Munajati
Munajati (Larabci: المناجاة)) mutum da Allah ko yin addu'a, kevancewar mutum da Allah, ya zo a cikin Alkur'ani mai girma ta fuskoki daban-daban, kamar "Najaitum", "Najwakum", "Nida'ul khafiyya". Akwai hadisai a litatafai na ruwaya da suka yi bayani kan muhimmancin addu'a, da ladubbanta, da sharuddanta, kamar khushu'in zuciya, da zaɓar kalmomin da suka dace da buƙatar bawa, da yin munajati a mafifitan lokuta, kamar lokacin sallar asuba. Shi munajati ya bambanta da addu'a wajan yadda ake magana da Allah.
Akwai manajatin da suke sanannu na wasu annabawa da Imamai ma'asumai (a.s), kamar misalin munajatina annabi Musa (a.s) a lokacin da yake dutsin ɗuri a lokacin da ya shafe darare arba'in, kuma akwai munajti na Annabi Dauda (a.s)a cikin zabura da kuma munajatin Sha'abaniyya da munajatul khamsati ashar.
Gabatarwa
Munajati shi ne mutum ya bayyana abin da yake cikin zuciyar shi a sirri, ta yadda ba bu wanda zai san da wannan abin da yake cikin zuciyar shi sai wanda ya aminta da shi.[1] Amma munajatin ga Allah shi ne yin addu'a da rokonshi a wani guri keɓaɓɓe ba tare da wani ya sani ba.[2] amma wasu malaman Luga suna ganin munajati shi ne faɗawa Allah buƙato tare da yaban shi, a wasu lokuta kuma ya haɗa da tuba daga zunubi.[3]
Nasir Makarim Shirazi a cikin tafsirul Amsal ya tafi kan cewa munajati kalma ce wacce aka cirota daga kalmar Najwa ita kuma tana nufin tudun ƙasa wanda ya yi sama dayawa kuma yasha banban da sauran saboda tudunta, to saboda haka ake anfani da kalmar kan duk abin da ɗan adam ya yi shi kaɗai a keɓe yayin da yake yin magaan da ubangijinsa a ɓoye.[4]
Amma bisa ra'ayin Fadlu ɗan Hasan ɗabarsi a cikin Majma'ul al-bayan ya tafi kan cewa munajati kalma ce da aka cirota daga Najwa wadda take nufin nisa, kamar yadda munajati yana nuna nesantuwar masu munajati daga waɗanda ba sa yin munajati.[5] Amma bisa ra'ayin wasu masu bincike kalmar Munajat tasha banban da kalmar Munada, saboda kalmar Munada ba'a yi anfani da ita ba sai ga wanda yake nesa, saboda haka ake kiran mutumin da yake nesa, kamar ace wane, amma ita kalmar munajati ta keɓanta ga kusa da abu, wato ana anfani da ita ga abin da yake kusa ba nesa ba,[6] to bisa wannan ne yasa ake kiran sallah da munajati,kamar yadda annabi tsira da aminci su tabbata a gareshi yace wanda yake sallah yana yi munajati da ubangijin shi ne.[7]
Kuma wataƙila ana yin anfani da kalmar munajati domin tashin mutane su yi Sahur a watan azumin ramadan, kuma a wasu lokuta munajati ya ƙunshi abubuwa irin su Tuba da kuma nisantar zunubi.[8]
Ita kanta kalmar munajati ba ta zo a cikin Alkur'ani mai girma ba, amma an yi ishara kanta a cikin wasu ayoyi kamar kalmomin Najawaku da “Najaitum a aya ta 12 da 13 a cikin Suratul Mujadala.[9] da kuma kalmar Nida'an Khafiyya a aya ta 3 a cikin suratul Maryam.[10] kuma an rubuta wasu babuka a litatafai na hadisi waɗanda ƙunshi sharuddan munajati da ladubbanshi da muhimmancinshi, sannan kuma sun tabo magana kan wasu daga cikin fitatton munajati.[11]
Banbanci Tsakanin Addu'a Da Munajati
Munajati yasha banban da addu'a kan halin bawa yayin da yake magana da ubangijinshi,saboda shi munajati ana yinshi ne a lokacin da bawa yake magana da ubangijinshi cikin kwanciyar hankali da magana ta masamman kamar yarda da kuskuranshi ko kuma nuna so ga Allah, a yayin da ita addu'a tana nufin kira ga Allah da kuma neman taimakonshi a bayyane.[12]
Ladubban Munajati
Haƙiƙa munajati yana da ladubba waɗanda aka anbata a litattafan hadisi daga cikin su ga wasu kamar haka;
- Zabar mafifitan lokuta, wato Sallar Asuba, kamar yadda wasu tafsirai suka yi nuni da su a wasu ayoyi a cikin Alkur'ani mai girma, kamar aya ta 142 a cikin Suratul A'araf [13] da aya ta 64 a cikin Suratul Furƙan,[14] da aya ta 16 a cikin suratul Sajdah.[15]
- Kiran Allah da sunayenshi da sifofinshi da suka dace da bukatu da buƙatar mutum, haka nan idan mutum yana buƙatar gafara daga Allah, sai ya kira shi da sifofi kamar Mai gafara, mai lulluɓe ko ɓoye zunubi, Mai bayarwa.[16]
- Yin amfani da kalmomin da Allah ya koyar da mutane ko kuma aka ambata a cikin munajatin Imamai, Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su).[17]
- Tawali'u na zuciya, kamar yadda Allah ya umurci Annabi Musa (A.S) da ya yi magana da shi da zuciya mai kaskantar da kai da tsoro.[18]
Tasirin Munajati
Kamar yadda ya zo a cikin wasu litattafan tafsiri da Ulumul Alkur'ani, akwai tasirin da munajati ke samarwa, wadanda suka hada da karbar tuba, gafarar zunubai, kariya daga azabar wuta,[19] samar da iklasi na gaskiya a cikin zuciyar mutum,[20] da tausayin zuciya, da tsarkin zuciya, da karfin ruhi.[21]
Shahararrun Munajati
Duk da cewa munajati ya zo a cikin litattafai na addini da na Irfani, amma wasu daga cikinsu sun shahara, kamar munajatin wasu daga cikin annabawa da imamai ma'asumai(a.s). Alkur'ani mai girma ya yi ishara da nuni ga wasu daga cikin munajati wanda aka rawaito daga bakin annabawa, waɗanda mafiyawancisu suka fara da kalmar Ubangijinmu waɗanda suka hada da:
- Munajatin Annabi Musa (a.s) a cikin dare arba'in a dutsen ɗuri.[22]
- Munajatin Annabi Yunus (a.s) a cikin kifi (Hut).[23]
- Munajatin Annabi Yusuf (a.s) a lokacin tsanani a rayuwar shi.[24]
- Munajatin Annabi Ibrahim (a.s)a lokacin da yafuskanci jarabawa daga Allah.[25]
Kamar yadda wasu malaman tafsiri suka ce littafin Zabura na Annabi Dawud ((A.S) ya kunshi nasihohi da addu'o'i da munajati, kuma babu wasu sabbin hukunce-hukunce a cikinsa.[26] wannan shi ne abin da ya banbanta littafin Zabura daga sauran littafan sama.[27] Haka nan akwai sanannun munajati fitattu daya daga harshen bayin Allah.[28]
Munajatin Imamai (A.S)
Ta yi wu akira wasu daga cikin addu'0'in imamai da sunan munajati, haka yasa wasu suka shahara, kamar manajatul Sha'abaniyya.[29] da munajatin Imamu Ali a masalacin kufa,[30] da munajatul khamsati ashar na Imamu Sajjad (a.s)[31]
Munajatun Ba'arin Arifai
haka nan ba'arin munajatin ariafi sun samu shahara , misalin munajatin khajo nasirid-dini ɗusi da munajatin hassan zade amoli.[32]
Bayanin kula
- ↑ «معنى المناجاة»، موقع العتبة الحسينية المقدسة؛ الحميري، شمس العلوم، 1420هـ، ج10، ص75.
- ↑ Al-Madani, Riyad Al-Salkin in Sharh Sahifa Sayyid Al-Sajideen, juzu'i na 7, shafi na 80
- ↑ Dehkhoda, Lughat-nama, zailu kaleme monajat.
- ↑ Makarim Al-Shirazi, Nasser, Al-Athmal fi Tafsiri kitabil munazzal, 1421H, juzu'i na 7, shafi na 276.
- ↑ Al-Tabarsi, Al-Fadl bin Al-Hasan, Majma’ al-Bayan fi Tafsir al-ƙur’an, 1372 AH, juzu’i na 5, shafi na 81.
- ↑ Muhammad bin Bahadur, Zarkashi, Al-Burhan fi Ulum Al-ƙur’an, 1410 AH, juzu’i na 2, shafi 431
- ↑ Allama Al-Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 68, shafi na 216.
- ↑ Anwari, Farhang Buzorg Sakhn, 1381 A.D., Dhayl Wajeh Monajat.
- ↑ Suratul Mujadila, aya ta 12-13.
- ↑ Suratul Maryam, aya ta 3.
- ↑ Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 660; Al-Majlisi, Mir'atul uƙol, 1404H, juzu'i na 12, shafi 562.
- ↑ Al-Tarihi, Majalisar Bahrain, 1416 AH, juzu'i na 1, shafi na 408-409; ƙurashi, Kamus na Kur’ani, 1412 AH, juzu’i na 2, shafi na 344-345; Al-Tabatabai, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 14, shafi na 7.
- ↑ Al-Tabatabai, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 8, shafi na 235; Hashemi Rafsanjani, Tafsir Rahnema, 1386 AH, juzu'i na 1, shafi na 137.
- ↑ Makarim Al-Shirazi, Nasser, Al-Athmal fi Tafsirin Kitabil munazzal, 1421 AH, juzu'i na 11, shafi na 304.
- ↑ Al-Tabarsi,Majma Al-Bayan 1372 AH, juzu'i na 8, shafi na 517
- ↑ Kira'ati, Tafsir Nour, 1388 AH, juzu'i na 8, shafi na 108.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Namuna, 1371 AH, juzu'i na 1, shafi na 2.
- ↑ Ibn Shu'bah Harrani, Tuhaf al-Uƙul, 1404 AH, shafi na 492.
- ↑ Hashemi Rafsanjani, Tafsir Rahnema, 1386 AH, juzu'i na 16, shafi 144.
- ↑ Imam Khumaini, Tafsirin Suratul Hamdi, 1375H, shafi na 146-147.
- ↑ Naƙi Pour Far, Pyzhoushi Peramun Tadabbur dar ƙuran, 1381 AH, shafi 506.
- ↑ Suratul A'araf, aya ta:142.
- ↑ Suratul Anbiya, aya ta 87.
- ↑ Suratul Yusuf, aya ta 33.
- ↑ Suratu Ibrahim, aya ta 34-41; Sharifipour, sharh Munajat Sayyidina Ibrahim (a.s) a cikin Alkur'ani mai girma, 1395H.
- ↑ Makarem Al-Shirazi wa digaran, Nafhat Al-ƙur’an, D.T. Darasi na 7, shafi na 378.
- ↑ Makarim Al-Shirazi, Nasser, Al-Athmal fi Tafsirin Littafin Allah da aka Saukar, 1421 AH, juzu'i na 9, shafi na 32.
- ↑ Al-Tabatabai, Al-Mizan, 1390 BC, juzu'i na 4, shafi na 88.
- ↑ Ibn Tawus, Iƙbal al-A’mal, 1409 BC, juzu’i na 2, shafi na 687.
- ↑ Kafami, Al-Balad Al-Amin, 1418 BC, shafi na 319.
- ↑ Majlisi, Bahar Al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 91, shafi na 142-153.
- ↑ Ansari, Manajat Nameh, 1382H.
Nassoshi
- Kira'ati, Mohsen, Tafsir Nour, Tehran, Farhangi Darshayi Az Quran Center, 1388 AH.
- Makarem Al-Shirazi, Nasser wa digaran, Nafhat Al-Qur’an, Beirut, Dar Sader, D.T.
- Al-Ansari, Khawaja Abdullah, Manajat Nameh, Gyara: Muhammad Hamasian, Kerman, Farhangi khadmat Kerman, 1382 AH.
- Al-Himyari, Nashwan bin Saeed, Shamsuddin ulumi wa dawa'u kalam al-arab min Al-Kulloum, Beirut, Darul Fikr Al-Mu’asir, 1420H.
- Al-Kafami, Ibrahim bin Ali, Baladul amin wa dar'ul alhasin, Beirut, Al-alami Publications Foundation, 1418H.
- Al-Kulayni, Muhammad bin Yaqoub, Al-Kafi, bincike: Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, 1407H.
- Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar Al-Anwar, Beirut, Larabawa Heritage Revival House, 1403H.
- Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Mir'atul uqool a Sharh Akhbar Al-Rasul, bincike: Hashim Rasouli Al-Mahallati, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, 1404H.
- Al-Tabarsi, Al-Fadl bn Al-Hasan, Majma’ al-Bayan fi Tafsir al-Qur’an, edited by: Tabatabai _ Rasouli, Tehran, Nasir Khusraw, 1372 AH.
- Al-Tabatabai, Muhammad Hussein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Dar Ihya al-Tarat al-Arabi, 1390 AH.
- Al-Turaihi, Majma'ul Fakhrul-Din, Al-Bahrain, Tehran, Al-Murtadawi Library, 1416H.
- Dehkhoda, Ali Akbar, Laghat Nameh, Tehran, Tehran University Publications, 1377 AH.
- Hashemi Rafsanjani, Ali Akbar, Tafsir Rahnama, Qom, Bustan Kitab, 1386H.
- Ibn Shu'bah al-Harrani, Hassan bin Ali, Tuhaf al-Uqul, edited by Ali Akbar Ghafari, Holy Qum, Qum Seminary Teachers Association, 1404 AH.
- Ibn Tawus, Ali bin Musa, Iqbal al-A’mal, Tehran, Darul Kutub al-Islamiyyah, 1409H.
- Imam Khumaini, Ruhollah, Tafsirul Suratil Hamdi, Tehran, Mu'assasa Tsara da Buga Ayyukan Imam Khumaini, 1375H.
- Makarem Al-Shirazi, Nasser, Al-Athmal fi Tafsirin kitabillahi al-munazzal, Qum Madaraseh Imam Ali bin Abi Talib (amincin Allah ya tabbata a gare shi), 1421H.
- Muhammad bin Bahadur, Zarkashi, Al-Burhan fi Ulum Al-Qur’an, edited by: Dhahabi _ Kurdi _ Maraashli, Beirut, Dar Al-Ma’rifa, 1410 AH.
- Naqi Pour Far, Valiullah, Peshushi Peramon Tadbeer der Qur’an, Tehran, Aswa, 1381 AH.
- Qurashi, Al-Sayyid Ali Akbar, Qamus Qur'an, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, 1412H.
- Ragheb Al-Isfahani, Al-Hussein bin Muhammad, Mufradat AlFaz Al-Qur'an, Lebanon - Syria, Dar Al-Ilm - Dar Al-Shamiya, 1412 AH.
- Sharifipour, Farzaneh, Sharh Munajat Ibrahim (a.s) a cikin Alkur'ani mai girma, Tehran, Majal, 1395H.
- «معنى المناجاة»، موقع العتبة الحسينية المقدسة.