Sanyayar Wuta Ga Annabi Ibrahim (A.S)

Daga wikishia
Karamin zanen Ibrahim a Golestan na Mahmoud Farshchian

Wuta ta yi sanyi ga Annabi Ibrahima (Larabci:برد النار لإبراهيم) wannan shi ne ceto na mu'ujiza da Ibrahim ya samu daga wutar da Namarud sarkin babila da masu bautar gumaka suka tanadar masa sakamakon karya musu gumaka da ya yi.[1] Alƙur'ani a aya ta 51 zuwa 70 a cikin suratul Anbiya da aya ta 85 zuwa ta 98 a cikin suratul safat da aya ta 24 a cikin suratul Ankabut da.[2] aya ta 69 a cikin suratul Anbiya Allah ya yi magana akan wuta da tai sanyi da aminci ga Annabi Ibrahim.[3] A cewar malaman tafsirin kur'ani, wannan umarni da aka yi wa wuta ta kasance mai sanyi ga Annabi Ibrahim Takwini ne.[4] Malaman tafsiri sun ba da ra'ayoyi da dama game da yadda Allah ya sanyaya wutar.[5] Wasu daga cikin ra'ayoyinsu sun zo kamar haka:

  • Yanayin wutar ya canza ya zama kamar lambu.[6]
  • Allah ya sanya shamaki tsakanin wuta da Ibrahim domin kada ta ƙona shi.[7]
  • Zafi kawai aka ɗauke daga wuta; Domin zafi ba ya cikin yanayin wuta.[8]
  • Allah ya sanya wata kariya a jikin Ibrahim domin kada wutar ta shafe shi; Kamar yadda jikin masu gadin gidan wuta yake kasancewa a ranar ƙiyama.[9]
  • Wannan lamari dai mu'ujiza ce ta Ubangiji kuma ba za mu iya ba da amsa ba.[10]

Kamar yadda wasu masu tafrisi suka nuna, labarin wannan waƙi'a shi ne kamar haka: Ibrahim yana da kimanin shekara goma sha shida.[11] a lokacin da mutane suka bar garin domin bikinsu na shekara, sai ya fara sarar gumaka da gatari. Sannan ya sa gatari a kafaɗar babban gunki.[12] Akwai wanda ya san ƙiyayyar Ibrahim da gumaka don haka shin e ya bayyana sunansa. Sai aka yi wa Ibrahim Shari'a da tuhumar ya ɗauki babban gunki a matsayin wanda ya kewa ƙiyayya ta Musamman; A ƙarshe sun yanke hukuncin cewa a ƙone shi a cikin wuta. wanda Mushrikai suka kwaɗaitar da mutane yin hakan, kuma sun ɗauki kona Ibrahim a matsayin taimakon gumaka.[13]

ta yadda wasu suka ba da itace don biyan bukatar shuwagabannin su, wasu kuma suna daf da mutuwa da rashin lafiya. suka yi wasiyya da sayen itacen wuta daga dukiyoyinsu, don su ƙona Ibrahim.[14] Wutar ta yi girman da har ba wanda zai i ya jefa Ibrahim a cikinta. A daidai lokacin Iblis ya ba da shawarar yin amfani da babban keji Anan ne Aka sanya Ibrahim a cikin wani katafaren keji sannan aka jefashi cikin wuta.[15]

Kamar yadda wasu riwayoyi suka ce, lokacin da aka jefa Ibrahim cikin wuta, an yi maganganu tsakanin Ibrahim da wasu mala'ikun Allah.[16] A bisa waɗannan hadisai, mala'iku sun roki Allah ya cece shi. Allah kuma ya ba su izinin taimakawa; Amma Ibrahim ya nuna ba ya bukatar tallafinsu.[17] A ƙarshe, Jibrilu ya miƙa masa taimako. Da yake mayar masa da martani, Ibrahim yana ganin Allah ya san halin da yake ciki don haka baya buƙatar taimakon su Allah ya isar masa.

Yazo a wasu riwayoyin cewa Annabi Ibrahim ya karanta wannan Addu'ar "Ya Allahu, ya Ahadu ya wahidu ya samadu, ya man lam yalid wa lam yulad, walam ya kun lahu kufwan Ahad, ya Allah ya makaɗaici, ya wanda bai da kowa bayan shi, "Ya Allah ina rokonka ka tseratar da ni daga wannan wuta saboda Annabi Muhammadu da alayen Muhammadu, kuma Allah ya sanyaya wuta a gare ni, ya kuma amintar da ni.” [18]

A cikin Tafsir Kabir, Fakhrur razi ya amsa wasu tambayoyi game da ƙonewar Ibrahim. Daga cikin tambayoyin akwai wannan: Shin da gaske ne da a ce Allah bai ba da umurni cewa a sami lafiya ba bayan umarnin sanyi, da Ibrahim ya kamu da mura da ciwan sanyi ? Sai ya amsa da cewa sanyin wutar daga Allah ne, kuma da wuya Allah ya fara yin umarni da sanyi mai mutuƙar yawa sannan ya bada umar nin aminci da sanyi mai daɗi.[19]

Bayanin kula

  1. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1371, juzu'i na 13, shafi na 446-433.
  2. Makarem Shirazi, Tarjameh Alqur'an, 1372, shafi 326, 327, 399, 449.
  3. Makarem Shirazi, tarjameh Alqur'an, 1372, shafi na 327.
  4. Tabatabai, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 14, shafi na 303; Makarem Shirazi, Tafsir al-Nashon, 1371, juzu'i na 13, shafi na 446
  5. Sajjadizadeh, Mirzaei, "Nakhde wa Barasi Sarde shodane atesh bar Ibrahim (A.S)", shafi na 158.
  6. Tayeb, Ateeb Al Bayan, 1369, juzu'i na 9, shafi na 208.
  7. Tusi, Al-Tabayan, Dar Ehiya al-Trath al-Arabi, juzu'i na 7, shafi na 263.
  8. Iraqi, Al-Qur'ani da Al-Aql, 1362, juzu'i na 3, shafi na 327; Tusi, Al-Tabayan, Dar Ehiya al-Trath al-Arabi, juzu'i na 7, shafi na 263.
  9. Fakhrazi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 22, shafi na 159.
  10. Fazlullah, Min Wahayi al-Qur'an, 1419 AH, juzu'i na 15, shafi 241.
  11. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1371, juzu'i na 13, shafi na 436.
  12. Majma al-Bayan fi Tafsirin Kur'an, juzu'i na 7, shafi na 84 da 83; Misalin fassarar, juzu'i na 13, shafi na 437 da 436.
  13. Makarem Shirazi, Tarjumeh Alqur'an, 1372, shafi na 327.
  14. Makarem Shirazi, Tafsir namuneh, 1371, juzu'i na 13, shafi na 444; Tabarsi, Majma al-Bayan fi Tafsirin Qur'an, 1372, juzu'i na 7, shafi na 87.
  15. Tabarsi, Majma al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, 1372, juzu'i na 7, shafi 85-87; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1371, juzu'i na 13, shafi na 436 da 446.
  16. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 12, shafi na 24; Tabarsi, Al-Ihtjaj, 1403 AH, Juzu'i na 1, shafi na 48.
  17. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 68, shafi na 155.
  18. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 12, shafi na 24; Tabarsi, Al-Ihtjaj, 1403 AH, Juzu'i na 1, shafi na 48.
  19. Fakhrazi, Tafsir Kabir, 1420 AH, juzu'i na 22, shafi na 159 da 160.

Nassoshi

  • Fadlullah, Mohammad Hossein, Man Wahayi Al-Qur'an, Lebanon, Darul Malak, bugun farko, 1419H.
  • Fakhrazi, Muhammad bin Omar, Al-Tafsir al-Kabir, Lebanon, Dar Ihya Al-Tarat al-Arabi, bugu na uku, 1420H.
  • Iraqi, Seyd Nuruddin, Al-Qur'an wa Al-Aql, Qom, Haj Mohammad Hossein Kushanpur Islamic Culture Foundation, 1362.
  • Majlisi, Mohammad Taqi, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ehiya al-Tarat al-Arabi, 1403H.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Darul-e-Kitab al-Islamiyya, bugu na 10, 1371.
  • Makarem Shirazi, Nasser, tarjameh Alqur'ani, Qum, Ofishin Tarihi da Ilimin Musulunci, bugu na biyu, 1373.
  • Tabarsi, Ahmad bin Ali, Al-Ihtjaj Ali Ahl al-Jajj, Mashhad, Mawallafin Morteza, 1403H.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Iran, Nasser Khosrow, bugu na uku, 1372.
  • Tabatabai, Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, bugu na biyu, 1390H.
  • Tayeb, Abdul Hossein, Atyeb al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Islam, bugu na biyu, 1369.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Tabyan fi Tafsir Al-Qur'an, Beirut, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, bugu na farko.
  • سجادی‌زاده، سید علی، میرزایی، مصطفی، «نقد و بررسی تفسیر آیه سرد شدن آتش بر ابراهیم(ع)»، دوفصلنامه آموزه‌های قرآنی، شماره ۲۵، ۱۳۹۶ش.