Gaskiya Kamar Yadda Take (Littafi)
Gaskiya Kamar Yadda Take, (arabic: الحقيقة كما هي (كتاب)) wani takaitaccen littafi ne cikin bayyana tunanin Shi'a Imamiya talifin Jafar Alhadi wanda ya rasu a shekara ta 1399 h shamsi, Malami ne na Shi'a, haƙiƙa marubucin littafin ya yi bahasi tare da Amfani da ayoyin Alkur'ani da hadisai da karkata da nazarinsa zuwa ga gabatar da mene ne Shi'anci, Alhaƙiƙa kama Hiya (haƙiƙa kamar yanda take) littafi ne da ya rubuta shi cikin harshen larabci, cibiyar Majma Jahani Ahlil-Baiti a shekara ta 1384 h shamsi, ta ɗauki nauyin buga wannan littafi da yaɗa shi har zuwa watan Mehr shekara ta1402 h shamsi, sannan an sanyawa tarjamar da aka yi ta farinsanci sunan Haƙiƙat Angune ke hast. An samar da kwafin sautin wannan littafi cikin harshen Sipaniyanci, Faransanci da Indunisiyanci,
Gabatarwa
Alhaƙiƙa kama Hiya (Haƙiƙat Angune ke hast) wani littafi ne cikin harshen Larabci da aka rubuta shi don bayyana Aƙidun Shi'a Imamiyya tare da Amfani da ayoyi da riwayoyi. [1] Marubucin wannan littafi ya kasance Jafar Alhadi wanda ya rasu shekara ta 1399 h shamsi, ya kasance Malamin Shi'a Mutumin ƙasar Iraƙ, kuma yana cikin Membobin Shura a cibiyar Majma Jahani Ahlil-Baiti (A.S) Malamin ya yi bakin ƙoƙarinsa da bada lokacinsa da karakata nazari zuwa ga dukkanin hujja da dalili da kuma ishara zuwa ga Shubhohi, tuhumomi, da saɓanin da yake tsakanin Firƙoƙin Muslunci, tare da gabatarwa da kuma taƙaitaccen bayani kan tushen tunanin Shi'a. [2] Marubucin ya tsara Maudu'ai guda Arba'in domin bahasi cikin wuraren da Aƙidun Shi'anci suka bambanta da Aƙidun sauran Firƙoƙin Muslunci. [3] an tarjama wannan littafi zuwa Harsuna 33 an buga an yaɗa su. [4]
Tsarin Littafi Da Abin da ya Tattaro
Alhaƙiƙa kama Hiya, taƙaitaccen littafi ne da ya tattaro Muƙaddimar wanda suka yaɗa littafin da kuma Muƙaddima daga Marubucinsa, Matanin littafin bashi da Fihirisa (Conteɗt) haka babu fasaloli, [5] littafin ya tattara kan zirin Maudu'ai guda Arba'in, na tsara lambobi kan bayanin Shi'anci da Aƙidunsa. [6] abin da littafin ya ƙunsa kan tsarin fihirisa ya kasance kamar yanda bayani zai zo a ƙasa:
- buƙatuwar dukkanin Mabiyan Mazhabobin Muslunci zuwa ga sanin junansu da kuma rayuwar zaman lafiya da juna.
- Saɓawar Shi'anci da rashin yarda da Mazhabobin Turawan Mulkin Mallaka kamar misalin Baha'iyyat, Babiyya da ƙadiyaniyya.
- Bayanin Aƙidun Shi'a Isna Ashariyya dangane da Tauhidi, Adalci, Annabta, Ma'ad (Alƙiyama) da Imamanci.
- imanin `Yan Shi'a da Ismar A'imma, Imaninsu da samuwar Imam Mahadi (A.F) da kuma jiran bayyanarsa, gamagarin Na'ibancin Malaman fiƙihu ga Imam zaman a zamanin Gaiba Kubra.
- Imani na aiki kan wajabcin yin sallah, Azumi, Hajji, Zakka, Khumusi, Jihadi, wilaya da bara'a da Amru bil ma'aruf wa nahayi Anil Munkar.
- Imani da halasci da ingancin aure Mutu'a da kuma haramcin Zina, Liwadi, Riba, Shan Barasa, kashe rai, Caca, ɓoyen kayan Abinci a lokacin tsananin buƙatarsu, kwace, tuhuma, gulma, zagi, ƙarya, ƙage dukkaninsu haramun ne kuma suna daga Manya-manyan zunubai.
- Himmatuwar Shi'anci da Mas'alar Makarimul Akhlaƙ da falalolin Akhlaƙ, da kuma zage dantse cikin gina Ma'anawiyya da karkata zuwa ga Addu'o'in da suka zo daga Ma'asumai (A.S) da `ya`yan Imamai, da kuma bada amsoshi kan shubuhohi da tuhumomin Masu Saɓani da Mazhabar Shi'a dangane da ziyara, ceto, Tawassuli, taƙlidi, girmama Ma'asumai, zagi da la'anar Khulafa, DDS…
- Gabatar da muhimmai masadir na riwayoyin Shi'a daga Kutubul Al-Arba'a, Nahjul Balaga da Sahifa Sajjadiyya.
- Imanin `Yan Shi'a Jafariyya da haƙƙin Musulamai domin amfanuwa da hukumar Muslunci da ɗoru kan asasin Alkur'ani da sunna da manufar kare haƙƙoƙin Musulmai da kuma tabbatar da Alaƙoƙi na adalci da zaman lafiya da sauran ƙasashe da bada kariya ga iyakoki da kuma lamintar da cin gashin kan Al'adu, tattalin arziƙi da siyasar Musulmai domin samun izza wacce Alkur'ani ya yi wasicci da ita. [7]
Bayanin kula
- ↑ <a class="eɗternal teɗt" href="https://fa.abna24.com/story/1102381">کتاب گویای "حقیقت آنگونه که هست" به سه زبان تولید شد</a>
- ↑ Kermani wa Rouzbeh, Ayineh Asar, 1401, shafi na 339.
- ↑ Kermani wa Rouzbeh, Ayineh Asar, 1401, shafi na 339.
- ↑ Kermani wa Rouzbeh, Ayineh Asar, 1401, shafi na 18.
- ↑ Al-Hadi, Al-Haƙiƙah Kama Hiya, 1426H.
- ↑ Al-Hadi, Al-Haƙiƙah Kama Hiya, 1426H.
- ↑ a class="external text" href="https://hawzah.net/fa/News/view/82717">کتاب «حقیقت؛ آنگونه که هست» از سوی معاونت امور فرهنگی مجمع جهانی اهل بیت(ع) منتشر شد.
Nassoshi
- Al-Hadi, Jafar, Al-Haƙiƙah Kama Hiya, Markaz caf Nashar Ahlul Baiti Jahani, bugun farko, 1426 Hij* Kermani, Abdul Karim wa Seyyed Ali Rouzbeh, Ayineh Asar: Karnameh Tarjameh Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S.) 1399-1369), ƙum, Intihsharatu Majma Jahani Ahlul-Baiti ta Duniya, 1401.
- کتاب گویای "حقیقت آنگونه که هست" به سه زبان تولید شد خبرگزاری ابنا، تاریخ درج مطلب: ۲۸ آذر ۱۴۰۰ش، تاریخ بازدید: ۸ آبان ۱۴۰۲ش.
- کتاب «حقیقت آن گونه که هست» از سوی معاونت امور فرهنگی مجمع جهانی اهل بیت(ع) منتشر شد. پایگاه اطلاع رسانی حوزه، تاریخ درج مطلب: ۲۹ اسفند ۱۳۸۸ش، تاریخ بازدید: ۸ آبان ۱۴۰۲ش.
ira.