Hajara
Hajara (Larabci: هاجر) Matar Ibrahim (A.S) Mahaifiyar Isma'il (A.S), Hajara ta kasance Baiwar Sarkin Misra wace yayi kyautarta ga Saratu Matar Ibrahim ita kuma ta sayar da ita ga Ibrahim, bayan wani lokaci sai Hajara ta Haifawa Ibrahim Isma'il Bayan haihuwar Isma'il, sakamakon wata damuwar Saratu da samun haihuwar da Hajara ta yi ita kuma bata samu ba, karkashin Umarnin Allah sai Ibrahim ya dauki Hajara da `dan da ta Haifa daga Sham ya kai su Makka a wannan zamani Makka ta kasance Sahara babu shuke-shuke kuma babu wanda yake rayuwa a wajen, kan asasin abin da ya zo a cikin At-Taura sabanin abinda yake a cikin Masadir na Muslunci, na kawo Rahoton cewa Hajara tayi hijira zuwa Makka ne bayan Haihuwar Is'hak kuma ita kadai da danta ta tafi, Ibrahim (A.S) bai raka ta ba, Kabarin Hajara yana nan a Muhallin Hijru Isma'il.
Dangi
Kan asasin nakali hakika Hajara ta kasance Diyar Sarkin Misra, bayan wasu Gungun `yan tawaye da da suka fito daga Mutanen Ainul Shamsi sun yiwa Sarkin Misra bore lamarin da ya kai ga kifar da gwambatinsa, a wannan lokacin ne aka kamata aka sayar da ita ga sabon Sarkin Misra. Ya zo a riwaya cewa Annabi (S.A.W)[1] ya umarci Sahabbansa da su tausasa Mu'amala da Mutanen Misra saboda Hajara daga cikinsu ta fito[2]
Hajara, Hadiyyar da Sarkin Misra ya baiwa Saratu
Kan asasin abin da ya zo a rahotan Ibn Asir hakika hazrat Ibrahim lokacin da yake kusa da shekara 70 Ubangiji ya umarce shi da ya yi hijira daga Garin Babul[3] da wannan dalili shi da Matarsa Saratu da dan'uwansa Hazrat Ludu da wasu Mabiyansa suka yi hijira zuwa Misra, lokacin da suka je Misra sai Sarkin Misra ya yi kallon Shaidanci ga Saratu, Hazrat Ibrahim ya gaya masa cewa `yar'uwarsa ce saboda Takiyya, kan asasin Rahotan Ibn Asir, duk sanda Sarki ya nufi Saratu da mummunar manufa sai hannunsa ya bushe ya maimaita haka har karo uku sai hannunsa ya bushe, sai yake rokonta ta yi masa addu'a hannunsa ya koma yanda yake, bayan ta yi masa addu'a ya warware sai ya kyaleta ya kuma yi mata kyautar Baiwarsa Hajara wace ta kasance daga Kabilar Kibdawa[4] Allama Tabataba'i batun cewa Ibrahim ya gabatarwa da Sarki Saratu a matsayin `yar uwarsa hakika hakan yana cin karo da mukaminsa na Annabta, wannan Magana ce da take daga tufka da warwarar jirkitattar At-Taura ta yanzu da ta gangara cikin masadir din tarihi riwayoyin Ahlus-sunna[5] haka kuma kan asasin riwayar da Allama Tabataba'i ya nakalto daga littafin Alkafi ya bayyana cewa Hazrat Ibrahim (A.S) ya gabatar da Saratu a matsayin matarsa sannan duk sanda hannun Sarki ya bushe Ibrahim ne yake masa addu'a hannun ya koma yanda yake a da.[6]
Hijira daga Sham zuwa Makka
Hazrat Ibrahim bai samu haihuwa ba da Saratu da wannan dalili Saratu ta sayar masa da Baiwarta Hajara don ya samu haihuwa daga gareta, bayan wani lokaci sai Allah ya azurta Ibrahim da samun Haihuwa daga Hajara[7] lamarin da baiwa Saratu dadi ba[8] saboda ita bata samu ba[9] bayan fushin Saratu kan Haifar Isma'il sai Allah ya umarci Ibrahim da ya dauki matarsa Hajara da Isma'il daga Sham ya kai su Makka, a wannan lokaci Makka ta kasance bushashen wuri Sahara babu wanda yake rayuwa a wurin[10] a wannan wuri da ya ajiye Iyalinsa a Makka anan ne aka gina Dakin Allah kusa da Rijiyar Zamzam[11] hakika Sunan Hajara bai zo a cikin Alkur'ani ba, sai dai cewa cikin Suratul Ibrahim anyi ishara kan daukar iyalansa daga Sham zuwa Makka[12] Kan asasin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) lokacin da Ibrahim ya kai Hajara da Isma'il garin Makka ya ajiye su a can ya juyo, hakika Isma'il ya ji kishirwa mai tsanani, sai Hajara ta tashi tafi nemo ruwan da zai sha, a yunkurin nemo masa ruwa ne tayi Sa'ayi kai kawo sau bakwai tsakanin Dutsen Safa da Dutsen Marwa amma tare da haka ba ta samo ruwan ba, lokacin da ta dawo wurin Isma'il sai ta ganshi yana jan kasa da kafafunsa saboda kishi sannan ruwa na bulbulowa daga kasa wannan idan ruwan ne ake kiransa da Rijiyar ZamZam, wannan Waki'a ce ta zama sababin wajabcin sa'ayi da kaikawo tsakanin Dutsen Safa da Dutsen Marwa matsayin daya daga ayyukan Ibadar Hajji[13]
Hajar ta yi wa Ibrahim magana: "Shin kana barinmu ne a cikin kasar da babu ruwa, babu ruwa, babu abin ci a cikinta?" Ibrahim ya ce mata: Allah da ya umarce ni da yin haka ya isar maki
Kan asasin Masadir na Muslunci hijirar Hajara ta kasance kafin haihuwar Is'hak sakamakon fushi da damuwar da saratu ta yi kan samun haihuwar Isma'il[14] a daidai lokacin da rahoton Attaura Hajara ta yi Hijira ne bayan Haihuwar Is'hak[15] Attaura an kawo Rahoto cewa dalilin da ya sanya hijirar Hajara daga Sham zuwa Makka Saratu ce ta ga Isma'il yana cin zalin Is'hak yana takura masa, sai Saratu ta cewa Ibrahim wannan Baiwar Hajara matukar dana yana nan to fa babu rana da danta zai kasance Magajinka, ka kore su daga gidanka[16] kan asasin rahotan da ya zo a Attaura sabanin riwayoyin Muslunci[17] an bayyana cewa Ibrahim bai raka Hajara da `danta ba zuwa Makka su kadai suka tafi[18]
Wafati
Kan asasin abin da aka nakalto Hajara ta rasu[19] tana da shekaru 90 a duniya, sannan bisa abin da aka nakalto daga Imam Sadiƙ (A.S) Isma'il ya binne Hajara a Mahallin Hijru Isma'il, ya dan daga Kabarinta ya dan sanya Katanga kan Kabarin don kada mutane su tattaka Kabarin[20] Kan asasin ba'arin wasu riwayoyi don girmama Kabarinta ne Musulmai lokacin da suke Dawafi suke kewayawa ta geffan Dutsen kuma baya halasta su shiga ciki su taka Kabarinta[21]
Bayanin kula
- ↑ Balami, Tarikhnameh Tabari, 1373, juzu'i na 3, shafi na 503.
- ↑ Ibn Athir, Al-Kamel, 1385 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 101.
- ↑ Ibn Athir, Al-Kamel, 1385 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 100.
- ↑ Ibn Athir, Al-Kamel, 1385 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 101
- ↑ Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, Juzu'i na 7, shafi na 226-229.
- ↑ Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, Juzu'i na 7, shafi na 231-232.
- ↑ Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 7, shafi na 231.
- ↑ Ibn Athir, Al-Kamel, 1385 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 101.
- ↑ Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 288.
- ↑ Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 288.
- ↑ Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 288.
- ↑ Suratul Ibrahim, aya ta 37.
- ↑ Sheikh Sadouq, Ilalul Shara'i, 1385, juzu’i na 2, shafi na 432.
- ↑ Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 288.
- ↑ Kitabu Mukaddas, takwin, 21:9-12 .
- ↑ Kitabu Mukaddas, takwin, 21:9-12
- ↑ Sheikh Sadouq, Ilalul Shara'i, 1385, juzu'i na 2, shafi.432; Qummi, Tafsir Qummi, 1404H, juzu’i na 1, shafi na 60.
- ↑ Kitabu Mukaddas, takwin, 21:9-12
- ↑ Ibn Sa’ad, Tabaqat Al-Kubra, 1410H, juzu’i na 1, shafi na 44.
- ↑ Sheikh Sadouq,Ilalul Shara'i, 1385, juzu’i na 1, shafi na 37.
- ↑ Sheikh Sadouq, Man Laihdara al-Faqih, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 193.
Nassoshi
- Allameh Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Qum, Al-Nashar al-Islami School, bugu na biyar, 1417H.
- Alqur'ani
- Balami, Tarikh Tabari, Mohammad Roshan ya yi bincike, Tehran, Alborz Publications, 1373.
- Ibn Athir, Al-Kamal fi al-Tarikh, Beirut, Dar Sadir - Dar Beirut, 1385H.
- Ibn Saad, Tabaqat al-Kabri, Bincike na Muhammad Abd al-Qadir Atta, Beirut, Darul Katb Al-Elamiya, bugun farko, 1410H/1990 Miladiyya.
- Kitabu Mukaddas.
- Kulaini, Mohammad bin Yaqoob, Al-kafi, Tehran, Islamia, bugu na 4, 1407H.
- Qomi, Ali Ibn Ibrahim, Tafsirin Qami, Tayyab Musawi Al-Jaziari, Qum, Darul Katab, 1404H.
- Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Dalilan Sharia, Qum, Shagon Littafin Davari, 1385/1966 Miladiyya.
- Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Man Laihdara al-Faqih, edita ta Ali Akbar Ghafari, Qum, ofishin da'a na Musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta Qum, 1413 AH.