Dukiya ta Halas wadda ta cakuɗa da Haram

Daga wikishia
Wannan wani rubutu ne mai bayyanawa game da ra'ayi na fikihu kuma ba zai iya zama ma'auni na ayyukan addini ba. Koma zuwa wasu tushe don ayyukan addini
Risala

Dukiyar da ta haɗe da haram,(Larabci:المال المخلوط بالحرام) dukiya ce wacce wani ɓarayi na ta an same shi ne ta hanyar halal, wani ɓarayi kuma an same shi ta hanyar haram[1] kuma yana da banbanci da dukiyar Shubuha domin ita dukiyar shubuha ana shakkar haɗewarta da haram.[2] A fikihun musulunci bai halasta ayi amfani da dukiyar da ya cakuɗa da haram.[3]

Kamar yadda malaman fikihun Shi'a suka ce, idan an san adadin kuɗin da mai shi, to sai a mayar mi shi.[4] Amma idan an san adadin kuɗi, amma ba a san mai su ba , to bisa fatawar wasu malaman fikihu, to dole ne a yi sadaka a madadin ma'abucinsu, kuma wajibi ne a sami izini daga wurin Hakimul shari'a.[5] Sabanin haka, idan har an san wanda ya mallaki kuɗin, amma ba a san adadin kuɗin ba, wasu malaman fikihu sun ce dole ne a ba shi yadda zai gan su, idan kuma bai gamsu ba, to sai a ba shi adadin kudin da ake da yaƙini haka ne.[6]

Amma idan ya zamo ba'asan adadin kuɗin ba, malaman Shi'a suna ganin irin wanna kuɗin ɗaya ne daga cikin gurin wurare bakwai da yake wajibi a fitar da Kh[7]umusi wannan fatawar ita ce ra'ayi sananne a gurin malaman fikihu na Shi'a[8] amma wasu daga cikin malaman Ahlus-suna sun tafi kan cewa ba wajibi bane fitar da Kumusi daga dukiya ko kuɗin da ya cakuɗa da haram ba.[9]

Idan aka sami mai kuɗin da aka cakuɗa da haram, kamar yadda wasu malaman addini suka ce, kamar Imam Khomaini Sayyid Ali Al-Sistani, Makarim Shirazi, ya wajaba a biya adadin kudin ga mai shi. a matsayin taka tsantsan na wajibi, amma wasu kamar su Sayyid Kuyi, Sayyid Muhammad Rida Al-Gulfaigani, Muhammad Ali Al-Araki, Mirza Jawad Al-Tabrizi, suna ganin cewa babu wani abu da yake wajibi da za'a bashi.[10]

Bayanin kula

  1. Duba: Montazeri, Mabani Fiqh hukumat Islami, 1409H, juzu'i na 6, shafi na 184.
  2. Duba: Montazeri, Mabani Fiqh hukumat Islami, 1409H, juzu'i na 6, shafi na 184.
  3. Misali, duba: Sheikh Ansari, Kitab al-Khams, 1415 AH, shafi 111; Shahid Sani, Masalak al-Afham, 1413 AH, juzu'i na 3, shafi na 141.
  4. Bahrani, al-Hadaeq al-Nadrah, 1405 AH, juzu'i na 12, shafi na 364; Esfahani, Wasileh al-Najat (tare da bayanin al-Golbayigani), 1393 AH, juzu'i na 1, shafi na 318.
  5. Khumaini, Tauzihul Al-Masa'il (Mohshi), 1424 AH, sashen Khums, fitowa ta 1814.
  6. Khumaini, Tauzihul Al-Masa'il (Mohshi), 1424 AH, sashen Khums, fitowa ta 1815.
  7. Misali, duba: Najafi, Jawahirul alKalam, 1404 AH, juzu’i na 16, shafi.69; Khumaini, Tauzihul Al-Masa'il (Mohshi), 1424 AH, juzu'i na 2, shafi na 47.
  8. Muassaseh dayiratul ma'arif fikh islami ,Farhang fikh mutabik mazhab Ahlul-Baiti (AS), 1426 AH, juzu'i na 3, shafi na 499; Esfahani, Wasileh Al-Najat (Al-Golbayigani bayanin kula), 1393 AH, juzu'i na 1, shafi na 318; Khumaini, Tauzihul al-Masa'il (Mohshi), 1424 AH, baksh Khums, fitowa ta 1813.
  9. Ansari Shirazi wa digaran, Mausu'atu Ahkami Atfal, 1429 AH, juzu'i na 1, shafi na 470.
  10. Khomeini, Tauzihul al-Masal (Mohshi), 1424H, sashe Khums, fitowa ta 1817.

Nassoshi

  • Esfahani, Sayyid Abu Al-Hassan, Wasila Al-Najat (ma'a Al-Golpaygani Margins), Qum, Mawallafin Mehr, bugu na 1, 1393H.
  • Ansari Shirazi, Kudratullahi wa digaran, Mausu'atu Ahkami Atfal, Qum, Markaz fikhi A'immeh Athar (A.S)1429H.
  • Bahrani, al-Hadaiq al-Nadrah fi Haqam al-Utrah al-Tahira, 1405H.
  • Khomeini, Sayyid Ruhollah, Tauzihul Masa'il (Mohshi), Tahkik wa tashihi Sayyid Mohammad Hasan Bani Hashemi, Qum, Ofishin Daba'ar Musulunci, bugu 8, 1424H.
  • Shaheed Thani, Zain al-Din bin Ali, Masalak al-Afham al-Tankih Shar'e al-Islam, wanda kungiyar bincike ta Cibiyar Nazarin Musulunci ta Qom, Cibiyar Al-Maarif al-Islami, bugun farko. 1413 AH.
  • Sheikh Ansari, Morteza, Kitab al-Khums, kungiyar bincike a majalisa, Qum, Congress girmama Sheikh Azam Ansari, bugu na farko, 1415 AH.
  • Muassaseh dayiratul ma'arif fikh islami, farhang Fikihu mutabik mazhab Ahlul-Baiti (AS), karkashin kulawar Sayyid Mahmoud Hashemi Shahroudi, Qum, Institute of Islamic Jurisprudence Encyclopaedia on Ahlul-Bait (AS), bugu na farko, 1426 AH.
  • Montazeri, Hossein Ali, mabani Fiqhu hukumat Islami, Mahmoud Salvati wa Abulfazl Shakuri, Qom, Cibiyar Kayhan, bugun farko, 1409H.
  • Najafi, Mohammad Hasan, Javaher al-Kalam fi Sharh Shar'e al-Islam, Abbas Quchani wa Ali Akhundi, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na 7, 1404H.