Shekara Ta 10 Hijira
Shekara 11 Hijira Ƙamari Shekara 9 Hijira Ƙamari | |
| 631 da 632m | |
|---|---|
| Imamanci | |
| Annabtar Sayyidina Muhammad (S.A.W) | |
| Hukumomin ƙasashen Muslunci | |
| Muhammad Bin Abdullah (S.A.W) a Madina | (Hukuma: 1-11 hijira) |
| Muhimman abubuwan da suka faru | |
| Hajjin ƙarshe da Annabi (S.A.W) ya yi | |
| Ayyana halifan Annabi (S.A.W) | |
| Saukar Ayar Tablig | |
| Saukar Ayar Ikmal | |
| Kyautar Zobe da Imam Ali (A.S) ya yi | |
| Haihuwa | |
| Muhammad Bin Abubakar | |
| Wafati/Shahada | |
| Ibrahim Ɗan Manzon Allah | |
Shekara ta 10 hijira, (Larabci: سنة 10 للهجرة،) ita ce shekara ta goma a lissafin hijira ƙamari. Rana ta farko ta kasance 1 Muharram daidai da Seshanbe 22 ga watan Farwardin shekara 10 kalandar Farsi kuma daidai da 12 Afrilu 631 miladiyya. Rana ta ƙarshe ta kasance 30 Zil-Hijja, daidai da Shanbe 11 Farwardin shekara ta 11 kalandar Farsi, wanda ya yi daidai da 31 Maris 632 miladiyya.[1]
Hajjin bankwana, Waƙi'ar Ghadir da bayanin da Annabi Akram (S.A.W) ya yi ƙarara a fili game da halifancin Imam (A.S), Mubahalar Annabi (S.A.W) tare da Kiristocin Najran da kuma Sariyyatu Imam Ali (A.S) a Yaman da musluntar mutanen wannan yanki suna cikin jumlar abubuwan da suka faru a wannan shekara.
Muhimman Abubuwan Da Suka Faru
- 25 Shawwal. Kusufin Rana da ya faru rana ɗaya da rasuwar Ibrahim Ɗan Manzon Allah (27 Janairu shekara 632)[2]
- Hajjin bankwana da Annabi (S.A.W) ya yi a watan Zil-Hijja.[3]
- Waƙi'ar Ghadir da ayyana halifan Annabi (S.A.W).[4]
- Saukar ayar tablig a hajjin bankwana (18 Zil-Hijja)[5]
- Saukar ayar ikmal a hajjin bankwana (18 Zil-Hijja).[6]
- Musluntar Jarud Bin Mu'alla[7]
- Mubahalar Annabi tare da Kiristocin Najran[8] bisa ra'ayin masshur malaman tarihi (A wani ra'ayin kuma da bai shahara ya faru a shekara ta 9 hijira)[9]
- Annabi (S.A.W) ya aika da Khalid Bin Walid tare da mutane 400 zuwa wurin Bani Haris/Balharis Bin Ka'ab a Najran da Yaman domin kiransu zuwa Muslunci.[10]
- Sariyyatu Imam Ali a Yaman da musluntar ƙabilar Hamdan[11] da Muzhij.[12]
- Naɗa Khalid Bin Sa'id da Annabi (S.A.W) yankin da yake tsakanin Najran da Zubaidu domin shugabanci.[13]
- Aswad Ansi a Yaman ya yi da'awar annabta da bore.[14]
- Kyautar zobe da Imam Ali (A.S) ya yi a halin ruku'u a 24 Zil-Hijja a wani ƙaulin.[15]
- Zuwan wasu adadin wakilan ƙabilu daban-daban Madina domin karɓar Muslunci.[16]
Haihuwa
Muhammad Bin Abubakar daga cikin na kusa-kusa a sahabban Imam Ali (A.S).[17]
Wafati
- Ibrahim Ɗan Manzon Allah (S.A.W) a 18 Rajab.[18]
- Abdu Amru Bin Saifi baban Hanzalatu Bin Abi Amir wanda ya kafa masallacin Dhirar.[19]
Bayanin kula
- ↑ سایت تبدیل تاریخ هجری.
- ↑ «Solar Eclipses of Historical Interest»،Shafin NASA.
- ↑ Waqidi, Al-Maghazi, 1966, juzu'i. 3, shafi na 1088-1089; Tabari, Tarikh Tabari, 1387 AH, juzu'i. 3, shafi. 148; Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1410H, juzu’i. 2, shafi. 131.
- ↑ Yaqubi, Tarikh Yaqubi, Dar Sadr, juzu'i. 2, shafi. 112; Tabarsi, Al-Ihtijaj, 1403 AH, juzu'i. 1, shafi. 56.
- ↑ Qomi, Tafsir al-Qomi, 1412 AH, juzu'i. 1, shafi. 179; Ayyashi, Tafsir al-Ayyashi, 1380 AH, juzu'i. 1, shafi. 332.
- ↑ Amini, Al-Ghadir, 1416 AH, juzu'i. 1, shafi na 447 zuwa 456; Hosseini Milani, Nafhat al-Azhar, 1423 AH, juzu'i. 8, shafi. 261.
- ↑ Tabari, Tarihin Al’umam Wa Alk-muluk, 1387H, juzu'i. 3, shafi. 136.
- ↑ Tabari, Tarihin Al’umam Wa Alk-muluk, 1387H, juzu'i. 3, shafi. 139.
- ↑ Duba Mohammadi Rayshahri, Farhangenameh Mubahele, 2016, shafi na 83-87.
- ↑ Waqidi, Al-Maghazi, 1966, juzu'i na 3, shafi na 883-884; Tabari, Tarikh al-Umam Wa al-Muluk, 1387 AH, juzu'i na 3, shafi na 128-126.
- ↑ Tabari, Tarikh Tabari, 1387 AH, vol. 3, shafi na 131-132; Masoudi, Al-Tanbih wa al-Ishraf, Alkahira, shafi. 238.
- ↑ Ibn Juzi, al-Muntazem, 1412 AH, juzu'i na 4, shafi na 5.
- ↑ Ibn Athir, Al-Kamil fi al-Tarikh, 1385 AH, Juzu'i. 2, shafi. 336.
- ↑ Duba Ibn Athir, Al-Kamil fi al-Tarikh, 1385H, juzu'i. 2, shafi. 337.
- ↑ Sheikh Mufid, Masar al-Shi'ah, 1414 AH, shafi. 41.
- ↑ Tabari, Tarikhul Al’umam Wal Muluk, 1387H, juzu’i. 3, shafi na 130-145.
- ↑ Ibn Athir, Usdul al-Ghabah, 1409 AH, juzu'i. 4, shafi. 326.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1418H, juzu’i. 1, shafi. 115; Balazuri, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 451.
- ↑ Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, 1383H, juzu'i na 2, shafi na 424.
Nassoshi
- Ibn Athir, Ali bn Abi al-Karam, Al-Kamil fi al-Tarikh, Beirut, Dar Sader-Dar Beirut, 1385H.
- Ibn Athir, Ali ibn Muhammad, Asad al-Ghabeh, Beirut, Darul Fikr, 1409H.
- Ibn Jawzi, Abd al-Rahman bn Ali bn Muhammad, Al-Muntazem fi al-Tarikh al-Umam wa al-Muluk, wanda Muhammad Abdulkadir Atta suka yi bincike da Mustafa Abdulqadir Atta, Beirut, Darul Kutb al-Ilmiyah, 1412 AH.
- Ibn Sa’d, Muhammad bn Sa’d, Al-Tabaqat al-Kubra, Muhammad Abdulqadir Atta, Beirut, Darul Kutb al-Ilmiyah ya yi bincike, 1410H.
- Ibn Hisham, Al-Sirat al-Nabawiyya, Muhammad Muhyiddin Abdul Hamid, Alkahira, 1383H ya yi bincike.
- Abu al-Futuh Razi, Husayn bn Ali, Tafsir Rawd al-Jinan wa Ruh al-jinan, Abu al-Hasan Sha’rani da Ali Akbar Ghaffari suka yi bincike, Tehran, 1382-1387 Hijira.
- Amini, Abdul Hussein, Al-Ghadir Fil KItabi Was Sunnah Wal Adab, Tehran, Bina, 1366.
- Baladzuri, Ahmad bin Yahya, Ansab al-Ashraf, Beirut, Darul Fikr, 1417 Hijira.
- Husayni Milani, Ali, Nafhat al-AzharFi Khulasatil Aƙabatil Anwar. Qum, Cibiyar Bincike da Fassara da Bugawa Alaa, 1423H.
- Dhahabi, Muhammad bin Ahmad, Tarik Islam Wa Wafayatul Mashahir Wal A'alam, Beirut, Omar Abdul Salam Tadmur, 1417H.
- Sheikh Mufid, Muhammad bin Muhammad, Masarush Shi'a, Beirut, Darul Mufid, 1414H.
- Tabarsi, Ahmad bin Ali, Al-Ihtijaj, Mashhad, Al-Murtaza Publishing, bugun farko, 1403H.
- Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh Al'umam Wa Al-muluk, Beirut, Darul-Turat, 1387H.
- Ayyashi, Muhammad bn Masud, Tafsir al-Ayyashi, bugun Hisham Rasuli Mahallati, Tehran, Al-Muktab al-Islamiyyah, 1380H.
- Qummi, Ali ibn Ibrahim, Tafsir Qummi, Beirut, Al-alami Press Foundation, 1412 AH.
- Kulayni, Muhammad bn Yaqub, Al-Kafi, bugun Ali Akbar Ghaffari, Beirut, Darul Ta'rif, 1401H.
- Mas'udi, Ali bn al-Hussein, Al-Tanbiy wa al-Ashraf', edited by Abdullah Ismail al-Sawi, Cairo, Dar al-Sawi, Beta.
- Waqidi, Muhammad ibn Omar, Kitab al-Maghazi, Marsden Jones Publishing, London, 1966 AH.