Ibrahim Ɗan Manzon Allah
Ƙabarin Ibrahim a maƙabartar baƙi'a | |
| Cikakken Suna | Ibrahim Bin Muhammad |
|---|---|
| Ranar haihuwa | Zil-Hjja shekara ta 8 hijira |
| Wurin haihuwa | Madina |
| Nasaba/Ƙabila | Ƙuraishawa |
| Fitattun dangi | Sayyidina Muhammad (S.A.W)-Mariya Ƙibɗiyya |
| Tarihin rasuwa | Shekara ta 10 hijira |
| Ƙabari | Baƙi'a |
| Dalilin shahara | Kasancewa ɗan Manzon Allah |
Ibrahim (Larabci: ابراهيم بن محمد ص) ɗan Annabin Muslunci (S.A.W) tare da matarsa Mariya Ƙibɗiyya, an haifi Ibrahim shekara 8 hijira ya rasu bayan watanni 18 da haihuwa, haƙiƙa haihuwarsa ta janyo farin ciki ga Annabi (S.AW), ya kuma shirya masa bikin yankan aƙiƙa.
A ranar da Ibrahim ya rasu Rana ta yi kusufi, sai dai cewa Annabi (S.A.W) ya nesanta tasirantuwar kusufin Rana da rasuwar ɗansa Ibrahim, ya bayyana cewa kusufin Rana al'amari ne na ɗabi'ar halitta, an binne Ibrahim a maƙabartar baƙi'a
Annabi (S.A.W) ya yi kuka kan mutuwar ɗansa sannan ya karanta ayar istirja'i. Malaman fiƙihu sun yi amfani da kukan da Annabi ya yi a lokacin makokin ɗansa kan halascin yin kuka kan mamaci.
Haihuwar Ibrahim
Ibrahim ya kasance ɗan manzon Allah (S.A.W) tare da Mariya Ƙibɗiyya[1] wanda aka haife shi a Madina watan Zil-Hijja shekara ta 8 hijira.[2] Annabi (S.A.W) ya ce: Na sa masa sunan babana Ibrahim[3] A rana ta bakwai da haihuwarsa, Annabi ya yanka masa aƙiƙa, ya aske gashin kansa ya auna nauyin gashin da azurfa ya ba da ita sadaka ga talakawa.[4]
Haihuwar Ibrahim ya sanya Annabi (S.A.W) farin ciki sosan gaske[5] Jabra'il ya kira Annabi da laƙabin Aba Ibrahim.[6] Annabi (SAW) ya ambaci kamannin dawannan yaro yake yi da shi[7]
Ungozoma Da Mai Renon Yaro
Bisa rahotannin litattafan tarihi, Salma hadimar Annabi ce ta yi wa Ibrahim Ungozoma, Abu Rafi'i, shi ne ya isar da labarin haihuwar Ibrahim ga Annabi, sai Annabi ya masa kyautar bawa.[8] Bayan haihuwarsa, matan mutanen Madina sun yi sauri sun zo neman shayar da shi nono, amma daga ƙarshe Annabi (S.A.W) ya zaɓi Ummu Burda Ƴar Munzir Bin Zaidi matsayin wace za ta reni Ibrahim.[9]
Rasuwa
Bisa rahotannin tarihi, a goman ƙarshen watan Rabi'ul Awwal shekara ta 10 hijira, Ibrahim ya rasu yana da watanni 16 hijira ƙamari.[10] A wani naƙalin an ce ya rasu yana da watanni 18[11] A naƙali na uku kuma an ce ya rasu yana da shekara 1 da watanni 2 da kwanaki 8.[12]
Bisa abin shafin yanar gizo na hukumar "NASA" suka fitar game da kisfewar Rana da ya faru a tarihi, kisfewar Rana da ya faru lokaci ɗaya da rasuwar Ibrahim, ya kasance 27 Janairu shekarar 632 miladiyya wanda ya yi daidai da 25 Shawal shekara ta 10 hijira ƙamari.[13]
An binne Ibrahim a maƙabartar Baƙi'a kusa da ƙabarin Usman Bin Maz'un (Rasuwa: 2 hijira).[14] Annabin Muslunci (S.A.W) ya sanya wani dutse kan ƙabarinsa ya kuma yayyafa masa ruwa.[15]
Riwayar Ibn Shahre Ashub
Bisa wata riwaya da Ibn Shahre Ashub ya kawo a cikin littafin Manaƙib daga Ibn Abbas, wata rana Annabi (S.A.W) a daidai lokacin da ya rungume ɗansa Ibrahim da jikansa Husaini (A.S), sai Jabra'il ya sauko ya kawo masa saƙon Allah cewa: Allah ya isar da gaisuwa yana kuma cewa: ba zaka haɗa biyun ba dole ne ka fanshi ɗaya da guda ɗaya, sain Annabi (S.A.W) ya zaɓi Imam Husaini (A.S) ya yi bayani kan dalilin zaɓarsa kamar haka: "Na rinjayar da damuwata kan mutuwar Ibrahim kan damuwar da Faɗima da Ali za su yi kan mutuwar Husaini" kan asasin wannan riwaya, an ce bayan kwanaki uku da faruwar wannan al'amari sai Ibrahim ya rasu.[16]
Martanin Annabi (S.A.W) Game da Wafatin Ibrahim
Bayan rasuwar Ibrahim, Annabi ya yi matuƙar baƙin ciki ya yi kuka ya ce: "Idanu suna kuka zuciya na baƙin ciki, amma ba za mu furta kalmomin da za su fusata Allah ba"[17] Haka kuma a cikin wata riwaya daban ya zo cewa Annabi (S.A.W) ya tsaya kan wani dutse cikin tsananin baƙin ciki ya ce: Da ace abin da ya sauka kanmu zai sauka kanka da ya murƙusheka. Amma mu kamar yadda Allah ya faɗa, mu ma haka za mu maimaita: Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, walhamdu lilla rabbil alamin.[18]
Martanin Annabi Madogara Ce Kan Halascin Makoki
Malaman fiƙihu tare da jingina da kukan da Annabi ya yi cikin makokin Ibrahim, sun halasta yin kuka ga mamaci. A cewar Sahibul Jawahir (Rasuwa: 1266 hijira) riwayoyi masu yawa suna jaddada cewa kuka da waƙa ta baƙin ciki ta halasta kan mamata, daga jumla akwai riwayar da take hakaito kukan da Annabi (S.A.W) ya yi kan rasuwar ɗansa Ibrahim.[19]
Kusufi A Ranar Wafatin Ibrahim
A ranar da Ibrahim ya rasu, lokaci ɗaya da mutuwarsa Rana ta yi kusufi, ba'arin mutane sun danganta wannan al'amari da rasuwar Ibrahim ɗan Annabi (S.A.W), sai dai kuma Annabi (S.A.W) ya yi watsi da wannan da'awa ta su yana mai cewa: "Rana da Wata alamomi ne guda biyu na Allah ba sa kisfewa saboda mutuwa ko rayuwar wani mutum."[20] A cewar Murtada Muɗahhari haƙiƙa Annabi baya son amfana da jahlici da rashin ilimin mutane cikin cimma haduffansa, bari dai shi ya kasance ne yana sa'ayi da ƙoƙarin ɗaukaka da haɓɓaka wayewa da basirar mutane, yana mai shiryar da su hanyar ilimi da ma'arifa.[21]
Ziyarar Ibrahim Ɗan Manzon Allah
Ziyarar Ibrahim da ake karantawa ta zo cikin littafin Mafatihul Al-Jinan.[22]
Ku Duba
Bayanin kula
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1418H, juzu’i. 1, shafi. 200.
- ↑ Ayati, Cekide Tarikh Payambare Islam, 1378, shafi. 215.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1418H, juzu’i. 1, shafi. 108.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1418H, juzu’i. 1, shafi. 107.
- ↑ Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 450.
- ↑ Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 450.
- ↑ Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 450.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1418H, juzu’i. 1, shafi. 107; juzu'i. 8, shafi. 212.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1418H, juzu’i. 1, shafi. 108.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1418H, juzu’i. 1, shafi. 115; Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 451.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1418H, juzu’i. 1, shafi. 115; Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 450.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1418H, juzu’i. 1, shafi. 115; Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 451.
- ↑ «Solar Eclipses of Historical Interest»، NASA Website.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1418H, juzu’i. 1, shafi. 115; Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 451.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1418H, juzu’i. 1, shafi. 115; Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 451.
- ↑ Ibnshahrashob, al-Manaqib, 1379 AH, juzu'i na 4, shafi na 81.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1363 AH, juzu'i. 79, shafi. 91; Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1418H, juzu’i. 1, shafi. 114.
- ↑ Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 452.
- ↑ Najafi, Jawaher al-Kalam, 1404 AH, juzu'i. 4, shafi na 264-265.
- ↑ Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 452; Majlisi, Bihar al-Anwar, 1363 AH, juzu'i. 79, shafi. 91.
- ↑ Motahari, Majmu'eh Asare Shahid Motahari, 2011, juzu'i. 16, shafi. 109.
- ↑ Qommi, Mafatihul al-Jinan, 2007, shafi na 455-457.
Nassoshi
- Ayati, Mohammad Ibrahim, CekideTarikh Payambare Islam, Mashhad, Astan Quds Razavi Islamic Research Foundation, 1378.
- Ibn Saad, Al-Tabaqat al-Kubra, Beirut, Darul Kutub al-Ilmiyah, bugu na biyu, 1418H.
- Ibn Shahr Ashub, Mohammad bin Ali, Manaqib, Qum, Wallafar Allamah, 1379H.
- Balazari, Ahmad bin Yahya, Ansab al-Ashraf, Beirut, Darul Fikr, bugu na daya, 1417H.
- Dar Tawaf Al-Dil, Cibiyar Nazarin Aikin Hajji, Buga Mashaar.
- Qummi, Abbas, Mafatihul al-Jinan, 2007 AH, Tehran, Mashaar.
- Majlisi, Mohammad Baqir, Bihar al-Anwar, Tehran, bugun Islamiya, bugu na biyu, 1363H.
- Motaheri, Morteza, Majmu'eh Asare Ustad Shahid Motaheri, Tehran da Qum, Bugawar Sadra, 1391H.
- Najafi, Muhammad Hassan, Jawahirul Al-kalam Fi Sharhi Shara'i'il Islam, Beirut, Dar Ihya' al-Turaht al-Arabi, bugu na 7, 1404H.
- «Solar Eclipses of Historical Interest»، Gidan yanar gizon NASA, kwanan wata ziyara: Oktoba 2, 1925.