Suratul Nasi

Daga wikishia
Suratul Nasi

Suratul Nasi (Larabci: سورة الناس) sura ce ta 114 wacce ita ce sura ta karshe a Kur’ani kuma tana daga cikin Surorin da suka sauka a garin Makka, tana cikin Juzu’I 30, Suratul Nasi tana jerin Surori guda hudu da suka fara da Kul an umarci Annabi (S.A.W) da ya nemi tsarin Allah daga sharrin Masu Wasi-wasi, a bara’arin wasu tafsirain Ahlus-Sunna ya zo cewa lokacin da wannan sura ta sauka wani mutum Bayahude ya yiwa Annabi (S.A.W) Sihiri sai Annabi (S.A.W) ya kamu da rashin lafiya, amma bayan Mala’ika Jibrilu ya kawo masa Suratul Falaki da Nasi ya kuma karanta ayoyi kan Annabi (S.A.W) sai ya tashi daga Shimfidar da yake jiyyar ciwo, sai dia cewa Wasu ba’ari daga Malaman Shi’a sun yi suka kan wannan Magana tare da raddi kan cewa Sihiri da Tsafi basa tasiri kan Annabi (S.A.W) Ana kiran Suratul Falaki da Nasa da Ma’uzataini, saboda ana karanta su domin neman tsari da kariya, cikin Falalar Tilawarsu an nakalto cewa duk wanda ya karanta Suratul Falaki da Nasi, daidai yake da wanda ya karantu baki dayan litattafan da aka saukarwa Annabawan Allah, haka kuma an nakalto daga Annabi (S.A.W) surori biyu Falaki da Nasi sun kasane mafi soyuwar Surori a wurin Allah

Gabatarwa

  • Sanya Suna

An sayawa wanna Sura suna Nasi, Nasi yana nufin (Mutane) an kuma ciro wannan suna daga aya ta farko, ana kiran suratul Nasi da Ma’uzataini, ta samu wannan suna ne sakamakon karanta ta da ake domin neman tsari da kariya daga Wasi-wasin Shaidan, haka kuma lokacin da mutum yake jin wani hatsari a wani wuri yana karanta wannan sura domin samun kariya da kubuta, haka ana kiran da Mushakshakiyatu, surori biyu Falaki da Nasi ana kiran su da Mushakshakitaini da Ma’uzataini [1]

  • Jeranta da Mahallin Sauka

Suratul Nasi tana cikin jerin surorin da suka sauka a Makka, sannan cikin jerin sauka tana cikin surori na 21 da suka sauka wurin Annabi (S.A.W) wannan Sura jerin sura ta 114 a tsarin Kur’ani na yanzu [2] kuma tana cikin Juzu’i na 30, Allama Tabataba’i Marubucin littafin Almizan ya tafi kan cewa ta sauka a Madina ne kamar dai suatul Falaki sakamakon dogara da wasu riwayoyi ya tafi kan cewa Suratul Falaki da Suratul Nasi sun sauka tareda juna [3]Jawadi Amoli Malamin tafsiri na Shi’a a wannan zamani ya tafi kan cewa suratul Falaki da suratul Nasi zai iya zama sun sauka a Makka kuma sun sauka a Madina sakamakon kasancewar su tareda Hususiyoyin Makka koma bayan na Madina [4]

Adadin Ayoyi da wasu Hususiyoyi

Suratul Nasi tana Aya 6 Kalmomi 20 Haruffa 78, sannan wannan Sura bisa la’akari da girma tana cikin jerin surori Mufassalat (Masu Gajerun Ayoyi) har ila yau Suratul Nasi tana cikin jerin surori guda hudu da farkonsu ya fara da Kul [5]

Abinda take Tattare da Shi

Cikin suratul Nasi Allah ya umarci Manzonsa da ya nemi tsarin Allah daga sharrin Wasi-wasin Khannasi (Mai Wasi-wasi a Boye) [6]abinda wannan sura ta tattare kai yayi kama da na suratul Falaki, duka su biyun suna Magana kan neman tsari daga sharri da cuta, tareda bambancin da yake cikin Suratul falaki daga nau’uka daban-daban na sharri daka bijiro da su cikinta, amma a suratul Nasi kadai an bijiro da sharrin Mai Wasi-wasi Mai buya (Wasi-wasul Khannasi) [7]

Silsilar Martabobin a Tsarin Samuwa

Jawadi Amoli Mashhurin Malamin tafsirin Shi’a cikin Tafsirinsa kan Surar da maimaicin Kalmar Rabbi yana cewa a duk lokacin da mutum ya samu kansa cikin matsala a farko yana komawa wurin Majibancin lamarinsa yana fakewa da Mai shiryar da shi Shugabansa Mai gudanar da lamurransa (Ubangijhin Mutane) idan matsalarsa bata warware ta wannan hanya sai koma ga Sarkinsa Mamallakinsa Amin Masaratarsa (Mamallakin Mutane) idan Mas’ulai da Daraktoci suka gaza warware matsalar sai ya koma zuwa ga fakewa da Ubangijin Talikai (Abin Bautar Mutane)

Rabe-raben Mutane cikin suratul Nasi

Wasu Ba’arin Malaman tafsiri sun tafi kan cewa Kalmar Nasi (Mutane) da ta zo a farkon suratul Nasi tana nufin dukkanin Mutane, amma wacce ta zo tsakiyar surar

( الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ )

Tana nufin mutane daga Makiya Mutane da Aljanu suke kai hari kan mutum, sannan wacce ta zo kasrhe surar (مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ) Wadanda aka jingina da Aljanu, Mutanen da su a kankin kansu Masu wasi-wasi ne, haka kuma suratul falaki itama tana nufi kan wadannan gabbai uku [8]

Aikin Wasi-Wasul Khannas

Shaik Saduk cikin littafin Amali Saduk ya rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) lokacin da wannan aya (و الذین اذا فعلوا فاحشه او ظلموا انفسهم ذکروا الله فاستغفروا لذنوبهم ) Ta sauka sai Iblis ya je ya Hau saman Dutsen Suwairu [yadasht] da yake Makka ya daga murya da mafi girman sautin Ifiritai (Masu Wasi-wasi da Yaudara) dukkanin Iyalinsa suka taru a gabansa, suka tambaya shi ya kai Babban cikinmu me ya faru ka kira mu? sai yace wannan aya ta sauka wane ne daga cikinsu ya karya tasirinta, sai Ifritu cikin Shaidanu ya mike tsaye yace: ni zan karya tasirinta ta wannan hanya, Shaidan yace: a’a ba zaka iya ba, sai wani Ifiritun daban ya mike tsaye shima ya maimaita abinda na farko ya fada =, shima yace masa ba zai iya ba, sai Wasu-wasul Khannasi ya ce: ka bar wannan aiki a hannuna, sai ya tambaye shi ta wacce hanya zaka karya tasirinta? Yace: zan musu alkawari, zan sa musu buri su aikata zunubi da sabo, idan suka afka cikin aikata zunubi sai na mantar da Istigfari, sai Shaidan yace: eh lallai zaka iya na bar wannan aiki a hannunka har zuwa ranar tashin Kiyama [9] [yadasht]

Sha’anin Sauka

Dangane da sha'anin saukar wannan sura an nakalto wata riwaya daga Ahlus-Sunna wacce Malaman Shi’a basu karbeta ba [10] ya zo cikin littafin Addurul Almansur daya daga cikin Litattafan Ahlus-Sunna cewa wani Bayahude yayi sihiri kan Annabi (S.A.W) sai Jibirilu ya zo wurin Annabi (S.A.W) ya kawo Suratul Falaki da Nasi yace masa wani Bayahude yayi maka Sihiri kuma sihirin da yayi yana cikin wata Rijiya, sai Annabi (S.A.W) ya tura Ali Bn Abi Talib ya dauko Sihirin, sannan ya bada umarni a kwance sihirin a kan kowanne kulli a karanta Falaki da Nasi ana karantawa sai baki dayansa ya kwance ya bude, sai Annabi (S.A.W) ya samu lafiya [11] Allama Tabatabi’i cikin tafsir Almizan ya rubuta cewa babu wani dalili da yake nuna cewa jikin Annabi (S.A.W) ya kamu da ciwo sakamakon tasirin waccan sihiri, bari dai gaskiya magana shine ayoyin Kur’ani sun nuna cewa tsafi da sihiri da kutsen Shaidanu bai iya cutar da lafiya ko Ran Annabi (S.A.W) [12]

Falala da Hususiya

Asalin Makala: Falalolin surori an rawaito daga Annabi (S.A.W) cewa duk wanda ya karanta surori biyu Falaki da Nasi zai kasance kamar wanda ya karanta dukkanin litattafan Annabawa [13] an nakalto daga Imam Bakir (A.S) duk wanda ya karanta Falaki da Nasi da suratul Iklasi cikin sallar Wutri, za ace masa ya kai Bawan Allah lada ya tabbata a kanka an karbi sallarka [14] haka na nakalto daga Annabi (S.A.W) cewa wadannan surori sune mafi soyuwar surori a wurin Allah [15] dangane da hususiya suratul Nasi an nakalto cewa Annabi (S.A.W) kowanne yana karantawa Hassan (A.S) da Husaini (A.S) Falaki da Nasi, [16] a wani Nakali daga Annabi (S.A.W) cewa duk wanda ya Karanta Suratul Tauhid da Falaki da Nasi kowacce kafa goma daidai yake da wanda ya karanta Kur’ani baki dayansa kuma zai fita daga cikin zunubansa kamar misalin Ranar da Mahaifiyarsa ta haife shi idan kuma ya mutu a wannan rana ko wannan dare to ya yi mutuwar shahada [17]

Matani

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ ١ مَلِكِ النَّاسِ ٢ إِلَهِ النَّاسِ ٣ مِنْ شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ ٤ الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ ٥ مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ ٦﴾



(Quran: Suratul Nasi)


Bayanin kula

  1. Daneshnameh Kur'an wa Kur'ani Fajuhi, 1377, juzu'i na 2, 1271-1272
  2. Marafet, Amuzeshi Ulum kur’an, 1371, juzu’i na 2, shafi na 166.
  3. Tabatabaei, Al-Mizan, 1394 AH, juzu'i na 20, shafi na 395.
  4. <a class="external free" href="http://javadi.esra.ir/-/%D8%AA%D9%81%D8%B3%DB%8C%D8%B1-%D8%B3%D9%88%D8%B1%D9%87-%D9%86%D8%A7%D8%B3-1399-01-29">http://javadi.esra.ir/-/%D8%AA%D9%81%D8%B3%DB%8C%D8%B1-%D8%B3%D9%88%D8%B1%D9%87-%D9%86%D8%A7%D8%B3-1399-01-29</a>
  5. Daneshnameh Kur'an wa Kur'ani Fajuhi, 1377, juzu'i na 2, 1271-1272
  6. Tabatabai, Al-Mizan, 1974, juzu'i na 20, shafi na 395.
  7. Makarem Shirazi, Barguzideh Tafsri Namuneh, 1382, juzu'i na 5, shafi na 538 da 632.
  8. <a class="external free" href="http://javadi.esra.ir/-/%D8%AA%D9%81%D8%B3%DB%8C%D8%B1-%D8%B3%D9%88%D8%B1%D9%87-%D9%86%D8%A7%D8%B3-1399-01-29">http://javadi.esra.ir/-/%D8%AA%D9%81%D8%B3%DB%8C%D8%B1-%D8%B3%D9%88%D8%B1%D9%87-%D9%86%D8%A7%D8%B3-1399-01-29</a>
  9. Sheikh Sadouq, Amali, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 551.
  10. Tabatabai, Al-Mizan, 1974, juzu'i na 20, shafi.394.
  11. Siyuti,Addurul Al-Manthor, 1404 AH, juzu'i na 6, shafi na 417.
  12. Tabatabai, Al-Mizan, 1974, juzu'i na 20, shafi.394.
  13. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1415 AH, juzu'i na 10, shafi na 491
  14. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1415 AH, juzu'i na 10, shafi na 491
  15. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 92, shafi na 368.
  16. Daneshnameh Kur'an wa Kur'an Fajuhi, 1377, juzu'i na 2, shafi na 1271-1272.
  17. Aamili Kafami, Balad Al-Amin, shafi na 33.

Nassoshi

  • Alqur'an Alkareem, Muhammad Mehdi Fouladvand, Tehran, Darul Qur'an al-Karim, 1418H/1376H.
  • Daneshnameh Qur'an wA Qur'an Fajuhi, ta kokarin Bahauddin Khorramshahi, juzu'i na 2, Tehran, Dostane-Nahid, 1377.
  • Siyuti, Ad-Durrul Al-Manthor, Qum, Ayatullah Murashi Najafi Public Library, 1404H.
  • Sadouq, Al-Amali, Qum, bugu na Ba'ath, bugu na farko, 1417H.
  • Tabatabaei, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, bugu na biyu, 1974.
  • Tabarsi, Al Bayan Majma, Tehran, Makarantar Kimiyya, bugun farko, 1338.
  • Ameli Kafami, Ibrahim bin Ali, Al-Balad Al-Amin da Al-Dar'a Al-Hussein.
  • Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar Al-Anwar, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, 1403 AH.
  • Marfat, Mohammad Hadi,Amuzeshe Ulmul Kur'an, [ba a buga ba], Cibiyar Buga Cibiyar Farfagandar Musulunci, bugun farko, 1371.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Barguzideh Tafsir Namuneh, Ahmad Ali Babaei, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, 2002.