Abdullahi Jawadi Amoli

Daga wikishia
(an turo daga Jawadi Amoli)

Abdullah Jawadi Amoli, (Larabci: عبد الله جوادي الآملي) an haife shi a shekara ta 1351 bayan hijira masanin falsafa ne, kuma kwararren a ilimin fiƙihu, da tafsirin ƙur'ani, malami a hauzar ƙum, ɗaya daga cikin maraji'an taƙlidi a Shi'a, ya yi karatu a wurin Imam Khomaini da Allama Ɗabaɗaba'i , kuma ya koyar da ilimomi daban-daban kimanin fanni 60, kamar Falsafa da Irfani, da Fiƙihu da Tafsiri a makaratar hauza ta ƙum da Tehran, kuma yana da littafai da dama, waɗanda suka haɗa da: Tafsirul Tasnim da Al-Rahiƙ Al-maktum wanda yake sharhi ne na littafin Al'asfarul Al-rba'a.

Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ya ɗauki nauyin ayyuka da dama, ya kasance memba na majalisar ƙoli ta shari'a, da majalisar kwararru kan kundin tsarin mulki, da ƙungiyar malaman hauza a birnin ƙum, da kuma majalisar kwararrun jagoranci Shekaru saba'inat da tamaninat a ƙarni na 14, kuma shi ne limamin Juma'a na birnin ƙum, ya kuma isar da sakon Imam Khomaini ga Gorbajif a ziyarar da ya kai tsohuwar Tarayyar Sobiyat a shekara ta 1367 hijira shamsi.

Jawadi Amoli ya na bin manhajin hikima Muta'aliya, kuma ya na da ra'ayin fahimtar addini ta hanyar Ulum Al'insaniyya (Social sciences) da kuma Ilimin da ɗan adam yake samu ta hanyar gwaji ko jarrabawa (Ulumin tajribi) kamar ilimin tarihi da Falsafa da yare da sauransu, yana da fatawoyi waɗanda suka sha banban da sauran malamai daga cikin akwai, halascin yin taƙli da mace wanda takai matsayin Ijtihadi da Marja'iyya, da kuma halascin canja halitta da kuma ganin tsarki Ahlul-Kitab wato Yahudawa da kiristoci.

Karatu

An haifi Abdullah Jawadi Amoli a shekara ta 1312 bayan hijira a birnin Amol da ke arewacin ƙasar Iran[1] mahaifinshi ya kasance ɗaya daga cikin malaman addini a garin Amol.[2] ya fara karantun addini a makarantar hauza ta Amol. kuma a cikin shekara biyar ya kammala matakin darussan hauza na Suɗuh, wato adabin larabci, da Manɗiƙ, fiƙihu, Usulul fiƙihi, tafsirin Alkur'ani, da hadisi.[3]

A shekara ta 1329 bayan hijira, ya yi tafiya zuwa babban birnin Tehran, ya ci gaba da karatunshi a makarantar Marawi na tsawon shekaru biyar, a wannan yanayin ne ya halarci darussa a gun Muhammad Taƙiyu Amoli, Abu Al-Hasan Sha'arani, Mahadi Ilahi al-ƙamsha'i da Muhammad Husaini Al-Tuni bayan ilimin fiƙihu da Usul, ya karanta falsafa da sufanci, kuma a lokaci guda ya kasance ya na karatun darussa na hauza,[4] kuma a shekara ta 1334 bayan hijira ya tafi ƙum ya kammala karatunshi na ilimi a hauza a mataki mafi girma a gun malaminshi Ayatullah Burujirdi, Ayatullah Sayyid Muhammad Muhaƙƙiƙ Damad, Mirza Hashim Amoli, Imam Khomaini, da Allama ɗabataba'i.[5]

Koyarwa

Jawadi Amoli ya fara koyar da ilimin hauza tun ya na matashi, a lokacin da yake koyarwa a makarantar hauza ta Tahran,[6] a farkon karni na sha huɗu bayan hijira zuwa yanzu, wato kimanin shekaru sittin, inda ya koyar da darussan hauza daban-daban. darasi na fiƙihu, Falsafa, sufanci, tafsirin Alkur'ani, da sauransu a wannan lokaci ya sami damar koyar da darasin Asfar na Falsafa daurori uku na Mulla Sadra a makarantar hauza ta ƙum..[7]

Haka nan kuma ya fara ba da darussan tafsiri a shekara ta 1355H,[8] yana yin darasin tafsiri da fiƙihu a masallacin A'azam a birnin ƙum.[9]

Marja'iyya

An bude ofisoshi dama na Marja'in addini Ayatullah Jawadi Amoli a birnin ƙum, Tehran, Al-Rayyu, Tabriz, Urmia, Zanjan, Amul, da Shiraz,[10] kuma ya buga littafin Istifita'at da Risala amalyya.

Tunani

Akwai wasu daga cikin ɗaliban Jawadi Amoli waɗanda suke ganin cewa ra'ayin malaminsu ya ta'allaƙa da hikima Muta'aliya, don haka Amoli ya tafi kan dacewa tsakanin hankali da ilimi da Alkur'ani, kuma ba ya ganin iliminsu (wato: hankali, ilimi, da Kur'ani) ba su dace da ɗan adam ba.[11] a mahangarshi Hankali ba ya tsayawa a gaban addini, kai hankali shi ne fitilar addini, kuma ana iya amfani da hankali wajen fayyace da bayyana koyarwa irin ta addini da koyarwar da kyawawan ɗabi'u, da hukunce-hukuncen shari'a, da mas'alolin dokoki na shari'a.[12]

Ilimin Addini

Jawadi Amoli yana da cikakken imani da gamsuwa da ilimin addini, kuma hankali a gunsa ba wai kawai tunani yake nufi ba kuma ƙudirar fahimtar abubuwa ba, a a hanakali ya haɗa da amfani da shi a rayuwar mu ta yau da kullin wajan fahimtar dai-dai da kuma fahimtar abin da ba dai-dai ba, sabo da haka ilimin Tajriba (gwaji) ya ƙunshi ilimin karantar duniya da ulum Insaniya.[13] a ra'ayinshi ilimi a kankin kanshi bai saɓa da addini ba.[14] shi ilimin Tajribi ya koya mana sanin ɗabi'ar duniya, kuma kasantuwar ita wannan duniyar Allah ne ya halicceta, to duk wannan ilimomi su na nuna mana ayyukan Allah maɗaukaki, sabo da haka waɗannan ilimomi ana la'akari da su a matsayin ilimin addini.[15] sabo da duk abin da ya gabata zamu kai ga wannan sakamakon cewa duk wani ilimi idan na gaskiya ne, to babu yadda za ayi ya kai mutum ga yin Ilhadi ko kuma wani abin da ba addini ba.[16]

Ra'ayi Ko Tinaninshi A Siyasa

Jawadi Amoli ana daukarsa ɗaya daga cikin waɗanda suka yi imani da wilayatul faƙihu, kuma ya gabatar da hujjoji guda uku da suke tabbatar da hakan a cikin littafinshi mai suna Wilayatul Faƙih, Wilayatul Faƙih da Adalci, wadanda suka haɗa da dalilai na zallan hankali, da kuma hankali haɗe da nassi.[17] (wato ayoyi da ruwaya) ko kuma abin da ya shafi ruwaya da ayoyi kaɗai.[18] jihadi.[19] hukunce-hukunce na Haddi da hukunce-hukunce na Ta'azir (wanda alƙali ne yake faɗar yadda za'ayi).[20] kuma akwai dokokin dukiya kamar Anfal da Khumusi[21] a Musulunci, ba za a iya aiwatar da su ba a zamanin Gaiba [(akuwar imami) , sai ta hanyar gudanarwa ta malaman fiƙihu waɗanda suka cika sharuɗɗa.[21] kai barin al'ummar musulmi a zamanin fakuwa ba tare da wani majiɓinci ba wani abu ne da hankali bazai yarda da shi ba, don haka malaman fiƙihu waɗanda suka cika sharuɗɗa a wannan zamani su halifofi ne na ma'asumai, kuma su ne suke rike da shugabanci da jagorancin al'ummar musulmi.[22][23]

Fatawoyin Da Suka Keɓanta Da Shi

A cikin littafinshi Taudihul Masa'il, sabanin sauran littafan da aka rubuta da wannan salo, Jawadi Amoli ya taɓo hukunce-hukuncen mazhabobi [Firaƙ], zabe, da kayata adon rubutun Alkur'ani, hakkin mallaka da yaɗa litattafai, da wakiltar wasu mutane kan cin bashi da biyan bashi a yayin da farashi yake hau-hawa da kuma bayanin likitoci kan gawa bayan mutuwa,da canjin halitta ta'aziyya ko zaman makoki, da kuma hukunce-hukuncen kai ɗauki yayin annoba da hukunce-hukuncen Ahlul-Kitab.[24]

Halaccin koyi da mace daga mujtahida mafi ilimi a cikin mata,[25] magana kan halaccin canjin jinsi.[26] halaccin bugu da tarjama yaɗawa bayan tarjama, da samar da bashi irin na intanet.[27] duk waɗannan su na daga cikin fatawowin shi na musamman.

Ayyukan Siyasa Da Zamantakewa

Isar wasikar Imam Khomaini ga Gorbaceb ta hannun Ayatullahi Jawadi Amoli

Duk da cewa Jawadi Amoli ya kasance yana da hannu a cikin ayyukan ilimi fiye da sauran ayyuka, amma ya kasance yana da rawar da ya ketakawa a siyasa da zamantakewa kafin nasarar juyin juya halin Musulunci da kuma bayan juyin juya halin Musulunci, yana ɗaya daga cikin masu yaɗa ra'ayin Imam Kwamaini sau da yawa ana hana shi yin magana, kuma aka kama shi saboda haka.[28] Daga cikin ayyukan da ya yi bayan juyin juya halin Musulunci har da kasancewarshi mamba a majalisar koli ta shari'a ta Iran,[29] ya kasance yana shirya jerin dokokin shari'a,[30] kuma memba na majalisar kwararru ta jagoranci a zaman majalisa sau biyu, kuma mamba a majalisar dokokin Iran,kuma ɗan kungiyar malaman makarantun hauza a birnin ƙum..[31]

A shekara ta 1376 bayan jawabin Ayatullah Muntazari Jawadi Amoli ya halarci taron daliban ilmin addini da suka yi zanga-zangar adawa da Muntazari a babban masallacin juma'a[32] kuma a shekara ta 1378 bayan hijirar Annabi(S.A.W). Domin nuna rashin amincewa da buga hotunan batanci ga Misbahu Yazdi, wannan ya faru ne a shekara ta 1378 bayan hijirar (S.A.W) a lokacin da ya sukar manufofin al'adun ƙasar tare da gabatar da jawabi ga taron masu zanga-zangar.[33]

Jawad Al-Amoli ya kasance ɗaya daga cikin limaman Juma'a a birnin ƙum a shekara ta saba'in da tamanin a ƙarni na sha hudu bayan hijira Shamsi.[34] kuma ya yi murabus daga aikinshi a shekara ta 1388 bayan hijira Shamsiyya.[35]

Tafiya Zuwa Tarayyar Sobiyat Da Amurka

Jawadi Amoli ya tashi ne a shekara ta 1367 bayan hijira, tare da rakiyar Muhammad Jawad Al-larijani da Mardiya Hudid haji (Dabbag)[36] zuwa Tarayyar Sobiyat domin isar da sakon Imam Kumaini ga tsohon shugaban Tarayyar Sobiyat Mika'il Gorbajab, sannan ya karanta sakon zuwa ga Tarayyar Sobiyat,[37] Bayan wannan ganawa, Amoli ya rubuta bayanin wasiƙar Imam Kumaini, kuma ya kira ta da "Kira na Tauhidi", sannan ya aika da ita zuwa ga wasu hukumomin addini a kasashen turawa.[38] shekara ta 2000 miladiya ya tafi zuwa birnin New York domin karanta wasikar jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Aytullahi Khomaini na taro domin haɗin kai na addinai.[39]

Mu'assar Isra Da Mu'assar Imam Hasan Askari (A.S)

Jawadi Amoli shi ne ke kula da mu'assar Al-isra ta ƙasa da ƙasa ta ilimomi da aka yi wahayin shi, wadda daya ce daga cikin cibiyoyi na ilimi a birnin ƙum, manufarta ita ce yaɗa ilimomin addinin Musulinci a mahangarshi, da kuma horar da masu bincike a fanni na ilimin addinin musulunci.[40] kuma yana kula da mu'assar Imam Hassan Al-Askari (A.S) sabo da koyar da ilimi mai zurfi a makarantar hauza, wadda aka kafa a shekara ta 1387 bayan hijira a birnin Amol a arewacin kasar Iran.[41]

Rubuce-rubuce

Tushen kasida: Fihirisar Adadin Litattafan Abdulahi Jawadi Amoli

Jawadi Amoli ya yi rubutu a fage daban-daban da suka hada da: fiƙihu, Tafsiri, Falsafa da Hadisi, Littafin tafsir mai suna Tasnim wanda shi ne sakamakon darasinshi na tafsiri. Mai mujalladi 45 ɗayan littafinshi mai suna Rahiƙil Maktum wanda ya kasance sakamakon karantarwarshi ta littafin Arba'a Asfar wanda Mulla Sadra ya rubuta wanda ya fito a watan Iraniyawa na Shahribar a shekar ta 1397 hijira.[42]

Daga cikin sauran littafanshi akwai: Mafatihul Hayat, Zan dar Ayineyi Jamal wa Jalal (mace a cikin Madubin Kyau da Girmama), Adabu Fanaye Muƙaraban (sharhi ziyaratu Jami'a alkabira), da littafin Taudihil Masa'il.

Bayanin kula

  1. «السيرة الذاتية لسماحة آية الله جوادي الآملي من لسانه، الموقع الإعلامي للحوزة العلمية، 18 تیر 1385ش، آخر مراجعة في 25 اردیبهشت 1397.
  2. «السيرة الذاتية لسماحة آية الله جوادي الآملي من لسانه، الموقع الإعلامي للحوزة العلمية، 18 تیر 1385ش، آخر مراجعة في 25 اردیبهشت 1397.
  3. Bandali, Mehr Estad, 1391 AH, shafi na 37.
  4. "الحياة العلمية والقرآنية لآية الله جوادي الآملي"، موقع مؤسسة الإسراء الدولية للعلوم الوحيانية، آخر مراجعة في 29 اردیبهشت 1397.
  5. "الحياة العلمية والقرآنية لآية الله جوادي الآملي"، موقع مؤسسة الإسراء الدولية للعلوم الوحيانية، آخر مراجعة في 29 اردیبهشت 1397.
  6. "الحياة العلمية والقرآنية لآية الله جوادي الآملي"، موقع مؤسسة الإسراء الدولية للعلوم الوحيانية، آخر مراجعة في 29 اردیبهشت 1397.
  7. «السيرة العلمية والقرآنية لآية الله جوادي الآملي»، موقع مؤسسة الإسراء الدولية للعلوم الوحيانية، آخر مراجعة في 29 اردیبهشت 1397.
  8. "الحياة العلمية والقرآنية لآية الله جوادي الآملي"، موقع مؤسسة الإسراء الدولية للعلوم الوحيانية، آخر مراجعة في 29 اردیبهشت 1397.
  9. «برنامه دروس آیت‌الله جوادی آملی»، الموقع الإعلامي للحوزة العلمية، 30 شهریور 1389، آخر مراجعة في 29 اردیبهشت 1397.
  10. «دفاتر معظم‌له»، موقع مؤسسة الإسراء الدولية للعلوم الوحيانية، آخر مراجعة في 6 خرداد 1397.
  11. مصطفی‌پور، «منظومه فکری آیت الله جوادی آملی»، موقع مركز دراسات معارج، آخر مراجعة 25 تیر 1396ش.
  12. Vaezi, "Ilimu dini az manzare Ayatullah Javadi Amoli", shafi na 10.
  13. Waezi, "Ilimu dini az manzare Ayatullah Javadi Amoli", shafi na 11 da 12.
  14. jawadi Amoli, "Ilimu dini az manzare Ayatullah Javadi Amoli", shafi na 11 da 15.
  15. Waezi, "Ilimu dini az manzare Ayatullah Javadi Amoli", shafi na 16
  16. Waezi, "Ilimu dini az manzare Ayatullah Javadi Amoli", shafi na 16
  17. Javadi Amoli, Velayat Faqih, 1378, shafi 150-184
  18. Seeb Javadi Amoli, Velayat al-Faqih, shafi na 168.
  19. Javadi Amoli, Velayat Faqih, 1378, shafi na 168.
  20. Javadi Amoli, Velayat Faqih, 1378, shafi na 170.
  21. Javadi Amoli, Velayat Faqih, 1378, shafi na 168.
  22. Javadi Amoli, Velayat Faqih, 1378, shafi na 168.
  23. Sahifatu Jamhouri Eslami, 12 Mehr 1395, shafi na 12
  24. Sahifa Jamhouri Eslami, 12 Mehr 1395, shafi na 12.
  25. Javadi Amoli, Risaleh ilmiyeh, juzu'i na 1, shafi na 22.
  26. Javadi Amoli, Risaleh ilmiyeh, juzu'i na 1, shafi na 401.
  27. Javadi Amoli, Risaleh ilmiyeh, juzu'i na 1, shafi na 390.
  28. Bandali, Mehr Estad, Nuskha electronic, 1391 AH, shafi na 191 da 192.
  29. Bandali, Mehr Estad, Nuskha electronic, 1391 AH, shafi na 201.
  30. Bandali, Mehr Estad, Nuskha electronic, 1391 AH, shafi na 204.
  31. مدرسی، «تاریخچه زندگی آیت‌الله شیخ عبدالله جوادی آملی» (مختصر عن السيرة الذاتية لآية الله الشيخ عبد الله جوادي الآملي) .
  32. مدرسی، «تاریخچه زندگی آیت‌الله شیخ عبدالله جوادی آملی» (مختصر عن السيرة الذاتية لآية الله الشيخ عبد الله جوادي الآملي) .
  33. مدرسی، «تاریخچه زندگی آیت‌الله شیخ عبدالله جوادی آملی» (مختصر عن السيرة الذاتية لآية الله الشيخ عبد الله جوادي الآملي) .
  34. ينظر «خطبه‌های نماز جمعه»، موقع بنیاد بین المللی علوم وحیانی اسراء، آخر مراجعة في 6 خرداد 1397.
  35. «آخرین خطبه نماز جمعه آیت‌الله جوادی آملی قرائت شد»، موقع وكالة أنباء فارس، 6 آذر 1388، آخر مراجعة في 24 تیر 1396.
  36. «قضية رسالة الإمام إلى غورباجف بقلم سماحة آية الله جوادي الآملي»، الموقع الإعلامي للحوزة العلمية، 12 بهمن 1395، آخر مراجعة في 1 خرداد 1397.
  37. مدرسی، «تاریخچه زندگی آیت‌الله شیخ عبدالله جوادی آملی» (مختصر عن السيرة الذاتية لآية الله الشيخ عبد الله جوادي الآملي) .
  38. مدرسی، «تاریخچه زندگی آیت‌الله شیخ عبدالله جوادی آملی» (مختصر عن السيرة الذاتية لآية الله الشيخ عبد الله جوادي الآملي) .
  39. مدرسی، «تاریخچه زندگی آیت‌الله شیخ عبدالله جوادی آملی» (مختصر عن السيرة الذاتية لآية الله الشيخ عبد الله جوادي الآملي) .
  40. «اساسنامه بنیاد بین المللی علوم وحیانی اسراء»، موقع مرکز پژوهش‌های مجلس، 24 آذر 1392، آخر مراجعة في 26 تیر 1396.
  41. «نیم‌نگاهی به بنیاد بین‌المللی علوم وحیانی اِسراء»، افق حوزه، ص12.
  42. «إزاحة الستار عن مجلدات 17-20 لكتاب الرحيق المختوم في المؤتمر الدولي لتنامي وتطور العلوم على ضوء العقلانية الوحيانية»، موقع بنیاد بین المللی علوم وحیانی اسراء، 15 اردیبهشت 1397، آخر مراجعة في 29 اردیبهشت 1397.

Nassoshi

«آخرین خطبه نماز جمعه آیت‌الله جوادی آملی قرائت شد»، موقع وكالة أنباء فارس، 6 آذر 1388، آخر مراجعة في 24 تیر 1396..

Vaezi, Ahmed, "Ilimu dini az manzare Ayatullah Javadi Amoli", Hanyar Ilimin Dan Adam, No. 54, 2017.