Zabihullah

Daga wikishia
Babban Allo na zanen kwamitin gwaji na Master Farshchian

Zabihullah (Larabci: ذبيح الله) Lakabi ne na Isma’il Bn Hazrat Ibrahim wanda Allah ya bada umarni yanka shi ga Ibrahim, hakika Alkur’ani ya kawo Kissar yankan amma bai ambaci sunan wanda za a yanka ba, hakika `Yan Shi’a sun tafi kan cewa Zabihullah Lakabi ne na Hazrat Isma’il, su kuma Yahudawa suna ganin Lakabin Hazrat Is’hak ne, Ahlus-sunna suna da sabanin ra’ayi kan cewa shin lakabin Isma’il ne ko Is’hak.

Kissar Yanka

Asalin Makala: Yanka Isma’il zabihullah ma’anarsa shi ne abinda aka sadaukar aka yanka saboda Allah, zabihullah Lakabi na daya daga `ya`yan Annabi Ibrahim (A.S) wanda Allah ya bashi umarni ya yanka shi saboda Allah, [1] kan asasin rahotan da Alkur’ani ya bayar Hazrat Ibrahim ya yi mafarki yana yanka dansa, bayan ya farka daga barci sai fadawa dansa abin da ya faru, sai dansa ya ce ya zartar da umarnin Allah a kansa, lokacin da dukkaninsu suka sallamawa umarnin Allah, sannan Ibrahim ya kwantar da dansa domin yanka shi kwatsam sai wani kira ya zo : ya Ibrahim! Hakika ka gasgata Mafarkinka, lallai haka muke sakawa masu kyawunta aiki [ma’ana muna karbar kyakkyawar niyyarsu mayin aiki] da yakini wannan bayyananniyar jarrabawa ta kasance, hakika mu mun fanshi dansa da wani abun yanka mai girma. [2] kan asasin riwayoyi Jibrilu ne bisa umarnin Allah ya yi sauri ya janye dan Ibrahim ya ajiye wani Rago da ya dauko daga Aljanna sai Wukar da take Hannun Ibrahim ta yanka rago maimakon dansa. [3] Sunnar layya da ake a ranar Idin Babbar Sallah ta kasance don tunawa da Kissar Yankan Ibrahim. [4] Zabhu a luggance yana nufin yanke Kai. [5]

Wane ne ake yi wa Lakabi da zabihullah?

Zanen zabihullahi Ismail na Mohammad Zaman

Alkur’ani ya kawo labarin yanka, amma bai fadi sunan wanda aka yi yunkurin yankawa ba. [6] zabihullah Lakabin wane ne cikin `Ya`yan Ibrahim, akwai ra’ayoyi guda biyu, wasu sun ce Lakabin Isma’il ne wasu kuma sun tafi kan cewa lakabin Is’hak ne, Allama Majlisi a cikin Bihar-Anwar ya tattaro riwayoyin ra’yoyin biyu. [7]

Isma’il

Malaman tafsiri na Shi’a tare da dogara da ayoyi 101-103 Suratul Saffat [yadasht1] sun yi Imani cewa Lakabin Isma’il ne, sakamakon kasancewar busharar haihuwar Is’hak [8] ta kasance ne bayan busharar haihuwar Isma’il da kuma Kissar Yanka, [9] da aka aikowa Ibrahim [10] a cewar Ayatullahi Makarim Shirazi wadanda suka zabi cewa zabihullah Lakabin Is’hak ne suna ganin busharori biyu da aka yiwa Ibrahim da suka zo cikin Alkur’ani duka sun zo ne kan Is’hak, bushara ta farko dangane da haihuwarsa ta biyu dangane da Annabtarsa, a ra’ayin Malamin ayoyin da aka ambata a bayyane suna nuni kan cewa busharorin biyu suna da alaka da `ya`yan Ibrahim guda biyu, [11] haka kuma Allama Tabataba’i ya yi Imani kan cewa siyaki da koro ayoyin da bayyana karara ya na nuni kan cewa Isma’il shi ne wanda ayar yanka take Magana kansa. [12] Cikin ba’arin wasu riwayoyi an ambaci Isma’il da lakabin zabihullah, daga jumla a wata riwaya da Annabi (S.A.W) yake kiran kansa da Ibnu Zabihaini (`dan abin yanka guda biyu) [13] haka kuma cikin Du’a’u Mashlul da ake dangantata ga Imam Ali (A.S) [14] da kuma cikin wata riwaya da aka nakaltota daga Imam Sadik [15] da Imam Rida (A.S) [16] an gabatar da Isma’il da unwanin zabihullah, haka cikin Ziyaratu Gufaila ziyarar da ta kebanci Imam Husaini (A.S) a tsakiyar Rajab cikin Kalmar:

«السَّلامُ عَلَیک یا وارِثَ إسماعیلَ ذَبیحِ اللّه»

Amincin Allah ya Magajin Isma’il zabihullah. [17] Wasu ba’ari Marubuta suna ganin Kissar Hijirar Hajara da haihuwa isma’il suna da alaka da batun Yanka, sannan Kissar yanka Isma’il ita ce take kamala Kissar, [18] Shaik Saduk cikin ishara zuwa ga sassabawar Riwayoyi, ya tafi kan cewa Isma’il ne zabihullah, yana cewa kasancewar an haifi Is’hak bayan waki’ar Yanka, ya kasance yana burin ace shi ne wanda aka umarci Mahaifinsa ya yanka shi, sai shima ya sallamawa umarnin Allah kamar dai misalin Isma’il, ya lazimci hakuri sai ya samu ladan da Isma’il ya samu. [19]

Wasu ba’ari Malaman tafsiri na Ahlus-sunna tare da jingina da wani curi daga wadannan riwayoyi na yanka sun tafi kan cewa Isma’il ne wanda aka bada umarni a yanka, an jingina wannan Magana zuwa ga Abu Huraira, Amir bn Wasila, Abdullahi Bn Umar, Ibn Abbas, Sa’idu Bn Musayyab, Yusuf Bn Mihran da Rabi’u Bn Anas, [20] haka kuma Fakhrur Razi da Ibn Ashur sun kawo tsammani kan cewa Isma’il ne zabihullah. [21]

Is’hak

Wasu ba’arin Malaman tafsiri daga Ahlus-sunna suna ganin zabihullah lakabi ne na Is’hak, an danganta wannan Magana zuwa ga misalin Umar Bn Khaddab, Sa’idu Bn Zubair, Ka’abul Ahbar, Katada, Zuhri,Tabari da Malik Bn Anas, [22] Ayatullahi Makarim Shirazi yana ganin cewa riwayoyin da suke bayyana cewa Is’hak ne zabihullah, riwayoyi da suka kasance karkashin tasirin Isra’iliyat, kuma akwai tsammanin kasancewarsu kikrkirar Yahudawa. [23] Haka kuma a cikin At-Taura an gabatar da Is’hak matsayin zabihullah, [24] na’am a wasu wuraren ya zo cewa zabihullah da ne daga `Yayan Ibrahim. [25]

Ibnu Zabihaini

A wasu riwayoyi kan asasin labarin Bakancen Abdul-Mutallib da ya yi alkawarin cewa zai yi layyan da daya daga cikin `ya`yansa cikin tafarkin Allah, sai ya zamana ana kiran Abdullahi Mahaifin Annabi (S.A.W) da Zabihu shi kuma Annabi (S.A.W) da lakabin Ibn Zabihaini. [26] [yadasht 2]

Bayanin kula

  1. Suratul Safat, aya ta:102.
  2. Suratul Safat, aya ta 101 zuwa 108
  3. Kilini, Al-Kafi, 1407, juzu'i na 4, shafi na 208
  4. Sadeghi Tehrani, Al Balag, 1419 AH, shafi na 450; Sayyid Qutb, fi Zilalul Alqur'an, 1412 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 299
  5. Dehkhoda,Luggannameh, ƙarƙashin kalmar Zibhu.
  6. Duba Suratul Safat, aya ta:102.
  7. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 12, shafi na 132-137.
  8. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 12, shafi na 132-137.
  9. Suratul Safat, aya ta 101-107.
  10. Makarem Shirazi, Tafsir namuneh, 1374, juzu'i na 19, shafi na 129.
  11. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 19, shafi na 129.
  12. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 155.
  13. Sheikh Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 210; Sheikh Sadouq, Al-Khasal, 1362, juzu'i na 1, shafi na 56-58.
  14. Kafami, al-Mesbah, 1405 AH, shafi na 263.
  15. Qommi, Tafsirin Qummi, 1404, juzu'i na 2, shafi na 226; Sheikh Sadouq, Man Laihzar al-Faqih, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 230.
  16. Kulaini, Al-Kafi, 1407H, juzu'i na 6, shafi na 310.
  17. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Husaini (AS), 1388, juzu'i na 12, shafi na 127.
  18. Makarem Shirazi, Tafsir namuneh, 1374, juzu'i na 19, shafi 120
  19. Sheikh Sadouq, Al-Khasal, 1362, juzu'i na 1, shafi na 57-58.
  20. Qortubi, Al-Jamae Lahkam Al-Qur'an, 1364, juzu'i na 16, shafi na 100.
  21. Fakhrazi, Mofatih al-Ghaib, 1420 AH, juzu'i na 26, shafi.351; Ibn Ashur, Tahrir wa al-Tanvir, Beta, juzu'i na 23, shafi na 70-69.
  22. Qortubi, Al-Jamae Lahkam Al-Qur'an, 1364, juzu'i na 16, shafi na 100.
  23. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 19, shafi na 119-120.
  24. Attaura, Sefer Paidayesh, 22:1-14.
  25. Attaura, Paidayesh, 22:2.
  26. Sheikh Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 210.

Nassoshi

  • Ibn Ashur, Muhammad Ibn Tahir, Tahrir da al-Tanvir, Beirut, Cibiyar Tarihi, 1420H.
  • Ibn Hisham, Abdul Malik Ibn Hisham, Al-Sira Al-Nabawiyyah, Dar al-Marifa, Beta.
  • Mohammadi Rishahri, Muhammad, Danshnameh Imam Hossein (a.s) bisa Alqur'ani, Hadisi da Tarihi, Wallafar Cibiyar Kimiyya da Al'adu ta Dar al-Hadith, Qum, bugu na biyu, 2008.
  • Dehkhoda, Ali Akbar,Luggatname, Tehran, Dehkhoda Dictionary Institute, 1341.
  • Sayyid Qutb,Fi Zialul Alqur'an, Darul Shoroq, Beirut, Alkahira, 1412H.
  • Sheikh Sadouq, Ayun Akhbar al-Reza (AS), Mehdi Lajordi, Tehran, Nash Jahan, bugun farko, 1378H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Al-Khesal, editan: Ali Akbar Ghafari, Kum, Jamia Modaresin, 1362.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Man Laihzara al-Faqih, edited by Ali Akbar Ghafari, Qum, Islamic Publications Office, 1413 AH.
  • Sadeghi Tehrani, Mohammad, Al-Balaagh fi Tafsir Alkur'an bil Alkur'ani, marubuci, Qum, bugun farko, 1419 Hijira.
  • Tabatabaei, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Qum, Islamic Publications Office, bugu na biyar, 1417H.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, Mufatih al-Ghaib, Dar Ahya al-Trath al-Arabi, Beirut, bugu na uku, 1420H.
  • Qortubi, Muhammad bin Ahmad, Al-Jame Lahkam Al-Qur'an, Tehran, Nasser Khosrow Publications, 1364.
  • Qommi, Ali Ibn Ibrahim, Tafsirin Qummi, Seyyed Tayyeb Musawi Al-Jazairi ya gyara, Darul Katab, Qum, bugu na uku, 1404H.
  • Kafami, al-Mesbah, Ibrahim bin Ali, Kum, Dar al-Rezi (Zahidi), 1405H.
  • Kulaini, Al-Kafi, edita: Ali Akbar Ghafari da Mohammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1407H.
  • Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, Al-Wafa Foundation, 1403 AH.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiyya, bugun farko, 1374.