Jump to content

Shirka

Daga wikishia
(an turo daga Mushrikai)
Aƙidun Shi'a
‌Sanin Allah
TauhidiTabbatar Da AllahTauhidi ZatiTauhidi SifatiTauhidi Af'aliTauhidi IbadiSiffofin ZatiSiffofin Fi'ili
RassaTawassuliCetoTabarrukiIstigasa
Adalcin Allah
Husnu Wa ƘubhuBada'uAmrun Bainal Amraini
Annabta
Ismar AnnabawaKhatamiyyatAnnabin MuslunciMu'ujizaAsalantuwar Kur'ani
Imamanci
AƙiduIsmar AnnabawaWilaya TakwiniyyaIlmul GaibiKhalifatullahiGaibaMahadawiyyaIntizarul FarajBayyanaRaja'aImamanci Na Nassi
ImamanImam AliImam HassanImam HusainiImam SajjadImam BaƙirImam SadiƙImam KazimImam RidaImam JawadImam HadiImam AskariImam Mahadi
Ma'ad
BarzahuMa'ad JismaniHasharSiraɗiTaɗayurul KutubMizan
Fitattun Mas'aloli
Ahlil-BaitiMa'asumai Goma Sha HuɗuKaramaTaƙiyyaMarja'iyyaWilayatul FaƙihiImanin Mai Aikata Manyan Zunubai

Shirka (Larabci: الشرك) tana daga cikin manya-manyan zunubai, ma'ana sanya wa Allah abokin tarayya. Shirka kishiya ce ga tauhidi, malaman Muslunci sun rarraba shirka kamar dai tauhidi zuwa wasu rabe-rabe, misalin shirka a cikin zati, siffofi da ayyuka da kuma shirka cikin ibada, shirka kaso biyu ce, bayyananniyar shirka da ɓoyayyar shirka, ana yin bahasi game da bayyananniyar shirka a cikin aƙidu da ɓoyayyar shirka cikin akhlaƙ.

Bautawa son rai, biyewa mariskan ɗabi'a, kokwanto da kuma jahilci su na daga cikin dalilai da illololin da suke janyo shirka, a cikin an bayyana lalacewar ayyuka, haramtuwa daga samun gafarar Allah, haramtuwa daga shiga aljanna da janyo shiga jahannama, su na daga cikin abubuwa yi wa Allah shirka ke janyowa.

Ibn Taimiyya da mabiyanSa wahabiyawa su na jingina shirka ga musulmai da suke tawassuli da mutane masu daraja a Muslunci da kuma neman ceto daga gare su, daidai lokacin da musulmai musamman ma Shi'a su na ganin tawassuli da mutane masu daraja a addini yana daga girmama ibadoji da alamomi na addini su na masu imani da cewa tawassuli da matattu kaɗai yana kasancewa shirka idan ya kasance haɗe da bauta musu da imani da kasancewarsu alloli. Haka nan tare da jingina da ayoyin kur'ani, ceton manya a addini da izinin Allah abu ne mai sauƙin gaske.

Nazarin Maana

Shirka shi ne jinginawa Allah abokin tarayya cikin abubuwan da suka keɓanta da shi misalin wajabcin samuwa, bauta gudanar da al'amuran halittu.[1] Shirka tana kasance kishiyar tauhidi (Kaɗaita Allah).[2] Na'am Ayatullahi Jawadi Amoli ya ajiye shirka a matsayin kishiya ga imani, ya tafi kan cewa ba kodayaushe ne shirka take kasancewa sababi da illar fita daga tauhidi da halƙar muminai ba, bari dai a kur'ani an yi amfani da shirka kan masu bautar gumaka[3] Ahlul-Kitabi[4] kai a wani wurin ma an yi amfani da ita[5] hatta kan muminai.[6]

Mushriki shi ne wanda yake sanya wa Allah abokin tarayya ko kuma ya na imani da cewa wanin Allah ya na da siffofinsa ko kuma dai ya na jingina wani sashe daga al'amrin halitta zuwa ga wanin Allah, ko yana ganin dacewar umarni da hani daga wanin Allah[7] ko kuma bautawa wanin Allah.[8]

Martabobi

Kamar dai misalin tauhidi ita ma shirka ta na da martabobi, daga jumla akwai:

  • Shirka cikin zatin Allah; wani sashe daga shirka yana da ma'ana biyu; ɗaya shi ne imani da cewa zatin Allah ya harhaɗu ne daga abubuwa guda biyu ko wasu adadin juzu'ai.[9] ɗayan kuma shi ne imani da adadin Alloli masu zaman kansu.[10]
  • Shirka cikin siffa, shi ne imani da cewa siffofin Allah su na da bambanci da zatinsa, siffarsa tana cin gashin kanta daga zatinsa.[11]
  • Shirka cikin ayyukan Allah; tana kasancewa kishiyar tauhidi af'ali, kamar dai misalinsa ita ma ta na da rassa daban-daban misalin shirka cikin halitta da shirka cikin ubangijintaka da gudanarwa
  1. Shirka cikin halitta; imani da samuwar mahalicci biyu ko wasu adadi masu zaman kansu ta yadda babu wani cikin da yake ƙarƙashin ikon wani. Imani da mahalicci biyu, mahaliccin alheri da mahaliccin sharri yana daga cikin samfuran shirka cikin halitta wanda kan asasinsa kaɗai Allah yana halittar abubuwa masu kyau, shi kuma mahaliccin sharri shi ne yake halittar miyagun halittu da kuma sharri.[12]
  2. Shirka cikin ubangijintaka da gudanarwa nau'i biyu ce:
  3. Shirka cikin gudanarwa ta halitta, shi ne imani da cewa Allah ya halicci duniya amma kuma sarrafa ta da tafiyar da ita ya miƙa shi ga wasu iyayen giji daban.
  4. Shirka cikin gudanarwa ta shari'a, shi ne yarda da dokoki da ƙa'idojin wanin Allah a rayuwa da kuma imani da larurar zartar da umarnoninsa.[13]

Na'am malamai sun rarraba shirka zuwa gida biyu shirka Nazari da shirka amali wace take kasance kishiyar tauhidi nazari da tauhidi amali. Wata shirka ce da take da alaƙa da ɓangaren aƙida misalin shirka cikin zatin Allah da siffofinsa, shirka cikin gudanarwa da halitta, duka shirka ce nazari, amma shirka cikin ibada wace yawanci tafi karkata zuwa aiki, ana lissafa ta a shirka amali.[15]

Matsayi Da Muhimmanci

Wasu adadin ayoyi daga kur'ani sun keɓantu game da shirka da hani kan ta. Cikin ba'arin ayoyin kur'ani ya zo cewa mushrikai ba su da wani dalili kan da'awar da suke yi,[Tsokaci 1][16] bari dai kawai su na zato da kirdado ko kuma kawai su na biyewa son ransu.[17][Tsokaci 2] Bisa ayar «إِنَّ اللَّـهَ لَا يَغْفِرُ أَن يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَاءُ» (Allah ba ya gafartawa shirka da shi amma yana gafartawa abin da ba shirka ba ga wanda ya so).[18] In banda shirka, Allah yana iya gafarta baki ɗayan zunubai, ba'arin malaman tafsiri sun ce abin nufi shi ne cewa ita shirka ita ce mafi girman zunubai a wurin Allah, idan har aka yafe ta to sauran zunubai ma za a yafe su.[19] Idan mushriki bai tuba har ya bar duniya, to ba za a taɓa yafe masa ba, malamai sun tafi kan cewa an togace tuba a cikin wannan aya, ma'ana idan mushriki ya tuba daga shirka akwai yi wuwar gafarta masa.[20] A cikin ba'arin riwayoyi ya zo cewa yi wa Allah shirka ya na cikin mafi girman zunubai, a wata riwaya daga Abdullahi Bin Mas'ud daga Annabi (S.A.W) mafi girman zunubi shi ne sanya wa Allah tsara da misali.[21]

Imam Ali (A.S) ya rarraba shirka bisa mahangar kur'ani zuwa gida huɗu, shirka ta fatar baki, shirka ta aiki, shirka ta zina da shirka ta riya, ya dogara da ayoyin kur'ani cikin tabbatar da ko wace guda daga cikinsu. Kan shirka ta fatar baki ya kawo ayar «لَقَدْ كَفَرَ الَّذِینَ قَآلُواْ إِنَّ اللَّـهَ هُوَ الْمَسِیحُ ابْنُ مَرْیمَ؛ (Tabbas Waɗanda suka ce Allah shi ne dai Almasihu ɗan Maryam, sun kafirta)[22] shirka ta aiki ayar«وَمَا یؤْمِنُ أَكْثَرُهُمْ بِاللَّـهِ إِلا وَهُمْ مُشْرِكُونَ؛ (Aksarinsu ba sa imani da Allah sai suna yi masa shirka[23] «اتَّخَذُوا أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّـهِ Sun riƙi malamansu (Yahudu) da ruhubanawansu (Nasara) ababen bauta koma bayan Allah[24] domin tabbatar da shirka ta zina ya kawo ayar «وَ شارِكْهُمْ فِی الأَمْوالِ وَالأَوْلادِ؛ (Kuma ka yi tarayya da su cikin duniya da ƴaƴa)[25] domin tabbatar da shirka ta riya ayar «فَمَن کانَ یرْجُوا لِقاءَ رَبِّهِ فَلْیعْمَلْ عَمَلاً صالِحاً وَ لایشْرِکْ بِعِبادةِ رَبِّهِ أَحَدا؛ (Saboda haka duk wanda yake fatan haɗuwa da Allah to ya yi aiki nagari kuma ka da ya yi tarayya da kowa cikin bautawa ubangijinsa.[26] ya jingina da ita.[27] Kan asasin riwayoyi, jima'i na haramun da lomar haramun da mantawa da ambaton Allah lakacin saduwa da iyali da kuma ba'arin ayyuka, su na kasancewa sababin tarayyar Shaiɗan cikin samuwar ɗigon halitta jariri a mahaifa, kuma duk wurin da Shaiɗan ya shiga, tabbas ba za a samu tsaftataccen tauhidi ba, daga ƙarshe misalin wannan tarayya ta Shaiɗan ta na iya zama abin da yake amsa sunan shirkar zina.[Akwai buƙar kawo dalili]

Nau'uka

Shirka ta fuskacin bayyana da ɓuya ta rabu gida biyu, bayyananniyar shirka da ɓoyayyar shirka, bayyananniyar shirka ita ce aikata wani aikin ibada da ayyuka na musamman misalin ruku'u, sujjada da layya ga wani abin bauta ba Allah ba,[28] tare da ƙudurce muƙamin allantaka ga wannan abun bauta, ita kuma ɓoyayyar shirka ta ƙunshi duk wani nau'in bautawa duniya, bautawa son rai, riya da…[29] Imam Sadiƙ (A.S) cikin tafsirin aya ta 106 suratul yusuf[Tsokaci 3] ya bayyana kalmomi misalin idan babu wani ni zan halaka, idan babu wani zan shiga matsala kaza da kaza a matsayin shirka cikin da'irar hukumar Allah.[30] Annabin Muslunci (S.A.W) ya bayyana shirka matsayin mafi ɓoyuwa daga sautin tattakin tururuwa kan dutse cikin duhun dare.[31] Galibin bahasi game da ɓoyayyar shirka ya kasance cikin halƙoƙin ilimin Akhlaƙ

Dalilai Da Tushe

An yi bayani dalilai da sabubban shirka kamar haka:

  • Biyewa shakka da kokwanto: Cikin suratul yunus, lokacin da ake magana da mushrikai Allah yana cewa: "Babu abin da suke bi sai zato babu abin da suke faɗa sai ƙarya".[32]
  • Karkata zuwa ga imani da mariskan ɗabi'a kaɗai: Tushen ilimin ba'arin mutane sakamakon nutsuwa da duniyar ɗabi'a, yana taƙaituwa da iya abubuwan da ake iya riska kaɗai da mariskan ɗabi'a, ba sa iya cirata daga iyakokinsu, da wannan dalili ne suka ajiye Allah a layin abubuwan da suke iya riska da mariskan ɗabi'a.[33]
  • Jahilci: Kur'ani yana ganin jinginawa Allah ɗa domin shirka ya samo asalin daga jahilci da rashin ilimi.[34]

Kur'ani ya ambaci son duniya, bautawa son rai, mantawa da Allah, guluwi cikin mutane masu daraja a addini, ta'assubanci da kuma lalatattun hukumomi su ma suna daga dalilan karkata zuwa ga shirka.[35]

Saƙonni

Bisa ayoyin kur'ani, shirka ta na da saƙonni da suke biyo bayanta daga jumla akwai:

Hukuncin Fiƙihu

A mahangar addinin muslunci shirka haramun ce kuma tana cikin manya-manyan zunubai.[42] Malaman fiƙihu tare da jingina da ayar «إِنَّمَا الْمُشْرِكُونَ نَجَسٌ فَلاَ يَقْرَبُوا الْمَسْجِدَ الْحَرَامَ»[43] sun fitar da hukuncin najasar mushrikai sun kuma ce bai halasta su a barsu su shiga masallacin harami ba.[44] Shaik Ɗusi a cikin An-Nihaya ya tafi kan rashin halascin aure tsakanin musulmi maza da mata mushrikai aure na daimi, amma aure muwaƙƙati tare da mata Yahudawa da Nasara shi babu matsala.[45]

Tuhumar Da Wahabiya Suka Yi Shia

Wahabiyawa suna ganin imani da yin da tawassuli da matattu, istigasa da annabawa da waliyyan, neman tabarruki da ƙaburbura da neman ceto daga gare su a duniyar barzahu, suna daga cikin abubuwan da ake lissafa su a shirka cikin ibada. Ibn Taimiyya ya tafi kan ra'ayin cewa tawassuli da addu'ar Annabi (S.A.W) da salihai, a lokacin da suke raye ba shirka ba ne, amma tawassuli da su bayan mutuwarsu shirka.[46] A imaninsa, duk wanda ya je kabarin wani mutum ko wani daga salihai ya roƙi buƙata daga wurinsu, to shi mushriki ne, wajibi ne a tilasta shi ya tuba idan ya ƙi tuba to wajibi ne a kashe shi.[47] Abdul-Aziz Bin Baz bawahabiye kuma mufti shi ma a cikin rubuce-rubucensa ya lissafa addu'a da istigasa a kusa da wani kabari, neman waraka da nasara kan maƙiya a matsayin mabayyanan shirka mafi girma.[48]Wahabiyawa suna ƙiyasta waɗannan ayyuka na musulmi da ayyukan mushrikai a farkon Muslunci cikin bautar gumaka.[49]

Malaman Muslunci cikin amsa ga wahabiyawa sun ce: ayyukan mushrikai sun kasance tare da imani da tabbabatar da gudanarwa da mallaka ga gumaka; amma ayyukan musulmi cikin waliyyan Allah ba su kasance kan wannan aƙidu ba; bari dai gini kan kabarin waliyyan Allah da neman cetonsu, girmama Sha'a'ir (Ibadojin Allah) ne.[50] Haka nan musulmai da suke yin wannan ayyuka, babu sanda suka taɓa ƙudurce niyyar bautawa annabawa da waliyyan Allah, kuma ba su taɓa jingina musu muƙamin allantaka ba, bari dai kaɗai suna niyyar girmama annabawa da waliyyan Allah da kuma neman tabarruki daga Allah ta hanyar su.[51]

Bisa ayoyin kur'ani mai girma, ceto yana zama shirka kuma abun wurgi idan ya kasance an yi shi da shakali da yanayi na cin gashin kai ba tare da neman izinin Allah ba.[52] Saboda a irin wannan hali ya na zama shirka cikin ubangijintaka da gudanarwar Allah.[53] Haka nan malaman muslunci cikin amsa da suka baiwa wahabiyawa a cikin ayoyin kur'ani mai girma kaɗai an kore neman ceto daga gumaka ne, malaman sun yi ishara zuwa ga bambanci na tushe tsakanin neman ceto daga annabawa da neman ceton masu bautar gumaka daga gumakan, kuma sun yi imani cewa musulmi saɓanin masu bautar gumaka, har abada ba za su taɓa allantar da annabawa ko ubangijintar da su ko ɗaukar su matsayin masu tafiyar da duniya ba.[54] Muɗahhari masanin Allah kuma ɗanshi'a ya tafi kan cewa kan asasin mahangar kur'ani a cikin aya ta 86 suratul zukhruf(Kuma waɗanda suke kira (suna roƙo) wanin Allah ba su da ikon yin shafa’a, sai wanda ya shaida da gaskiya kuma suna masu sani)

Waɗanda suke kira (bautawa) ba tare da Allah ba, ba su da ikon yin ceto, sai wanda ya shaida gaskiya kuma su na da ilimi. Ma'ana ceto kaɗai yana ga waɗanda suka shaida gaskiya (Tauhidi) ko kuma dai ƙari kan shaida ta fatar baka sun yi iƙrari cikin faɗakuwa da kuma ilimi, saboda Kalmar «شَهِدَ» (Shaidawa) bawai kaɗai lafazi ba ne, bari abin nufi shi ne waɗanda suke iya shuhudi da riska gaskiya da tauhidi, kuma sun kasance ido buɗe kan ayyukansu kuma sun san daga su wane ne za su nemi ceto daga su wane ne ba za su nemi ceto ba, a imanin Muɗahhari, shi ceto sha'ani ne na tauhidi da ahalinsa, su gumaka ba su da hankali ko fahimta kwata-kwata ballantana su zama masu ceto.[55]Sayyid Muhammad Husaini Ɗabaɗaba'i malamin tafsiri na Shi'a shi ma yana ganin cewa Allah ne mafarar faila ga dukkanin halittu, kuma duk wani nau'in rayuwa da matuwa arziƙi da ni'ima da ire-irensu a tsarin sabubba da musabbibai su na hannun Allah (Ko wani ɗaya daga waɗannan al'amura bisa alaƙa ta musamman kuma ayyananniya yana da alaƙa da Allah) kuma ceto shi ma wani sashe ne daga wannan tsari na sabubba da musabbibai shi da yake iko kan samuwa, ta ko wace fuska ba ya kasancewa da ma'anar lalata dokokin Allah da sunnoninsa da suke gudana suke jagorantar duniya, kuma ba karkacewa ba ne daga madaidaicin siraɗi miƙaƙƙe.[56]

Ku Duba

Bayanin kula

  1. Ibn Manzoor, Lهsan al-Arab, 1405, juzu'i na 1, shafi na 223-227.
  2. Mustafawi, At-Tahqiq Fi Kalimati Kur'an Al-karim, 1360, juzu’i. 6, ku. 49.
  3. Suratul Tawbah, aya ta 5; Suratul Tauba, aya ta 2.
  4. Suratul Tawbah, aya ta 30-31.
  5. Suratul Yusuf, aya ta:106.
  6. Javadi Amoli, Tauhid Dar Qur'an, 2016, shafi. 571.
  7. Hosseini Shirazi, "Taqreebbil Al-Kur'an Ilal Al-Azhan", 1424 AH, juzu'i na 2, shafi na 390.
  8. Mustafavi, At-Tahaqiq fi kalamat al-Qur'an al-Karim, 1360, juzu'i na 6, shafi na 50.
  9. Mustafavi, At-Tahaqiq fi kalamat al-Qur'an al-Karim, 1360, juzu'i na 6, shafi na 49.
  10. Javadi Amoli, Tauhidi Dar Qur'an, 2016, shafi. 578.
  11. Javadi Amoli, Tauhidi Dar Qur'an, 2016, shafi. 578.
  12. Javadi Amoli, Tauhidi Dar Qur'an, 2016, shafi. 579-580
  13. Javadi Amoli, Tauhidi Dar Qur'an, 2016, shafi. 580-583
  14. Javadi Amoli, Tauhidi Dar Qur'an, 2016, shafi. 581-582
  15. Duba: Javadi Amoli, Tauhidi Dar Qur'an, 2016, shafi na 581-595.
  16. Makarem Shirazi, Payame Qur'an, 1374, juzu'i. 3, shafi na 209-210.
  17. Makarem Shirazi, Payam Quran, 1374, juzu'i. 3, shafi na 211-215; misali Suratul Najm aya ta 23 da suratun Anbiya aya ta 24.
  18. Suratul Nisa’i, aya ta 48.
  19. Qomi, Tafsirul Qommi, 1367, juzu'i. 1, shafi. 148.
  20. Allameh Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 165
  21. Muhaddith Nouri, Mustadrak al-Wasail, 1408 AH, juzu'i. 14, shafi. 332.
  22. Suratul Ma'idah, aya ta 17.
  23. Suratul Yusuf, aya ta:106.
  24. Suratul Tauba, aya ta 31.
  25. Suratul Isra’i, aya ta 64.
  26. Suratul Kahf, aya ta:110.
  27. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i. 69, shafi. 102; juzu'i. 90, shafi na 61-62.
  28. Amoli, Tafsir al-Muhit al-a'Azam, 1422 AH, juzu'i. 3, shafi na 189-190.
  29. Javadi Amoli, Tauhid Dar Qur'ani, shafi na 591-592.
  30. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i. 5, shafi. 148.
  31. Ibn Shu'bah Harrani, Tuhaf al-Uqol, 1404 AH, shafi na 487.
  32. Suratul Yunus, aya ta 66.
  33. Javadi Amoli, Tauhid Dar Qur'an, 2016, shafi. 644.
  34. Suratul An'am, aya ta 100.
  35. Javadi Amoli, Tauhid Dar Qur'ani, 2016, shafi na 635-680.
  36. Suratul Ma'idah, aya ta:72.
  37. Suratul Nisa’i, aya ta 116.
  38. Suratul Nisa’i, aya ta 48.
  39. Suratul Ma'idah, aya ta:72.
  40. Suratul Zumar, aya ta 65.
  41. Javadi Amoli, Tauhid Dar Qur'an, 2016, shafi na 681-691.
  42. Suratul Nisa’i, aya ta 48.
  43. Suratul Tauba, aya ta:28.
  44. Fadhil Lankarani, Tafsilul al-Shari'ah, 1409 AH, shafi. 206.
  45. Sheikh Tusi, Al-Nihayah, 1400 AH, shafi. 457.
  46. Ibn Taimiyyah, Majmu’ul Fatawa, 1416H, juzu’i. 1, shafi. 159.
  47. Ibnu Taimiyyah, Ziyaratul Qubur Wal Istinjad Bil makbur, 1412H, shafi na. 19.
  48. .https://lms.motahari.ir/advance-search?searchText=شفاعت%20&isSameWord=true&
  49. Qaffari, Usulu Mazhab Ash-Shi'a, juzu'i. 1, shafi. 480.
  50. Sobhani, Ayineh Wahabiyyat, shafi. 41.
  51. Jagora, Shi'a Wa Pasokh Be Cand Purseshe, 2006, shafi. 84.
  52. Suratul Taha, aya ta:109.
  53. Suratul Taha, aya ta:84-85
  54. Sobhani Tabrizi, Marzehaye Tauhid Wa Shirk Dar Qur'an, 2001, shafi. 159; Javadi Amoli, Tauhid Dar Qur'an, 2016, shafi na 600-6004.
  55. .https://lms.motahari.ir/advance-search?searchText=شفاعت%20&isSameWord=true&
  56. Tabatabaei, Al-Mizan, 1393 AH, juzu'i. 1, shafi na 163-164

Tsokaci

  1. Misalin:«وَ مَنْ یدْعُ مَعَ اللَّـهِ إِلهاً آخَرَ لابُرْهانَ لَهُ بِهِ. Tarjama:Duk wanda yake kiran wani abun bauta daban tare da Allah ba tabbas ba shi da wani dalili kan hakanSuratul Muminun Aya Ta 17
  2. وَ ما یتَّبِعُ الَّذینَ یدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّـهِ شُرَكاءَ إِنْ یتَّبِعُونَ إِلاَّ الظَّنَّ وَ إِنْ هُمْ إِلاَّ یَخْرُصُون. Tarjama: Kuma waɗanda suke kiran wanin Allah da sunan abokin tarayya gare Shi, suna bin tunanin banza ne, kuma su fa ba sa faɗin gaskiya.
  3. وَمَا یؤْمِنُ أَكْثَرُهُمْ بِاللَّـهِ إِلا وَهُمْ مُشْرِكُون.Tarjama:Kuma mafi yawansu ba sa yin imani da Allah sai da suna yin shirka.(Suratu Yusuf, aya ta 106)
  4. «إِنَّهُ مَن يُشْرِكْ بِاللَّـهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللَّـهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ وَمَأْوَاهُ النَّارُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ»(سوره مائده، آیه ۷۲).
  5. «إِنَّهُ مَن يُشْرِكْ بِاللَّـهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللَّـهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ وَمَأْوَاهُ النَّارُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ»(سوره مائده، آیه ۷۲).
  6. وَلَقَدْ أُوحِيَ إِلَيْكَ وَإِلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكَ لَئِنْ أَشْرَكْتَ لَيَحْبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ(سوره زمر، آیه۶۵.)

Nassoshi

  • Amoli, Seyyed Haider, Tafsir al-Muhit al-a'Azam Wa Bahr al-Khasam fi Tawwil Kitab Allah al-Aziz al-Mahkam, bincike na Mohsen Mousavi Tabrizi, Qom, Noor Ali Noor Cultural Institute and Publication, 1422/1380.
  • Ibn Taimiyyah, Ahmad bn Abdul Halim, Ziyaratu Al-qubur Wal Istinjad Bil Maqbur, Darul-Sahaba na Tarihi, Tanta (Masar), 1412H.
  • Ibn Taimiyyah, Ahmad bin Abdul Halim, Majmu'ul al-Fatawi, bincike na Sheikh Abd al-Rahman bin Qasim, al-Madina al-Nabawiyah, Majma al-Mulk Fahd, na bugun al-Musaf al-Sharif, 1416 Hijira.
  • Ibn Shuba Harrani, Hasan bin Ali, Tohaf al-uqool, gyara: Ali Akbar Ghafari, Kum, Jamia Madrasin, 1404 AH/1363 AH.
  • Ibn Manzoor, Muhammad Bin Makram, Lisanul Al-arab, Qum, Adab al-Hawza, 1405.
  • Ostadi, Reza, Shi'a Wa Pasookh Beh Cande Pursesh, Tehran, Mashaar, 2005.
  • Javadi Amoli, Abdullah, Tauhid Dar Qur'an, Qum, Israa Publishing Center, 2016.
  • Hosseini Shirazi, Sayyid Muhammad, Taqribu Al-Qur'an Ila Al-Azhan, Beirut, Darul Ulum, 1424H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bn Hassan, Annhaya Fi Mujarradil Al-Fiqhe Wal Fatawi, Beirut, Darul Kitab al-Arabi, 1400H.
  • Sobhani Tabrizi, Jafar, Marzeahaye Tauhid Wa Shirk Dar Qur’an, Mahdi Azizan ya fassara, Tehran, Mashaar, 1380.
  • Allameh Tabatabaei, Muhammad Hussein, Al-mizan FI Tafsir Alqur'an, Qum, ofishin yada labaran musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta Qum, shekara ta 1417 bayan hijira.
  • Fadel Lankarani, Muhammad, Tafsilul al-Shari'ah FI SHarhe Tahrir al-Wasilah - Al-Nijasat Wa Ahkamiha, Qom, 1409H.
  • Qaffari, Nasser bin Abdullah, Usulu Mazhaba Shi'aIsna Ashariyya Ardu Wa Naqzu.
  • Qummi, Ali bin Ibrahim, Tafsir Qummi, Sayyid Taabib Musawi Jazayeri ya yi bincike, Qum, Darul-Kitab, 1367H.
  • Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya al-Turaht al-Araby, 1403H.
  • Muhaddith Nouri, Hussein bin Muhammad Taqi, Mustadrak al-Wasael wa Mustanbat al-Masal, Qum, Aal al-Bait Foundation, amincin Allah ya tabbata a gare su, 1408H.
  • Mustafavi, Hassan, At-Tahqiq FI Kalemat Qunr'an Al-karim, Tehran, Kamfanin Fassara da Bugawa, 1360H.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Payam al-Quran, Qom, Hadaf Press, 1374 AH.