Daƙiƙa:Shekara Ta 1 Hijira
Appearance
Shekara 2 Hijira Ƙamari Shekara 0 Hijira Ƙamari | |
| 622-623M | |
|---|---|
| Imamanci | |
| Manzancin Sayyidina Muhammad | |
| Hukumomin ƙasashen Muslunci | |
| Muhammad Bin Abdullahi (S.A.W) a Madina | (Hukuma:1-11H) |
| Muhimman abubuwan da suka faru | |
| Hijira Annabi (S.A.W) daga Makka zuwa Madina | |
| Waƙi'ar Lailatul Mabit | |
| Kafa Masallacin Ƙuba, masallaci na farko na Musulmi, | |
| ƙulla ƴan uwantaka tsakanin Muhajirun da Ansar | |
| Haihuwa da mutuwa | |
| Mukhtar Saƙafi | |
| Abdullahi Bin Zubair | |
| Ziyad Bin Abihi | |
| Wafati/Shahada | |
| As'ad Bin Zurara | |
Shekara ta 1 bayan Hijira ita ce shekarar farko ta kalandar Hijira ta Musulunci. Wannan shekarar ta yi daidai da shekara ta 14 bayan aiko da Annabi Muhammad (S.A.W) da Manzanci,[1] kuma shekara ta 53 bayan Shekarar Giwa (Amul Fil).
A wannan shekara ne Annabi Muhammad (S.A.W) tare da wasu daga cikin Musulmi suka yi Hijira daga Makka zuwa Madina. Haka kuma, a wannan shekarar ne aka aza harsashin ginin Masallacin Ƙuba da kuma Masallacin Annabi.
Muhimman Abubuwa Da Suka Faru A Wannan Shekara
- 1 Rabi'ul Awwal: Shugabannin Ƙuraishawa sun shirya makircin kashe Annabi (S.A.W), kuma a wannan dare ne aka sami waƙi'ar Lailatul Mabit.[2]
- Hijirar Manzon Allah (S.A.W) daga Makka zuwa Madina.[3]
- Salmanul Farisi, sahabin Annabi (S.A.W), ya musulunta a watan Jumadal Ula.[4]
- Abdullah Bin Salam, ɗaya daga malaman Yahudawan Madina, ya musulunta.[5]
- 15 Rabi'ul Awwal: An aza harsashin Masallacin Ƙuba.[6]
- Annabi (S.A.W) ya jagoranci Sallar Juma'a ta farko, kuma ya gabatar da huɗubar Juma'a ta farko.[7]
- An gina Masallacin Annabi.[8]
- An gudanar da Sallar Jana'iza ta farko.[9]
- Annabi (S.A.W.) ya ƙulla ƴan uwantaka tsakanin Muhajirai da Ansar.[10]
- An ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da rashin kai hari tsakanin Manzon Allah (S.A.W) da Yahudawan Madina.[11]
- Annabi (S.A.W.) ya tsara Kundin Tsarin Mulkin Madina.[12]
- Annabi (S.A.W.) ya auri A'isha.[13]
- A watan Shawwal, an aika Sariyyar Ubaida Bin Haris domin fuskantar mushrikan da ake zargin za su kai hari a kewaye da Madina.[14] Sai dai Ibn Hisham ya bayyana cewa wannan sariyya ta faru ne a shekara ta 2 bayan Hijira.[15]
Waface-waface Da Haihuwa
- Rasuwar Walid Bin Mugira, ɗaya daga cikin manyan maƙiyan Musulunci da Manzon Allah (S.A.W) a Makka.[16]
- Rasuwar Asu Bin Wa'il Sahmi, ɗaya daga cikin mutane biyar da suka kasance suna yi wa Annabi Muhammad (S.A.W) ba'a da izgili.[17]
- Rasuwar Bara'a Bin Ma'arur, daga cikin Ansar kuma sahabin Manzon Allah (S.A.W.).[18]
- Rasuwar As'ad Bin Zurara, wanda ake wa laƙabi da As'ad al-Khair, daga cikin sahabbai kuma ɗaya daga cikin Musulman farko na Yasrib (Madina).[19]
- Haihuwar Mukhtar Saƙafi, daga cikin Tabi'ai, wanda daga baya ya jagoranci tawaye domin ɗaukar fansar jinin imam Husaini (A.S).[20]
- Haihuwar Abdullahi Bin Zubair, wanda ya yi iƙirarin halifanci bayan rasuwar Mu'awiya a Makka.[21]
- Haihuwar Ziyad Bin Abihi,wanda ya kasance Jami'an gwamnatin Imam Ali (A.S.) da ta Banu Umayya.[22]
Bayanin kula
- ↑ Ɗabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, juzu'i na 2, shafi na 392.
- ↑ Ɗusi, Al-Misbahul Mutahajjid, shafi na 791.
- ↑ Ɗabrisi, I'lamul Wara, shafuka na 146–148.
- ↑ Shirazi, Ad-Darajatul Rafi'a, shafi na 199.
- ↑ Mas'udi, At-Tanbihu Wal Ishraf, shafi na 201.
- ↑ Ɗabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, juzu'i na 2, shafi na 397.
- ↑ Ɗabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, juzu'i na 2, shafi na 394.
- ↑ Ibn Zabala, Akhbarul Madina, shafi na 74.
- ↑ Ibn Sa'ad, Attabaƙatul Kubra, juzu'i na 3, shafi na 465.
- ↑ Ibn Hisham, Asl-Siratun Nabawiyya, juzu'i na 1, shafi na 505.
- ↑ Ibn Is'haƙ, Siratu Rasulillah, juzu'i na 2, shafi na 561.
- ↑ Amili, As-Sahihu Min Siratin Nabi, juzu'i na 5, shafuka na 127 da 136.
- ↑ Ibn Abdul-Barr, Al-isti'ab, juzu'i na 4, shafi na 1881.
- ↑ Ɗabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, juzu'i na 2, shafi na 402.
- ↑ Ibn Hisham, As-Siratun Nabawiyya, juzu'i na 1, shafi na 591.
- ↑ Tabari, Tarikhut Tabari, juzu'i na 2, shafi na 398.
- ↑ Ɗabari, Tarikhɗ Ɗabari, juzu'i na 2, shafi na 398.
- ↑ Jafar Murtada, As-Sahihu Min Siratin Nabi, juzu'i na 33, shafi na 170.
- ↑ Ibn Sa'ad, Attabaƙatul Kubra, juzu'i na 3, shafi na 459.
- ↑ Ibn Asir, Usdul Ghaba, juzu'i na 4, shafi na 347.
- ↑ Ibn Hajar Asƙalani, Al-isaba, juzu'i na 4, shafi na 80.
- ↑ Ibn Abdul-Barr, Al-isti'ab, juzu'i na 2, shafi na 523.
Nassoshi
- Ibn Abdul-Barr, Yusuf Bin Abdullah, Al-isti'ab Fi Ma'arifat Al-Ashab, Beirut, Dar al-Jil, 1412H.
- Ibn Is'haƙ, Siratu Rasulillah, fassarar Rafi'ud--Din Is'haƙ Muhammad Bin Hamadani, bugun Asghar Mahadawi, Tehran, 1361Sh.
- Ibn Sa'ad, Muhammad Bin Sa'ad, Attabaƙatul Kubra, Beirut, Darul Kutubil Ilmiyya, 1410H.
- Ibn Zabala, Muhammad bn Hassan, Akhbarul Madina, Madina, Cibiyar Buhus Wa Dirasatul Madianatil Munawwara, 2003M.
- Ibn Asir, Ali Bin Muhammad, Usdul Ghaba Fi Ma'arifat As-Sahaba,' Beirut, Dar al-Fikr, 1409H.
- Ibn Hajar Asƙalani, Ahmad Bin Ali, Al-isaba Fi Tamyiz As-sahaba, bincike Adil Ahmad Abdul-Maujud da Ali Muhammad Mu'awwad, Beirut,Darul Kutubil Ilmiyya, 1415H.
- Mas'udi, Ali Bin Husain, A-Tanbihu Wal Ishraf, bincike Abdullah isma'il As-sawi, Alkahira, Dar As-sawi, ba tare da shekarar bugu ba.
- Sayyid Jafar Murtada Amili, As-Sahihu Min Siratin Nabiyil A-a'zam (S.A.W), Qum, 1385Sh.
- Sayyid Jafar Murtada Amili, As-Sahihu Min Siratin Nabiyil A-a'zam (S.A.W), Qum, Dar al-hadis, 1426H.
- Shirazi, Sayyid Ali Khan, Ad-Darajatul Rafi'a Fi Ɗabaƙatush Shi'a, Beirut, Cibiyar al-Wafa, 1983M.
- Ɗabari, Muhammad Bin Jarir, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, bincike Muhammad Abu al-Fadl Ibrahim, Beirut, Darul Turas, bugu na biyu, 1387H.
- Ɗusi, Muhammad Bin Hassan, Misbahul Mutahajjid, Beirut, Cibiyar Fiƙhush Shi'a, bugu na farko, 1411H / 1991M.
- Waƙidi, Muhammad Bin Umar, Al-Magazi, Beirut, Mawallafar al-A'lami, 1409H.
- Ibn Hisham, Abdul-Malik, As-Siratun Nabawiyya, Beirut, Dar al-Ma'arifa, ba tare da shekarar bugu ba.