallama sai a yi sujjada a karanta wannan addu'a : kafa 100 «اَستخیر اللّٰه فی جمیع اُموری خيرةً فی عافیة (Ina neman zaɓin alheri daga Allah cikin dukkanin al'amurana cikin lafiya) to bayan nan duk abin da ya zo a zuciyarsa shi ne abin da zai aikata.[4]

Istihara Da Kur'ani

Akwai hanyoyi daban-daban na yin istihara da kur'ani,[5] daga jumlarsu akwai:

  • Kan asasin riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) ɗaya daga cikin hanyoyin istihara da kur'ani shi ne cewa duk sanda muke yake samun kansa cikin halin kokwanto tsakanin yin wani aiki ko barinsa , lokacin da ya shirya yin sallah sai ya ɗauki kur'ani ya buɗe duk abin da ya fara gani a kur'ani sai ya yi aiki da shi, idan ayar tana bushara da kyawun aikin da yake son yi sai kawai gabatar da shi, idan kuma misali aya ce ban tsoro to ya nesanci wannan aiki.[6]
«قُلْ اللَّهُمَّ إِنِّی تَفَأَّلْتُ بِکِتَابِکَ وَ تَوَکَّلْتُ عَلَيْکَ فَأَرِنِی مِنْ کِتَابِکَ مَا هُوَ الْمَکْتُومُ مِنْ سِرِّکَ الْمَکْنُونِ فِی غَیْبِک»

(ya Allah ina kyawunta zato da littafinka na kuma dogara da kai ka nuna min abin da yake ɓoye daga littafinka, ka bayyanar min ɓoyayye sirrinka cikin gaibunka) bayan nan sai ka buɗe kur'ani sai ka fitar da istihararka daga saɗara ta farko cikin shafi na farko.[7] Kan asasin ba'arin naƙali, bayan buɗe kur'ani sai a buɗe shafuka bakwai zuwa takwas a jere a fitar da istiharar a shafi na bakwai ko na takwas.[8]

Istihara Da Takarda

Cikin yin istihara da takarda akwai hanya guda ɗaya rak, takardu ne guda biyu ɗaya an rubuta kalmar «اِفْعَل» (aikata) ɗayar kuma an rubuta «لا تَفْعَل» (kada ka aikata) mai yin istihara zai bayan wasu ladubba na musamman sai ya ɗauki ɗaya daga waɗannan takarku guda biyu ya buɗe duk abin da ya gani sai ya yi aiki da shi sawa'un ya dace da aikata ko kuma ya ci karo da kada ka aikata.[9] Ibn Idris Hilli ya raunana hadisan da suka kawo bayanin istihara da takarda;[10] amma Shahidul Awwal ya yi watsi da maganar cewa istihara da takarda abu ne da ya shahara a wurin imamiyya.[11]

Istihara Da Carbi

Istihara ana yinta ta hanyoyi daban-daban.

  • Cikin littafin Zikra Shahidul Awwal yana cewa bayan karan ko wace sura daga cikin kur'ani sai ka karanta fatiha ƙafa uku idan ba a dace ba sai ka karanta ƙafa ɗaya, bayan suratul ƙadri ƙafa goma tar eda wata addu'a ta musammam [Tsokaci 1] sai ka ware cikin tafin hannun daga carbi ko kuma wasu adadin ƙananan duwatsu, ka dinga ƙidaya biyu-biyu, idan na ƙarshe ya kasance guda biyu, to an dace kenan sai aikata abin da kake son aikatawa, idan kuma guda ɗaya ne ya zo ƙarshe to sai a haƙura kada ayi.[12]
  • Isitihara ta daban da ake yi da carbi wace ta cikin mafatihul jinan da aka naƙalto ta daga Muhammad Hassan Najafi wace ta yaɗu sosai a zamaninsa (a ra'ayin sahibul jawahir za a iya jingina wannan istihara ga Imam Mahadi ) bayan karanta kur'ani mutum zai cika tafun hannunsa da carbi zai dinga ƙidaya kwaya takwas-takwas idan kwara ɗaya ta rage a ƙarshe, hakan alama ce ta kyawunta da alherin aiki, idan kuma kwara biyu ce ta rage daga ƙarshe to babu alheri cikin aikin, idan kwara uku to yinsa da barinsa duk ɗaya ne, idan guda huɗu to akwai hani biyu ciki, idan kuma biyar ne wasu ba'ari sun ce akwai wahala da tsanani cikin aiki, wasu kuma sun ce akwai zargi ciki, idan shida ne suka rage akwai alheri mara iyaka a ciki kuma ya kamata ya gaggauta aikatawa, idan kuma bakwai ne suka rage hukunci ɗaya da idan biyar ne suka rage, idan takwas ne suka akwai hani huɗu cikinsa.[13] sahibul jawahir bayan naƙalto wannan istihara ya ce a daɗaɗɗun litattafai da sababbi ba mu samu wani sawu ko alama daga waɗannan litattafai ba, duk da cewa wasu manyan malamai sun yi magana kan wannan istihara.[14]

A cewar Shahidul Awwal, sanadin istihara da ake yi da carbi ko adadin ƙananan duwatsu ya tuƙewa ga Raziyud Ad-dini Abi.[15] na'am Sayyid Ibn ɗawus ya komar da sanadin zuwa ga Imaman Shi'a.[16] a cewar sahibul jawahir (Rayuwa:1202-1266. h, ƙ.) a zamanin malamai sun kasance suna yin istihara ta wannan hanya.[17]

  • Sayyid Musa Shubairi ya naƙalto istiharar da ake dangantawa Imam Mahadi (A.F) ta hanyar Sayyid Ali Shushtari, ana yi misalin za a karanta bismilla ƙafa uku, salati ƙafa uku, tare da karannata sau ɗaya, bayan nan asai a ɗauki carbi a ƙirga biyu-biyu har zuwa na ƙarshe idan ya zama ɗaya ya rage a ƙarshe to akwai alheri, idan kuma guda biyu ya rage to babu kyau sai a bari.[18]

A cikin littafin Mafatihul jinan na Shaik Abbas ƙummi ya kawo ba'arin hanyoyin yin istihara.[19]

Halascin Istihara

Tun kafin muslunci akwai wata istihara da ake kira da sunan istiƙsam bi azlam (rabo da kibiya) wace ta yaɗu tsakanin larabawa.[20] wace ake yinta da kwari da baka.[21] [Tsokaci 2] Shaik Shaltut malami ahlus-sunna, bisa jingina da aya ta 3 suratul ma'ida wace cikin maganar istiƙsam bi azlam ta zo, ya bayyana cewa istihara ɗaya ce daga abubuwan da akai hani kansu cikin wannan aya, kuma yana ganinta matsayin abin da ya haramta a shari'a.[22] amma Ayatullahi Safi Gulfaigani ɗaya daga cikin maraji'an taƙlidi na shi'a, yana ganin akwai bambanci tsakanin istiƙsam bi azlam da istihara, ya kuma yi watsi da ra'ayin Shaltut.[23] an jingina da adadin riwayoyi game da tabbatar da mustahabbancin istihara.[24]

Ladubba Da Sharuɗɗa

An yi bayanin ladubba da sharuddan istihara, wasu daga cikinsu sun kasance kamar haka:

  • Dole aikin da za ayi istihara kansa ya kasance halas: istihara ana yinta ne domin kawar da kokwanto cikin ayyukan halas ba wai ayyuka da ana tabbacin alherinsu ba.[25]
  • Istihara domin kankin kai: a cewar Allama Majlisi babu wani hadisi da ya zo kan cewa wani ya wakilta wani domin yi masa istihara. Sabida abin da ya fi dacewa sbi ne kowa ya yi wa kansa istihara da kansa ba wai ya wakilta wani ya yi masa ba,[26] na'am ya naƙalto daga Sayyid Ibn ɗawus cewa ya halasta mutum ya wakilta wani daban ya yi masa istihara.[27]
  • Istihara bayan yin shawara: ma'ana kafin istihara a fara da yin shawara idan ba a samu amsa ba sai ayi istihara.[28]
  • Lokaci: Faizul Kashani a cikin littafin Taƙwimul Al-muhsinin ya ambaci lokutan da ake yin istihara da kur'ani a ko wace rana a ranakun mako; sai dai kuma ya ce lokutan da aka ambata sun shahara tsakankanin ma'abota Imani sai dai kuma ba su zo ba cikin hadisai.[31] amma a cewar Sahibul Jawahir babu wani keɓantaccen lokacin yin sallar istihara,[32] na'am game da istihara da kur'ani an naƙalto cewa a yi ta lokacin sallah.[33]
  • Aiki da istihara: shari'a ba ta wajabta yin aiki da istihara ba, amma abu ne mai kyau.[34]

Karanta keɓantattun addu'o'i,[35] karanta ba'arin wasu surorin kur'ani,[36] salati,[37] suma duka suna daga cikin ladubba da aka yi umarni da yinsu kafin istihara.

Sanannun Istiharori

Sanannun Istiharori su ne kamar haka:

  • Istiharar Muhammad Ali Shah ƙajar: ya yi wannan istihara kan mabambantan buƙatu daga jumlarsu rufe majalisar shura ta ƙasa a shekarar 1287 h, shamsi, tare da korar wasu ɗaiɗaikun mutane.[38]
  • Istiharar Nasirud Ad-dini Shah domin samun karɓuwar mulkin Iran kan garin Hirat na ƙasar Afganistan:[39] a shekarar 1296 h, shamsi, ƙasar birtaniya ta miƙa mulkin garin Herat hannun Iran ba tare da ƙayyade lokaci ba, Nasirud Ad-dini Shah bayan shawarar mai yawa da ya yi sai ya yi kamun kafa da istihara.[40]
  • Istiharar Abdul-Karim Ha'iri Yazdi domin zama a garin ƙum: Ayatullahi Ha'iri wanda ya kafa hauzar ƙum, a shekarar 1340 h, ƙ, ya tafi garin ƙum, zuwansa ke da wuya sai wasu adadin malamai da ɗalibai suka roƙe shi ya zauna a garin, da farko ya yi kokwanto kan zama ko rashinsam amma bayan kafewa da dagewar malamai sai ya yi istihara ya zauna a garin ƙum.[41] [Tsokaci 3]
  • Istiharar dattawan garin Najaf domin Mulla ƙurban Ali Zanjani: ya kasance mazaunin garin zanjan sai dai cewa bai yarda da sabon tsarin mulki ba, masu son sabon tsarin mulki sun buƙaci zaunar da shi a birnin Tehran domin sanya idanu kansa, sai dai cewa dattawan garin Najaf da suke kasance suna goyan bayan tsari mulki sun yi istihara kan asasin istiharar da suka yi suka nemi a turo shi ƙasar Iraƙi.[42]

Cikin littafin "Kendekawe darbaraye Istikare wa Taf'al" an kawo istiharorin malaman shi'a misalin Shaik Ansari, Faizul Kashani, Shahidul Sani da Sayyid Ibn ɗawus.[44]

Hukuncin Shari'a Game da Aiki Da Sakamakon Istihara

Bisa fatawar malaman fiƙihu ba wajibi bane aiki sa sakamakon da ya fito daga istihara, babu haramcin kan saɓa masa, duk da cewa yafi kyau ace ba saɓa ɗin ba.[45] a ra'ayin Ayatullahi Shubairi Zanjani yana ganin ya kamata a yi taka tsantsan ta fuskanin kasancewa saɓawa sakamakon istihara na iya zama sababi da sanadin cutuwa.[46]

Faɗaɗa Nazari

An rubuta litattafai masu zaman kansu game da istihara, littafin :Istikara" na Ayyash da "Al-istikhara wal Istishara" na Zubairi Shafi'i suna daga cikin na farko-farkon litattafai da aka rubuta a wannan fage, sauran litattafan da aka wallafa game da istihara su ne kamar haka:

Bayanin kula

  1. Dehkhoda, Lughatanatamah, zailu Istikhara.
  2. Mu’assasa Dayiratul marif fikh islami, farhng Fiki Farisa, 1382H, Juzu’i na 1, shafi na 430.
  3. Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 12, shafi 162.
  4. Ibn Idris, Al-Sara’ir, 1410 BC, juzu’i na 1, shafi na 314.
  5. Ibn Tawus, Fath al-Abwab, 1409 AH, shafi na 277-279.
  6. Tusi, Tahdhib al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 3, shafi na 310.
  7. Ibn Tawus, Fathul-Abwaab, 1409H, shafi na 156. ↑
  8. Ibn Tawus ya ruwaito, Fathul Abaab, 1409 Hijiriyya, shafi na 278 da 279.
  9. Kulayni, Al-Kafi, 1407 BC, juzu'i na 3, shafi na 473.
  10. Ibn Idris Hilli, Al-Sara’ir, 1410H, juzu’i na 1, shafi na 313 da 314.
  11. Shahidul Awwal, Zikr al-Shi’ah, 1419H, juzu’i na 4, shafi na 246-247.
  12. Shahidul Awwal, Zikirin Shi’a, 1419 Hijira, juzu’i na 4, shafi na 269 da 270.
  13. Qomi, Mafatih al-Jinan, Adab Istikhara; Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 12, shafi 172.
  14. Najafi, Jawahir al-Kalam, 362 Sh, juzu’i na 12, shafi na 173.
  15. Shahidul Awwal, Al-Zikri Al-Shia, 1419H, juzu'i na 4, shafi na 269.
  16. Shahidul Awwal, Al-Zikri Al-Shia, 1419 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 249-270.
  17. Najafi, Jawahir al-Kalam, 1404 BC, juzu'i na 12, shafi 163.
  18. Shabiri Zanjani, Jur’ah Ya Az Darya, juzu’i na 1, shafi na 501.
  19. Qumī, Mafātiḥ al-Jinān, 1376 AH, shafi 842, 851, bayanin kula ga littafin.
  20. Ibn Habib, Al-Mukhbar, Dar Al-Afaq Al-Jadedh, shafi na 196.
  21. Jassas, Ahkam al-Qur’an, 1405 BC, juzu’i na 3, shafi na 306.
  22. Abbasi Moghadam, "Barasi mabani wa mahiyat Istikhara", p 32.
  23. Golpayegani, Buhus haula Al-Istaqam (Mahsru'iye Al-Isthikhara), shafi na 1-8.
  24. Golpayegani,Buhus haula Al-Istaqam (Mahsru'iye Al-Isthikhara), shafi na 7-9.
  25. "Daanavisi wa Istikhara", daftarehifze wa nashar Ayatollah Khamenei.
  26. Majlisi, Bahar Al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 88, shafi na 285.
  27. Majlisi, Bahar Al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 88, shafi na 285.
  28. "Daanavisi wa Istikhara", daftarehifze wa nashar Ayatollah Khamenei
  29. Shahidul Awwal, Zikra al-Shia, 1419 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 267.
  30. Shahidul Awwal, Zikra al-Shia, 1419 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 267
  31. Fayd Kashani, Taqweem al-Muhsinin, 1315 AH, shafi na 58 da 59. ↑
  32. Najafi, Jawahir al-Kalam, 1404 BC, juzu'i na 12, shafi 155.
  33. Tusi, Tahdhib al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 3, shafi na 310.
  34. "Daanavisi wa Istikhara", daftarehifze wa nashar Ayatollah Khamenei
  35. Kulayni, Al-Kafi, 1407 BC, juzu'i na 3, shafi na 473.
  36. Shahidul Awwal, Al-Zikra Al-Shia, 1419 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 249-270.
  37. Kulayni, Al-Kafi, 1407 BC, juzu'i na 3, shafi na 472.
  38. Tawakkoli, “Waqārī Az-Tārīkh Mashtula, Chand Istikhara Az Muhammad Ali Shah Ba Jawabaha Anha,” shafi na 57.
  39. Taymouri, "Nasser al-Din Shah wa Istikhara baraye qabul hakimiyat Iran dar Herat," shafi na 265.
  40. Taymouri, "Nasser al-Din Shah dwa Istikhara baraye qabul hakimiyat Iran dar Herat," shafi na 252-253.
  41. Tariqa Dar, Kandukawi Darbara Istikhara wa Tafa’al, 1377H, shafi na 38.
  42. Shabiri Zanjani, Jur’ah Ya Az Darya, 1393 AH, juzu’i na 3, shafi na 352 da 353.
  43. «مستند راه طی شده»، سایت آپارات.
  44. Tariqa Dar, Kandukawi Darbara Istikhara wa Tafa’al, 1377 AH, shafi na 25-77.
  45. عدم وجوب عمل به استخاره، وبگاه آیت‌الله مکارم شیرازی
  46. Shabiri Zanjani, Jur’ah Ya Az Darya, juzu’i na 1, shafi na 505.
  47. Tariqa Dar, Kandukawi Darbara Istikhara wa Tafa’al, 1377 AH, shafi 101-113.

Tsokaci

  1. a karanta wannan addu'a kafa uku: اللهم إني أستخيرك لعلمك بعاقبة الأمور، و أستشيرك لحسن ظني بك في المأمول و المحذور. اللهم إن كان الأمر الفلاني مما قد نيطت بالبركة اعجازه و بواديه، و حفّت بالكرامة أيامه و لياليه، فخر لي اللهم فيه خيرة ترد‌ شموسه ذلولا، و تقعض أيامه سرورا. اللهم إما أمر فائتمر، و اما نهي فانتهي. اللهم إني أستخيرك برحمتك خيرة في عافية؛. (شهید اول، ذکری الشیعه، ۱۴۱۹ق، ج۴، ص۲۶۹و۲۷۰)
  2. Istiqsam a lugga yana da ma'anar karkata zuwa ga aikata daya daga cikin abubuwa guda biyu, neman ayyana kibiyarka daga sauran kiboyi. haka kuma kokarin da nema da bincike domin sanin mikdarin kibiyaraka daga sauran kibiyoyi da ba naka ba
  3. Karimi jahrami aya nakalto daga murtada ha'iri dan gidan Shaik Abdul-karim ha'iri cewa babansa bayan dagiyar adadi malamai da daliban garin Qum da mutanen tehran kan zama a Qum sai ya yi istihara a kan kabarin sayyida ma'asuma (a.s) sai wannan aya ta fito:وَأتُؤني بِأَهْلِكُمْ اَجْمعينَ». suratul yusuf aya 93,»https://www.hawzahnews.com/news/350149/.

Nassoshi

  • Abbasi Moghaddam, Mustafa, "Barsasi Mabani wa m,ahaiyat Istikhara", a cikin Jarida na Nazarin Tarihi na Kur'ani da Hadisi, Shamarah 42, Bahar da Tabistan, 1387 Hijira.
  • Fayd Kashani, Takwamil Mohsenin,dar kitabe tauzihul Maqasid be zamimeh takwimil mushinin, published by Shaykh Bahayi, Bija, Bina, 1315 BC.
  • Ibn Athir, Mubarak bin Muhammad, Al-Nahiya Fi Gharib Al-Hadith da Al-Athar, Kum, Cibiyar Jarida ta Ismailiya, Beta.
  • Ibn Faris, Ahmad Ibn Faris, Mujam Maga'is al-Lughga, Bincike na Abdus Salam Muhammad Haroon, Kum, Wallafar ofishin yada farfagandar Musulunci na makarantar hauza ta Kum, 1404H.
  • Ibn Habib, Muhammad Ibn Habib, Al-Mohbar, bincike na Ilze Lichten-Schetter, Beirut, Dar al-Afaq al-Jadideh, Bita.
  • Ibn Idris Hilli, Muhammad bin Mansour, Al-Saraer al-Hawi na Tahrir al-Fatawi, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta Kum Seminary Teachers Society, 1410H.
  • Ibn Tawoos, Ali Ibn Musa, Fathul Abwab baina zawai al-Abab wa baina Rab al-Arbab, bincike da gyara na Hamed Khafaf, Qum, Cibiyar Al-Bait (A.S.), bugu na farko, 1409H.
  • Jasas, Ahmed bin Ali, Akhmat al-Qur'an, wanda Mohammad Sadiq Qomhawi, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi ya yi bincike, 1405H.
  • Majlisi, Muhammad Baqir, Bahar Al-Anwar, Beirut, Larabawa Heritage Revival House, 1403 BC.
  • Najafi, Muhammad Hassan, Jawaher al-Kalam fi Sharh Sharia al-Islam, edita na Abbas Qochani da Ali Akhundi, Beirut, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, 1404 BC.
  • Qafadar, Abulfazl, Kenmdekawe darbaraye Istikhara wa Tafaal, Qum, ofishin yada farfagandar Musulunci na Seminary na Kum, 1377.
  • Qomi, Sheikh Abbas, Mafatih al-jinan, bugun Hussein Estadouli, Kum, Siddiq, babin farko, 1376H.
  • Shahidul Awwal, Muhammad bin Makki, Dhikr al-Shia fi Haqm al-Sharia, Qum, Cibiyar Al-Baiti, 1419H.
  • Shubairi Zanjani, Seyyed Musa,Jur'eh az dary, Qum, Institute of Bibliography, 2009.
  • Tawakli, Ahmad,Waraki az Tarikh Mashruteh: Cande istikhara az Muhammad Ali Shah ba jawabahaye anha. mujallar Yadgar, lamba 48 da 49, Afrilu da Mayu 1328.
  • Timuri, Ibrahim, "Naser al-Din Shah wa Istikhara baraye kabul hakimiyat Iran dar Herat", a cikin Mujallar Bukhara, No. 100, Yuni da Yuli 2013.
  • Tusi, Muhammad bin Hasan, Tahzib al-Ahkam, Hasan Mousavi Khorsan, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, ya gyara, 1407H.
  • اسفندیاری، آمنه، «استخاره اینترنتی صحیح است؟!!»، وبگاه تبیان، تاریخ درج مطلب:‌ ۱۳ تیر ۱۳۹۱ش، تاریخ مشاهده: ۳۰ تیر ۱۳۹۸ش.
  • ضميرى، محمدتقی و سیدعبدالرسول حسينى‌زاده، «استخاره»، در دایرة المعارف بزرگ قرآن، تاریخ مشاهده:‌ ۳۰ تیر ۱۳۹۸ش.
  • «دعانویسی و استخاره»، وبگاه دفتر حفظ و نشر آیت‌الله العظمی خامنه‌ای، تاریخ مشاهده: ۳۰ تیر ۱۳۹۸ش.