Annabi Ibrahim (A.S)

Daga wikishia
(an turo daga Ibrahim)
Ibrahim

Hazrat Ibrahim (Larabci: النبي إبراهيم عليه السلام) wanda ya fi shahara da sunan Ibrahim Khalil, shi ne na biyu cikin jerin Annabawa Ulul Azmi, an aiko Ibrahim da Annabta a yankin da yake tsakanin ƙoramu guda biyu (ƙoramar Furat Da ƙoramar Dajla) da suke ƙasar Iraƙ, Annabi Ibrahim (A.S) ya kira Namarudu wanda ya kasance Sarkin wannan gari tare da mutanensa zuwa Tauhidi, babu waɗanda suka amsa kirasa sai ƴan tsiraru, sakamakon ɗebe tsammani da sa rai daga yin imanin sauran mutanen garin sai Annabi Ibrahim (A.S) ya yi hijira zuwa ƙasar Palasɗinu. Kan asasin abin da ya zo daga ayoyin Alkur'ani, haƙiƙa mutanen zamanin Annabi Ibrahim (A.S) sun kasance Masu bautar Gumaka, sakamakon Annabi Ibrahim (A.S) ya kakkarya musu Gumakan da suke bautawa sai suka yanke shawarar jefa shi cikin wuta, sai dai kuma cewa wutar da suka jefa shi ta yi sanyi saboda Allah ya umarceta da ta yi sanyi ga Ibrahim, cikin ikon Allah Hazrat Ibrahim (A.S) ya fito daga cikin wannan wuta lafiya ƙalau ba tare da ta ƙona shi ba. Isma'il (A.S) da Is'haƙ (A.S) sun kasance ƴaƴan Hazrat Ibrahim (A.S) kuma magadansa, nasabar ƙabilar Banu Isra'ila waɗanda aka aiko Annabawa da yawa cikinsu ta kasance daga ƴaƴan Annabi Ibrahim (A.S) haka kuma Maryam Mahaifiyar Hazrat Isa (A.S) ta kasance cikin Jikokin Hazrat Ibrahim (A.S) ta hanyar wasiɗar Is'haƙ (A.S) sannan Annabin Muslunci shima nasabarsa tana danganewa zuwa ga Hazrat Ibrahim (A.S) ta hanyar wasiɗar Hazrat Isma'il (A.S) Haƙiƙa Alkur'ani ya danganta ginin ɗakin Ka'aba da kiran mutane zuwa ga aikin Hajji ga Hazrat Ibrahim (A.S) haka kuma ya gabatar da shi matsayin Khalilullahi (Masoyin Allah), kan asasin Ayoyin Alkur'ani, bayan gama jarraba shi da bala'i daga jumalarsu umartarsa da yanka ɗansa sai ya samu muƙamin Imamanci ƙari kan muƙamin Annabta da aka aiko shi da ita.

Tarihin Rayuwa

Haihuwa Da Mutuwa

Haihuwa da wafati Aksarin masu bincike suna ganin an haifi Hazrat Ibrahim (A.S) a cikin ƙarni na ashirin gabanin haihuwar Almasihu (A.S), wasu ba'ari kuma sun tafi kan cewa cikakken tarihin haihuwar ya kasance shekaru 1996 kafin miladiyya[1] cikin littafin Hawadisul Al-Ayyam an bayyana cewa an haife shi goma ga watan Muharram[2] wasu ba'ari Malaman tarihi suna ganin an haife shi a farkon watan Zull-Hijja.[3]

Cikin Masadir ɗin Muslunci an kawo adadin wasu garuruwa da ake tsammanin anan ne aka haife shi, a cewar Tarikh ɗabari wasu suna ganin an haife shi a garin Babul ko Kusa a Nahiyoyin Kufa ta ƙasar Iraƙ, a wancan zamanin Namarudu ne Ya kasance kan karagar Sarauta, wasu kuma suna ganin an haife shi a garin Alwarka'u ko Harran, sun ce bayan haihuwarsa sai Mahaifinsa ya kai shi garin Babul ko Kusa,[4] a wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) ya bayyana cewa a garin Kusa aka haifi Ibrahim kuma Namarud Sarki a zamanin[5] Ibn Baɗuɗa wanda ya kewaya duniya a ƙarni na 6 h ƙamari, ya bayyana cewa an haifi Hazrat Ibrahim (A.S) a garin Bursa tsakanin Bagdad da Hilla.[6]

Wurin ziyartar Annabi Ibrahim (a.s) a garin Khalil palasɗin

Haƙiƙa Annabi Ibrahim (A.S) ya rayu shekaru 179-200 sannan ya rasu a garin Hebron wanda yake ƙasar Palasɗinu.[7]

Mahaifin Ibrahim

Akwai saɓanin Malamai kan sunan Mahaifin Hazrat Ibrahim (A.S) a tsohon Alkawari (Old Testment) an rubuta Tarih matsayin sunan Mahaifinsa,[8] cikin masadir ɗin Musulmi suke kiransa da Tarukh,[9] ko Tarah[10] cikin Alkur'ani ya zo misalin:

«وَ إِذْ قالَ إِبْراهِیمُ لِأَبِیهِ آزَرَ»

yayin da Ibrahim ya cewa kawunsa Azara.[11] kan asasin wannan aya wasu Malaman tafisirin Ahlus-sunna sun bayyana cewa Azara shi ne Mahaifin Ibrahim.[12] amma Malaman tafsirin Shi'a sun tafi kan ra'ayin cewa Kalmar (Abbu) wacce ta zo a wannan aya ba ta da Ma'anar Uba Mahaifi.[13] a harshen Larabci ana amfani da Kalmar (Abbu) kan Kawu da Kaka da ma Mai kula da yaro ƙari kan uba Mahaifi. Allama Ɗabaɗaba'i a cikin Tafsirin Almizan yana cewa: babu kokwanto (Azara) da sunansa ya zo cikin wannan aya bai kasance Mahaifin Ibrahim ba, amma sakamakon Wasiɗar wasu hususiyoyi da Unwanai da ya kasance tare da su sai aka kira shi da uba, misalin kasancewarsa Kawun Ibrahim, kuma a mahangar lugga ana amfani da Kalmar (Abbu) kan Kaka da Kawu.[14] Ibrahim ya barranta kansa daga Azara wanda ya kasance yana kiransa da Uba amma a haƙiƙa bai kasance Mahaifinsa ba.[15] Kan asasin wasu rahotanni daga Masadir na tarihi a shekarar da aka haifi Ibrahim a shekarar ne Sarki Namrudu ya bada umarnin kashe duk wani yaro Namiji da aka Haifa saboda Masu duba ƙasa sun gaya masa cewa a cikin shekarar ne za a haifi yaron da zai zo da wani sabon addini saɓanin wanda Namrudu yake kai, kuma wannan yaro zai girma ya kakkarya Gumakan da suke bautawa, da wannan dalili ne Hazrat Ibrahim sakamakon Tsoron Namarudawa ya je ya shiga wani Kogo da yake kusa da gidansa bai fito daga cikinsa ba sai bayan watanni goma sha biyar.[16]

Aure Da Samun Haihuwa

Saratu ita ce ta kasance farkon Matar da Hazrat Ibrahim (A.S) ya aura kan asasin Naƙalin At-Taura ya aure ta a garin Uru Kaldaniyan[17] kan asasin bayanin Dehekhoda a ƙamus na lugga Ur ko auru a cikin Attaura wani gari ne a tsohuwar Nahiyar Somir a kudancin garin Babul, wannan gari yana nan a kudancin ƙasar Iraƙ, wanda a yanzu yana nan kusa da titin jirgin ƙasa da yake tsakanin garin Basra da Bagdad, yana daga cikin muhimman cibiyoyin tarihi da Al'adu na Somari, a faɗin At-Taura nan ne aka haifi Annabi Ibrahim (A.S), sunan wannan babban gari wanda aka kafa tun zamanin da can tun ƙarni na huɗu kafin Miladiyya, bayan wannan zamani garin ya nutse cikin ƙasa an manta da shi ba a gano garin ba sai a a ƙarni na 19 m,[18] ya zo a littafin At-taura cewa Saratu ta kasance ƴar'uwar Ibrahim amma ba daga gidansu ba.[19] amma abin da ya dace daga riwayoyin Shi'a haƙiƙa Saratu ta kasance ƴa ga gwaggon Ibrahim kuma ƴar'uwa ga Annabi Lut (A.S)[20] kan asasin ɗaya daga cikin waɗannan riwayoyi, Ibrahim (A.S) ya auri Saratu a garin Kusa, Saratu ta kasance Mace mai tarin dukiya da tarin Dabbobi da ƙasa, bayan ta auri Ibrahim sai ta yi kyautar dukiyarta gare shi, Hazrat Ibrahim (A.S) ya haɓɓaka dukiyar ta ƙaru sosai ta kai ga babu wanda ya kaishi tarin dukiya a garin da yake rayuwa.[21] Da farko dai Hazrat Ibrahim bai samu haihuwa daga Saratu ba, da wannan dalili ne Saratu ta bashi kyautar baiwarta mai suna Hajara, Allah ya azurta Ibrahim da samun Haihuwa ta hanyar Hajara aka samu ɗa Namiji mai suna Isma'il[22] bayan wasu shekaru sai ya samu haihuwa da Saratu da ɗa Namiji da aka sama suna Is'haƙ, an haifi Is'haƙ bayan shuɗewar shekaru 5 ko 13 da haihuwar Isma'il.[23] kan asasin ba'arin naƙali, yayin da aka haifi Is'haƙ, haƙiƙa Hazrat Ibrahim (A.S) ya tsufa har ya haura shekaru 100 a[24]duniya, a wani ƙaulin ance ya kai shekaru 120 a duniya.[25] Malaman Tarihi sun ce, Hazrat Ibrahim (A.S) bayan rasuwar Saratu ya auri wasu matan har guda biyu kuma ya samu ƴaƴa huɗu tare da ɗaya daga cikinsu ya kuma samu ƴaƴa guda bakwai tare da ɗayar, adadin ƴaƴansa goma sha uku.[26] Mazi, Zamran, Sarehajji da Sabaƙ sun kasance ƴaƴansa daga Matarsa mai suna (ƙanɗur), Nafis, Madin, Kishan, Sharukh, Amimu, Lut da Yaƙshan sun kasance ƴaƴansa daga matarsa mai suna (Hajjuni),[27]

Ibrahim A Cikin Alkur'ani

An ambaci sunan Ibrahim ɗaiɗai har karo 69 a cikin Alkur'ani[28] sakamakon bayanin ƙissar Ibrahim an samu sura sukutum guda da ta zo da sunansa.[29] Alkur'ani ya yi bayani kan Annabtarsa, kiransa zuwa ga tauhidi, Imamancinsa, da ƙissar Yanka ɗansa, Mu'ujizar raya Tsuntsaye guda huɗu bayan kashe su da kuma ƙissar sanyaya wutar da ya shiga.

AnnabtaDa Imamanci

A cikin wasu adadin ayoyin Alkur'ani an kawo bayanin Annabtarsa da kiransa zuwa ga tauhidi. 30 haka kuma a cikin aya ta 35 cikin suratu Ahkaf ya zo cikin Annabawa Ulul Azmi,[30] kan asasin riwayoyi, Ibrahim ya kasance na biyu cikin Jerin Annabawa Ulul Azmi bayan Annabi Nuhu (A.S)[31] daidai da aya ta 124 cikin suratul Baƙara, Allah ya baiwa Hazrat Ibrahim (A.S) muƙamin Imamanci bayan jarraba shi da wasu adadin bala'o'i, a ra'ayin Allama ɗabaɗaba'i haƙiƙa Muƙamin Imama da ya zo cikin wannan aya ya zo da ma'anar shiryarwa ta baɗini, muƙamin da kafin kaiwa gare shi dole ya zamana an samu kamala ta samuwa da muƙamin Ma'anawiyya na musamman bayan an sha mujahada mai tarin yawa.[32]

Khalilullahi

Asalin Makala: Khalilullahi

Khalilullahi (Masoyin Allah),[33] laƙabi da da ya kebantu Annabi Ibrahim (A.S).[34] mukami ne d ayake saman mukamin Annabta da manzanci.[35] Akwai riwaya daga Imam Sadik (A.S) cewa Allah ya dauki Ibrahim da farko a matsayin bawa, sannan annabi, sannan a matsayin manzo, sannan kuma a matsayin aboki (Khalil).[36] Ya zo a cikin aya ta 125 a cikin suratun Nisa’i:«و اتَّخَذَ اللَّهُ إِبْراهیمَ خَلیلاً؛, Allah ya zabi Ibrahim matsayin masoyi, kuma aboki[37] A farkon wannan ayar an yi wasicci da bin addinin Ibrahim.[38] Bayan haka, don ya ƙarfafa wasu su yi biyayya ga Ibrahim, ya ce Allah ya zaɓe shi ya zama abokinsa.[39]

Ibrahim Uban Annabawa

Daidai da abin da ya zo a cikin Alkur'ani haƙiƙa Ibrahim ya kasance Kakan wasu adadin Annabawa[40] haƙiƙa ɗansa Is'haƙ ya kasance kakan Banu Isra'ila wanda daga tsatsonsa ne aka samu Yaƙub, Yusuf, Dawud, Sulaiman, Ayyuba, Musa, Haruna da sauran wasu Annabawa.[41] Haka kuma Nasabar Hazrat Isa (A.S) ta hanyar Mahaifiyarsa ta na danganewa zuwa ga Hazrat Yaƙub ɗan Annabi Is'haƙ (A.S).[42] kan asasin abin da ya zo daga riwaya nasabar Hazrat Muhammad (S.A.W) shi ma tana danganewa ga Isma'il ɗan Hazrat Ibrahim,[43] ta wannan fuskar ne ake kiran Hazrat Ibrahim[44] da laƙabin Abul Anbiya (Uban Annabawa)[45]

Mu'ujizozi

Kan asasin abin da ya zo daga ayoyin Alkur'ani, sanyaya wuta da kuma raya matattun tsuntsaye guda huɗu ana kirga shi daga cikin Mu'ujizozin Hazrat Ibrahim (A.S):

  • Sanyaya Wuta: Ayoyi na 57-70 Suratul Anbiya, bayan Hazrat Ibrahim ya ga mutanensa sun karkatu zuwa ga bautar gumaka kuma ya fahimci ba zasu dena ba, sai ya kakkarya Gumakan, sannan ya jingina aikin ga Babban Gunki tsakanin Gumakan, ya ce musu su tambayi Gumakan su gaya musu wanda ya kakkarya su idan har gumakan suna iya Magana, sai masu bautan Gumaka suka kunyata kan hujjar Ibrahim, sai dai cewa tare da haka basu tuba daga bautar gumakan ba, sai suka yanke shawarar jefa shi wuta sakamakon kakkarya musu Gumaka da ya yi, sai dai cewa bayan sun jefa shi cikin wutar sau wutar ta yi sanyi bata ƙona shi ba.[46]
  • Raya Matattun Tsuntsaye Guda Huɗu: kan asasin aya ta 260 Suratul Baƙara, ciki amsa roƙon da Ibrahim ya yi daga Ubangiji na Ubangiji ya nuna masa yanda yake raya Matattu, Allah ya umarce shi da yanka Tsuntsaye guda huɗu sannan ya caɗanya namansu da juna sannan ya ajiye curi ɗaiɗai kan adadin wasu Duwatsu sannan ya kira waɗannan Tsuntsaye sai suka tashi rayayyu suka nufo inda yake.

Hijira

Cikin aya ta 71 Suratul Anbiya da ta zo game da Ibrahim (A.S): (kuma muka tseratar da shi tare da Lut zuwa wata ƙasa da muka albarkaceta)[47] wasu ba'arin litattafan tafsiri sun bayyana cewa wannan ƙasa da aka yi ishara zuwa gareta a wannan aya ita ce ƙasar Sham[48] ko kuma a ce Palasɗinu ko Baitul Muƙaddas[49] haka kuma ta kasance wurin hijirar Ibrahim (A.S)[50]

Gina ɗakin Ka'aba Cikin aya ta 127 Suratul Baƙara ya zo cewa Hazrat Ibrahim tare da Taimakon ɗansa Isma'il ya gina ɗakin Ka'aba.[51] kuma ƙarƙashin umarnin Ubangiji ya kira mutane zuwa aikii ibadar Hajji.[52] daidai da abin da ya zo a riwaya, an fara gina ɗakin Ka'aba ne ta hannun Adamu (A.S) shi kuma Hazrat Ibrahim (A.S) ya sabunta gininta.[53]

YankaƊansa

Asalin Maƙala: Zabihullahi Daga cikin Jarrabawar Allah kan Hazrat Ibrahim akwai umartarsa da Yanka ɗansa. Daidai da rahotan da ya zo daga Alkur'ani haƙiƙa Ibrahim (A.S) ya yi mafarki yana Yanka ɗansa, bayan farkawa sai ya gayawa ɗansa abin da ya faru a mafarki, sai ɗansa ya nemi ya zartar da umarnin Ubangiji a kansa da ya ba shi a mafarki, sai dai cewa bayan Ibrahim ya kwantar da ɗansa zai yanka sai ya ji wani sauti ya zo (Ya kai Ibrahim haƙiƙa ka gasgata mafarkinka, lallai haka muke sakawa masu kyawunta aiki, da muke karbar kyakkyawar niyyarsu a matsayin aiki) da yaƙini wannan bayyananniyar jarrabawa ce haƙiƙa mun fanshi ɗanka da wani babban abin yanka.)[54] Alkur'ani bai faɗi sunan ɗan Ibrahim da aka fanshe shi daga yanka ba da wani babban abin Layya, cikin wannan batun na wanene daga cikin ƴaƴan Ibrahim akwai saɓani tsakanin Shi'a da Ahlus-sunna, wasu ba'ari suna cewa Isma'il wanda aka kusa yankawa, wasu kuma suna cewa Is'haƙ ne[55] Shaik ɗusi ya tafi kan cewa riwayoyin Shi'a sun nuna cewa Isma'il ne.[56] Mulla Salihu Mazandarani cikin Sharh Usulul Alkafi ya tafi kan cewa ra'ayin cewa Isma'il ne wanda aka fansa daga yanka ya kasance ra'ayin da Mashhur ɗin Malaman Shi'a suka tafi a kansa,[57] cikin Ziyaratu Gufaila keɓantacciyar Ziyarar Imam Husaini (A.S) a tsakiyar watan Rajab nan ma ya zo kamar haka (Amincin Allah ya tabbata a gareka ya magajin Isma'il Zabihullahi)[58]

Ibrahim Tareda Alƙawari Guda Biyu

A cikin tsohon Alƙawari (Old Testment) da farko an ambaci Ibrahim da sunan Abhraham amma a cikin babi na 17 ya zo kamar haka: (Amma yanzu alkawarina yana tare da kai, za ka zama Uban al'ummai da yawa, ba kuwa za a kira sunanka da sunan Abram ba.[59] Maimakon haka, sunanka zai zama Ibrahim. Domin na sa ka uban al'ummai da yawa)[60] Kan asasin ruwayar Tsohon Alkawari, (Old Testment) Ibrahim yana da dangantaka da ƙabilun Aramic da suka yi hijira daga yankin Larabawa zuwa gabar kogin Furat a arewacin Siriya.[61] daidai da babi na 11 Sifru Faidayesh, Tarah Mahaifin Ibrahim (A.S) ya yi hijira tare da Ibrahim da Saratu da Lut zuwa Kan'ana yayin da suka isa Harran sai suka ɗan tsaya suka yada zango, a wannan wuri ne ya rasu,[62] wasu sun fitar da natija daga wannan labari cewa an haifi Ibrahim a garin Kaldaniyan, tare da dukkanin bayanai a farkon babi na 12 an bayyana cewa Harran ta kasance Mahaifar Ibrahim kuma ƙasar Mahaifinsa Tarah.[63] Bisa riwaya At-taura Ibrahim har zuwa shkeara 75 ya kasance a garin Harran, bayan nan ƙarƙashin umarnin Ubangiji ya tashi daga Harran zuwa Kan'ana ya kuma tafi ne tare da matarsa Saratu da `dan dan'uwansa wato Lut da wasu ba'arin mutane, ya yada zango a gabashin Bai'ilu anan ya kafa Tanti ya kuma gina Mayanka a wurin.[64] bayan wani lokaci sakamakon faruwar Fari (rashin samun ruwan sama) dole ya yi hijara zuwa Misra,[65] bayan wannan lokaci sai ya ƙara dawowa baitu'il,[66] bayan nan kuma ya tafi Hebron (Alkhalil) ya zauna a can.[67] A cikin At-Taura ya zo cewa lokacin da Ibrahim ya shiga ƙasar Misra ya gabatar da matarsa Saratu a matsayin ƴar'uwarsa domin kareta daga cutarwar Misrawa don kada su yi kwaɗayi cikinta; daga ƙarshe Sarkin Misra na wannan zamanin ya fitinu da kyawun da Saratu take da shi, kai tsaye ya riketa matarsa saboda ita ya kyautatawa Ibrahim, amma sai Allah ya jarrabci wannan Sarki da bala'i mai tsanani.[68] Allama ɗabaɗaba'i ya yi watsi da wannan sashe daga ƙissar da ta zo dangane da Ibrahim sakamakon rashin dacewarsa da mukƙamin Annabta tare da kuma cin karo da sauran ƙissoshin Ibrahim (A.S) ya nuna cewa an jirkita At-Taura.[69] Tsohon Alkawari (Old Testment) ya gabatar da Is'haƙ matsayin wanda aka Umarci Ibrahim da yanka shi a mafarki.[70] a wasu wuraren kuma ya kawo cewa an umarci Ibrahim da Yanka ɗansa ba tare da ambaton wanene cikin ƴaƴansa ba.[71] haka kuma ya zo cikin Attaura Allah ya ƙulla Alkawari da Ibrahim a Kan'ana da ya bada kyautar Kogin Furat ga ƴaƴansa da za su fito daga tsatson ɗansa Is'haƙ.[72] Haka zalika cikin Sabon Alkawari (New Testment) an ambaci sunan Ibrahim a wurare har guda 71 haka nasabar Isa Almasihu da wasiɗa guda 39 kamar yanda ya zo a Matta (Matta, 1:1-7) ko wasiɗa 54 (Luka 3:24-25 tana danganewa zuwa Ibrahim. Imanin Ibrahim cikin Sabon Alkawari an bayyana shi da mafi ɗaukakar Imani, saboda ya yarda ya rayu cikin baƙunta a ƙasar Palasɗinu ƙasar da ba tasa ba amma ya karɓi hukuncin Allah ya rayu cikinta tare da layya da ɗansa a wurin.[73]

Siffofin Hazrat Ibrahim A Cikin Irfanin Muslunci

A ra'ayin da yawa yawan Arifan Muslunci, suna ganin Hazrat Ibrahim (A.S) matsayin Saliki cikin Sairin baɗini, ya keta gadojin suluki ya kai ga ƙololuwar Martabobin Kamala, Abdul Kareem ƙushairi Arifi kuma Malamin tafsiri a ƙarni na huɗu zuwa na biyar h ƙamari, yana ganin malakut da Annabi ya yi a matsayin jazaba (abin jan hankali) kafin suluki,[74] Rashid-dini Mubidi ya yi Imani da cewa wannan jazabar dagane da bakiɗayan Tajalli itace Mabayyanar Ubangiji, ta samar da sha'awa; Amma tare da ganin rashin wanzuwar waɗannan bayyanuwar, ya gane cewa ba za su iya kasancewa cikin cikakkiyar ƙauna ba,[75] A ra'ayin Arifai gaɓoɓin ƙissoshin Hazrat Ibrahim (A.S) da suka zo a Alkur'ani misalin Sanyaya wuta, Layya da ɗansa Isma'il, Nisantar jikunan sama (Taurari, wata da rana), neman raya matattu, da kashe Tsuntsate da raya su, da dai sauransu. Cike suke da isharorin Irfani da Tawilai na baɗini.[76] alal misali, A cikin Kissar ciratuwa daga tauraro zuwa wata da rana da kuma fuskanta zuwa fagen gaskiya, (Fadar Allah) da Annabi Ibrahim (AS) ya yi, ƙushairi ya fassara tauraro da ɓoyayyen hasken hankali, wata a matsayin ilimi da rassansa. dokokin allahntaka, rana a matsayin sufanci,[77] Abdul-Razak Kashani yana ganin waɗannan kalmomi guda uku matsayin martabobin nafsu da Ruhu da Zuciya, Hazrat Ibrahim tare da samu Ma'arifa cikin gushewar waɗannan martabobi yake kaiwa ga samun muƙamin kaɗaita.[78] Malam Shabastari ya rera waƙe kan wannan Muƙami.

Bayanin kula

  1. Sajjadi, “Ibrahim Khalil (AS)”, shafi na 499.
  2. Marashi Najafi, Hawadisul Al-Ayyam, shafi na 46 (electronic copy).
  3. Marashi Najafi, Hawadisul Al-Ayyam, shafi na 46 (electronic copy).
  4. Tabari, Tarikh Al-Umam wa Al-Muluk, 1967, juzu'i na 1, shafi na 233.
  5. ƙutb Raɓandi, Kasas Anbiya, Astan ƙuds Razaɓi, juzu'i na 1, shafi na 298.
  6. Ibn Battuta, shafi na 101.
  7. Tabari, Tarikh Al-umam wa Al-Maluk, 1967, juzu'i na 1, shafi na 312; Ibn Kathir, al-Bedaya wa Al-Nehaya, juzu'i na 1, shafi na 174.
  8. Faidayesh, 11:24, matane Abri; ƙS: Tarjameh Farsi keh Tarah Amade.
  9. Tabari, Tarikh Al-Umam wa Al-Muluk, 1967, juzu'i na 1, shafi na 233.
  10. Ibn Kathir, Al-Bedayah wa al-Nehayah, 1986, juzu'i na 1, shafi na 142; Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Darul Marafah, juzu'i na 1, shafi na 2
  11. Suratul An'am, aya ta 74
  12. Fakhr Razi, Mufatih Al-Ghaib, 1420 AH, juzu'i na 13, shafi na 31.
  13. Abul Fattuh Razi, Rouz Al-Jinnan wa Ruh Al-Jinnan, 1408 AH, juzu'i na 7, shafi na 340 da 341; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 5, shafi.303.
  14. Ɗabaɗaba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 7, shafi na 165.
  15. Ɗabaɗaba'i, Al-Mizan, Ismailian Charters, juzu'i na 7, shafi na 217.
  16. Tabari, Tarikh Al-Umm wa Al-Muluk, 1967, juzu'i na 1, shafi na 234
  17. Faidayesh, 11:29.
  18. Dehkhoda, luggatnameh, zailu Ur
  19. Faidayesh, 20:12.
  20. Ɗabaɗaba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 7, shafi na 229; Ayyashi, Tafsirul Ayyashi, 1380 AH, juzu'i na 2, shafi na 254.
  21. Kulainy, Kafi, 1407 AH, juzu'i na 8, shafi na 370; Ɗabaɗaba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 7, shafi na 229.
  22. Ibn Athir, Al-Kamel, 1385 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 101.
  23. Masoudi, Isbatul Al-wasiyya, 2004, shafi na 41-42
  24. Masoudi,Isbatul Al-wasiyya, 2004, shafi na 46.
  25. Ibn Sa’ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1410H, juzu’i na 1, shafi na 41.
  26. Ibn Sa’ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1410H, juzu’i na 1, shafi na 41.
  27. Ibn Sa’ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1410H,Nashir darul Sadar juzu’i na 1, shafi na 48.
  28. Firouzmehr, “Mukayaseh Kisseh Ibrahim (A.S) dar Kur’an wa Attaura” shafi na 88.
  29. refKhorramshahi, DaneshNameh ƙuran wa ƙuran Fajuhi, 1377, juzu'i na 2, shafi 1240
  30. Suratul Maryam, aya ta 41-48 – Suratul Anbiya, aya ta 51-57 – Suratul Shaara, aya ta 69-82 – Suratul Safat, aya ta 83-100 – Suratul Zakharf, aya ta 26 da ta 27 – Suratul Matahnah.Aya ta 4- Suratul Ankabut, aya ta 16-25.
  31. Ɗabaɗaba'i, Al-Mizan, juzu'i na 18, shafi na 218
  32. Ɗabaɗaba'i, Al-Mizan, 1393 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 272.
  33. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 4, shafi na 145.
  34. Abul Fattuh Razi, Ruz al-Jinnan wa Ruh al-Jinan fi Tafsirul Qur'an, 1408 AH, juzu'i na 6, shafi na 129.
  35. Mughniyeh, Tafsir al-Kashif, 1424 AH, juzu'i na 2, shafi na 448.
  36. Kulaini, Al-Kafi, 1407H, juzu'i na 1, shafi na 175.
  37. Suratul Nisa’i, aya ta 125
  38. Hosseini Shirazi, Tabyin al-Qur'an, 1423 AH, shafi na 109.
  39. Ibn Kathir Damashki, Tafsirin Kur'anul Azeem, 1419H, juzu'i na 2, shafi na 374
  40. Suratul Ankabut, aya ta:27.
  41. Suratul An'am, aya ta 84.
  42. Mughniyeh, Tafsir Al-Kashif, 1424 AH, juzu'i na 1, shafi na 208.
  43. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Dar al-Marafah, juzu'i na 1, shafi na 2; Ibn Abd Rabbah, al-Iqdul al-Farid, 1402H, juzu'i na 5, shafi na 89.
  44. Ibn Hisham, Al-Sirah Al-Nabawiyyah, Dar Al-Marefah, juzu'i na 1, shafi na 2; Ibn Abdu Rabbihi, Al-iƙdul Al-Farid, 1402H, juzu'i na 5, shafi na 89
  45. Sayyid ƙutb, fi Zilalul Alƙur'ani, 1425 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 2997.
  46. Suratul Anbiyya, aya ta 57 zuwa 70.
  47. Suratul Anbiya, aya ta 71
  48. Mulhala wa Siyuti, Tafsir Al-Jalalaini, 1416 AH, shafi na 402; Abul-Fatuh Razi, Rouz al-Janan, 1408 AH, juzu'i na 15, shafi na 200.
  49. Kashani, Tafsir Manhaj Al-Sadeghin, 1336, juzu'i na 6, shafi na 8.
  50. ƙutb Raɓandi,Kasas Anbiya, Astan ƙuds Razaɓi, juzu'i na 1, shafi na 298.
  51. Suratul Baƙarah, aya ta:127.
  52. Suratul Hajj, aya ta:27.
  53. Faizul Kashani, Tafsir Al-Safi, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 189 da 190.
  54. Suratul Safat, aya ta 101 zuwa 108
  55. Duba ƙurtubi, Al-Jame Al-Ahkam Al-ƙur'an, 1364, juzu'i na 16, shafi na 100; Bahrani, Al-Burhan fi Tafsirul Kur’ani, juzu’i na 4, shafi na 616 zuwa 622.
  56. Tusi, Al-Tabayan, Dar Ehiya al-Trath al-Arabi, juzu'i na 8, shafi na 518
  57. Mazandarani, Shahrah Furu Al-Kafi, 1429 AH, juzu'i na 4, shafi na 402
  58. السَّلامُ عَلَيكَ يا وارِثَ إسماعيلَ ذَبيحِ اللّه‏. محمدی ری‌شهری، دانشنامه امام حسين(ع)، ج‏١٢، ص١٢٧
  59. Faidayesh, 11:26.
  60. Faidayesh, 17:4-5, Tarjameh Fazel Khan Hamdani (Grosi).
  61. Sousse,Al-Arab wal Al-Yahud fi Al-tarikh, 1972, shafi na 252
  62. Faidayesh, 11:31-32
  63. Faidayesh, 12:1-4
  64. Faidayesh, 12:1-8 .
  65. Faidayesh, 12:10.
  66. Faidayesh, 13:1-4
  67. Faidayesh, 13:18.
  68. Faidayesh, 12:11-19.
  69. Ɗabaɗaba'i, Al-Mizan, 1417 AH, Juzu'i na 7, shafi na 225 da 226.
  70. Faidayesh, 22:1-14.
  71. Tekwin, 22:2
  72. Faidayesh, 15:18.
  73. Sajjadi, “Ibrahim Khalil (AS)”, shafi na 506.
  74. ƙashiri, Lataef Al-Esharat, 1981, juzu'i na 1, shafi na 484.
  75. Meibodi, Kashf Al-Asrar, 1371, juzu'i na 1, shafi na 351.
  76. cf. Nezhat, "Tahawuli Shaksiyat dar Negareshe Tawili tafasir Irfani ba Takid bar Kisseh Hazrat Ibrahim", zamistan 2019, shafi 41-13; Kermani, "Hazrat Ibrahim (AS) dar Irfane Islami", 1399, shafi na 1-18.
  77. ƙashiri, Lata'ef Al-Esharat, 1981, juzu'i na 1, shafi na 485.
  78. Kashani, Sharh Fusus Al-Hekam, 1422, juzu'i na 1, shafi na 206.

Nassoshi

  • Alƙur'anul Al-Kareem
  • kitabe Mukaddas.
  • Ibn Athir, Ali Ibn Muhammad, Al-Kamil fi Al-Tarikh, Beirut, Dar Sadir - Dar Beirut, 1385H.
  • Ibn Saad, Muhammad Ibn Saad, Thabaƙat Al-Kabra, Bincike na Muhammad Abd al-ƙadir Atta, Beirut, Dar Al-Kitab Al-Alamiya, bugun farko, 1410H/1990 Miladiyya.
  • Ibn Saad, Muhammad Bin Saad, Thabaƙat Al-Kubra, Al-Matababa: Dar Sadr - Beirut, Al-Nasher: Dar Sadr - Beirut, B.
  • Ibn Abd Rabbihi, Ahmad, Al-Eƙd Al-Farid, na Ahmad Amin da sauransu, Beirut, 1402H/1982 Miladiyya.
  • Ibn Arabi, Mohi al-Din, Majmu'eh Rasa'il Ibn Arabi, Beirut, Dar Ahya Al-Trath al-Arabi, 1367.
  • Ibn Kathir, Ismail Ibn Umar, Al-Bedayah wa Al-Nehayah, Beirut, Darul Fikr, 1407 AH/1986 AD.
  • Ibn Hisham, Abd al-Malik, Al-Sirah al-Nabawiyyah, bincike na Mustafa al-Saƙƙa, Beirut, Dar al-Marafa, Bita.
  • Abulfatuh Razi, Hossein bin Ali, Rouz Al-Jinnan da Ruh al-Jinan, Mashhad, Astan ƙuds Razaɓi, 1408H.
  • Azraƙi, Abdullah bin Ahmad, Akhbar Makkah, Makkah al-Mukramah, Darul Taƙƙafa, 1403H.
  • ƙutb Rawandi, Saeed bin Hebatullah, ƙasses al-Anbia, Mashhad, Astan ƙuds Razaɓi.
  • Mahali, Jalal al-Din da Jalal al-Din Siyuti, Tafsir Al-Jalalaini, Beirut, Al-Noor Press Institute, 1416 AH.
  • Sajjadi, Sadegh, "Ibrahim Khalil (a.s.)",dar Daneshnameh Islami, Juzu'i na 2, shafi na 497-506.
  • Sayyid ƙutb,fi Zalalul Alƙur'an, Beirut, Darul Shrouƙ, bugu na 35, 1425H.
  • Sheikh Mahmoud Shabestri, Golshan Raz, Kerman, Kerman Cultural Serɓices Publications, Ch. 1, 2013.
  • Sadouƙ, Muhammad Bin Ali, Ilalul Shara'i, ƙum, Shagon Littafin Daɓari, 1966/1385.
  • Taheri, Mohammad Hossein, "Ibrahim (a.s) wa khandanesh dar Attaura wa Alƙur'an", a cikin Mujallar Ilimin Addini na ƙuarterly, lamba 1, Winter 2008
  • Ɗabaɗaba'i, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsirin ƙur'an, ƙum, Islamic Publications of the Seminary Society of Teachers, 5th, 1417 AH.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Muhama al-Bayan fi Tafsir al-ƙur'an, Gabatarwa na Mohammad Jaɓad Balaghi, Tehran, Nasser Khosrow Publications, 1372.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh Al-Umam wal Al-Maluk, Beirut, Dar al-Tarath, Tathaniyyah, 1967.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, al-Tabayan fi Tafsir al-ƙur'an, Beirut, Dar Ehiya al-Trath al-Arabi.
  • Ayashi, Mohammad Bin Masud, Tafsirul Ayyashi, Tehran, Islamia, 1380H.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, Mufatih al-Ghaib, Beirut, Dar Ihya Al-Tarat al-Arabi, bugu na uku, 1420H.
  • Firouzmehr, Mohammad Mahdi, " Mukayaseh Kisseh Ibrahim (amincin Allah ya tabbata a gare shi) dar Alkur'ani wa Attaura", Miƙat Hajj, hunturu 2001, shafi na 42.
  • Faiz Kashani, Mulla Mohsen, Tafsirul Al-Safi, Tehran, Sadr Publications, 1415 AH.
  • ƙashiri, Abdul Karim, Lata'if Al-Esharat, Al-Hiyeh al-Masriyyah al-Ame na littafin, 1981.
  • Kashani, Mulla Fethullah, Tafsirul Manhaj al-Sadeghin, Tehran, kantin sayar da littattafai Mohammad Hasan Elmi, bugu na uku, 1336.
  • Kashani, Abd al-Razzaƙ, Sharh Fusus Al-Hekam, ƙom, Bidar Publications, 1422.
  • Kermani, Alireza "Hazrat Ibrahim (PBUH) in Islamic Mysticism", Binciken Sufi, Na 5, bazara da bazara 2019.
  • Masoudi, Ali bin Hossein, Isbatul Al-Wasiyya Imam Ali bin Abi Talib, ƙum, Ansari, 2004.
  • Mughniyeh, Mohammad Jaɓad, Tafsir Al-Kashif, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiyya, 1424H.
  • Mazandarani, Mohammad Hadi bin Mohammad Saleh, Sharh Furu Al-Kafi, malami kuma mai karantawa: Mohammad Jaɓad Mahmoudi da Mohammad Hossein Daraiti, ƙum, Dar al-Hadith don bugawa da bugawa, bugu na farko, 1429 AH.
  • Mohammadi Rayshahri, Muhammad, Daneshnameh Imam Hossein (a.s) bar Paye Alƙur'ani, Hadisi wa Tarikh, mujalladi 14, Buga Cibiyar Al'adun Darul-Hadith, ƙum, bugu na biyu, 1388.
  • ‌ مرعشی نجفی، سید مهدی، حوادث الایام: گاهشمار تاریخ شیعه، ترجمه علی عطائی اصفهانی (نسخه الکترونیکی منتشر شده توسط مؤسسه فرهنگی-اسلامی شبکة الامامین الحسنین(ع)).
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, 1374.
  • Meybodi, Abulfazl Rashiduddin, Kashf Al-Asrar wa Adeh Al-Abrar, gyara ta Ali Asghar Hekmat, Tehran, Amir Kabir Publications, 1371.
  • Neishaburi, Nizam Al-Din, Tafsir Ghareeb al-ƙur'an, Tabari Tafsir margin, Beirut, Dar Reha'a Tarath al-Arabi.
  • Nazhat, Bahman, "Tahawwul shaksiyat dar negareshe tafasir Irfani ba takid bar kisseh Hazrat Ibrahim", Irfaniyat dar adab Farsi, shekara ta 11, shafi na 45, hunturu.