Jump to content

Daƙiƙa:Suratul Mulki

Daga wikishia
Suratul Mulki
Suratul Mulki
Lambar Sura67
Juzu'i29
Jerantuwa Ta Sauka77
Adadin Ayoyi30
Adadin Kalmomi328
Adadin Haruffa1436
Makkiya/MadaniyyaMakka


Suratul Mulki ko Tabarak sura ce ta 57 cikin juzi'i na 29 a Alƙur'ani mai girma, wannan sura tana cikin surorin da suka sauka a Makka, sunan wannan sura ya zo cikin aya ta farko ta wannan sura, surar tana magana kan mahalicci da siffofinshi da tsarin halitttar Allah, da magana kan Ma'ad wato koma da duk abin da zai gudana da magana kan gargaɗi da jan kunne ga azzalumai da kafirai.

Cikin ayoyinta waɗanda suka shahara akwai faɗar Allah maɗaukaki, cewa (Shi ne Wanda Ya halicci mutuwa da rayuwa domin Ya jarrabe ku, Ya ga wanene a cikinku ya fi kyautata aiki. Kuma Shi ne Mabuwayi, Mai gafara). wannan aya tana nuna Allah shi ne mai Mulki da iko na halittar ɗam Adam da mutuwarshi da rayuwarshi, kamar yadda wannan aya tana nuni kan kyan aiki ba yawanshi ba.

Ruwayoyi da yawa sun zo kan falalar karanta wannan sura, an rawaito daga Annabi (S.A.W) duk wanda ya karanta Suratul Mulki, to tamkar ya raya daren Lailatul ƙadri ne.

Sanya Suna Da Ayoyinta

Wannan sura ana kiranta da Mulku, saboda ayarta ta farko, saboda wannan sura tana magana ne kan mulkin Allah maɗaukaki kan wannan duniya da dukkan abin da yake cikinta hadda ɗan Adam[1] kazalika ana kiranta da Tabarak da Mani'a da Munjiya da Mujadala da Waƙiya[2] tana da ayoyi 30 da kalmomi 328 haruffa 1436, ana la'akarinta cikin surori Mufassalat, abin nufi surori masu ayoyi da yawa amma ƙanana ne,[3] kuma tana cikin surori Mumtahinat.[4]

Tsarin Da Aka Saukar Da Ita

Suratul Mulki ta sauka a Makka[5] ne kuma ta jerin sauka ita ce sura ta 77 data sauka ga Annabi (S.A.W) amma jerin yanzu cikin Alƙur'ani ita ce sura 67 a surorin Alƙur'ani.[6]

Ma'anonin Wasu Kalmominta

Ma'anoni masu muhimmanci na wasu kalmomi; (Liyabluwakum): Domin ya jarrabaku. (Fuɗur): Tsagewa. (Hasir): Wanda ya gaji kuma ya raunana. (Al-Gaizu): Fushi mai tsanani (Tamur): Tana girgiza kuma tana motsi. (Hasiban): Iska mai ƙarfi wacca take ɗauke ƙananan duwatsu, saboda haka ake cewa duk wanda yake jefa duwatsu Alhasib. (Gauran): Wanda ƙasa ta tsotse ko ya shige cikinta. (Bi Ma'in Ma'in): Ruwa mai gudana ko mai sauƙin sha.[7]

Abun Ciki

A taƙaice wannan sura taƙunshe abubuwa guda 3:

  1. Wannan sura tana magana kan siffofin Allah maɗaukaki da tsarin halitta mai ban mamaki, masamman halittar sammai da taurari da ƙasa, da halittar tsintsaye da ruwa mai gudana da mariskai, kamar kunne da ido da makamantansu.
  2. Wannan sura tana magana kan tashin alƙiyama da azabarta, da tattaunawar data gudanan tsakanin Mala'ikun azaba da ƴan wuta.
  3. Wannan sura tana Magana gargaɗe da jan kunne kan nau'o'i na azaba a duniya da lahira ga kafirai da azzalumai.[8]

Shahararrun Ayoyi

Faɗar Allah maɗaukaki, cewa (Shi ne Wanda Ya halicci mutuwa da rayuwa domin Ya jarrabe ku, Ya ga wanene a cikinku ya fi kyautata aiki. Kuma Shi ne Mabuwayi, Mai gafara),[10] ya zo cikin litattafan tafsiri, cewa wannan aya tana nuni kan hadafin halittar ɗan Adam da mutuwarshi da rayuwarshi, waɗannan abubuwa suna cikin Mulkin Allah da ikonshi, sannan ambatar mutuwa a nan kafin rayuwa ya faru ne sakamakon babban tasirin da take da shi ne dangane da rayuwa, ƙari kan cewa ita mutuwa ta kasance kafin rayuwa. Amma hadafin yin jarabawa ga ɗan Adam, ita ce tarbiya ga ɗan Adam, ya sami dakewa da taƙawa, kazalika wannan sura tana nuni kan kyautata aiki, ba yawanshi ba, wannan dalili ne kan cewa Musulunci yana bawa nagarta muhimmanci ba yawa ba, abin da yake da muhimmanci shi ne mutum ya yi aiki domin Allah, kuma mai amfani ga al'umma ko da ba shi da yawa kowa.[11]

Falaloli Da Fa'idoji

An rawaito falaloli da yawa kan suratu mulku;

  • An rawaito daga Annabi (S.A.W) duk wanda ya karanta Suratul Mulki, tamkar ya raya daran Lailatul ƙadri ne.[12] kazalika an rawaito daga gare shi cewa wannan sura ta Tabarak tana cikin zuciyar duk wani mumini.[13]
  • An rawaitao daga Imam Sadiƙ (A.S) duk wanda ya karanta Suratul Mulki kafin ya yi bacci, to zai kasance cikin amincin Allah har gari ya waye, kazalika zai ci gaba da kasancewa cikin aminci har ranar alƙiyama kuma har sai ya shiga aljanna insha Allah.[14]
  • An rawaito abin da ya keɓanta da wannan sura da yawa cikin wasu ruwayoyi, daga cikinsu an rawaito daga Manzon Allah (S.A.W) cewa duk wanda ya haddace ta, to za ta zama abin ɗauke mishi kewa a cikin kabari, kuma za ta cece shi a gun Allah ranar alƙiyama har sai ya shiga aljanna cikin aminci, duk wanda ya karantata ya sadaukar da ita ga ƴan uwanshi, zata isa zuwa gare su kamar walƙiya, kuma za ta sassauta musu halin da suke ciki kazalika za ta ɗebe musu kewa.[15]

Bayanin klula

  1. ↑ Musawi, Al-Wadihu Fit Tafsir, juzu'i na 16, shafi na 218
  2. ↑ Ɗabrisi, Majma'ul Bayan, juzu'i na 10, shafi na 61; Alusi, Ruhul Ma'ani, juzu'i na 29, shafi na 38.
  3. ↑ Khurramshahi, Mausu'atu Qur'an Wad Dirasatul Qur'aniyya, juzu'i na 2, shafi na 1258.
  4. ↑ Ma'arifat, At-Tamhid, juzu'i na 1, shafi na 313.
  5. ↑ Ɗusi, At-Tibyan, juzu'i na 11, shafi na 279; Fakhrur Razi, At-Tafsirul Kabir, juzu'i na 30, shafi na 46.
  6. ↑ Ma'arifat, Ulum Qur'an, juzu'i na 1, shafi na 168.
  7. ↑ Musawi, Al-Wadihu Fit Tafsir, juzu'i na 16, shafi na 219-245.
  8. ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Al-Amsal, juzu'i na 18, 298.
  9. ↑ Khamagar, Sakhtare Surahaye Qur'an Karim.
  10. ↑ Suratul Mulki aya ta 2.
  11. ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Al-Amsal, juzu'i na 18, shafi na 300; Ɗabaɗaba'i, Almizan, juzu'i na 19, shafi na 405.
  12. ↑ Zamakhshari, Tafsir Al-Kashshaf, juzu'i na 4, shafi na 1670.
  13. ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Al-Amsal, juzu'i na 18, shafi na 299.
  14. ↑ Ɗabrsi, Majma'ul Bayan, juzu'i na 10, shafi na 50.
  15. ↑ Bahrani, Al-Burhan, juzu'i na 9, shafi 337.

Nassoshi

  • Qur'an Karim
  • Alusi, Shihab, Ruhul Ma'ani fi Tafsiril Qur'anil Azim was Sab'ul Masani, Beirut, Lebanon, Daru Ihya'it Turas al-Arabi, bugu na 1, 1421H.
  • Bahrani, Hashim Bin Sulaiman, Al-Burhan fi Tafsiril Qur'an, Beirut, Lebanon, Daru Ihya'it Turas al-Arabi, bugu na 1, 1429H.
  • Ɗabaɗaba'i, Muhammad Husaini, Almizan fi Tafsiril Qur'an, Qom, Iran, Darul Al-Mujtaba, bugu na 1, 1430H.
  • Ɗabrisi, Fadl Bin Hassan, Majma'ul Bayan, Beirut, Lebanon, Cibiyar Al-Amira, bugu na 1, 1430H.
  • Ɗusi, Muhammad Bin Hasan, At-Tibyan fi Tafsiril Qur'an, Qom, Iran, Cibiyar Nashril Islami, bugu na 1, 1431H.
  • Fakhrur Razi, Muhammad Bin Umar, At-Tafsiril Kabir, Beirut, Lebanon, Darul Kutubil Ilmiyya, bugu na 4, 1434H.
  • Khurramshahi, Baha'ud-Din, Mausu'atul Qur'an Wad Dirasatil Qur'aniyya, Iran, Tehran, Cibiyar Al-Asdiƙa, 1377Sh.
  • Ma'arifat, Muhammad Hadi, Tadrisul Ulumil Qur'aniyya, fassarar Abu Muhammad Fakili, Daru Nashrid Da'watil Islamiyya, 1371Sh.
  • Ma'arifat, Muhammad Hadi, At-Tamhid fi Ulumil Qur'an, Kum, Iran, Zawil Ƙurba, bugu na 1, 1428H.
  • Makarim Shirazi, Nasir, Al-Amsal fi Tafsiri Kitabillahil Munzal, Beirut, Lebanon, Cibiyar Al-amira, bugu na 2, 1430H.
  • Musawi, Abbas bin Ali, Al-Wadihu Fit Tafsir, Beirut, Lebanon, Cibiyar Al-Ghadir, bugu na 1, 1433H.
  • Zamakhshari, Mahmud Bin Umar, Al-Kashshaf, Beirut, Lebanon, Daru Sadir, bugu na 1, 1431H.