Sallar Dare
- wannan wani rubutu ne game da sallar dare, domin neman ƙarrin bayani dangane da tashin dare domin sallah da addu'a, ku duba: Tahajjudi.
Imam Rida (A.S):
“ na horeku da tashin dare. Babu wani bawa da ya tashi karshen dare ya yi sallah raka'a takwas daga nafilolin dare, da raka'a biyu daga sallar shafa'i da raka'a daya daga sallar wutiri kuma ya nemi gafara sau saba'in a cikin Qunut ta, sai Allah ya kiyaye shi daga azabar kabari da wuta, kuma ya tsawaita rayuwarsa, ya buda masa cikin rayuwa. ... gidajen da ake sallar nafililolin dare, haskensu yana haskakawa ga halittun sama; Kamar yadda hasken taurari ke haskaka mutanen kasa.
Fattal Naishabusi,Raudatul Al-Wa'izin, bugun shekara ta 1375. juzu'i na 2 shafi na 320
Sallar dare, (Larabci: صلاة الليل) sallah ce ta mustahabbi, lokacinta yana farawa daga farkon tsakiyar dare har zuwa hudowar Alfijir, sallar dare, sallah ce da ta kasance wajibi kan Annabi (S.A.W), mustahabbi kan sauran mutane, an ƙarfafa magana kan yin wannan sallah, akwai riwayoyi masu yawan gaske dangane da falala da tasirin sallar dare, daga jumlarsu ana ƙirgata matsayin mafi fifitar sallah cikin sallolin mustahabbi, kuma alama ce ta ɗan Shi’a na gaskiya. Sallar dare raka’a goma sha ɗaya ce, wacce ake yinta cikin surar salloli biyar masu raka’o’i biyu-biyu da kuma guda ɗaya mai raka’a ɗaya, raka’o’in ukun ƙarshe sun fi falala kan sauran, wacce suka haɗa da raka’a biyu da ake kira Shafa’i da kuma raka’a guda ɗaya da ake kira da Wutiri.
Kwaɗaitarwa Kan Yin Sallar Dare
Sallar dare, tana daga salloli na mustahabbi da aka kwaɗaitar kansu cikin riwayoyi, daga jumlarsu hadisin Annabi (S.A.W) cikin wasiyyarsa zuwa ga Imam Ali (S.A.W) karo uku yana umartarsa da yin sallar dare, [1] haka kuma an naƙalto daga Hazrat lokacin da yake magana da Musulmai: “ku yi riƙo da sallar dare ko da kuwa raka’a ɗaya ce, saboda ita sallar dare tana kare mutum daga aikata zunubi, tana kashe fushin Ubangiji, kuma tana tunkuɗe ƙunan wuta ranar Alƙiyama.” [2] cikin litattafan hadisi akwai babi guda mai taken “Salatul Al-Laili” babi ne da ya keɓantu da riwayoyi kan wannan maudu’i. [3] A cewar Shaik Saduƙ wanda ya rasu shekara ta 381 h ƙamari, Malamin hadisi na shi’a, yana ganin sallar dare matsayin wajibi ce a kan Annabi (S.A.W) sannan kuma musthabbi ce kan sauran mutane. [4] Shaik Mufid shima yana ganin sallar dare matsayin mustahabbi kuma sunna mai ƙarfi. [5]
ƙaƙa ake Yin Sallar Dare
Ayatullahi Ali ƙazi yana magana zuwa ga Allama Tabataba'i:
ɗana, idan kana neman duniya, ka yi sallar dare, idan kana neman lahira ka yi sallar dare.
Sallar dare raka’a goma sha ɗaya ce: raka’a takwas ana yin su da surar salloli guda huɗu masu raka’a biyu-biyu ana yinsu da niyyar sallar nafila, sai kuma raka’a biyu da niyyar sallar Shafa’i, da kuma raka’a ɗaya da niyyar sallar wutiri, [7] Mustahabbi ne cikin raka’ar ta farkon sallar Shafa’i a karanta Fatiha da suratul Nasi, a raka’a ta biyu kuma a karanta Fatiha da suratul Falaƙi, haka kuma sallar wutiri bayan karatun Fatiha mustahabbi ne a karanta suratul Iklasi sau uku haka kuma karanta falaƙi da nasi kafa ɗai-ɗai. [8] mustahabbi ne cikin Alƙunutun sallar wutiri a yi wa Muminai guda arba’in addu’a ku istigfari. [9] haka kuma a karanta istigfari ƙafa 70 kamar haka: (Astagfirullaha Rabbi wa Atubu Ilaihi), a karanta (haza muƙamin Al-A’izi bika minan An-Nari) ƙafa bakwai, a karanta (Al-Afwu) ƙafa ɗari, bayan nan sai a karanta wannan Addu’a
Shaik ɗusi cikin Misbahul Al-Mutahajjid, ya yi wasicci da karanta Du’a’u Hazin bayan idar da sallar dare. [11]
Kufaifayi Da Falalolin Sallar Dare
Jabir ɗan Abdullahi Ansari daga Annabi (S.A.W):
Jabir Bn Abdullahi Ansari ya naƙalto daga Annabi (S.A.W): Allah bai zaɓi Ibrahim a matsayin Masoyinsa ba sai domin ayyuka guda biyu: ciyarwa da kuma sallar dare lokacin da mutane suke bacci.
Saduk Ilalul Ash-Shara’i, Manshuratu Al-Maktabatil Al-haidariyya, j 1 sh 35
Cikin riwayoyi, an ambaci kufaifayi da falaloli masu tarin yawa dangane ga sallar dare; daga jumlarsu cikin wata riwaya da ta zo a littafin Biharul Al-Anwar an naƙalto daga Annabi (S.A.W) cewa lallai sallar dare tana kasancewa sababin samun yardar Ubangiji, soyayyar Mala’iku, samun ilimi, haskakuwar gida, samun nutsuwar gangar jiki, ƙiyayyar Shaiɗan, amsa addu’a, karɓar ayyuka, haskaka ƙabari da kuma ɗaukar makami gaban maƙiya. [12] cikin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) yana cewa ita sallar dare tana kyawunta siffar mutum da kyawunta halayensa da ƙamsasa shi kuma tana haɓɓaka arzƙinsa, zai kuma samu damar biyan bashi, kuma tana tafiyar da baƙin ciki tana kuma haskaka ganin mutum. [13] cikin wata riwaya daban da aka naƙalto daga Imam Sadiƙ (A.S) “ dukiya da ƴaƴa ado ne na duniya, raka’a takwas a ƙashen dare tare da raka’a guda ɗaya ta wutiri ado ne na lahira” [14] Wasu ba’ari daga falalolin sallar dare da suka zo a riwaya, sun kasance cikin wannan sharhi da zai zo a ƙasa:
- mafi fifikon sallolin mustahabbi. [15]
- sababin Alfaharin Mumini. [16]
- sababin alfaharin Allah ga Mala’iku. [17]
- tana daga cikin alamomin ƴan Shi’a na gaskiya. [18]
Kan asasin riwayoyin da Shaik Saduk ya naƙalto daga Imamai a littafin Ilalul Ash-Shara’i, zunubi yana kasancewa sababin haramtuwa daga sallar dare. [19]
Hukunce-hukunce
امام صادق(ع): «شَرَفُ الْمُؤْمِنِ صَلاتُهُ بِاللَّیلِ، وَعِزُّهُ کفُّ الاَذی عَنِ النّاسِ؛ ɗaukakar Mumini tana cikin sallarsa ta dare, girmamarsa tana cikin kame hannu da ƙauracewa cutar da mutane.
Saduk Al-Khisal 1362 h shamsi, j 1 sh 6
Wasu ba’ari daga hukunce-hukuncen sallar dare, kan asasin litattafan fiƙihu:
Mafi falalar ɓangaren sallar dare shi ne Shafa’i da wutiri, kuma sallar wutiri ta fi fifita daga Shafa’i, cikin sallar dare za a iya wadatuwa da yin sallar shafa’ai da wutiri ko kuma iya wutirin ita kaɗai,. [20] Lokacin sallar dare a shari’ance yana farawa daga tsakiyar dare zuwa hudowar Alfijir (Lokacin fara sallar Asubahi), yinta daf da ketowar Alfijir ya fi falala, [21] Sayyid Ali Sistani daga Maraji’an taƙlidi, yana ganin lokacin yin sallar dare yana farawa tun farkon dare. [22] Idan ya zamana ana yin sallar ne a zaune ya fi dacewa duk ra’aka biyu a lissafa su matsayin raka’a ɗaya a tsaye. [23] Matafiyi da kuma wanda zai masa wahala ya tashi tsakiyar dare ya yi sallah, za su iya yinta tun farkon dare. [24] Idan ya zamana mutum bai yi sallar dare ba zai iya ramata. [25] Rama sallar dare ya fi falala daga yinta kafin tsakiyar dare. [26]
Nazari
An yi rubuce-rubuce daban-daban game da sallar dare, cikin maƙalar Kitabshinasi Namaze Shab, an gabatar da litattafai guda 70 waɗanda aka rubuta da harshen Larabci ko Farisanci, [27] ba’arinsu sun kasance kamar haka: Adabu Salatil Al-Laili, na Muhammad Baƙir Fasharki, wanda ya rasu shekara ta 1315 h ƙamari. Salatul Al-Lail; Fadluna Waƙtuha wa Adaduha wa Kaifiyatuha wal Al-Khususiyatul Al-Raji’ati min Kitabi was-Sunnati, na Gulam Rida Irfaniyan, wanda ya rasu shekara 1382 h shamsi, ya rubuta shi da harshen Larabci. Adabul Salatil Al-Laili wa Fadliha, na Sayyid Muhammad Baƙir Shafti, wanda ya rasu shekara ta 1260. [28]
Bayanin kula
- ↑ Sadouq, Man La-yahdara Al-Faqih, 1413 AH, Juzu'i na 1, shafi na 481 da Mujalladi na 4, shafi na 179.
- ↑ Motaghi Handi, Kanz al-Amal, 1410 AH, Juzu'i na 7, shafi na 791, 21431 H.
- ↑ Duba Sadouq, Man la Yahdrah al-Faqih, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi:484.
- ↑ Sadouq, Man La Yahdrah al-Faqih, 1413 AH, Mujalladi na 1, shafi na 484.
- ↑ Mufid, Al-Maqna, 1413 AH, shafi na 120.
- ↑ <a class="external text" href="https://farsi.khamenei.ir/speech-content?id=43304">«بیانات در ابتدای درس خارج درباره اثر نماز شب در از بین بردن گناهان»</a>
- ↑ Tabatabaei Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthgha, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 245; Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila, 1434H, juzu'i na 1, shafi na 143.
- ↑ Qommi, Mofatih al-Janan, 2004, shafi na 949.
- ↑ Qomi, Mofatih al-Janan, 2004, shafi na 949.
- ↑ شیخ طوسی، مصباح المتهجد، ۱۴۱۱ق، ص۱۶۳-۱۶۴.
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 87, shafi na 161.
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 87, shafi na 161.
- ↑ Hurrul Ameli, Wasal al-Shia, Mujalladi na 5, shafi na 272
- ↑ Sadouq, Ma'ani al-Akhbar, Daral al-Marafa, shafi na 324.
- ↑ Motaghi Hindi, Kanz al-Amal, 1410 AH, juzu'i na 7, shafi na 791, 21397.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 87, shafi na 140.
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 87, shafi na 156.
- ↑ Mufid, Al-Maqna, 1413 AH, shafi na 119-120.
- ↑ Sadouq, Ilalul Ash-Shara’i, Rubutun Al-Haydariyyah, Juzu’i na 2, shafi na 362.
- ↑ Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila, 1434H, juzu'i na 1, shafi na 143.
- ↑ Tabatabaei Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthgha, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 265-266.
- ↑ <a class="external text" href="https://www.sistani.org/persian/qa/01067">پرسش و پاسخ نماز شب</a>
- ↑ Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila, 1434H, juzu'i na 1, shafi na 144.
- ↑ Tabatabaei Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthghati, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 266.
- ↑ Duba Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthghati, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 266.
- ↑ Duba Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthghati, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 266.
- ↑ Ansari Qomi, “KItabe Shinasi Namaze Shab”, shafi na 170.
- ↑ Ansari Qomi, “KItabe Shinasi Namaze Shab”, shafi na 170-186
Nassoshi
- Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Tahrir al-Wasila (Mausu'atu Imam Al-Khomeini 22 and 23), Tehran, Cibiyar Gyara da Buga Ayyukan Imam Khumaini (A.S), bugu na uku, 1434H.
- Ansari Qomi, Naser al-Din, "Kitabe Shinasi Namaz", Mishkowa, zamistan1372.
- Hurrul Amili, Muhammad bin Hasan, Wasal al-Shi'a, Qum, Al-Bait Foundation, 1409H.
- <a class="external text" href="https://www.sistani.org/persian/qa/01067">پرسش و پاسخ نماز شب</a>
- Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila, 1434H, juzu'i na 1, shafi na 144.
- Tabatabaei Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthghati, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 266.
- Duba Tabatabaei Yazdi, Al-Urwa al-Wuthghati, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 266.
- Tabatabaei Yazdi, Al-Urwa Al-WUthghati, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 266.
- Ansari Qomi, “Kitabe Shinase Namaz Shab”, shafi na 170.
- Ansari Qomi, “Kiatbe Shinasi Namaze Shab”, shafi na 170-186.