Shekara Ta 9 Hijira
Shekara 10 Hijira Ƙamari Shekara 8 Hijira Ƙamari | |
| 630 da 631m | |
|---|---|
| Imamanci | |
| Annabtar Sayyidina Muhammad (S.A.W) | |
| Hukumomin ƙasashen Muslunci | |
| Muhammad Bin Abdullah (S.A.W) a Madina | Hukuma:1-11 Hijira |
| Muhimman abubuwan da suka faru | |
| Yaƙin Tabuka | |
| Isar Da Ayoyin Bara'a | |
| Mubahalar Annabi (S.A.W) Tare da Kiristocin Najran | |
| Saukar Ayar Ukhuwwa | |
| Waƙi'ar As'habul Aƙaba | |
| Gina Masallacin Dhirar | |
| Wafati/Shahada | |
| Wafatin Ummu Kulsum Ƴar Annabi (S.A.W) | |
Shekara ta 9 hijira ƙamari, (Larabci: سنة 9 للهجرة،) ita ce shekara ta tara a lissafin hijira ƙamari. Rana ta farko a wannan shekara ta kasance 1 Muharram daidai da Juma'a 2 ga watan Urdibeheshti shekara ta 9 kalandar Farsi kuma daidai da 23 Afrilu shekara ta 630 miladiyya, rana ta ƙarshe a wannan shekara ta kasance 29 Zil-Hijja, daidai da Dushanbe 21 ga watan Farwardin shekata ta 10 kalandar Farsi kuma dai da 11 Afrilu shekara 631 miladiyya.[1]
A cikin wannan shekara wakilan ƙabilu da daman gaske sun zo Madina wurin Annabi (S.A.W) sun bayyanar da musluntarsu, da wannan dalili ne ma ake kiran wannan shekara da sunan "Sanatul wufud" ma'ana shekarar ƙungiyoyi. Yaƙin Tabuka, fitowar hadis manzilat, isar da ayoyin bara'a ta hannun Imam Ali (A.S), Mubahalar Annabi (S.A.W) tare da Kiristocin Najran da waƙi'ar As'habul Aƙaba suna daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a wannan shekara.
Muhimman Abubuwa Da Suka Faru
- Wajabta ba da zakka da kuma farkon tattaro zakka ta hannun Annabi (S.A.W) tare da aika ma'aikata wurare daban-daban a 1 Muharram.[2]
- Halartar wakilan ƙabilu daban-daban na yankin Larabawa misalin ƙabilar Bani Asad da Lakham wurin Manzon (S.A.W) tare da karɓar Muslunci.[3] da wannan dalili wannan shekara ta ake kiran ta da sunan sanatul wufud (Shekarar ƙungiyoyi).[4]
- Isar da ayoyin bara'a:Maye gurbin Imam Ali (A.S) wurin Abubakar cikin isar da saƙon ayoyin bara'a a ranar 1 Zil-Hijja.[5]
- Mubahalar Annabi (S.A.W) tare da kiristocin Najran, bisa ra'ayin da bai shahara ba daga malaman tarihi a ranar 24 Zil-Hijja.[6]
- Neman uzuri da wasu da suke da iko da dama don gujewa zuwa yaƙin Tabuka da kuma saukar aya kansu.[7]
- Kawo cikas da munafukai suka yi daga ƙin shiga yaƙi da kuma saukar ayoyi kansu.[8]
- Halifantar da Sayyidina Ali (A.S) a garin Madina da Annabi (S.A.W) ya yi a lokacin yaƙin Tabuka da kuma bayanin hadis manzilat.[9]
- Waƙi'ar As'habul aƙaba wace ba'arin sahabbai suka yanke shawarar kashe Annabi (S.A.W).[10]
- Gina masallacin Dhirar da munafukai suka yi da kuma rushe shi da Annabi (S.A.W) ya yi da saukar aya kansa.[11]
- Kakkarya gunkin Latu da Abu Sufyan da Mugira suka yi da umarnin Annabi (S.A.W).[12]
- Hasashen mutuwar Najashi sarkin Habasha da Annabi (S.A.W) ya yi da mutuwarsa a watan Rajab.[13]
- Aika Buraida Bin Husaibi da manzon Allah (S.A.W) zuwa ga ƙabilun Aslam da Gifar domin karɓo haraji.[14]
- Musluntar Tamim Bin Ausi Bin Kharija Dari daga magabata a fagen al'adar zantar da ƙissoshi a tarihin Muslunci.[15]
Yaƙe-yaƙe
- Afkuwar yaƙin Tabuka da niyyar gwabzawa da Rumawa a 19 Rajab.[16]
- Sariyyatu Uyaina Bin Hisni Farazi tare da ƙabilar Bani Tamim a Muharram.[17]
- Sariyyatu Ƙaɗba Bin Amir Bin Hudaida tare da ƙabilar Khas'am a Safar.[18]
- Sariyyatu Zahhak Bin Sufyan Kilabi tare da ƙabilar Bani Kilab a Rabi'ul Awwal.[19]
- Sariyyatu Alƙama Bin Mujazzar Mudliji tare da Habashiyawa a Rabi'us Sani[20]
- Sariyyatu Ali Bin Abi Ɗalib (A.S) domin ganin bayan gumakan ƙabilar Ɗayyu a Rabi'us Sani.[21]
- Sariyyatu Ukashatu Bin Mihsan tare da ƙabilar.[22]
Wafati
- Rasuwar Ummu Kulsum Ƴar Annabi (S.A.W) a watan Sha'aban.[23]
Bayanin kula
- ↑ سایت تبدیل تاریخ هجری
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1410H, juzu’i. 2, shafi. 121; Waqidi, Al-Magazi, 1409 AH, juzu'i. 3, ku. 973; Tabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, 1387H, juzu'i. 3, shafi. 123.
- ↑ Tabari, Tarikhul Al’umam Wa Al-muluk, 1387H, juzu’i. 3, shafi. 96.
- ↑ Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawieh, Beirut, juzu'i. 2, shafi. 560.
- ↑ Tabari, Tarikh al-Umam Wa al-Muluk, 1387 H., juzu'i na 3, shafi na 122-123; Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 5, shafi na 3; Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyah, Beirut, juzu'i. 2, shafi. 545; Ayyashi, Tafsir al-Ayashi, 1380 AH, juzu'i na 2, shafi:73.
- ↑ Duba: Mohammadi Rayshahri, Farhnage NamehMubahele, 2016, shafi 83-87.
- ↑ Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiya, Beirut, juzu'i. 2, shafi. 516.
- ↑ Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiya, Beirut, juzu'i. 2, shafi. 517.
- ↑ Ibn Abd al-Barr, al-Istiyab, 1412 AH, juzu'i na 3, shafi na 1097.
- ↑ Yaqubi, Tarikh Yaqubi, Beirut, juzu'i. 2, shafi. 68; Masoudi, Al-Tanbih wa al-Ashraf, Alkahira, shafi. 236; Waqidi, Al-Magazi, 1409 AH, juzu'i. 3, shafi. 1044. Ibn Qutaybah, Al-Ma’arif, 1992 miladiyya, shafi na. 343.
- ↑ Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyah, Beirut, juzu'i. 4, shafi. 173; Moghrizi, Imta'ul al-asma, 1420 AH, juzu'i na 1, shafi na 480.
- ↑ Al-Tabari, Tarikh al-Al-Umam Wa al-Muluk, 1378H, juzu'i. 3, shafi. 99.
- ↑ Al-Tabari, Tarikh al-Al-Umam Wa al-Muluk, 1378H, juzu'i. 3, shafi. 122.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1410H, juzu’i. 2, shafi. 121.
- ↑ Balazri, Fatuh al-Baldan, 1987, shafi. 638.
- ↑ Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiya, Beirut, juzu'i. 2, shafi. 515; Baihaqi, Dala'ilul al-Nubuwwa, 1405 AH, juzu'i. 5, shafi. 469.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1410H, juzu’i. 2, shafi. 122
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1410H, juzu’i. 2, shafi. 122-123
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1410H, juzu’i. 2, shafi. 123.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1410H, juzu’i. 2, shafi. 123-124
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1410H, juzu’i. 2, shafi. 124.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1410H, juzu’i. 2, shafi. 124-125
- ↑ Tabari, Tarikh Tabari, 1387 AH, juzu'i na 3, 124; Ibn Hajar Asqlani, al-Isabah, 1415 AH, juzu'i na 8, shafi:460; Ibn Khayyat, Tarikh Khalifa Ibn Khayyat, 1415 Hijiriyya, shafi na. 45.
Nassoshi
- Ibn Hajr al-Asqlani, Ahmed bin Ali, Al-Isaba Fi Tamyizis Sahaba, binciken Adel Ahmad Abd al-Mojood da Ali Muhammad Moawad, Beirut, Darul-Kitab al-Elamiya, 1415H.
- Ibn Saad, Muhammad Ibn Saad, Tabaqat Al-Kubra, bincike na Muhammad Abd al-Qadir Atta, Beirut, Dar Al-Kitab Al-Alamiya, 1410H.
- Ibn Qutaiba, Abdullahi bin Muslim, al-Maarif, binciken dukiyar Akasha, Alkahira, Al-Masriyyah El-Masriyya Al-Katab, bugu na biyu, 1992.
- Ibn Abd al-Barr, Yusuf bin Abd Allah, al-Istiyab fi Marefah al-As-hab, bincike na Ali Muhammad al-Bajawi, Beirut, Dar al-Jeel, 1412 AH.
- Ibn Hisham, Abd al-Malik, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Ebrahim Iriri da sauransu suka gyara, Beirut, Darul Marafa, Bita.
- Balazuri, Ahmad bin Yahya, Jamal Min Ansab al-Ashraf, wanda Sohail Zakar da Riaz Zarkali suka yi bincike a Beirut, Darul Fikr, Beirut, 1417 bayan hijira.
- Balazuri, Ahmed bin Yahya, Fatuh al-Baldan, Beirut, Dar da Al-Hilal Library, 1988.
- Baihaqi, Abu Bakr Ahmad bin Hossein, Dala'ilul al-Nubuwwa, bincike na Abdul Moati Qalaji, Darul Kutb al-Alamiya, Beirut, 1405H.
- Ibn Khayyat, Khalifa, Tarikh Khalifa bin Khayyat, Fawaz Research, Beirut, Dar al-Kitab al-Elamiya, 1415H.
- Tabarsi, Fazl bin Hasan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, gyara daga Fazllullah Yazdi Tabatabai da Hashem Rasouli, Tehran, Nasser Khosrow, bugu na uku, 1372.
- Tabari, Muhammad bn Jarir bn Yazid, Tarikhul Al'umam Wal Muluk, Beirut, Darul-Turaht, 1378H.
- Ayashi, Muhammad bn Mas'ud, Tafsir al-Ayyashi, Hisham Rasuli, Tehran, Maktaba al-Ilmiyah al-Islamiyah, ya yi bincike, 1380H.
- Mohammadi Rayshahri, Muhammad, Sayyid Rasul Mousavi, Hassan Farzanegan, Dictionary of Mubahila, Qom, Dar al-Hadith, 1395H.
- Masoudi, Ali ibn Husayn, Al-Tanbih wa al-Ishraf, editan Abdullah Ismail al-Sawi, Alkahira, Dar al-Sawi, Beta.
- Mufid, Muhammad bn Muhammad bn Nu'man, Al-Irshad, wanda Mu'assasar Ahlul Baiti (AS) ta yi bincike a kan Farfadowar Al'adun gargajiya, Qum, Al-Mu'utamar al-Layfiyyah al-Sheikhul Mufid, 1413H.
- Al-Maqrizi, Ahmad bn Ali, Imta'ul Asma, bugun Muhammad Abdul-Hamid al-Numisi, Beirut, Darul Kuttab al-Ilmiyah, 1420H.
- Al-Waqidi, Muhammad ibn Omar, Kitabul Al-Magazi, bugun Mercedes Jones, Beirut, Musassa al-Alamy, bugu na uku, 1409H.
- Al-Yaqubi, Ahmad ibn Abi Yaqub, Tarikhul Al-Yaqubi, Beirut, Dar Sader, Beta.